Showing 72001 words to 75000 words out of 124968 words

Chapter 25 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5497

wlhy, dan wannan shinema adalcin dazan maka, sannan kuma namik'a komai a hannun d'ana Ashir dashi zakuyi nabarka lafiya .
Wani haushine ya turnik'e Abba, Dama ga zuciyarsa a kusa take, jira yake a ta6osa ya fidda fushinsa, cikin tsantsar bala'i shima ya dakatar da Alhaji garba dake shirin katse kiran.  To naji d'in saime, ank'i a baka auren Nata, waishin kasheni zakuyi da haukankune?, shin da wanne zanji? Kama tambayeni yanda akayi mana amma saika hau kaina saboda wata banzar miliyan hamsin, Kai da mutuncinafa babu Wanda ya isa ya takani .
Tsaki Alhaji garba yayi ya yanke wayarsa.
 Amma Abban kalifa da bakai masa hakaba ai, gara ka lalla6ashi ko Zarah saika bashi madadin Jiddar ko? .
Wata uwar harara ya zuba Mata, kafin yasaka hannu ya hankad'ata baya, tareda tad'e k'afarta dake hanyar dazai wuce, a take k'ashin k'afar yay k'arar samun rauni.
dukda k'arar wahala data saki baibi takantaba ya tsallaketa yafuce a fusace.



Turk'ashi=?F?

('('('('('('('('('('('

Gaba d'aya yau Sheikh Aliyu bai fita ko inaba tunda yadawo sallar asuba, dukda kuma yau litinin amma sai yay lafewarsa gida, ga Maimuna ma dai bawani isashen lafiyane da itaba, amma dayake tanada dauriya sai bata cika langa6ewa ba, da taimakonshi suka gyara gidan, kicinma shine ya tayata had'a musu Karin kumallo sannan suka gyara komai tsaf. Wanka yatafi yi yabarta tana shirya abincin a falo.
Yad'an jima a bayi kafin ya fito, wayarsa daketa haske ya kalla takawa yay inda take a saman durowan gefen gado ya d'auka, mamakine ya kamashi ganin sak'one aka turo da Number Jiddah daya saya mata jiya. Bud'e sak'on yayi zuciyarsa na mamakin kona minene?, saida ya zauna a baking gado kafin yafara karantawa.
*_ Amincin ALLAH ya tabba ga adalar zuciya ma'abociyar tsoron ALLAH da addini, ina fatan ka Isa gida lafiya? Kakuma iske Y'ar uwata lafiya itama?. Fatana karayu cikin aminci da tsaftataccen farin ciki a wannan yini na litinin ya kai jarumina tauraron Al-umma a k'ark'ashin duniyar musulunci, nagode kwarai da gaske da alkairinka a gareni, ALLAH yak'ara bud'e na alkairi mai albarka kuma>?? _Taka Hauwa'u-Jiddah_.

Idanunsa ya lumshe yana sauke wani nannauyan numfashi, yayinda can k'asan ransa yake kuma gauraya dawani farin ciki na musamman, ko kad'an baiyi zaton hakan ga jiddahr ba, musamman idan yay dubi da yanda suka k'are a jiya.
Idanunsa ya bud'e akan wayar yana sake maimaita karanta sak'on, saida ya tisashi sau babu adadi kafin ya danna kiranta dan bazai iya hak'uri ba.

Jiddah suna zaune a falo gaba d'ayansu suna Karin kumallo Walida ce kawai babu taje makaranta, Zarah kuwa batajeba suna shirye-shiryen fara jarabawane ta SSCE. hankalinsu kwance sukecin Taliyar da Jiddah ta dafa musu (Y'ar Hausa) wayar Jiddah dake hannun Balu da Zarah tashiga tsuwa, kallon juna sukai sukai murmushi, Zarah taima Balu alamar Jinjina da fad'in  Aikinmu Na k'yau nida uwata .
Hannu balu taba Zarah suka tafa kafin ta mik'ama Jiddah dake kallonsu wayar. Su Umma ma dai kallon Su Zarahn sukeyi, amma basuce komaiba, saima Yaruwaiya datacema Jiddah  Wai bazaki tashi kije ki amsaba saita tsinke .
Tashi Jiddah tayi tafita jikinta a sanyaye, kafin ta Isa d'akinsu ta d'aga har kiran ya yanke an sake Kira. 'Dagawa tayi tana zama a bakin katifarsu.
Jin ta d'aga sai Aliyu ya d'an sauke ajiyar zuciya yana fad'in,  Assalamu alaiki warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu .
Wani yarrr Jiddah taji tsigar jikinta ta tashi, cikin had'iye yawu da k'yar da janyo numfashi, ta amsa da  Wa'alaikassalam, ina kwana .
Murmushi yayi daga can yana shafa gemunsa zuwa k'asumba, cikin kuma sanyaya murya yace,  Lafiya lau Amarsu, ina fatan kema kina lafiya? .
 Lafiya lau, ya jikin Aunty .
 To masha ALLAH, jikin auntynki kuma Alhamdulllahi .
Shiru Jiddah tayi, dan batasan kuma mi zataceba (abinka da farin shiga=??), sai dai a k'asan ranta tarasa miyasa muryarsa ke sakata a wani yanayi?.....
Katse Mata tunani yay da fad'in  Naga sak'o Na gode sosai, sakallahu khairan Juddatulkhair .
Mamaki ya kama Jiddah, tana shirin tambayarsa wane sak'o? Dan itadai tasan bata tura masa wani sak'oba saiya katse Mata hanzari da fad'in  Lallai Na yarda anyi mafarkina daga farkon dare zuwa k'arshe da gaske, wannan sak'o ya cancanci tukuyci mai nagarta, Na bayar anan? Kosai nazo kusa? .
Cikin shagwa6ar da Jiddah batasan tayiba tace,  Nidai Na yafe .
 A'a madam yada saurin karaya haka kuma? Nifa ba fad'ar tukuycin dazanyiba nayi aiko, yanzu dai kin amince nazo anjima na bada? .
Da sauri Jiddah tace,  A'a nagode, abama aunty a maimakona .
 Kin yarda Na bata? .
 Eh wlhy Na yarda nikam .
 To shikenan, Zan bata rabi nazo nabaki rabi .
 A'a kabata duka nidai .
Murmusawa yayi yana mik'ewa tsaye, ya k'arasa gaban mirror yana fad'in  To ai shikenan tana godiya sosai, yasu Zarah? .
 Lafiyarsu lau suna gaidaku suma .
 Muna amsawa, suna kusa dake kenan? .
 A'a .
Zaiyi magana Maimuna ta shigo da sallama, yanda yake murmushi yasata tsarguwa ko yana waya da matarsane? Dan haka tai niyyar juyawa. Saurin damk'o hannunta yayi yana k'arema kwalliyarta kallo, tayi k'yau sosai tana baza k'amshi.
Jin yayi shiru gakuma d'an motsi Jiddah Na jiyowa yasakata itama tsarguwar k'ila matarsace, saitai saurin fad'in  Sai anjima .
Matse Maimuna yayi a jikinsa shima yace,  To sai anjima a gaishe dasu Ummi .
 to kawai Jiddah tace ta yanke wayar. Haka kawai taji ranta ya sosu, wato da shikad'aine shiyyasa yaketa wani narke Mata, amma yanzu matarsa tazo yama kasa magana,  humm halin maza saisu tai maganar a fili tareda ta6e baki ta mik'e takoma wajensu Umma, sai dai k'asan ranta abun ya tsaya Mata sosai. (Madam Jiddah yayane=?F? Data dawoma daina saka baki a firarsu Umman tayi, har Yaruwaiya da Balu da Zarah suka shirya suka fita kasuwa k'arasa sayayyar Jiddan data rage, aka barta itada Umma kawai.
Umma nakula da zum6ure-zum6uren da Jiddah keyi, amma sai bata kulata ba balle ta tambayeta ma.
Saima zama datayi tana tambayarta akan magungunan sanyi data bata Tasha tun kwanaki.
 Wai Jiddah magungunan Dana baki kuwa kina amfani dasune? .
 Eh Umma inayi .
 Idanma bak'yayi kekika sani dai, dan wannan shine gatan dazan miki, a zamaninnan da sanyi yayma Mata katutu, ba maganin mata kawai yakamata mu iyaye muyita Danna mukuba idan zakuyi aure, yakamata mufara bincikar lafiyarku ta 6angaren sanyi kafin wad'annan magungunan, dan duk macen dake tare da sanyi kozatasha tirelar maganin gyaran Kanta to wlhy tamkar a banzane, dan bazai Mata amfanin komaiba, dan haka idanma zaki maida hankalinki ki maida, yanzu hakama hajiya ladidi mai adashe tace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata kawo miki wani .
Kan Jiddah a k'asa tace,  To Umma nagode .


('('('('('('('('('('('

Aliyu kam ya ajiye wayar yay yana maida hankalinsa ga Maimuna, dan kimarta tawuce ya amsa wayar wata mace a gabanta, a ganinsa hakan tamkarma cin fuskane da had'a k'iyayya a tsakanin matan nasa.
 Hiya-huwa kinyi k'yau ainun Masha ALLAH .
Wani dad'ine ya ratsata jin sunan daya kirata dashi, ta kama hannunsa ta sumbaci tsakkiya, cikin narke masa tace,  Hilmy yanzu kaima zakayi fiyema dani .
 haba-haba, ai idan ana dara fidda uwa ake gimbiyata, samun k'yak'yk'yawa irinki acikin Mata sai an tona, kina kallon kaniki a madubi kuwa? .
 Kai yayana kadaina fasamin Kai hakanan fa, kaidai zauna Na shiryaka muje ka karya, dan sak'onin daka sakani Na amsa wad'anda Zan iya jiya naci Karo dawani mai muhimmanci .
Kallonta yayi sosai,  Mi sak'on yace? .
 A'a kabari saika karya .
 Karki damu fad'amin kinji .
Mai tafara shafa masa, _ Cayay ka taimakeshi da shawara akan lafiyarsa, yanada Mata harda yara a tsakaninsu, iya gwargwadon iko suna gamsar da juna a shimfid'a, dukda dai ya fuskanci shi mutumne mai rauni dan baya iya jan lokaci wajen tarayya da ita amma sai bata ta6a nuna damuwartaba akan hakan, Sai kuma dukda wannan matsalar daya sani saiya k'ara aure, to a yanzu halin dayake ciki shine baya iya gamsar dasu su biyun, amaryar tashi kuma tafara nuna itafa bazata iyaba, itama Uwargidan haka, hakan kuma yafara kawo musu matsalar yawan hayaniya da matan nasa musamman Amaryar, shikuma yarasa yanda zaiyi, ya gwada magunguna da ake saidawa Na gargajiya sai dai tasirinsu kuma bawani mai tsayi baneba agaresa ake komawa Y'ar gidan jiya, shikuma duk yanason matansa yanason cigaba da rayuwa dasu. _
Ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, ya taimakama Maimuna dake k'ok'arin saka masa kaya, saida suka kammala tasa masa turare sannan suka fito yana fad'in  Wannan matsalar abar dubawace, kuma insha ALLAH zanyi magana akanta yau a masallaci, dan munada majalisi, matsalace babba wannan Maimoon data dabaibaye Mazajenmu Na arewaci, ammafa tamafi illa a kudancinmu, kawai sudai sun fimu himmar gyara kansune, matsalarmu mu mazan arewa shine mun d'auka mace ita kad'ai yadace ta gyara mana kanta, mukuma abinda muka iya kawai munemo kud'i muyita aure Ana kiranmu jarumai a waje, a cikin gida kuwa bama iya hasalama iyalinmu komai, Mata da yawa suna cutuwa ta wannan sigar, saidai basa iya magana saboda kunya, soyayyar mutumin arewa a iya wajene kawai saikuma amarcin watanni uku, ita kuma mace kota tsufa tana buk'atar tattali da soyayya ga mijinta, koda bakada wadatar dukiya soyayyar dazaka nuna Mata kad'ai wlhy zakiga ta gamsar da ita da jagorantar zamanku har k'arshen rayuwa .
 Wlhy Yaya maganarka gaskiyace kuma . Maimuna dake zuba masa a bincin tafad'a cikin damuwa.
Ajiyar zuciya shima ya sauke, dan abi yana Sosa masa rai, amma insha ALLAH a wannan Karon zai amayar dashi ya huta, dan ba Neman ilimi da tafseer kawai al'umma suke buk'ataba, akwai wasu manyan abubuwa Na rayuwa da muhimmancinsu yakai adinga tunatar da mutane shi kodan samun sauk'in da duniyar aurarrakinmu ke fuskanta a halin yanzu.


('('('('('('('('('('('

Jiddah da Umma na a tsakar gida suna shirin girkin rana da hira wadda rabinta duk ilimin zaman aure Umma ke k'arama Jiddah haske akai cikin hikima.
Tamkar an jefo Abba ya banko k'ofa jikake garam!!!, duk zabura sukayi suna kallonsa, Kai tsaye kan Jiddah dake tsaye a bakin rijiya yayi tamkar wani bajimin zaki...........
'



=?(?Abba zakari mi zakai mata kaikuwa?.=?F?

_Barbarawa ayimin afuwa (Au bare-bari=?F??-?). wata tace ba sunansu hakaba, Barbarawa kamar bunsuru wai=??, bani Na fad'aba Y'ar uwarkuce tace, karku dafani yau su tawan (miss Xoxo)?&
@&?&
@&?&
@&._



*_Albishirinku fa, CIKI DA GASKIYA mafa ya sauka a gareku adai YouTube channel tv na Abban Dausayi, saiku garzaya kar ayi babuku gayis_*.?&
@&?&
@&?&
@&









*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?O? [12/16/2019, 9:06 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[37?'38]_*


..............Da sauri Umma ta sha gaban Abba dake nufar Jiddah tamkar wani bajimi, ture Ummar yayi yasaka k'afa ya tad'e Jiddah dake Neman guduwa.
Fad'uwa tayi k'asa akan hannunta, dan haka ta fashe dakuka saboda zafin daya ratsata.
Waya ya jefa Mata,  'Dauki wayar nan kikira Wanda aka d'aura miki aure dashi yanzunan kice ya sakeki .
Kuka Jiddah takuma fashewa dashi, ta d'auki wayar ta rik'e, da sauri Umma ta kwace tana fad'in  Bazata kirashinba, Kai mizai hanaka kiranshi kace ya saketan? .
 Yagana! Yagana!! Kina shigarmin hanci da yawafa .
 To mizai hana ka fyatoni ka huta, wlhy wannan karon duk abinda zakayi sai dai kayi amma bazan d'auki wannan masifar ba.......
A fusace ya d'aga hannu zai Mari Umma
 Wlhy karka sake ka ta6ata!! .  Yaruwaiya dasuka shigo yanzu babu dad'ewa tafad'a a matuk'ar tsawace, dan sunji mafi yawan abinda ke faruwa .
Cak Abba ya dakata, bai marentanba baikuma sauke hannunsa ba.
Zarah da Balu sukazo suka d'aga Jiddah dake kuka zaune, hannunta harya fara kumbura alamar taji ciwo. Itama Yaruwaiya zuwa tai ta janye hannun Umma suka bar Abba a wajen, yakasa motsi balle dogon tari.
Hayawaye kawai Umma taji sun gangaro Mata, duk k'ok'arinta Na 6oye mugayen halayyar Abba ga danginta yau sai da ya tonama kansa asiri, shekaru ashirin suna tare bata ta6a Kai k'ararsa wajen iyayentaba idan yamata Abu, aganinta hakuri shine maganin komai, sannan yawan Kai k'arar miji gidanku ko gidansu tamkar zubarwa da kanku darajane, dan iyayenka zasu rage ganin darajarsa, idan kuma iyayensane suma zasu rage ganin darajarka.
Zarah da Jiddah ma hawaye suketayi, ga hannunta dake Mata azabar zogi, shiru babu Wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, kowa da abinda zuciyarsa take sak'awa.
A tsakar gida kam kwafa Abba yayi yafita yanamai jin haushin Yaruwaiya, amma ko giyar wake yasha bai isa cigaba da abinda yay niyyaba, dan Yaruwaiya ba kanwar lasa baceba, kad'an daga aikints ta ketashi gaban y'ay'ansa.


('('('('('('('('('('('

Tuni zufa ta jik'e hajia Hindu saboda azabar da k'afarta kemata, k'arar data kwallane yasaka kalifa zuwa d'akin.
 Momy miya sameki? .
 Kalifa Abbanku ne ya karyamin k'afa . Tafad'a cikin jin azaba. Gabanta yazo ya zube yana Kama k'afar dahar tafara kumbura,  Momy mikikai masa yay miki haka? .
 Babu abinda nai masa kalifa, dan kawai Na fad'a masa gaskiyane .
 Kiyi hak'uri Umma ALLAH ya saka miki, bara Na Kira direba mukaiki asibiti.

Da k'yar Kalifa ya iya taimakama Hindu tafito suka shiga mota, Wanda aka aiko daga makarantar su kalifa danyaje da Abba ganin yanda jama'ar gidan suke kamar a tashin hankali saiya sulale ya koma makaranta Kai rahoto.
A asibiti kam anduba hajia Hindu data samu targad'e a k'afa, nanda akaimata gyaran datasha azaba. Magunguna aka bata suka dawo gida.
Saidaifa a k'asan zuciyarta tanajin bazata bar abinda Abba yay mata yatafi a banzaba, dolene saita rama wlhy. Tana zaune afalo tana cika da batsewa Abba ya shigo, harara tashiga watsa masa, amma ko kallon inda take baiyiba yay shigewarsa d'akinsa zuciyarsa nacigaba da tafasa, shi yanzu a ina zai samo wad'annan kud'ad'en yabama Alhaji garba? Kodai shawarar Hajia Hindu zaibi yabashi Zarah? To amma kuma shi Alhaji garban zai amince ne?, kansa yadafe cikin matsananciyar damuwa, gaba d'aya yama rasa miya dace yayine?. Yana cikin wannan halin wayarsa tashiga ruri, sharewa yayi tamkar bazai d'aukaba, saikuma yaja tsaki yana fisgo wayar saikace itace tai masa laifin.
Daga makarantar su kalifa ne, a fusace ya d'aga, ko sauraren sallamar da akai masa baiyiba yace,  Minene? .
 Babu komai Alhaji, akan maganar yaronkane da muka turo da d'an rakiya, yadawo mana babu Kai babu yaron kuma .
 Kaga da ALLAH karku dameni, harma nawa kalifa yake dazai zauna fad'a dawani akan mace, nifa banason sharri, suje can sunema Wanda ya fasama d'ansu kai, Mtsoww aikin banza kawai . K'itt ya yanke wayar.
Yin haka dakamar mintuna talatin saiga mai gadi yashigo wai ga y'an sanda sunason ganin Alhaji.
Da mamaki Hajia Hindu dake tule a zaune tace,  Y'an sanda kuma? To miya faru to? .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login