Showing 54001 words to 57000 words out of 124968 words

Chapter 19 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5484

nake magana wadda mukaje saudia, wannanfa damace akaro Na biyu tazo mana, Na fahimci tun a saudia akwai wani Abu a ranka game da ita, amma sakaci irin naku da wautar k'uruciya yasaka yima lamarin rik'on talala Wanda lallai idan kayi wasa zaka ciji yatsa a daga baya. Zancen danake maka yanzu haka tun muna saudia naji Sarkin Musulmi yana waya da Mai d'akinsa akan sha'awar naimawa d'ansa auren Jiddar .
Da sauri Sheikh Aliyu ya kalli malam cikin waro fararen idanunsa.
 Ba ido zaka zarominba, kana sontane? Kokuwa hasashenane kawai nakeyi? .
K'asa Sheikh Aliyu ya maida kansa yana susar k'eya, fuskarsa d'auke da murmushi yace,  Inason na cika maka burinka natun farko Baba, sannan harga ALLAH yarinyar ta kwantamin arai .
 Alhamdllh Aliy, lallai nayi farin ciki, ALLAH yaymaka albarka. Tofa a wannan karon bazamuyi sanyaba, dan insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zanje musami mahaifinta da zancen, sonake ana gudanar da taronan da za'ayi washe gari a d'aura auranku ..
Acikin Zuciyaryarsa yace,  ALLAH dai ya tabbatar Baba .

&&&&

Tun a ranar malam baiyi sanyaba ya Kira Uncle Yahya sukayi maganar.
Wannan zance ba k'aramin farin ciki ya saka Uncle yahya ba, dan haka shima baiyi sanyaba ya doka waya zuwa Adamawa domin gayyato kawunansu guda uku suzo ayi dasu, dan baya son Abba ya sake basu Matsala a wannan karon. Sannan yakira Abba ya Sanar masa shima, da to kawai ya amsa saboda a time d'in suna tare da Hajia Hindu.

Washe Gari tunda asubahi su Kawu Safiyanu suka baro Adamawa kuwa, cikin amincin ALLAH saigasu sun iso da wuri, sun huta sannan sukaje suka gaida Umma da tayata murna, Albarka dai Jiddah dasu Zarah sunshata. Uncle Yahya dai bai fad'a Mata abinda ya kawosuba, dan yafison a kammala komai sannan.
Daga nan gidan ABBA suka d'unguma, dukkan Abinda za'a iya buk'ata Na tarbar bak'i saida Uncle yahya ya tanada daga gidansa suka tafi dashi, dan baya buk'atar abinda zai 6ata ransa a gidan Abba.
Abba yayi mamakin ganin su Kawu Surajo sosai, dan haka yayta bin Uncle yahya da kallon tuhuma, yayinda shikuma yay biris tamkar bai gansaba. Sunyi kusan zaman mintuna talatin kafin hajia Hindu ta shigo gaishesu tana wani yatsine-yatsine, babu Wanda yabi takanta, dan Uncle yahya ma ko kallo bata isheshiba.
Tunda ta fita take masifa wai Uncle yahya yakawo su Kawu Bliya maula, duk sunzo sun cika Mata gida da warin talauci.
Tun Uncle yahya da Abba na zuba idon ganin hajia Hindu ta kawo ruwa har suka fidda ransu, dan haka Uncle yahya yamik'e ya fita, mintuna kad'an yafara shigowa da kulolin abinci, dandanan ya cika tsakiyyar falon da kayan arzik'i, ko zama baiyiba daga ajiye Na k'arshe sukaji shigowar mota. Hakanne ya saka Abba had'iye tambayar dake ransa suka mik'e suka fita domin tarbo su malam.

Gaisuwa sukai cikin mutunta juna, kafin Kai tsaye malam da kansa yafara fad'in abinda ya kawosu, dan a ganinsa da zafi-zafi akan daki k'arfe.
Kafinma Abba ya tofa nashi tuni su Kawu Safiyanu sun bada Jiddah tareda addu'ar sanya alkairi.
Dad'i ya cika zuciyar malam, cikin fad'ad'a murmushinsa yace,  Muda mukazo Neman izinin Fara Neman so Kuma sai ace amma bamu? .
Kawu Surajo yay Y'ar dariyarsu ta manya,  Ai malam Kai ubane, kimarka tawuce kazo Neman izinin zance kawai ka tafi, dan kaima mai iya aurar da Hauwa'u ne ko bama a wajen, to balle kuma babban mutum irin Sheikh Aliyu yaga yarinyarmu yace yanaso harma a tsaya jan dogon zance, badan badan bama mu saimuce ama d'aura ka tafi da amaryar kawai .
Dariya suka sanya gaba d'aya suna musabaha, Malam yace,  Wlhy da hakan zata kasance danayi murna kuwa. Amm to indai hakane mizai hana indai bamuyi gaggawaba ranar juma'a ta sama kawai a d'aura .
 Malam indai hakan yamaka tomu bamuda ja wlhy, tunda dai yarinyarnan ta ta6a aure, banga wani abun jan jikiba ma . Uncle yahya ne Mai maganar .
Atake kowa yayi na'am da wannan magana, ganin haka shima Abba saiyabi ayarin masu amsawa cikin yak'en dariya. Take annan malam ya ajiye sadaki naira dubu d'ari biyu, amma sai su Kawu Bilya suka nemi a rage.
Malam yace,  Lah-lah bazamu rage ko sisiba, k'arawama yakamata muyi, wato abinda muka kasa fahimta da 6al6alcewar aurarrakinmu na wannan zamanin da sakaci Na yawan sakin aure to k'arancin Sadaki yana ciki, inda za'a ajiye dukkan bidi'oi dake gudana yanzu a shagalin bukukuwa aringa tsawwala sadaki ga masu aure to lallai sai ansamu sauk'i sake-saken aure. Yaro ya biya dubu hamsin ko talatin sadaki, da anyi aure taimasa ba dai-daiba saiya sauta, idan anyi magana yace ga matanan ledar ruwa tafisu wahala, to yasan daya samo y'ar dubunsa d'ari biyu ta Isa masa wani auren, inda ace ana saka musu sadakin Mai tsauri mahaifin yarinya yace baya buk'atar kowacce bidi'a amma sadakin y'arsa dubu d'ari biyu ko uku ko hud'u to wlhy saisunji shakkar sakin, dan sunsan kafin su tara wani sadakin sun jigata, sannan za'a canja tunaninsu ga wanann shaid'ancin Na fati-fati dasukeyi, kunga mutum da kud'in sadaki zaiji kokuwa da kud'in bidi'ar aure?. To ni yarinyata jiddah ma ta girmi sadaki dubu d'ari biyu wlhy, kaf yarana ban yarda abani k'arancin sadaki a kansuba, bankuma yarda mazan sukai mafi k'aranci ba suma, sannan bana biyama yaro sadakinsa, zandai taimakeka da wani abun, amma kud'in sadaki ka nemo kayanka. Wannanma Aliyun da kansa ya bada abinsa .
Kai su Kawu duk suka shiga jinjinawa cikeda gamsuwa da maganar malam d'ari bisa d'ari, dajin a ransu suma zasuyi aiki da wannan shawara Mai k'yau da nagarta gamai hankali.
Fita sukayi sukabar su malam suci abinci, Wanda saida uncle yahya yayta rok'onsu sannan suka amince.


('('('('('('('('('('('

Bayan tafiyarsu Malam su Kawu Surajo tasa Abba gaba sukayi zuwa gidan Umma, lokaci Zarah da Jiddah basannan sunje gidan Aunty Nafisa, walida da Umma ne kawai a gidan.
Mamaki sosai Umma tayi, ita tunaninta ma ko dama Abba ne yakai k'ararta itada Uncle yahya wajen su Kawu Safiyanu akan barin Jiddah taje Saudia. Amma da suka zauna sai taji jawabin nasu bai doshi canba, tuni farinciki ya lullu6eta, dan ita wlhy d'ari bisa d'ari ta amince da wannan zance, saidai tabisu da addu'ar ALLAH ya sanya alkairi kawai.
Abba dai tunda aka zauna baice Uffanba, hakan kuma bai damu Umma ba, Ana cikin maganarma saiga su Jiddah sun dawo. Da hanzari tayi niyyar komawa cikin rawar jiki, Uncle yahya yace,  Daure ki shigo kinji Jidodona, k'arfafa zuciyarki kinji Y'ar albarka duk iyayenkine .
Jikinta na tsuma Zarah ta kamo hannunta suka ida shigowa, tuni harta had'a zufa, muryarta na rawa ta gaishesu.
Kawu Surajo yace,  ALLAH ya yaye miki kinji Hauwa'u, ALLAH ya warware wannan k'ulli cikin hikimarsa da rahamarsa, Yakuma gaggauta saka miki .
Da amin duk suka amsa, sai dai banda Abba dayay shiru yana saurarensu dajin haushin su Kawu surajo, kenan suma sun amince da k'aryar ciwon Jiddah Na shirme?, babu Mai bashi amsa dan da zuciyarsa yakeyi.
Kawu Bilya ne yaymata bayani akan abinda ya faru, sosai mamaki ya kamata, wannan babban malamin da duniyar musulinci ke alfaharine zaice yana sonta da aure? Halan kallon tsoro yaymata? Ina ita ina shi?.
 Kinyi shiru Hauwa'u, ko bak'ya sonsane? Kinsanfa yanzu ke bazawarace, kinada damar za6en miji da kanki, wannanma munyi miki katsalandan ne saboda ganin nagartarsa, kuma tunkan aurenki Na farko yanemi aurenki ALLAH ne kawai ya k'addara saikin aurin wancan da kika fito, ammafa idan baimikiba lokaci bai k'ureba, ki fad'a mana tunda ba d'aurawa akayiba .
Idon Jiddah Na kwarar da hawayen da batasan daliliba tace,  Kawu duk yanda kukayi wlhy ni Mai biyayyace a gareku, zankuma kar6i dukkan abinda kukazomin dashi hannu biyu, dan nasan bazaku cutaminba .
Ajiyar zuciya duk suka sauke, kowa yashiga saka Mata albarka sannan aka sallamesu. Dad'i tamkar zai kar Zarah da Walida, tunda suka shiga d'aki sai kwasar rawa suke, harda rairama Jiddah wak'ar amaryar ya sheikh.
Itadai shiru tai musu, saima kanta data kife a filo tana cigaba da hawaye marasa dalili.

Tuni zancen auren Jiddah yagama karad'e dangi, kowa yaji saiya tayata murna da wannan canjin alkairi.


('('('('('('('('('('('

Su malam suna dawowa yakira Aliyu ya shaida masa yanda akayi, dad'i sosai yaji a ransa, Wanda har kamilallaiyar fuskarsa saida ta nuna, ayayyanawa yake aransa nanda kwanaki sha uku zai zama ango a Karo Na biyu kenan, wannan hikimace ta ubangiji kawai, dan baima ta6a hasashen aurenba a kusa balle Mata biyu a lokacin da bashida tazarar nisa.
Sosai malam yaymasa nasiha akan adalcin had'a Mata biyu da shawarwari, dukda yasan shimad'in yasani.
Sheikh Aliyu yay godiya da kar6ar nasihar malam hannu biyu. Shi duk saima yaji shakkar tunkarar Maimunatu da batun, gashi dama batada lafiya a y'an tsakaninnan, kuma yana k'yautata zaton cikine da ita, dan dukkan alamun mace Mai yaron ciki sun bayyana a gareta, shiyyasama datak'i yarda yakaita asibiti bai matsa mataba yadai samo Mata magungunan da bazasu cutar da itaba.

Haka ya d'auki hanyar gida sukuku bayan yashiga ya gaida su hajia bah-bah ya fito.
Tun a yanayin tsaftar gidan yaji aransa mai gidan babu lafiya, dan Maimunatu akwai tsafta, ko yaushe gidan k'al yake cikin k'ok'arinta na gyarawa.
Bedroom yanufa bayan ya lek'a kicin yaga babu kowa a ciki.
Kwance ya iske Maimuna a kan gado k'udundune a bargo.
 Subahanallah ya fad'a yana zama kusada kanta, kafin ya janye bargon yakai hannunsa saman goshinta da wuyanta,  Ya salam yakuma ambata saboda jin jikinta zafi rau.
Da k'yar ta bud'e idanunta da sukai jaa ta kallesa tareda sakar masa murmushin k'arfin hali,  Yaya sannu da dawowa .
 Yauwa Maimoon, zazza6inne ya dawo? .
Hannunta ta d'ara saman nashi dake kan goshinta, tad'an yatsina fusaka alamun rashin jin dad'i,  Yaya shine ya dawo, amma karka damu nafasha magani .
 Ai tama shan magani tak'are, tashi muje asibitin can, tunda Na kud'ine nasan za'a iya samun likita, kuma banason musu .
Bata iya cewa komaiba ya taimaka Mata ta sakko, da kansa ya canja Mata kaya zuwa doguwar Riga ya saka Mata hijjab sannan ya kamota suka fito.
Cikin amincin ALLAH kuwa sai suka samu likita, dukda kuwa k'aramin asibitine.
Sosai doctor yay Mata tambayoyi kafin yasaka wata nurse tazo ta d'iba jininta.
Karin ruwa suka saka Mata saboda jikinta babu k'arfi sosai, malam Na zaune a kusa da ita hannunsu sark'e da Na juna ake Mata k'arin ruwan, kirane ya shigo wayarsa, dan haka yay k'ok'arin janye hannunsa dan ya amsa, amma sai ta sake damk'ewa, kallon hannun nasu yayi yana murmushi, saiya d'aga wayar da d'auyan hannun saboda Aunty Ruk'ayya ce.
Bayan sun gaisa ta tayasa murna akan k'arin NASA, Wanda malam yakirata ya sanar Mata.
Da amin ya amsa saboda addu'ar fatan zaman lafiya da take musu, kafin daga bisani ya sanar mata sunama asibiti Maimunatu babu lafiya, amma bai sanarma kowaba.
 Subahanallahi, muke damunta Aliyu? .
 To gadaimunan ana mata k'arin ruwa, sunkuma d'iba jininta zasu gwada .
 to yanzu ya jikin Nata? .
 A alhamdllh, barci takeyima .
 Ganinan zuwa yanzu insha ALLAH, yimin kwatancen asibitin .
Kwatance yay Mata kafin su katse kiran.


('('('('('('('('('('('

Alhaji garba da Abba ne ke gaisuwa a kasuwa, Wanda rabon da hakan ta faru tun bayan rabuwar aurensu da Jiddah, hasalima had'uwa tamusu wahala gaba d'aya, dan Alhaji Garba dainabin hanyarma dazaiga Abba yakeyi, shima Abban hakanne a garesa.
Yaukuma abin mamaki saiga Alhaji Garba har shagon Abba. Bayan sun gaisa Abba yasaka yaronsa Jabiru ya kar6oma Alhaji garba fura Mai sanyi.
Alhaji garba nashan fura suna hira har suka gangaro kan zancen Jiddah Wanda shine mak'asudin zuwan Alhaji garba.
 Wai nikam abokina da gaske Jiddah matata nagani a taronnan da akayi Na saudia? .
Cikin danne takaici Abba yace,  Eh itace wlhy Alhaji, ashe kaima ka gani? .
 Nagani dagani har iyalaina, harma mukaita gardama akan itace koba ita baceba .
 Aikuwa dai itace .
Alhaji garba ya washe hak'ora yana kur6ar fura,  Humm nikuwa abokina wlhy ganin yarinyarnan da abin arzik'in da tayi a k'asa mai tsarki ba k'aramin sake sha'awar komawarta a gareni nayiba, kasan kowa yanason yasama ma y'ay'ansa uwa tagari, inda hakan zata kasance kabani koman yarinyarnan da nikuwa wlhy Na barmaka dukkan kud'ad'ennan danake binka .
Abba ya washe baki yana fad'in  Alhaji da gaske kake wannan maganar? .
 Wlhy da gaske nake alhaji zakari, kuma a wannan Karon namaka alk'awarin bazan had'a Jiddah da Hajia deluwa ba, sakinma danai Mata sharrin shaid'anne, amma tun bayan barinta gidana da ita nake kwana a raina nake tashi .
Abba da k'asan zuciyarsa ke tunanin auren Jiddah da sukabama su malam Abdul-ra'uff yad'an sauke ajiyar azuciya a fili kafin yace,  To dukda ga magar wani auren nata ya shigo, dama kamin maganane da wuri? To amma wlhy tunda har kace ka yafemin kud'innan insha ALLAH zanyi iya k'ok'arina naga Na rusa wancan, dama k'arfina akafi, kawunnaina ne suka kar6i auren bisaga jagorancin munafincin k'anina yahya, to amma kabarni dasu, ai dai d'iyar tawace ko? To ka saka a ranka kasamu .
 A to lallai zankoyi farinciki, ammafa kasake bska dawomin da itaba to nanda kwana kad'an ka tanadarmin kud'ina gaskiya .
 Haba alhaji, ai insha ALLAHU bama za'ayi hakaba, indai nine Na haifi Jiddah to ka d'aukama ta sake zama matarka ta gama, sunsa aurenta sati biyu, Toni Zan saka sati d'aya kaida ita .
Baki Alhaji garba yashiga washewa yana k'ara gidiya da fatan sake tabbatar wannan lamari, a wannan Karon kuma yayi alk'awarin ba wariba da hauka komi Jiddah zatayi babu sanya Randa taje zai mallaki kayarsa...........
'


*_=?1?=?F? @&._*










*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [12/8/2019, 7:11 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[27?'28]_*


..............Babu dad'ewa Aunty Ruk'ayya ta iso asibitin, bisa kwatancen da Aliyu yay Mata ta iso d'akin.
Har yanzu yana zaune kusada Maimuna dake barci, hannunsu Na sark'e dana juna har yanzun, shigowar aunty Ruk'ayya da sallama ya sakashi zame hannunsa a hankaki dukdama tarigada ta gansu.
Hannu ya mik'a ya kamo hannun yaronta Najib fuskarsa d'auke da murmushi.  Najibullah kaine ka k'ara girma haka? .
Najib dako magana bai gama iyawaba ya lafe a jikinsa, yayinda Aunty Ruk'ayya ta zauna saman kujera tana dariyar maganarsa.
Yaranta Sadiya da Naja'atu suka shigo da sallama hannunsu d'auke da ledoji.
 A'a Aunty kice harda y'ammatana kike tafe? .
Sadiya da Naja'atu suka durkusa suna gaishesshi da tambayar ya Mai jiki?, fuskarsu washe da murmushi, shima cikin sakin fuska ya amsa yana tambayarsu makaranta.
Suka had'a baki wajen fad'in Alhmdllh Kawu.
 Naga gida gaba d'aya amma banga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login