Showing 24001 words to 27000 words out of 124968 words

Chapter 9 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5502

dake gargad'i, saikaji muryarta Na rawa alamar tahowar kuka, har sai tasaka handkerchief d'in hannunta ta share idonta. Dad'in sautin muryar tama ya hana a dakatar da ita, saida takai aya ta 68 sannan malam yasamu damar dakatar da ita, yayinda hawaye masu d'umi suka wanke fudakarta, handkerchief tasa tana tsanewa kanta a k'asa, yayinda shashshekar kukanta ke fita a hankali daga cikin lasifikan.
Guri fa yayi tsit babu Mai kwakwkwaran motsi, dan kukan Jiddah ya raunana zukatan jama'a da yawa, ita kanta batasan miya k'arfafa kukan nataba ma, bayaninma da kowa keyi Na mintuna biyar ita sai hak'ura akai aka barta.
Malam Abdul-ra'uff Kama sai ajiyar zuciya yake saukewa yana k'arabin Jiddah da kallo, yayinda ransa ke hamdala da samun irin wad'annan y'ay'a acikin al'ummar musulmai.

Malamin dake kiran sunayensu yay gyaran murya yana fad'in,
E'4'  'DDG  'DE9DE  ,/)  GJ 'D7'&A) 'DE3DE) 'D*J J-*',G' 'DE3DEHF  DB/ ('1C 'DDG -J'*C.
?????#GF& H'D/JC 9DI 'D-5HD 9DI 'DH69 'D1'GF  HG0' ('DF3() DF'  AJ CD E1) *B1# AJG' 'DB1"F H*B1#G (/EC HE9F'G HE' J*-/+ 9FG  (CD 71B 'D.HA EF 'DDG H BH) 'D%JE'F 3*C+1 #J6' AJ BDH(F'. C'F 'D#E1 CE' DH CF' B/ 3DEF' 7AD ,/) AJ 1-E 7ADG'.
 Masha ALLAH malama Jiddah, irinku sune al'ummar musulmi da musulinci ke buk'ata, ALLAH ya albarkaci rayuwarki. ina taya iyayenki farin ciki da samunki matsayin d'iya, wannan wa'azine a garemu, yanada k'yau idan kana karanta alk'ur'ani karingajinsa har cikin jininka, ma'anarsa da abinda yake magana akai, ta wannan hanyarne tsoron ALLAH da k'arfin imani zai kuma yalwatuwa a zukatanmu. kamar dai yanda mukaga malama Jiddah zakari yaro ta tsinci kanta a ciki yanzu .
 Kuma sauran d'alibanmu ALLAH ya albarkaci rayuwarku gaba d'aya .
A take wajen ya d'auki kabbara ta d'alibai da ambaton Amin.
Dad'i ya kama Uncle yahaya sosai, sai nanata godiyar ALLAH yake a zuciyarsa, da takaicin d'an uwansa daya gaza fahimtar baiwa da ni'imar da ALLAH yay masa ta samun wad'anan yara.
Jiddah kam wajen zamanta takoma ta zauna tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.
Abubuwa masu muhimmanci sun cigaba da gudana har zuwa k'arfe 3:40pm, lokacinne kuma taro ya tashi lafiya, cikeda addu'oi ga d'alibai da iyayensu.


*washe Gari*
Washe gari kam an gudanar da lecture ne, wadda gaba d'ayanta malam Abdul-ra'uff maina ne yayita, sosai tsohon ya birge Jiddah, jitake inama ita jininsace. Bayan kammala lecture d'in malam aka bada k'yauta gasu Jiddah, wadda cikin amincin Ubangiji tasamu babbar k'yauta da saka sunanata a jerin d'alibai uku da za'a tantance su wakilci Nageria musabak'a dazata gudana a k'asar saudia ta y'an shekaru 20 zuwa k'asa.
Wannan Abu bak'aramin farin ciki yasaka malam Abdul-ra'uff maina ba, ganin d'aya daga cikin d'aliban yankinsa kuma yarensa tasamu wannan dama.
Yayinda Jiddah ke gudanar da godiyarta ga ALLAH da jigogin wannan taro sai kuka ya sark'e.
Malam Abdul-ra'uff yay murmushi yana ambatar  sarkin kuka kenan akan la66ansa, shi kansa malam mustafa murmushi yayi, yayinda uncle yahaya idonsa yacika da hawaye, dan shikam ya fahimci kukan Jiddah da biyune.
Yau kam antashi karfe 1pm, yayinda manyan bak'i sukayi haramar tafiya.
Sukuma su Jiddah sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai..............
'

https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

Zaku iya samun Raina Kama a audio ta wannan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel=??=?L?

*_Larabawa Idan kunga kuskure alarabcina please azo amin gyara, kar a sakamin Ido nacigaba da tafka kuskure, kai adukama littafin, dan maganar addini tawuce gaban wasa, bilyn taku ajizace tana kuskure, dan Allah Da anga Na sauka alayi ayi azamar tunatar dani=?O?



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [11/25/2019, 11:08 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??

*_[10...]_*


..............Baje suke a falo su Kalil Na homework, yayinda Abba ke kallon labarai, hajia Hindu kam Ana zaune gefe ankashe kan d'auri Ana latsa waya da d'ora lemo.
 Lah Abba wannan tana Kama da Jiddahn gidan Umman gwammaja . Hussain yafad'a idonsa a TV shima.
Ware ido sosai Abba ya kumayi, itama hajia hindu dasu kalifa duk suka kalli TV.
Wata Y'ar zabura Abba yayi dan mamaki, tabbas wannan Jiddah ce y'arsa, wato dayace kartaje saida taje kenan?. Baikai k'arshen tunaninsaba aka wuce rahoton taron dasu Jiddah sukayi.
Hajia Hindu cikin ta6e baki tace,  Itace kuwa Hussain, anje nunamana su masu addinine ko, ai tsoron ALLAH a zuci yake dai .
Dariya Kalifa yay suna tafawa da Hassan tareda fad'in  Tab d'i, su ustaziya kenan .
Dariya duk yaran sukayi har hajia Hindu, amma banda Abba da Munner dayay barci. Abba kam ransane a 6ace wai jiddah batabi Umarninsa ba, da ace dare baiyiba da yanzu sai yaje ya saukema Umma ta cikinsa kafin jiddah ta dawo yaci Ubanta.


Humm=ض? @&=??.


('('('('('('('('('('('

Su Umma dai basusan wainar da ake toyawa ba, dansu ba kayan kallon ke garesuba, sai yau da yamma saiga Sadiq da majeed sunzo gidan (yaran uncle yahaya).
Da fara'a Umma ta taresu, hakama su Jiddah, walida da Sadiq Kansu d'aya, dan shekarunsu kusan d'ayane, dan haka take kiransa Hussain, shikuma yace bai yardaba itace Hussaina shine hassan.
Yauma tanajin sallamarsu da gaida Umma tafito daga d'akinsu tana fad'in  Oyoyo Hussain d'ina ,
Hararta yayi cikin wasa shima yana fad'in  Hassan dai, Umma dan ALLAH ni da ita wanene babba? .
Dariya Zarah dake wankin Uniforms d'insu ta saka musu,  Umma dan ALLAH yaudai kiraba gardamar gayunnan, kokuma abari sai Yaya Jiddah tadawo sannan .
Da sauri majeed shima yace,  Eh abari sai Yaya Jiddah tadawo, dan karsu musama, kunga anyi gaban kowa kenan .
Umma dake dariyarta har yanzu tace,  ALLAH ya shiryaku dai .
A tare suka amsa da amin Ummanmu.
 Kunsan wane albishirma mukazo fad'a wannan k'anwar tawa ta katse mana hanzari? .
Umma da Zarah sukace, a'a saika fad'a. Yayinda Walida ta antayama Sadiq harara shima ya rama yana Mata gwalo.
Da sauri Majeed yace,  Umma wlhy an nuna Yaya Jiddah a TV jiya .
 Dan ALLAH da gaske? .  Zarah tafad'a tana saurin ajiye kayan datake cud'awa a hannunta .
Umma da walida ma a d'okance sukace da gaske majeed?.
 Wlhy kuwa Umma...........
Zama sukayi suna basu labari, farin ciki duk ya cika su Umma, harda hawayen dad'i suka cika mata idanu.
Anan su Majeed sukakai har dare, basu tafi gidaba har saida sukaci abinci.

Daga Umma harsu Walida kwana sukai mik'a godiyarsu ga Ubangiji ga wannan nasara da Jiddah tasamu. Fatansu ALLAH ya dawo musu da ita lafiya.



('('('('('('('('('('('

Tunda malam suka baro Abuja sai yarinya Mai kuka keta masa Kai kawo a zuciya, haka kawai yakejin farinciki da kasantuwarta Y'ar yankinsa kuma yarensa, dad'in dad'awa kuma gashi a makarantarsa take karatu, yana mamakin yama akai bai Santantaba, lallai dolene yayi bincike akan yarinyarnan, dan yana ganin zata dace da tunaninsa.....
Yad'anyi murmushi saboda hangota tana kuka, kokad'an ya Lura kuka baya Mata wahala saikace Aliyunsa. Shima abu kad'an ke tada masa hankali Yakama kuka tamkar wani mace, mutumne shi Mai yawan tausayi.
Malam Yakuma murmushi saboda jin k'arin k'a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?unar Aliyun Wanda jama'a ke kira magajinsa.
Har suka iso gida da tunanin Jiddah a ransa.


('('('('('('('('('('('

A yau k'arfe 12 su Jiddah suka baro cikin Abuja cikeda kewar k'awayensu d'alibai, dakuma murnar nasarar da suka dace da ita acan.
Gaba d'aya Jiddah cikin zumud'in son ganin y'an Uwanta take da Ummanta, saikace wadda ta shekara bata gida.
Sai kusan biyar Na yamma suka iso cikin kano, kaf d'aliban da iyayensu kowanne har gida aka kaishi, su Jiddah sune Na ukun saukewa a k'ofar gidansu.
Yau ko Addu'ar shiga gida bata tsaya yiba ta shiga gida da murna tana kwala kiran sunansu Zarah.
Ummace kawai a gidan, dan haka tafito daga d'aki itama cike da murna.
Jiddah ta ajiye kayan hannunta ta mak'alk'ale Ummansu tana sakin kukan farin ciki. Umma ma cikeda murna taimata kwakkwaran rik'o, a haka Uncle yahaya yashigo ya samesu yana waya. Murmushi kawai yayi yacigaba da amsa wayarsa.
Jiddah da suka saki juna da Umma tafara tambayar  Umma ina y'an uwana? .
 Yanzu zasu dawo, gidan indo sukaje siyo awara. Yanzu zaki gansunan, d'akkoma babanku tabarma mana ambarsa a tsaye.
'Dakin Umma Jiddah ta shiga ta d'akko tabarma ta shimfid'ama Uncle yahaya da har yanzu yake waya.
Walida da Zarah ne suka shigo da sallama, ganin Jiddah yasakadu ajiye kayan hannunsu suka mak'alk'aleta suna ihun murna. Tuni sun haukata gidan da hayaniya. Umma da Uncle daya gama waya sai dariya suke musu da mamakin wannan soyayya. Saida suka gama murnarsu kafin Umma da Uncle yahya su sami damar gaisawa, suma sukazo suna gaisheshi da masa sannu da zuwa.
Yayinda su Jiddah ke murnarsu Uncle yasami damar yima Umma bayanin komai daya faru, farincikine sosai ya kamata, tama rasa yanda zata musalta, video d'in dayayma Jiddah da waya ya kunna Mata tana gani, tuni hawaye sun wanke fuskarta, suma su Zarah suka amsa suka gani, jisuke tamkar su lashe Y'ar uwar tasu dan dad'i.
Da k'yar Uncle ya tsaya aka bud'e k'yautar da Jiddah ta samo, litattafaine da kud'i naira dubu Hamsin. Atake duk suka zaro idanu dan mamaki, Umma ta ajiyema Uncle kud'in duka a gabansa tace ya d'auka ita Jiddah tunda ga littatafai.
Murmushi yayi yana mamakin kawaici irinna yagana, ya mik'e yana fad'in  Lallai Maman Nafisa, to wannan tsarin naki kam baiyiba, jiddodo ALLAH ya huta gajiya ni nayi nan .
Duk magiyar da Umma kemasa bai sauraretaba ya fice abinsa.
Sabon shafin murna suka k'ara bud'ewa bayan fitar Uncle. Walida Na had'a wutar gawayin da zasu soya awara, Zarah kuma Na yankan su albasa da kabeji, Jiddah dake kusa da Umma zaune tanata basu labarin komai daya faru a wajen.
Haka suka kasance a wannan dare cikin firar yaushe gamo, yayinda sukaci awaransu sukayi nak.


=? ?=? ?=?+?nima zanci awara dan ALLAH.


Washe Gari tunda safe saiga Abba a gidan, Walida da Zarah na shirin tafiya makaranta, yayinda Jiddah ke gaban rijiya zaune zatayi wankin kayansu.
Duk tsit sukayi daga dariyar da sukeyi saboda shogowarsa, hakan yasaka Umma dake falo fad'in  Su auta suntafine naji gidan tsit? .
 A'a Umma .  Zarah tafad'a a hankali kamar munafuka .
Fitowa Umma tayi, saitaci karo da Abba dake tsaye tamkar tsohon soja, sai harare-harare yakeyi. Tuni Umma ta had'e fuska itama sannan tace,  Zarah kuwuce ku tafi karku makara .
Sum-sum suka fice daga gidan.
Cikin tsantsar masifa Abba yace,  Idanma sun zauna Uwarmi zasumin? K dan Ubanki bance karkije Abuja ba? .
Ya kare maganar yana nuna Jiddah da kanta ke a kasa tana hawaye.
Jikinta Na rawa ta d'ago ta kalleshi,  Abba wlhy bansan ka hanaba da.......
Katseta Umma tayi da sauri.
 Jiddah tashi kiwuce gidan Sa'adatu (makwafciyarsu).
Ai tunkan Umma takai k'arshe Jiddah ta zari hijjab tafice da hanzari tamkar zata kifa dan har tuntu6e tayi da k'ofar zaure babban yatsanta ya fashe, amma bata kula da zafi da jinin da yakeba tafita abinta.

 To tafita, saiki nemo iccen dukana Yagana .
Murmushin takaici Umma tayi, cikin fushin dabai ta6a sanin tanada shiba tace,  Ka kwantar da hankalinka Alhaji, yagana batada k'arfin dukanka, amma lallai akwai babbar kotu Mai hukuntaka, yanzu dan ALLAH bakaji kunyar d'akko k'afa kazo cin zarafin yarinya akan taje taron addini ba? Anya kuwa Alhaji kana tsoron rad'ad'in d'aukar rai da kwanciyar kabari kuwa? Wlhy kaji Na rantse a wannan Karon kace zakayima yarinyata wani Abu akan zuwa taro namasu k'yak'yk'yawar manufa ALLAH saimun gurfana kotun musulinci dakai. Idan kuma kaji k'arya bismillah gata ga kanan ai .
Tana gama fad'a tayi shigewarta d'aki tabarsa tsaye zororo a waje. Takaici ya kumeshi yakasa koda motsi, sai huci da hura hanci yakeyi. Kusan mintuna biyar Umma taji fitarsa cikin buga murfin gidan da k'arfin tsiya.
Ta6e baki Umma tayi tana fad'in  Oho dai, wannan shashancin ya isheni, ka tsaya a rashinson nasu, amma bazan lamunci a zugoka kazo kana cimin zarafin yara akan hanyarsu ta aikata dai-dai da alfaharin kowad'anne iyayen kwaraiba wlhy .

Jiddah kam saida taga lokaci yaja sannan tadawo gidan tacigaba da wankinta, bata tambayi Umma Abba ba, itama Umma batace Mata komai akan Saba, saima d'akko Mata hirar zuwa Barno datayi wajen bikin Y'ar kaninta autansu.
Nanfa Jiddah tashiga murna sosai, dan tanason zuwa danginsu saboda tarbar mutunci da koyaushe ake musu, ga dad'in zama da kakarsu dasukeji over. (Mahaifiyar Umma=؃?

('('('('('('('('('('


Tsawon kwanaki goma kenan da dawowarsu daga taron Abuja, amma gaba d'aya tunanin yarinyar yakasa barin malam, dan haka yau ya buk'aci ganin malam mistafa.
Bayan la'asar lis malam Mustafa ya iso, lokacin malam yana waya da Aliyu.
Malam Mustafa na zaune har suka kammala sannan ya gaidashi cikin girmamawa. Malam ya amsa yana tambayarsa ya k'ok'ari da d'alibai?.
 Alhamdllh malam .
 To Masha ALLAH mustafa. Niko wata tambaya biyu Zan maka .
 To malam ALLAH yasa inada ilimin sani .
Murmushi malam yayi yana gyara zamansa,  Abokinka bashida wata wadda yake so ne? .
 Gaskiya malam babu, dan nidai tun Asma'u ban sakejin zancen wata mace a bakinsa ba, koda yadawo ma banji yanama maganarba, nakan tsokaneshi akan maganar Aure lokaci-lokaci amma amsata dashi shine (ba yanzuba), har Maimuna danaga kamar tana nuna alamar sonshi nabashi shawarar aurenta amma baima tankaminba a lokacin .
Nanma murmushi malam yayi yana girgiza kansa kafin yace,  Maimunatu tanan gidana? .
 Eh ita malam .
 To Masha ALLAH. tambaya ta biyu akan yarinyar datai karatu awajen taron ranar ce, d'iyar wanene? Konace mizaka d'an fad'amin game da ita? .
Gaban malam mustafa ne, Yay mugun fad'uwa a ransa yace wayyo ALLAH badai Jiddah taba? Yarinyar da kullum nake kaffa-kaffa da duk wani motsinta. Amma a fili saiya had'iye abinda ya toshe mak'oshinsa, cikin danne abinda ke ransa yace,  Malam itama d'alibarmuce, maikuma tsananin hazak'a da rik'o da addini, duk yanda kake zatonta ta zarce hakan, tarbiyya da duk k'yak'yk'yawan hali Na *MACE TA GARI* za'a iya samunshi gareta. Mahaifinta kam da wuya idan zaka sanshi, sunansa Alhaji Zakari yaro, ni kaina sau d'aya nata6a ganinsa, dan komai Nata k'anin mahaifinta kezuwa makaranta yay Mata a koyaushe aka buk'aci ganin iyaye .
Kai malam ya jinjina cikin gamsuwa,  Mustafa kana ganin zata iya dacewa da tsarin abokinka kuwa? .
Bak'aramin wuntsilawa cikin malam mustafa yayiba, harya d'ago yad'an kalli malam d'in, amma sai yay saurin maida kansa k'asa ya duk'ar, muryarsa nad'an shak'ewa yace,  Insha ALLAH malam zasu dace, dan dukkan abinda zai iya buk'ata Na tarbiyya daga gareta zai iya samu insha ALLAH .
Malam dayaso fahimtar wani Abu yay d'an shiru yana kallon Mustafan, kafin yace,  To Alhmdllh, amma kana ganin babu maganar auren wani kanta?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login