Showing 105001 words to 108000 words out of 124968 words

Chapter 36 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5493

garau-garau da Walida ta dafa ba, wai sai dai aimusu miya, su Mom bata basu abinci da mai da yaji.
Daga Walida har Zarah watsar dasu sukayi suka cigaba da hidimarsu, idan yunwar ta rarakesu ai saci.
Ilai kuwa zuwa dare da sukaga babu mafita sai suka Wauka sukacin.


('('('('('('('('('('('

Washe gari su aunty Hannatu dawasu a cikin dangi suka iso, Abba dai ya farko, sai dai ko magana baya iyayi saboda kumbura da fuskarsa tayi dam, tsakaninsa da mutane sai dai ido, ga karaya har biyu a ?afarsa da ?ugunsa saboda duka sukai masa na fitar hankali.
Itama hajia hindu ta farko, kuma ita da sau?i sosai, dan nata gocewar ?ashine.
Duk wanda yaga Umma da Uncle yahya a wanan lokacin saisun baka tausayi, dan dukkan lokacinsu yanakan Jinyar Abba da hajia hindu ne, hakama hidimar asibitinsu sai da kuWinsa akeyi.
Zuwa dare su Aunty Sauda suka ?arasa gida dansu huta. Dukda ba abin daWi bane ya kawosu, kuma basu daWe da tafiyaba daga bikin Jiddah hakan bai hanasu Zarah murnar zuwansuba.
Su kalifa kam sai suka hau kumbure-kumburen baki wai basason wanan gidan hayaniya tayi yawa da ?auyawa.
Hakanne ya fusata Aunty Nafisa ta zubama kalifa mari har biyu ?warara, aiko ya zauna yana zaginta, Aunty Zulai tasa wayar caja ta zaneshi sosai, dama haushin yaran sukeji to>?#?
Wanan duka da akaima kalifa yasaka su Hassan nutsuwa waje Waya suka haWiye tasu rashin kunyar, shi dama Munner bashida matsala, kasancewarsa ?arami baikai sauran wayoba.
Zarah ce ta sanar musu Jiddah fa bata san halin da ake cikiba, Uncle yahya ya hana a sanar mata.
Numfashi Aunty Sauda ta sauke tana faWin,  Nidai a ganina yakamata ta sani, dan gaskiya Abba yanajin jiki, mubama Uncle shawarar ya sanarma koda mijintane koya kukace? .
 Wanan shawarar taki tayi aunty Saudah wlhy . Cewar aunty Nafisa dake bama yaron aunty hannatu akamu.
Sun yanke shawarar masa magana da safe idan sunje asibiti.


('('('('('('('('('('('

Yau Jiddah cikin Woki take Aliyu zai koma wajen Maimunatu. Dan kwanakinta goma sun cika harda kwana shidan da maimuna ta ?ara musu. Dukda ba takurata yakeba itadai sotake ya koma can.
Su kaWaima sukai hirar dare yau, danshi tunda safe yay tafiya shida malam dawasu malaman yin wa'azi jihar katsina.
Har sukai sallama Jiddah tatafi sashenta bai shigoba.
Saida tagama shirin barci tana ?o?arin kwanciya taji bugun ?ofa da sassanyar muryarsa yana kiran sunanta.
Hijjab ta saka tazo ta buWe masa ?ofar falon.
TaWanyi mamakin ganinsa da jallabiya, kenanma harya dawo yay wanka, haka kawai saitaji wani iri a zuciyarta, ya dawo amma ba'a sanar mataba balle tafito masa sannu da zuw.......
Numfashi ta sauke saboda jinta a jikinsa, cikin kunnenta ya raWa mata  Yadai Jiddatulkhair? Ko bakiyi kewata baneba? .
 Humm nayi mana .
 Shine kika?i zuwa tarbata? .
Shiru tai bata bashi amsaba, hakan yasakashi Wago kanta yana kallon fuskarta data canja alamar damuwa.
 Mike faruwa? Naga kamar ranki a Sace .
 Babu komai tai maganar tanason janye jikinta daga nasa.
Rikota yayi da?yau, yajata zuwa saman kujera, saida ya zauna sanan ya Worata a cinyarsa.
 Mike faruwa? FaWamin kinji Habibty .
 Nifa nace babu komai .
 Uhm-uhm ban yardaba wlhy Jiddah, karkiga ban daWe da saninkiba kiyi tunanin ban fara fahimtar halayyarkiba, wani abun akai miki .
 Ba aimin komaibafa ni, Amma shine ka dawo bamsaniba har saida ka daWe, bayan tun Wazun muna dakon zaman jiran dawowarka tare da auntyn .
Murmushine ya ?wace masa babu shiri, wato duk yanda mace take baka rabata da kishi, wanan jinin jikinsune, rungumeta yay sosai yana faWin  To amin Afuwa amarsu, nayi tunanin kar in takurakine, dan kina baro sashen auntynki babu daWewa ina shigowa .
Yin?urawa tai zata tashi yay saurin maidota a cinyarsan, zatayi magana ya Wora bakinsa kan nata.....=?J?

Ajiyar zuciya taita saki bayan ya saketa, uffan bata iya cemasaba har ya kawota Waki ya kwantar, saida yay mata addu'a ya tofeta sanan yashiga mata tausa a hankali.
Luf tayi tamkar tayi barci, hakanne yasaka Aliyu barinta, ya kashe mata fitila sanan ya fita tareda ja mata ?ofar.
Yana fita hawayen da batasan dalilinsuba suka ziraro mata, itadai tasan tayi murna dazaije can ya kwana, dan itadai takura takeyi da kwanciyarsu a gado Waya, amma batasan dalilin dayasa wani sashen zuciyarta yakejin Waciba, komi hakan yake nufi oho?.
Ta daWe batayi barciba tanata juye-juye, sai can tsakkiyar dare barci Sarawo yay awon gaba da ita.

&&&&&&&

Da asuba lokacin daya le?o tashinta salla harta tashi, tana zaune a bakin gado tana addu'ar tashi daga barci ya shigo. Kallo Waya taimasa tai ?asa da idonta tana gyara wuyan rigarta take a buWe sosai.
baice da ita komaiba ya juya ya fita, ta Wanbi bayansa da kallo harya Sacema ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tami?e zuwa bayi Wauro alwala............
'


_Masoyan Abba zakari Amin afuwa fa, babu ruwana Al?aline=?J??&
@&?&
@&?&
@&>?#?_.


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*?AURIN ?OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ?ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ?AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA?UMI..!* (Bilyn Abdull)

=?G?
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi? daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN? ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*>??????


*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?O? [12/29/2019, 1:44 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[57?'58]_*


.............Ciwon dake ?afarta ba shine matsalarta ba, hankalinta naga kuWin hannun ?aninta, gashi bataga alamun wayarta na tare da itabama........
Umma ta katse mata tunani da faWin,  Maman Hussain ki daure kici abincin nan, ciwo bayason zama da yuwafa .
Hajia hindu ta Wan sauke numfashi, ta ?asan ido ta harari Umma kafin ta yatsine fuska,  Zanci Maman Nafisa, abincinne gaba Waya bayamin daWima ni wlhy .
Umma taWan murmusa, saboda tasan ba?a hajia hindu ta faWa mata. Abba ma na jinsu, sai dai babu bakin magana, a zuciyarsa kam babu abinda yake jinjinawa sai ?ya?y?yawar zuciyar Umma, wai ita wace irin mutumce mai maida sharri da alkairi?. Bashida mai bashi wannan amsar, sai hawayen da suka gangaro masa ta gefen ido wanda su Umma basu gsniba. Shi kansa baisan dalilin zubarsuba, zafin ciwone? tausayin kansane? Kokuwa nadamace?, shidai yasan har yanzu baiji a ransa ya aikata badaidaiba gasu Umma, yanzu da ace ?a?ansane maza sukazo a manya da ?asar waje za'a kaisama jiyyarnan.........

Shigowar Uncle yahya ce ta katse tunanin Abba, tare yake da mijin Aunty Nafisa, saisu Aunty Zulai dake a bayansa suduka harsu kalifa.
Da gudu su Hassan suka nufi uwarsu, Maneer ne kawai yaje wajen Abba yana faWin  Abbanmu bakada lafiya? Miya sameka? .
Ummace ta janye Muneer ganin zai fara kuka, Abba ya janye idonsa daga Muneer da Umma ya maida kansu Kalifa da ko sau Waya basu kalli inda yakeba, sun zagaye uwarsu suna faWa mata ?arya da gaskiya da akai musu a gidan Umma. Tuni ita kuwa launin fuskarta yagama canjawa...
Tsawa Uncle yahya ya dakamusu, kafin ya zubamusu da??uwa da faWin,  Kunci gidanku, toku su wanene da idan kukai laifi baza'a hukuntakuba?, waWannan ba yayyenku baneba?, ko Walida ce ta tsawatar muku ba dole kujiba balle Zulaiha da Nafisa, duk wanda na ?arajin bakinsa saina zanesa a asibitinnan, gida kam ai dole kuzauna tunda bakuda kamarsa yanzu. Kekuma maman kalifa kin zauna saurarensu bazaki ko tsawatar musuba .
Cikin Kumbura fusaka tace,  Yo yahya minene abin tsawatarwa anan?, daba a cuta musuba zasu faWane .
Tsit gurin yay duk suna kallonta, Abba ne kawai yaji daWin abinda tayi a ransa, danshima yaji haushin an dokar masa ?an lelensa, saidai babu bakin magana.
Daganan babu wanda yakuma tofa baki acikin lamarin su kalifa, anan suka yini a asibitin har yamma li?is sanan Uncle yahya yace su koma gida.
Hajia hindu naji na gani Uncle yahya ya kora su kalifa daketa ?un?unai su bazasu komaba, wai tuwo da koko da shinkafa kawai akeci a gidan, sukuma basu iya ciba (hhhhh ?a?an turawa=?9?).
Ko kallonsu Uncle yahya baiyiba, danshi dariyama suke bashi wlhy.
Su Aunty Saudah suka tuntuSi Uncle yahya akan batun faWama Jiddah, murmushi yayi,  Karku damu zata sani, amma sonike sai zuwa kamar jibi haka, duka yaushe taje gidan mijin da za'a sakata fitowa?, sonake sai zuwa jibi ta cika sati biyu insha ALLAH, suma zuwa sanan sun fara samun sau?i, kunsan Jiddah da ruWiya, kuma zuwanta bashine zai basu lafiyaba ai .
Sun amsa da to, tareda gamsuwa da maganarsa.

('('('('('('('('('('('

*_Bayan kwana biyu_*

Har zuwa yau Jiddah batasan mike faruwaba, kuma tana waya da Umma da Uncle yahya, hakama aunty Nafisa, babu kuma wanda ya faWa mata.
Yauma dai haka ta yini ita kaWai a sashenta, saboda zuwan da Amina da Hassana sukayi gidan, sanda sukazo tana sashen Maimuna suna kallon wani tafseer Win Sheikh Aliy, amma tundaga shigowarsu jikinta yay sanyi, dan wani kallon banza sukaita binta dashi, koda ta gaidasu babu wanda ya amsa saida Maimuna tace Auntys jiddah nafa gaisheku. Duk a yatsine sukace  oh ALLAH sarki, bamuji bane .
Jiddah bata gazaba takuma maimaita musu gaisuwa, lokacin ita Maimunatu taje kicin kawo musu ruwa, tsaki sukayi mata basu amsaba, hakanne ya sakata mi?ewa tabaro sashen ta dawo nata jikinta sanyi ?alau da tunanin sukuma su wanene? Tagadai Waya na bala'in kama da Maimunatu (Hassana). Koda ta dawo sashenta sai abin yakuma ?untata zuciyarta, tana cikin tunani a falo saigasu sun shigo Maimuna ta rakosu wai zasuga Waki, dan ita maimuna batasan abinda suka kuma yima Jiddah ba.
Jiddah ta saki fuska takuma tarbarsu da mutuntawa a nan ma, babu inda basu shigaba, amma sai wani yatsine fuska suke, komai suka gani sai Amina tace,  Aunty Hassana nikam ba wanan abun bane ranar muka taya a wajen ?an gwangwan Wincan dubu uku? .
 Shinefa ?ar uwa, kinma manta dubu biyu suka barmana daga baya .
 Hakanefa wlhy, nama manta .
Gadajen Jiddah ma da kujerunta haka sukaita musu iskanci, wai Hassana taje kasuwa akace za'ai mata a dubu arba'in, amma tace basuyi mataba tawuce nan.
Ran Maimunatu ya Saci sosai, dan haka taja hannun aunty hassana suka fice, amma saita fisge tana mata masifa.
Acan kuma Amina nata gaggasama Jiddah magana ta rashin mutunci, itadai jiddah batace mata komaiba, saima kanta data du?ar a ?asa tana wasa da yatsun hannunta, har Amina tayi tagama ta fice sanan ta Wago tana kallon ?ofa hawaye na ziraro mata, ta daWe a falon tana kuka kafin ta koma bedroom ta kwanta, ganin zata ?untata kanta da yawa ta kunna karatun Al-Qur'ani tana saurara, a haka barci ya kwasheta.
Sai da Maimuna tazo kawo mata Wanwake da tamusu na ranane ta tadata dan har anyi salla ma.
Sannu tamata da godiya, Maimuna tafita saboda su Amina basu tafiba, da zama ta kawo mata abincinan da hanawa sukayi sunata mata masifa, sai da tace wlhy zata kira Malam ta sanar masa kafin shima Aliyu ya dawo ta faWa masa, sannan ne suka bata hanya suna zaginta wai baiwar kishiya. Itadai batabi takansuba ta fito kawoma Jiddah abincin.

Har yamma lis su Hassana suna gidan, sai bayan la'asar ne suka tafi, jiddah najin tafiyarsu saboda dariyar da sukeyi suna sakin magana a kanta, amma sai ta?i fita, dan duk zuciya nason mai ?yautata mata.
Maimuna sashenta ta koma, duk zuciyarta babu daWi itama, dolene tasaka a takama su Aunty Amina birki akan zuwa gidan, dan itadai baza'azo a haWa mata fitina a gidan aurenta ba, suna zaune lafiya a Sata musu zama, badan Jiddar tanada hankaliba da biyema su Aunty Hassana zatayi sosai, dan ba kowa zai yarda da wannan cin kashinba, jitai Jiddah takuma birgeta, sai dai yanzu tsoronta karta faWama Aliyu abinda ya faru ne.


('('('('('('('('('('('

Alhmdllh jikin Abba yaWanyi sau?i, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai daifa yanashan azamar ?afa da ?ugu, wanima tashin hankali shine Worin karayar ?ugunsa bata Woruba, likitoci sukace sai an sake, ankumayi yau da safe yaci azaba iya iyawa amma ba'a daceba, shine Uncle yahya ya yanke shawarar kiran wani na gargajiya, dan haka yaro?i likitan akan su sallami Abba za'a canja masa asibiti, sunyi hakanne dan sunsan idan sukace na gargajiya za'a likitocin bazasu yardaba, shikuma tsoro yake kar goma ta lalace biyar bata gyaruba.
Sosai hajia hindu tayi murna da wanan sallama, dan itafa ba damuwarta Abba ba, hankalinta nakan kuWin data saka ?aninta yazo yay musu fashi. Kamar ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? nda Umma da Uncle yahya suka yanke shawara haka akayi, kai tsaye gidansu Umma aka wuce dasu Abba, Wakin dake soro Uncle yahya yasaka aka hudo ?ofa ta cikin gida tun jiya, ita kuma hajia hindu aka kwashe kayansu Zarah daga Wakinsu aka gyara mata.
Su aunty sauda duk basuso hakaba, dan yanzu dai ba gidan Abba baneba na Jiddah ne, saida Umma taita tausarsu sannan suka bar zancen.
Sosai hankalin hajia hindu ya tashi, wai ana nufin wanan gidan data bari tsawon shekara sha shida dawasu watannine za'ace ta dawo da zama?, wanan ai ci bayane, dolene ta nemo ?aninta a yau yakawo kuWin nan tanemi ?aramin gida tasai musu itada ?a?anta, shiko Abba yazauna nan yayi jiyya, idan ya warke ya nemesu.
Abba kam yana cikin azabar ciwo, bayama tantance a ina yake balle asan sirrin ransa
Gidan dai yamusu kaWan sosai, amma haka sukai maleji, da daddare wasu sukaje gidan Uncle yahya suka kwana.
Su kalifa kam abufa ya damesu, sai kuka sukema hajia hindu basa son wanan gidan, sudai akoma gidansu. Hajia hindu saita sake rikicewa, dan ita kaWai yaran suke addaba, basayi gaban su Uncle yahya.
Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon Wori ya sakema Abba a ?ugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban ?a?an nata dukda tsiyatakun daya shuka mata.
An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta.
 Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho? .
aunty Zulai dake sharo Wakin Umma tace,  Eh Uncle tana nan Wakinta a jar jaka .
 yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na ro?i alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za'a iya lode waWan nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani kaWai muka bari, acikin kuWinne ma akabama mai gyaranan kuWinsa, dan wlhy nidai kuWin dake wajena sun ?are, a jiyama saida na taSa kuWin sadakin jiddah dubu ashirin aka Wako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda kuWin cigaba da biyan kuWin gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya ?o?ari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi .
A Wage hajia hindu ta amsa da  Uhhum . Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga kuWinan.
Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login