Showing 69001 words to 72000 words out of 124968 words

Chapter 24 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5476

malam? .
 Niba malaminki baneba yarinya, amsarki kuma sai a nan gaba zaki samu, nidai k'aramin .
Tashi Jiddah tai ta k'ara masa, ita dai yau gaba d'aya bata fahimtar maganganunsa, sannan yana k'ara bata mamaki, batai zaton yana magana hakaba itakam.
Haka yayta d'ora kunun aya yana Mata hirar da rabinta duk sakata kunya yakeyi, iyakarta murmushi ko e ko a'a.
Goma da rabi nayi ya mik'e,  To Juddatulkhair bara Na matsa ga Uwargida itama, zuwa talata insha ALLAH zankuma zagayowa gaisheki, a gaidamin Umminmu da k'yau .
Itama Jiddah tashi tayi tsaye,  Zataji insha ALLAH, ka gaida aunty, ALLAH yabata lafiya .
Harya d'an Fara tafiya yadawo da baya kusa da ita sosai yana fuskantarta,  Yanzu nan ba'amin oyoyoba, Na gaida gidanma bazan samuba kenan? .
Yunk'urin ja tayi da baya yay azamar d'ora hannunsa a k'ugunta ya matsota jikinsa ya rungume, duk tsumar da jikinta yake da rawa bai saketaba, saima bakinsa daya d'ora saman goshinta ya sumbata kafin yace,  wannan lalurar taki batamin adalciba, dolene kafin ki tare da izinin ALLAH na nemo mafita . Yana gama fad'a ya sumbaci la66anta sannan ya saketa.
Dukda halin datake ciki Na gushewar nutsuwar wucin gadi hakan bai hanata yomasa rakkiyaba kamar yanda Gajiram ta gargad'eta.
Tun a bakin k'ofa ya Danna key d'insa motarsa takawo haske day'ar tsuwwa, bud'ewa yay yashiga yana d'ebo ledojin gefensa ya mik'o Mata.
K'in kar6a tayi tana shirin juyawa. Da hanzari ya damk'o hannunta yana fad'in  Hajiyata tunadai miji nake ba saurayiba .
Dariya maganarsa ta bata, ledojin ya zura mata a hannu yana sumbatar hannun,  Kiyi mafarkina daga farkon dare har k'arshe .
Kanta a duk'e tace,  Nagode ALLAH ya k'ara bud'i na alkairi, yakaika gida lafiya .
 Amin *Qurratul ain*, maza shiga gidan dan bak'aramin k'ok'ari naiba barinki fitowa nan da wannan gyalen, danma kawai Darene kuma mota ta kare .
Murmushi tayi tana d'an risinawa da fad'in  saida safe .
Harta shige idonsa k'yam akan bayanta, ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tareda jingina da kujera yana lumshe idanunsa, yakai hannu yana shafa gemunsa Na sunnah kafin ya maida hannun ga cikinsa, a hankali ya furta  Kunun aya yafara aiki kenan .
Bud'e idonsa yayi yatada motar a kasalance yabar anguwar tamkar bayason tuk'in.


('('('('('('.

Duk a falo Jiddah ta iskesu har Uncle yahya dasu Sadiq da basuyi barciba, gaba d'aya suka zubo Mata idanu, hakanne yasakata yin kasa da kanta tana sakin ledojin hannunta a k'asa, gani take kamar duk sunsan miya faru tsakaninta da Sheikh Aliyu.
 A'a Jiddodo yada sakin ledoji haka? .
Uncle yahya yafad'a fuskarsa a washe da murmushi.
 Babu komai Uncle .
 To Alhamsullhi, ya tafi ne? .
 Eh .
 To ALLAH ya tsare, basaikin zaunaba kumuje Na rakaku gida dare yayi .
Ledojin Jiddah ta d'iba takaima Maman Sadiq.
 A'a Walida d'aukar Mata, wannan nakine ai .
 A'a mama bafa nawa baneba .
Uncle yahya ya katse zancen da fad'in  Kinga walida d'auka Mata kumuje .
Babu Wanda yay masa musu sukabi Umarninsa.
Jiddah ta d'auki hijjabinta ta saka suka fita sunama Maman Sadiq dasu Mageed saida safe.
Har k'ofar gida ya rakasu, saida yaga sun Shiga sannan ya juya batareda yashigaba shi.

Su Umma duk suna zaune basuyi barciba suna jiransu.
Balu ce ke fad'in  A lallai wannan d'an nawa ya iya zuwa, amarya mikika samo mana? .
Fita Jiddah tayi takoma d'akinsu takasa bata amsa, nanfa suka shiga yimata dariya da tsokanarta, tana jinsu amma tak'iyin ko tari, sai abinda ya faru tsakaninta da Aliyu keta dawo Mata kamar wata almara ko shirin film.
A can kuwa Gajiram ta bud'e ledojin dasukazo dasu. Kayan marmarine sai ice-cream da kaji guda biyu, sai kuma kwalin waya harda Sim card.
Nanfa suka shiga godiya ga Aliyu da fatan alkairi dana zaman lafiya garesu.
Gajiram tace walida ta d'auka takaima Jiddah, amma sai Umma ta dakatar da ita.  Ba haka ya kamata ba, ki raba kowama ya samu, wannan shine dai-dai .
Gajiram tasan hal??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in Y'ar uwarsu da k'yak'yk'yawan tsari akan yaranta, dan haka tabi umarninta, kaza d'a aka ajiyema gidansu Uncle yahya, kayan marmarinma aka d'iba musu, ice-cream aka ajiye roba d'aya, ta raba komai nasu tabama su Jiddah rabi suma su uku suka d'auki rabi.
'Dauka su Zarah sukai da wayar Jiddah suka nufo d'akinsu zuciyarsu wasai dakumajin lallai yanzune Y'ar uwarsu tayi aure.
A tsanake sukaci komai sukai gidiya ga ubangiji, kafin su dasa fira da k'ok'arin had'a wayar Jiddah dukda babuma wuta.
Suma su Umma dai hirar tasu duk akan tariyar jiddahrne, sunayi sunacin abin arzik'in da ya sheikh Aliy ya kawo.


('('('('('('('('('('('.

A haka ya lalla6a hanyar gida bayan ya tsaya yasayama Maimunatu abin motsa baki itama.
Dukda dare yafarayi hakan bai hana ya iske tsirarun mutane a bakin masallacin k'ofar gidansaba, dayake akwai wuta a anguwar tasu su, dukda yabaro anguwarsu Jiddah babu kuwa.
Wani saurayine dasuke a bakin masallacin ya tashi ya bud'e masa gate, bayan yashiga ya rufe, saida ya tsaya Aliyu yafito a mota ya gaidashi sannan yafito yana masa saida safe.
Aliyu kuma ya kulle gidan danya shigo kuma kenan, tsarabar Maimunatu ya d'iba yanufi cikin gidan duk a matuk'ar kasalance, Wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bashida kuzari ko kad'an, dukda shi mutumne mai sanyi dama amma saiya kuma narkewa yanzu.
A yanda Maimunatu dake zaune a falo taji sallamarsa kawai saida ta d'ago da sauri ta kallesa da k'yau.............
'








*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?O?
[12/15/2019, 3:10 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[35?'36]_*


..............Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta tana murmushin k'arfin hali, jikinta duk sai ya kuma sanyi, itadai tasan Aliyu ba mutum bane mai yawan fitina, hasalima sunkan jera kwana hud'u batareda ya nemeta ba, sannan baya d'aukar dogon lokaci tare da ita, wannan dalilin yasakashi dagewa wajen gyara kansa, dan a ganinsa ba mace kawai yakamata taima miji gyaraba, suma mazan yadace suna gyarawa........
 Ko ba'ayi murna da dawowataba Na koma Gimbiya . Maganarsa ta katsema Maimunatu tunaninta, mik'ewa tayi ta nufosa, sai da ta rungumesa da sumbatar kumatunsa kafin ta sakesa ta amshi kayan hannunsa tana danne kwallar data cika idonta, dan sosai taji k'amshin turaren daba nashiba a jikinsa, tasan kuma bai wuce Na amarya ba, a yandama yadawo mata kad'ai ya isheta amsa.
Bin bayanta yay ya zauna yana sauke numfashi, kallonsa tad'anyi batareda tace komaiba tawuce kicin, babu dad'ewa tadawo d'auke da tire.
Gabansa ta dire, ya d'ago kansa daya jingina a kujera yana kallonta, itama shi take kallo, cikin danne zuciyarta tasaki murmushi tana fad'in  Wai miya sakaka laushi haka Annur? .
Zamansa ya gyara sosai tareda kamo hannunta ta zauna a gefensa. Muryarsa a matuk'ar sanyaye yace,  Babu komaifa madam, naga kin damu .
 To ba doleba Yaya, kafita muna farin ciki kadawomin a sanyaye, kaga sainaga ko wani abune yafaru da jiddan ko wani a gidansu ai? .
 To kwantar da hankalinki, babu abinda yafaru tanama gaisheki. Bani ruwa nasha kedai .
 ALLAH Sarki, ina amsawa nima, kuma Alhmdllh tunda babu wata damuwa . Jug dake kan tire ta d'auka tafara tsiyaya abin ciki a k'aramin kofi.
 Minene wannan zaki bani? .
Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli jug d'in,  Yaya had'in kwakwar dakace namakane d'azun ai, to wlhy nama manta, sai bayan fitarnan taka dasuka kawo wuta Na tuna shiyyasa nayi, kajiko harma yayi sanyi .
Amsar jug d'in da kofin yayi ya ajiye k'asa,  Barshi dan ALLAH Maimoon inba kasheni zakuyiba .
Cikin waro ido Maimuna tace,  Yaya kashewa kuma? .
 Eh mana, ba dole nace kashewa ba, ita tabani kunun aya, kekuma zaki bani had'in kwakwa? .
Babu shiri Maimuna ta kwashe da dariya, haba no wonder tagansa a sanyaye.
Harara ya zuba Mata yana wani shagwa6e fuska da fad'in  Abindama zakimin kenan ko? Maimakon kiji tausayina .
Baki Maimuna ta toshe da hannu tana had'iye dariyarta da k'yar,  ALLAH Yaya kaid'inne kaban dariya, ni duk kasakani a tsorone da farko .
 Humm bazaki ganeba wlhy, tsautsayi kawai ya sakani shan kunun ayarnan da yawafa, gashi kuma yasha had'i kamar yanda kikemin, Nidai Ahmad ai yagama dani daya bani wannan sirrin .
 Haba dai Yaya godiya yakamata Kai masa ai .
Hannu yasa ya jawota jikinsa, murya k'asa-k'asa yace,  Wayace ban gode masaba, badan iyakancewar Mahaliccina da taimakon Ahmad ba da yanzu ban mallaki koda mace d'aya ba balle Mata biyu ma ai Sarauniyata, amma wad'annan had'in ba k'aramar harmutsani sukeba .
Hanu Maimuna tasaka ta rufe fuskarta tana Y'ar dariya. Shima saiyay murmushi yana kuma sakata a jikinsa.
Tarigada tasan muhimmmanci duk irin wad'annan abubuwan ga mijinta, hakanne yasakata kar6arsa d'ari bisa d'ari tun a falo aka fara canja hanya.


=?F? @&.



('('('('('('('('('('('

Jiddah dai gaba d'aya tama rasa yanda zata fassara abinda sheikh Aliy yay Mata, wani iri duk takeji a jikinta, duk hirar dasu Zarah keyi hankalinta baya tare dasu, har aka maido wuta suka saka cajin wayar.
 Wai Yaya Jiddah mike matsalarkine? Tunda muka dawo kinyi sukuku .
Kallon Zarah tayi mai maganar, kamar bazata tankaba saikuma ta sauke numfashi tana cewa,  Babu komai, kaina ked'anmin ciwo kawai .
Sannu suka shiga jero Mata cikin tausayawa, Walida harda zuwa ta samo Mata magani. Bata musaba ta kar6a tasha sannan tayi shirin barci suka kwanta.
Barcinma k'in d'aukarta yayi, sai tunane-tunane takeyi, tunda take bata ta6a soyayyaba, hasalima baifi sau uku zuwa hud'uba ta ta6a tsayawa da saurayi, dan dawahala tana tafiya samari su tareta a hanya ko yimata magana (Muhimmancin nagartacciyar sutura ga d'iya mace, yakan saka mutanen banza shakkar zuwa gareka, abinda y'anmatan yanzu dama matan auren muka gaza fahimta kenan), wannan yasaka komai Na Aliyu take masa kallon *Sabon al'amari* a gareta, ganin barcin yama gagareta saita mik'e tafito domin d'aura alwala.
Nafilfili taita gabatarwa, kafin tayi zaman karatun littafi mai tsarki, a wannan time d'inne suma su Zarah suka farka, sai suma sukayo alwala.

Koda Jiddah tasamu ta kwanta sai barcinta yazama mafarkin Aliyu kusan gaba d'aya, da asuba abin ya tsaya mata a rai, tasara miyasa ya mannema zuciyarta har irin haka?.


Fans zasu baki amsa jiddodo>?)??&
@&.


('('('('('('('('('('('

Gaba d'aya Abba zakari a takure yake, yasaba harkokinsa Na kasuwanci a kullu yaumin, amma anzo nan an ajiyeshi wai dan ya huta, anyama kuwa wannan ba tsarin Yahya baneba? Zumbur yamik'e saboda amsar da zuciyarsa ta basa, lallai wannan haka yake, akwai munafinci a wannan lamarin, tunda dai ai shine ya kawo likitan, to waima miyasa yagaza tariyo yanda suka k'are a Station ne?, shiru yay nawani lokaci, kafin babu shiri ya lailayo wani ashar ya dire a k'asan tayis, a lallai yahya yagama ganin gadon barcinsa, yanzu kuwa zaije ayita tak'are wlhy.
Batareda jiran likitaba ya had'a inasa-inasa ya nufo gidansa da Hajia Hindu ke a ciki.


('('('('('('('('('('('.

Hajia deluwa hakimce a falonta Na alfarma tana waya da hajia Hindu akan auren Jiddah, sai dariya take kwasa tasamun nasara, dan yanzu sakayau takejinta tamkar an sauke Mata kaya a Kai, Alhaji Garba datun farkon fara wayar yashigo yay tsaye tamkar gunki yana saurarenta, dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi, cikin zumud'i yanufo sashenta saboda shigar bazata yay mata batasan da dawowarsaba yau, amma saiyaci Karo da abinda ke Neman fasa masa zuciya.
Jiddah tayi aure bashiba, mahaifinta ya yaudaresa, matarsa itace ta ruguza masa dukkan shiri ta k'ark'ashin k'asa.
A fusace ya fisge wayar ya ratsata da k'asa akan tayis, nan take tayi kwatsa-kwatsa.
Hajia deluwa data mik'e a fusace tuni mamaki da tsoro ya baibaiyeta, dan batasan da shigowarba ko kad'an, amma dayake manyan matane sunsan takan duniya saita dake tana kallonsa hankali a kwance.
 Alhaji lafiya kuwa? Ya daga dawowa sai fushi haka? Mi wayata Tamaka? .
 Ban saniba Yahanasu, yanzunan kece da kanki zaki aikata shed'anci Na ruguza auren sunna? Dama son aurena da Jiddah dakiketa nunawa da farko munafuncine Ashe? Lallai yau nakuma yarda makircin mace yafi Na shaid'an girma, anyama kuwa bakece kika kori Jiddah daga gidannanba? .
 Yo Alhaji kaga laifinane? idanma ni d'ince .
 No ya za'ayi inga laifinki, ban ganiba wlhy yay wata dariya ta basawa, kafin ya nunata yana cigaba da fad'in  Kijira sakamakon aikinki Na ruguzamin auren Jiddah da kashe mana aure .
Yana gama fad'a yay ficewarsa, mamakine ya kama hajia Deluwa, tafara safa da marwa Na tunanin to mizai Mata? Miya shirya? Kodai sakinta zaiyi?. Gabantane yay wata mummunar fad'uwa, jikinta Na rawa tabi bayansa.
Amma saita tarar ya gark'ame k'ofarsa, duk Nokin d'in datai masa bai kulataba. Kuma yana jinta sarai, dan yanama zaune a falonsa yana k'ok'arin kiran Abba Zakari a wayane.

Abba datunda yabaro gidan doctor yadawo gidan hajia deluwa ta tareda da farin cikin samun lafiyarsa, dukda tagansa awani tsume alamun zuciyarsa a kusa take hakan bai hanata tarairayarsa yay wanka yaci abinci ba, harzai fita gun Uncle yahya ta dakatar dashi da maganar kalifa daya shigo gidan yanzu babu jimawa sannan Abba yana wanka.
 Kin dakatar Dani, bakice komaiba kin zubamin idanu .
 A'a Abban kalifa, bafani nakar zomonba, dama kalifane aka koro daga makaranta sunyi fad'a dawani yaro akan budurwa ya fasa masa Kai, yanzuma haka abinda ake ciki iyayen yaron sunce bazasu yardaba, shiyyasa aka koro kalifa yazo yaje da mahaifinsa yana d'akinsu, Wanda aka turosu tare kuma yana a bakin gate yana jiranka .
Zugudi yayi yana kallonta, bakinsama yamasa nauyin daya gaza furta komai, harma yaushe Kalifan yagama balaga dazai fasa kan wani akan mace?, ina wannan sharrine kawai za'aima yaronsa, dan haka babu inda zayi yanada matsalar data girmi wannan shirmen........
K'arar wayarsa daya kunna babu dad'ewa ta katse masa tunani. Wata mummunar fad'uwa gabansa yayi saboda ganin mai kiran, yanda ya gwalalo idanune yasaka hajia Hindu lek'a wayar, itama saida ta fiddo ido kafin tace,  Abban kalifa ka d'aga mana .
Kallonta yayi awani yanayin data kasa fassarawa, wayar Na tsinkewa aka sake bugowa, amma Abba yakasa d'auka.
Hakanne Yakuma fusata Alhaji Garba daga can, a matuk'ar harzik'e yakuma dannoma Abba Kira.
 Alhaji ka d'auka mana hajia Hindu tafad'a tana nuna masa wayar, ganin bashida niyyar amsawa ita saita amsa tana saka masa a kunne.
Yanda Alhaji garba yay magana dagacan a harzuk'ene yasaka Abba kwarewa da yawu yahau tari.
 A lallai Alhaji zakari, ni zakaima d'ibar albarka, k'in amsa wayata da kayi kawai ya isa bani shaidar kana kan sani ka aurar da y'arka, to ni bazan zauna 6ata lokacina akan hayaniya dakaiba, saidaifa ina mai tuna maka maganar kud'ina miliyan hamsin cif nanda wata d'aya kacal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login