Showing 15001 words to 18000 words out of 124968 words

Chapter 6 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5501

da iyakarta islamiyyar anguwarsu, a yanzu haka kuma sune ke a aji shida fanin y'an Mata. Tunda Jiddah ta shigo makarantar take samun nasarori, kwakwalwarta takuma bud'ewa, dan ayanzu haka babu wani Kalmar larabci dazata layance mata, a littatafai kuwa Na fannin Addini tuni tayi babbar zarrah, 6an garan Qur'an tadad'e dayin sauka tana akan hadda. Kai bama itaba dukkan Wanda kagani a ajin su Jiddah to kwarone a makarantar, makarantace daduk Wanda yake cikinta lallai ya kwankwad'i ilimi ya k'oshi, dan ana tatosune daga wasu k'ananun makarantu Ana kawosu nan, babu ruwan wannan makaranta dakai d'an wanene?, duk Wanda kagani kaifin kwakwalwace ta kawoshi.
Kamar yanda dokar makarantar take duk Wanda ka iske a aji dolene kayi sallama, Na ciki su amsa maka, sannan kabisu d'ai-d'ai kabasu hannu kuyi musabaha>?? Yanzuma hakace ta kasance ga Jiddah, bayan tayi sallama duk suka amsa, ta yaye nik'ab d'inta tanabinsu d'ai-d'ai suna gaisawa cikin musabaha da murmushi shinfid'e akan fuskarta, saida takai har k'arshe sannan tadawo mazauninta Na gaba ta zauna kusa da Madeena Isma'il da kusan itace k'awarta da suke mutunci sosai a makarantar.
Murmushi sukaima juna bayan sun kuma kama hannun juna suna gaisawa.
 Ukti yau naga kin iso da wuri? .
Jiddah tace,  ki Bari kawai ukti, yau dai naji fad'anki banyo tafiyar k'asaba .
 To Alhamdllh da farajin maganata .
Y'ar dariya sukayi a tare, wadda shigowar malam Mustafa ta katsesu. Duk suka mik'e suna gaisheshi kafin yabasu izinin zama.
Jawabin daya kawoshi ya fara musu, danshi ba koyar dasu yakeba, shine Vice principal na makaranta.
 Umm Assalamu alikum, nasan zakuyi mamakin ganina a wannan lokacin, wani uzirine ya tasomana Na gaggawa, an gayyaci wannan makarantar cikin jerin taron k'arama juna sani Na k'asashe goma da aka shiryama d'alibai, taron kuma zai gudana ne a sati mai zuwa, insha ALLAH zamu za6i d'alibai biyarne kacal, wannan ajin shine Na manya idan aka cire ajin matan aure, dan haka mun yanke shawarar d'aukar d'alibai biyu a cikinku, insha ALLAH malam Usman zaizo anjima ya za6i wad'anda zasu jagoranci tafiyar amma ta hanyar rubuta jarabawa, daganan zuwa awa d'aya kunada damar yin nazari, zamu dakatar da malamai yau gaba d'aya daga kowanne darasi .
Atare ajin ya d'auki kabbarar *ALLAHU AKBAR!!!*.
Malam mustafa yay musu sallama ya fita.
Nanfa kowacce tashiga duba littatafanta da fatan dacewa.


('('('('('('('('('('('

Abba kam yana isa katafaren gidansa ya iske su kalifa tsaitsaye a harabar gidan suna jiransa. Babu Wanda ya gaidashi, saima tunzura masa baki da suka shigayi wai sunyi fushi.
Fuskarsa cike da fara'a ya hau fad'in  O shalelen Abba amin afuwa kunji, maza kushiga mota Na kaiku karku makara, Abba yayi laifi ayi hak'uri .
Cikin tura baki Hassan yace,  Amma Abba tunfa d'azu muke jiranka, kabarmu dukmun bushe a tsaye .
 Ai nace ayi hak'uri ko Hassan, Muneer taho kaji . Yak'are maganar yana Kama hannun autansu Muneer.
Kalifa kuwa da Hussain uffan basuceba, shi kalifa ma iyafis ya saka a kunne, Hussain kam yayi cid'in-cid'in da fuska yana wani shan k'amshi.
Ko'a mota Muneer ne kawai ke fira da Abba, amma Hussain da kalifa da Hassan tamkarma babusu a motar.
Ya diresu a makarantarsu mai tsananin k'yau ta y'ay'an manya y'an gata, ya zaro dubu d'aya yabama Kalifa, babu ko godiya yay wucewarsa aji, Hussain da Hassan kuma d'ari biyar?, suma dai babu godiyar, amma sun d'aga masa hannu alamar bye.
Munner ne aka bama d'ari biyu dukda an shiryo masa abinci a lunch box nashi kuwa.
Kalifa ajinsa uku 6angaren sakandire, Hussain da Hassan su kuma aji biyu, Munner kuwa yana firamare 5 ne.
Saida Abba ya raka Munner har sashen y'an firamare sannan yashiga motarsa ya fito daga makarantar................
'


Kuyi manage please=??=?L?

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? [11/21/2019, 2:43 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[7.....]_*


..............Kamar yanda malam Mustafa ya fad'a bayan awa d'aya malamin da zaima su jiddah jarabawa ya shigo, sallama yay suka amsa masa tare da gaisheshi.
Ajin yayi shiru kowa yana kallon malam Sulaiman, yad'an tura hularsa baya yana shafa gaban goshinsa da nazarinsu, saikuma yay murmushi ganin duk sunyi tsuru-tsuru sun zuba masa idanu. Zama yay inda aka tanada domin zaman malamai kafin ya kuma maida hankalinsa Kansu.
 Inaga nama canja shawara kawai, zanyi jarabawar da baki .
Kallon kallo aka komayi tsakanin su Jiddah, kowanne a sanyaye ya amsa da,
 Na'am ya mu'allim .
Fita malam Sulaiman yayi, babu jimawa ya dawo shida Malam Shu'aibu da malam mika'il. Nanma su Jiddah gaidasu sukayi. Malam Sulaiman yabasu izinin fita waje su duka, zuwa wajen wata bishiyar dake gaban aji. Ahaka zasu ringa zuwa d'aya bayan d'aya.
Da yawansu sun rikice, dan kowa baisan miza'a tambayeshiba, ga malam Sulaiman gwanine wajen iya zak'ulo tambaya.
Amirar ajin mai suna Shamsiyya jamilu yasaka ta rubuto sunayen kaf y'an ajin tazo saman baranda tana kiransu d'aya bayan d'aya. Hakan kuwa tafaru, bayan tagama rubuta sunan kowa aka Fara, gaba d'ayansu dama su 38 ne a ajin, dan haka aka fara komai a tsanake. Kowa ya fito saikaga yana mazurai, nanfa cikin Jiddah Yakuma d'urar ruwa, (dama ita kwai tsoro) saima Madina ce ked'an k'arfafa Mata gwiwa. Tunda aka kira Bilkisu Ahmad Jiddah takuma tsurewa, dan daga bilkisun sai madina sai ita. Bayan fitowar bilkisu aka kira Madina daga nan sai Jiddah, tamkar wadda k'wai ya fashewa a ciki haka ta shiga ajin, inda kowa ke zama idan ya shigo ta zauna itama.
Malam Sulaiman dake kallonta ya karanto mata tambaya,
* Malama Jiddah ko zaki iya fad'a mana Kalmar shahada da Manarta? *.
Dak'yar Jiddah ta iya had'iye yawu, k'asan zuciyarta tana addu'ar Neman nasarar yin bayani cikin nutsuwa, zamanta tad'an gyara cikin sanyinta tace,

*_ SHAIDAWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH , KUMA MUHAMMADU MANZON ALLAH NE _*
_Wad'an nan kalmomin shahada guda biyu, sune kofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka k'unsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
*_MA'ANAR KALMAR SHAHADA_*

_Ma anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma anarta, da kuma yin aiki da abin da tak'unsa, zahiri da bad'ini, malamai sun had'u akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma anarta ko yin aiki da abin da ta k'unsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kad'ai matsarkaki mad'aukaki._

Rukunan wannan kalmar (shahada) sune (korewa da tabbatarwa), wato kore hak'k'in bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kad'ai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta
K'unshi kafircewa d'agutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Mad'aukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha awa), da nuna masa k'iyayya da yin kubuta daga gare shi.Wanda ya fad'i wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta

musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai fad'eta
ba.
ALLAH Mad'aukaki sarki ya ce:


 Kuma abin bautarku abin bauta ne guda d'aya. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Mai

rahama Mai jink'ai .(Bak'ara: 163).

Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:


 Babu tilastawa game da (shiga) addinin

(musulunci), hak'ik'a shiriya ta bayyana daga 6ata, saboda haka wanda ya kafirce wa d'agutu kuma ya yi

imani da ALLAH, to hak'ik'a ya rik'i igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masani
ne . (Bak'ara: 256).

Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya kudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko Wanda yake da ikon kirkira, kuma ya kudurci cewa yin imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kad'aita
ALLAH da ibada ba, to hak'ik'a fad'in kalmar (La Ilaha illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shiba daga azaba madawwamiya.

ALLAH Mad'aukaki ya ce:

 Ka ce (da su):  Wane ne yake arzutaku daga

sama da k'asa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al amura? To za su ce:  ALLAH ne . To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba? (Yunus: 31).

ALLAH Mad'aukaki ya ce:


 Ko wane ne ya halicci sammai da k'assai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki masu k'ayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare
da ALLAH, A a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya) .(Naml: 60).
Kuma ALLAH Mad'aukaki ya ce:

 Kuma lallai idan ka tambayesu,  Wane ne ya halicce su?, Lallai za su ce:  ALLAH ne To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)? (Zukhruf: 87) . Jiddah ta k'are jawabinta cikin sauke numfashi da ajiyar zuciya.

 ALLAHU Akbar . malam uku suka had'a baki wajen ambata. yayinda jiddah keta addu'ar dacewa da tsoron yin kuskure.
Malam mika'il yace,  zaki iya tafiya .
Kamar an bige mata gwiwoyi haka ta mik'e ta fito, a bakin barandar ta zauna kamar yanda su madina sukayi. Murya k'asa-k'asa madina tace,  Ukti mi aka tambayeki? .
Jiddah tai murmushi cikin sanyinta tace,  Ma'anar Kalmar shahada. Kefa? ,
 Ni sharud'd'an Kalmar tauhidi guda biyar. Amma wlhy duk saina rud'e ukti .
 Bake kad'aiba ALLAH, har yanzu ni kaina gabana baibar fad'uwaba . Cewar Jiddah tana kar6ar ruwan da madina ta mik'a mata. Sosai tasha ruwan harta d'an samu nutsuwa. Suna zaune a wajen suna d'an ta6a hira har aka gamawa kowa suka koma aji. Bayan fitar malaman kowa ya shiga k'us-k'us da makwafcinsa a kan tambayar da akai masa. Da wannan suka cinye lokacin tashin.


('('('('('('('('('('('

Sai kusan 9:30am Malam Aliyu yasamu tashi, kansa yad'an rage ciwon amma yanayi k'asa-k'asa har yanzu.
Tashi yay bakinsa d'auke da addu'a, yayi mamakin barcin da yayi, a gaggauce ya mik'e yayo alwala domin gudanar da sallar walha kamar yanda ya Saba, yau barci yasashi zai makara. Koda ya idar d'akin ya kimtsa, ya d'auki filas d'insa Na tea ya fita zuwa cikin gidan dan Neman ruwan zafi. Ta k'ofar cikin gidansu yabi inda Kai tsaye zata kaishi sashen iyalan malam. Shiru gidan babu wata hayaniya, Kai tsaye kicin ya nufa, nanma babu kowa dama baiyu tunanin samun kowanba, yana tsaye zuciyarsa Na tunani d'aura ruwan zafin sai yaji motsi a bayansa.
Waigawa yay da mamakin wanene?.
Maimuna dake bayansa tsaye ta saki murmushin basarwa tana fad'in  Yaya Aliyu ina kwana? mikake buk'ata ne? .
Batare da yayi magana ba ya nuna mata filas d'in daya ajiye.
K'arasowa tayi ciki kicin d'in  Kaje Yaya bara Na dafa maka, asaka kayan k'amshi .
 Eh ki saka, amma miya hanaki zuwa makaranta? .
 Uhm... Uhm wlhy Yaya ciwon.......
Saikuma tayi shiru ta kasa k'arawa.
Kad'an ya kalleta ya d'auke kansa, can k'asan mak'oshi yace,  Ba dole kuyi ciwon maraba kullum kunacin zak'i, yakamata kafin sati d'aya da zuwan jini ku ringa d'agama duk wani Abu mai zak'i k'afa, Ku kuma yawaita amfani da ruwan zafi yayin da yazo....
Yana gama fad'a ya wuce abinsa tamkar bashi yayi maganarba. Ita kanta Maimuna da kallo ta bishi baki bud'e, sum-sum dashi sai zaro magana, komai girmanta babu ruwansa shi, to ita yaushema tace masa ciwon mara takeyi?  Kai Yaya Aliyun nan ni wlhy harma yaban kunya, a inama yasan Mata na ciwon Mara dalilin period=?H?? . Ta k'are maganar da rufe ido.
Shikam gogan naku ko'a jikinsa, hankalinsa kwance ya koma 6angarensu yashiga wanka.

Koda Maimuna tagama dafa ruwan batai gigin d'auka takai masaba, a kicin d'in ta barsa, dan basa Shiga sashen samarin gidan kwata-kwata.

Koda ya fito saiya koma cikin gida ya d'akko filas d'insa, yana shirin fita Maimuna ta shigo kicin d'in hannunta d'auke da kula madaidaiciya.
Kanta a k'asa tace,  yaya gashi inji iya ..
Baice komaiba, yadai mik'a hannu ya amsa yay ficewarsa, saida yafita sosai sannan yace,  kice Mata nagode .
Maimuna ta girgiza kai tana fad'in  ALLAH ya k'yauta, shidai kullum baki 6am, idan kaji yana dogon bayani sai a tafseer ko k'arin karatu kokuma shida Malam .
bakuma dan baya maganarba, danshi ba miskili baneba, kawai dai fahimtace bataiba, dan itad'ince baya sakewa da ita, dadukma macenda ba muharramarsa ba, muharamman nasama taka tsantsan yake dasu, sannan shi ba'a surutun banza dashi Mara ma'ana.

Baimasan tanaiba, dan shi tuni yaje d'akinsa. Tea ya had'a babu madara, sai wasu abubuwa daya zuba wad'anda suka saka turirin shayin fita da wani k'amshi mai dad'i da saka kwad'ayin shan shayin. Saida ya bud'e kular da Maimuna ta bashi yaga fankasune sai miya a robar kular tanata tashin k'amshi, maidawa yayi ya rufe, saida ya shanye shayinsa daya had'a sannan yafara cin fankasun a tsanake.
Bayan kammala cin abincinsa daduk wani uzirinsa yay shiri cikin shadda ruwan makuba mai duhu, d'as taimasa k'yau daka gansa kaga cikakken d'an Arewa, yad'au hularsa Zanna bukar kalar shaddar ya saka. Kafin kace me d'akin ya gauraye da wani mayatacen k'amshi mai sanyaya zuciya da sakata nishad'i.

Tunda ya fito aketa gaishesa a k'ofar gidan, yayinda shikuma yake gaida dattijan da suka girmesa, tuni wani saurayi yazo ya kar6i littatafan hannunsa, agogonsa ya kalla, dan yanason shiga wajen malam kafin ya wuce inda zaije, ganin sha d'aya saura saiya nufi cikin soron, dan yasan malam ya fito yanzu, a zauren farko ya iskeshi shida wasu mutane guda biyu a rukunin kujerun da'aka shirya tamkar falo acan gefen soron kasancewar babba, annan malam ke karatu da d'alibansa dakuma ganawa da b'aki.
Sallamar Aliyu ya sakasu amsawa a tare suka juyo suna kallansa, ya cire takalminsa a gefen kafet d'in kafin yak'arasa shiga rukunin kujerun, hannu ya mik'ama bak'in malam sukayi musabaha, sannan yaje gaban malam ya risina yana gaisheshi cikin mik'a masa hannu sukai musabaha (malam bai amince d'ansa yak'i samun ladan musabaha da shiba, shiyyasa kozai gaisa da yaransa suma yakanyi musabaha dasu tamkar kowa, hakama matansa).
 Ya ciwon kan Ali? .
 Alhmdllh baba . Aliyu yafad'a yana d'an murmushi kafin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login