Showing 63001 words to 66000 words out of 124968 words

Chapter 22 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5481

 Wa'iyazubillahi aunty Hassana, mak'iyinama bazan dangantashi da wutaba balle ku .
Basu tanka mataba suka fice, duk kiransu datake ta biyosu har gate basu sauraretaba.
Kuka tayi sosai akan hakan, a ganinta bai cancanci manya dasu su kawo mata rabuwar hankaliba.
Koda Aliyu ya dawo bata fad'a masaba, shima bai tambayeta ba dukda yakula ranta a 6ace yake, yanayinta kuma ya nuna masa tayi kuka. Kulawa yayta bata yanda hankalinta zai sake kwanciya da sake rarrashinta, dan tunda yaymata zancen aurennan duk sai ta susuce, dukda dai tana dannewa a gabansa.
Hakan saiya k'ara dasa masa k'aunarta da tausayinta, koba komai ya yarda da son da take masa mai nagartane, kamar yanda shima ayanzu yakejin sonta tun bayan aurensu, sokuma Na gaskiya mai gauraye da zallar k'auna.


('('('('('('('('('('('

A 6angaren Jiddah ma ranar kwana tai da tunanin Aliyu, hardasu mafarki.
Komai nasa yamata yanda take addu'a da fatan mijinta ya kasance, fatanta ALLAH yasa matarsa ba irin hajia Deluwa baceba.

('('('('('('('('('('('


*_RANA BATA K'ARYA_*

Yau take juma'atu babbar Rana, duk tarone Na maza kawai hakan bai hana su Maman Sadiq yin abinci ba dai-dai misali saboda y'an Adamawa maza su kusan goma da y'an barno biyar da sukazo d'aurin auren, a Mata kam gajiram da yaruwaiya ne kawai sukazo (Yayar Umma, da k'anwarsu wadda Balu ke bimawa).
Abba zakari dai baisan hidimar da akeba, amma har gida Uncle yahya yaje yacemasa yashiryo suje d'aurin auren wani yaron malam Abdul-ra'uff, da farko cayay akwai inda zaije, amma Hajia Hindu ta saka baki harya amince.
A babban masallacin juma'ar dake anguwar gwammaja sukaje sallah, mamaki ya Kama Abba ganin Kawunansa, Kawu Surajo da bashida 6oye-6oye yafito yasanarma Abba auren Jiddah za'a d'aura yau d'innan, kafin Abba yasamu zarafin magana tawagar malam Abdul-ra'uff data ango suka Iso.
Su Kawu Surajo basubi takansaba suka shiga hidimar tarbarsu, babu yanda ya iya dole yabi ayari dan karyaji kunya, dan manyan malaman sun cika masa idanu, amma daka gansa kasan a birkice yake gaba d'aya, kuma hankainsa baya jikinsa.
Ana idar da sallar juma'a wadda su malam sukayi anan suma aka d'aura Auren *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina da Jiddah Zakari Yaro* akan sadaki dubu d'ari biyu ciff>?)?>?s?..............
'




*_Munga idi, ya za'ayi da Abba zakari da Alhaji Garba kenan=?F??-??._*

*_?&
@&>???kayana a shirye suke nayin hijira walla, kad'an daga aikin Abba ya lallasa gayu>?#?>?#?=??_*


https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

*zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in na sama sisters, Abban dausayi YouTube channel tv=??>??

*_Ubangiji yabama d'an uwan momin khairi malam Adamu lafiya, bisaga had'arin mota da yayi, muna barar addu'arku. Dama dukkan y'an uwa musulmi dake kwance sanadin ciyo=???=?O?






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? [12/12/2019, 12:13 AM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[31?'32]_*


............Can na hango muku ango Sheikh Aliy shar cikin d'anyar shadda gizna ruwan toka mai haske, sai zabga k'amshi yake yana gaisuwa da jama'a da suketa masa ALLAH ya sanya alkairi, yau d'imma dai baka isa shaida yanayinsa ba tamkar lo???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kacin aurensa da maimuna.
Yazo ya gaida su Abba da gaba d'aya jinsa ya barsa, sama-sama yakejin hayaniyar mutane, koda Aliyu na gaisheshi saida Kalla ya zunguresa sannan ya amsa cikin alamun baya a hayyacinsa.
Shidai Aliyu ya gaidashi cikin mutuntawa tareda masa godiya ya mik'e
Aliyu Na barin wajen Abba ya fisgi hannun Uncle yahya sukai baya inda babu jama'a.
 Yaya wai miya farune kaketa jana? ina zaka kainine? .
Banza Abba yay masa bai tankaba, kuma bai Saki hannunsaba. Sai da suka Isa can bayan k'aramin d'akin da Gen......take Na masallacin, Sannan ya sakeshi tare hankad'a Uncle yahya jikin bango ya shak'eshi. Da farko Uncle yahya ya tsayane yaga iya gudun ruwan Abba, amma ganinfa da gaske yake saiya shiga k'ok'arin rik'e hannunsa domin kare kansa, amma Sam Abba yak'i sakinsa, sai kuma k'ok'arin shak'arsama yakeyi, tuni kiciniya ta 6arke a tsakaninsu.
Kawu Surajo dayaga fisgar da Abba yayma Uncle yahya ne yaji zuciyarsa takasa nutsuwa, dan haka yabiyo bayansu...
 Subahanallahi, Zakariyya! Kanada hankali kuwa? 'Dan uwan naka zaka kashe? Miyaymaka? .  Kawu Surajo yay maganar yana kiciniyar kwace Uncle yahya daga hannun Abba .
Uncle yahya ya k'yale Abbane kawai amma badan yafi k'arfinsaba, Abba dai bai Saki Uncle yahya ba saida Kawu Surajo ya maresa, saurin sakin Uncle yahya yay yana kalon Kawu Surajo dake huci (dan shima akwai zuciya dam) hannunsa dafe da kuncinsa yace,
 Kawu shine zaka mareni? .
 An mareka d'in kozaka Rama? Waishin Zakariyya mikakeson zama kaikam a rayuwarka? A ina ka gado wannan halinne? Wlhy mahaifinka bashida wannan bak'ar halayyar taka, hakama Mahaifiyarku, girma kake kullum amma halin yara da rashin sanin yakamata yakasa barinka, kanason gamawa da duniya lafiya kuwa? .
Cikin harzuk'owa Abba yace,  Yaza'a dakeni sannan a hanani kuka? Yazaku zauna Ku k'ulla munafuncin aurarmin da yarinya sannan ace bazanyi maganaba?, Jiddah dai nina haifi abata bawani ya haifarminba, wlhy yahya kayi maza ka saka ya sakarmin yarinya, bashi nai niyar bawaba kuma bazan bashiba, inko ba hakaba wlhy saina maka rashin mutuncin dabaka ta6a tunaniba .
Kawu Surajo zaiyi magana Uncle yahya ya dakatar dashi ta hanyar fad'in kaga  Kawu barshi, nima Zan bashi amsa dai-dai dashi, domin Yaya bai cancsnci kowacce irin girmamawa ba agareni yanzun. Yaya a wannan Karon bazan maka shiruba kamar yanda Na Saba, kaimin dukkan abinda zuciyarka ta fad'a maka dai-dai, sai dai kuma kasani Wannan auren yayi k'ulluwar da insha ALLAHU mutuwace kawai zata rabashi, duk kuma abinda kaga zakamin ga fili gamai doki nan, ko kunyar ALLAH bakaji ka saida yarinya akan kud'i kadawo kana hura hancin y'arkace, dan wannan wlhy saidawane, tunda batasan kaje kaci bashinkaba, k'ilama ko sisi bataci a cikiba.....
Duka Abba yakaima Uncle yahya amma sai Kawu surajo ya janye Uncle yahyan yana fad'in  Kaga yahya barsa muje kawai, wannanma kad'ai ta isheshi, yaje ya nemawa masu kud'i kud'insu .
K'iri-k'iri Abba yashiga mulmulo ashariya yana nakama Uncle yahya da tabbatar masa saiyayi dana sani, kuma aurene saiya rabashi.
Badan wajen babu kowaba kam dasun tara y'an kallo bana wasaba.


('('('('('('('('('('('

A gida kam Jiddah duk sai tayi wani sukuku, duk tsokanar dasu Aunty Nafisa kemata bata kulaba, dayake ba taro za'ayiba batayi wani kwalliyaba, tadaiyi wanka ta saka sabon d'inkinta. Zaune take a d'akinsu ta zuba tagumi tana tunanin rayuwa, wai itace aka d'aurama Aure sau biyu cikin shekara d'aya, rayuwa kenan, mai tafiya da jarabawa.
Dukda ba taro za'ayiba gidan nasu yad'an cika da makwafta, koda y'an d'aurin aurema suka dawo sai akaita bud'e-bud'e, wad'andama basu shigoma suka shishshigo sunama Umma ALLAH ya sanya alkairi.


&&&&

Bayan su Uncle yahya sungama cin abinci suka shiga tattauna batun Abba da yanda zasu 6ullo masa.
Ana cikin wannan magana saiga y'an sanda sunzo tafiya da Uncle yahya Abba yakai k'ararsa akan ya aurar masa da yarinya batare da saninshiba.
Wannan lamari kam ya girgiza kawunnansu sosai, batareda an Bari su Umma dake cikin gida sun saniba Uncle yahya dasu Kawu Bilya sukabi y'an sanda station.
Acan ma suka iske Abba a Office d'in d.p.o .
Jin da d.p.o yayi zancene Na family saiyay nufin sulhuntasu a office d'insa, amma sai Abba yace Sam bai aminceba, shidai kawai akira sheikh Aliyu yanzunnan ya sakar masa y'arsa.
Su Kawu Surajo kuma sukace bai isaba yayi kad'an. Nanfa rikici ya hark'ume sosai, babu Wanda Abba yake hara sai Uncle yahya, yayinda kuma yake datsama Su Kawu dukkan maganar datazo a bakinsa, har dare suna station ana abu d'aya, su kamsu police d'in yau dukkan aikinsu ya tsaya rikicin su Abba ya d'auke hankalin kowa.
Shi d.p.o jin Mijin da yarinyar ta aura yasakashi k'in goyama Abba baya, dan aganinsa babu wani mutumin kirki dazaice baya buk'atar had'a jini da Malam Abdul-ra'uff maina a k'asarnan, musamman ma ace d'ansa Sheikh Aliyu ne Mijin. Shiyyasama yak'i amincewa akira sheikh Aliyun, dan aganinsa zubar da kimane ga Abban.
Dadai d.p.o yaga kansa na Neman d'aukar zafi sai kawai yayma yaronsa inkiya da ya nemo masa maganin barci a lemo ko ruwa, babu dad'ewa kuwa yakawo lemo. Abba kawai akaba, ganin hakan yasaka Abba kuma yin fad'i irin shi an girmamasa, dandanan yafara zuk'ar lemo yana kumfar baki, ba a wani ja dogon lokaciba ya kife a tebirin ya hau barci.
A wajen babu Wanda bai sauke ajiyar zuciyaba, kafin su Uncle yahya sushiga yima d.p.o godiya.
 Ai babu godiya a tsakaninmu, domin wannan yima Kaine, Na fahimci Alhaji baya tare da hankalinsa yanzu, wane ubane mai mutunci ALLAH zai masa wannan ni'imar ya bijire?. Shekaranjiya muka gama makamancin irin Case d'innan naku, shima Uban bayason yara mata, ya watsar dasu uwarsu Nata wahala dasu, sai yanzu cikin y'ay'an wata ta auri mai arzik'i shine yadawo zaima uwar fin k'arfi, itako tace Sam bai isaba, rikici dai ya kawosu har nan. Wato shawarar dazan Baku shine kusami likitan dazaita dank'ara masa allurar barci daganan harta tare gidan mijinta, dan baima kamata kubari gidan malam suji wannan shirmen nasaba wlhy, kodan Ku nemama y'arku mutunci, lokacin dazai dawo hayyacinsa rikicinsa da wancan Alhajinma ya isa ya d'auke hankalinsa .
'Dari bisa d'ari sun gamsu da shawarar d.p.o, dan haka sukaita zubamasa godiya da fatan gamawa da duniya lafiya, kafin y'an sanda suyi kama-kamar Abba sukaishi mota.

Har gida su Uncle yahya suka kai Abba, Hajia Hindu zatai musu hauka suka taka Mata birki akan baida lafiyane, likita zaizo ya ringa dubashi.>?#?


&&&&..

Su Uncle yahya basu fad'ama kowa halin da ake cikiba har Umma, dan basason 6ata musu farimcikinsu.
Washe garima su Kawu Surajo suka juya bayan sunma Jiddah Nasiha mai ratsa jiki, akan ta Zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamanta, dan a wannan auren sunA k'yautata Mata zaton alkairi da samun kwanciyar hankali mai d'orewa har abadan insha ALLAH. Tadai sha kuka sosai.
Su Yaruwaiya dai nan aka barsu, dansufa da shirin gyaran y'arsu Jiddah sukazo, dan haka tun a washe garin d'aurin aure suka fara gyara Jiddodon Uncle lungu da sak'o, dansu duk zatonsu jiddar tarasa budircinta a aurenta Na farko, itakuma dayake ba yawan surutune da itaba takasa fad'ima kowa babu abinda yashiga tsakaninta da Alhaji Garba, sai dai a gefe kuma Umma datasan halayen yaranta kaf tuni ta fahimci Jiddarta har hanzu budurwace.
Umma na mamakin rashin zuwan Abba gidan, harma takasa hak'uri ta tambayi Uncle yahya, shine yace Mata bashida lafiya. Tsakanin Mata da miji sai ALLAH, duk sai ta damu kanta kuwa, harma ta matsa akan zata dubashi Amma Uncle yahya ya bata shawarar tayi zamanta, daga baya kuma saiyaga yadace suje d'in kodan kauda hankalin mutane..
Gaba d'ayansu gidan da iyalin Uncle yahya suka rankaya duba Abba, dukda ma sun iske yana barci, hajia Hindu sai cika take tana batsewa. Babu Wanda yabi takanta a cikinsu in banda Balu da taita yanka Mata habaici ita da Gajiram, sai da Umma ta tsawatar musu da harshen kanuri, duk dariyar dakecin Zarah da walida basuyiba, dan wannan ba tarbiyarsu bace saka Kansu a hurumin manya, tun suna k'anana Umma bata ta6a basu damar cin zarafin hajia Hindu ba ko Mata rashin kunya, koda kuskure kayi hakan kuwa ranar zakaci uwaka wajen Umma.
Tsakanin su Umma dasu kalifa kuwa babu ko gaisuwa, hasalima d'auke Kansu sukai suna cigaba da kallon ball d'insu da hayaniya da uhu kamar basu ga su Umma ba. (Sun manta Ubansu Na kwance=?F? Suma su Jiddah babu Wanda yashiga harkar yaran.
Garama Umma tamusu magana suka wani basar da ita, kuma sarai sunsan matsayinta a gunsu, Itama daganan saitayi shiru. Kuma hajia Hindu naji da kallonsu amma bata tsawatar musu ba.
Basu wani dad'eba suka taho, kuma ko a Hanya Umma Hana kowa maganarsu tayi balle asamu Na saka zuciya 6acin rai.

('('('('('('('('('('('

Maimunatu dai ta kuma kwantar da hankalinta a gaban jama'a da mijinta, amma inhar tana ita kad'ai takansha kukanta ta k'oshi, kullum kuma addu'arta shine ALLAH ya k'ara Mata dangana da juriya, yakuma basu zaman lafiya da amarya.
Ko'a ranar d'aurin auren da kanta ta shirya Aliyu, shikam yanata saka Mata albarka da kuma nuna Mata tsantsar k'aunar da yake mata. Amma yana fita saboda kiranda Malam mustafa kemasa a waya saita rushe da kuka, shikenan yau mijinta yazama nasu su biyu, komansa yanzu saita raba da wata.
A wannan halin Aunty Ruk'ayya da Aunty Siyama sukazo suka isketa, zama sukai suna lallashinta da Mata nasiha mai ratsa jiki, hakanne yasaka Mata jin sanyi a ranta, koba komai y'an uwan mijinta suna k'aunarta.
Su Hassana da sukazo sai sukai turus ganinsu Aunty Ruk'ayya a gidan, hakanne yasaka suka Kama Kansu.
Suna a gidan harsu Aliyu suka koma daga d'aurin aure, nanfa suka shiga masa addu'ar ALLAH ya sanya alkairi da fatan zaman lafiya.
Dukkan wani zumud'i ya danne a binsa a zuciya yanda ran matarsa bazai sosuba, daga k'arshema yaja abarsa suka shige d'akinsa ya hau lallashi, dan yakula tasha kuka, idonta kawai sun Isa shaida. Hakan dayay Mata saiya sake bata nutsuwa harta d'an Saki jikinta ma.
Har dare su aunty Siyama Na gidan, harma da sauran y'an uwansu da Matan yayyensu da sukaita zuwa daga baya. Wasa-wasa dai sai sukasha wani d'an k'aramin shagali a cikin gidan, Wanda kowa yake bama Maimunatu kulawa da nasiha tareda fatan zaman lafiya, bakuma su munana amarya ko k'intaba ko sau d'aya a gabanta, kowa dai Na fad'a Mata ta rik'e girmanta shine mutuncinta ga miji ga abokiyar zamanta harma dasu danginsa.
Aliyu kam tuni yabar musu gidan dayaga sunfara cika, bai dawoba sai dare.
Akuma lokacinne yakejin yakamata koda a wayane yaji muryar Jiddah, dan yanzu dai hak'k'inta yarigada ya rataya a wuyansa dukda bata tareba.
Amma kokad'an baibari wannan tunani yayi tasiri a ransaba dahar zai hanashi bama matarsa kulawa, koma a fuska bai nuna Mata yana tunanin Jiddah bane, saima ita dataketa yawan sakko sunan Jiddah a hirarta, harma ta tambayi number ta.
Kwanciyarsa ya gyara yana kallonta,  Maimoon k'anwar nan takifa banyi zaton tana rik'ema wayaba gaskiya .
 Haba dai Yaya miyasa? .
 Ban saniba nima, sai dai inaga daga gidansune suka hanata, kinsan wayoyinne yanzu sunada tasu illar suma, shiyyasa wasu iyayen kan Hana yaransu rik'ewa har sai sunyi aure .
 Hakane kuma, nikam banga laifinsu ba, dukda hakan ba shine zai tsare maka yaroba, amma to yanzu dai yakamata a barta ta rik'e .
 Insha ALLAHU zanyi k'ok'ari a saya Mata koda k'aramace kafin abubuwa su warware, dan a tsakaninan banida wani isashshen kud'i Maimoon, inaga aikinnan da aka bani nak'i Zan koma Na kar6a, dama ganinai nauyin zaimin yawa, kuma dai-dai gwargwado dai sana'ar magungunan nan tana rik'emu, ga wadda Adeel ke mana a saudia, to amma yanzu nauyi ya k'aru, inaga sai nahad'a da aikinnan kodan nasamu damar sauke nauyinku .
 Yaya bazance maka a'a ba, amma Zan saka lamarin cikin addu'a ALLAH ya za6a mana abinda yafi alkairi .
 To Amin matata . Aliyu yay maganar yana jawota jikinsa ya rungume.


('('('('('('('('('('('

Alhaji garba baya gari, dan haka baisan wainar da ake toyawa ba akan auren Jiddah, matarsa kuwa koda wasa bata sanar masaba ko a waya, dukda ita kuwa tanajin komai a wajen hajia Hindu, harma rashin lafiyar Abba da hajia Hindu batasan sirrinba saida hajia deluwa taji.

**********

Washe gari da yamma lik'is Abba ya farka, sai dai jikinsa duk babu wani k'arfi.
Ganin ya farka hajia Hindu ta Kira Uncle yahya kamar yanda ya buk'ata.
Uncle yahya najin haka yakira doctor Abbas doguwa akan yaje Abban ya farka.
Doctor Abbas kwararren likita a asibiti. Aminu kano, Wanda d.p.o ya had'asu Uncle yahya dashi. Yanajin shirin da sukai akan Abba saiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login