Amfanin Fasadabur (Custard Apple) ga Lafiyar Jiki
Mansur Usman Sufi
28 Aug 2025
311
Amfanin Fasadabur (Custard Apple) ga Lafiyar Jiki
Fasadabur / Fasadubar a Hausance
- Custard Apple da Turanci
- A wasu wurare kuma ana kiransa Sharifa
Yana daga cikin 'ya'yan itatuwa masu matuƙar amfani ga lafiyar ɗan adam.
Amfanin Fasadabur (Custard Apple) ga Lafiyar Jiki
- Ƙara ƙarfin garkuwar jiki
- Yana da yawan Vitamin C wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki, yana kare mutum daga mura da wasu cututtuka.
- Taimako wajen narkewar abinci
- Yana da fiber mai yawa wanda ke taimaka narkewa, yana hana kumburin ciki da maƙarƙashiya (constipation).
- Ƙarfafa ƙashi da haƙora
- Yana ɗauke da Calcium da Magnesium waɗanda suke taimaka wajen ƙarfafa ƙashi da haƙora.
- Inganta lafiyar zuciya
- Yawan potassium da magnesium da ke cikinsa na taimakawa wajen rage matsanancin hawan jini da kuma kare zuciya.
- Kariya daga ciwon sukari (Diabetes)
- Duk da cewa yana ɗan ɗauke da zaƙi, amma fiber ɗinsa yana taimakawa wajen daidaita sugar level a jiki.
- Kyautata gani da ido
- Yana ɗauke da Vitamin A wanda ke da muhimmanci wajen kula da lafiyar ido.
- Kara kuzari da ƙarfin jiki
- Saboda yawan carbohydrates da ke cikinsa, yana ba jiki kuzari, musamman ga masu yin aiki mai nauyi.
- Inganta lafiyar fata
- Vitamin C da antioxidants da ke ciki suna hana tsufa da wrinkles a fata, suna ba ta kyalli.
👉 Amma a lura: Ƙwayoyin (seeds) na cikin fasadabur ba a ci, domin suna ɗauke da guba (toxic). Abin da ake ci shi ne ’ya’yan cikinsa fararen nama mai zaƙi.
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(3)
-
(6)
-
(2)
-
(4)
-
(19)
-
(3)
-
(25)
-
(1)
-
(2)
-
(1)
-
(1)
-
(10)
-
(21)
-
(14)
0 Comments