KIDA A RUWA PART 2 BILLYN ABDULL

Mansur Usman Sufi

  

02 Oct 2025

567

KIDA A RUWA PART 2 BILLYN ABDULL

🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

 

 

 *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

 

_Chapter 2_

__________________

 

__________________

 

.A gaban ruwan nan da kowa yasan wajen zuwansa ne in har ba suna akan aiki ba ya iso, ya ɗan bi wajen da kallo cike da nazari, sai kuma a hankali ya furzar da huci mai ɗan nauyi da nuna damuwa. Dai-dai nan wani matashin soja ya iso wajen hannunsa ɗauke da roba cike da dawa. Ɗan kallonsa Zak-Shadow yayi, sai kuma ya miƙa hannu ya amshi roban dawar alamar baya buƙatar wata magana. Cikin girmamawa sojan ya bashi, ya juya yabar wajen. Tamkar tsuntsayen dake rayuwa a wajen sunji ƙamshin dawar ne, sai gasu suna sauka ɗaya bayan ɗaya a gabansa. Karo na farko yay wani ɗan murmushin gefen baki, tare da ɗibar dawar a hannunsa ya shiga watsa musu, ai kafin wani ɗan lokaci tsuntsaye kala-kala sun cika wajen, shiko yana cigaba da watsa musu dawar. Abin sha'awa harda masu sauka akan kafaɗarshi. Dan dai-dai nan ma wata ƙyaƙyƙyawa mai adon ja da blue a jikinta ta taso fiirrr ta sauka akan kafaɗarsa ta haggu. Juyawa yay a hankali ya zuba mata ido, kai da ganin kallon da yake mata kasan tunaninsa ya tafi wani waje ne kuma daban.

        Mafarkinsa ne ke dawo masa daki-daki tamkar Film da ake kallo zaune a cinema. Ba yau bane farko a garesa yin mafarkin, amma duk sanda yayi yana koma masa ne kamar sabo, kamar kuma a ranar ya fara yinsa, ga mafarkin a duk sanda zai yi shi cikin maimaita masa kansa yake abin kamar wani sihiri koma mi zai kirashi oho. Shekararsa bakwai da wasu watanni kenan da fara wannan mafarki, tun daga randa suka fara shigowa wannan jeji (2006) akan aikin da suke kai har zuwa yanzu lokacin yana ma a matsayin Major. Sun yo nisa sosai da jejin sukaci karo da wasu gayyar mata tafe da kayayyaki a kansu har da yara anata raira waƙar aure, ganin motocinsu da kayan jikinsu na kakin sojoji ga bindigu a hannu ya saka mutanen firgita suka shiga watsar da kayan kansu suka kwasa da gudu, masu ihu nayi masu kururuwa nayi. Sai mace ɗaya mai tsohon ciki data tsaya cak a hanyar, lallai itama a tsoracen take, sai dai da alama bazata iya gudun bane ba saboda ciki. Idanunta a rufe suke ga zufa ta gama wanke mata jikinta dake rawa. Duk abin nan dake faruwa kallo ɗaya yay musu ya maida kansa ga jaridar da yake dubawa, sai da abokinsa, koma ace amini da ya zama ɗan uwa na jini dake gefensa a motar da suke su biyu rak sai driver ya furta, “Ikon ALLAH irin wannan cin gudu kamar kunga dodanni! Ita kuma wannan halan cikin jikinta ne ya hanata gudun..?”

      A karo na biyu ya ɗan ɗago a hankali jin furucin Imran ɗin, akan matar dake tsayen ya sauke kyawawan idanun nasa da kullum suke a juye da sirkin ja kamar wani mai afa ƙwaya, baya ganin fuskarta saboda ta juya musu baya, atamface a jikinta kalar blue da zanen barewa yallow. Zanen atamfar shine a matsayin gyale data lulluɓa, sai fanteka madaidaiciya a kanta dake haɗe kusan guda goma. Ƙafarta takalman danƙo ne da ake kira ɗan-madina suma blue. Tunaninsa ya katse sakamakon fitar wani yaron sojansu inda matar take yana mata tsawar data sakata daburcewa har tana neman zubar da kayan kan nata. Shi kansa baima san ya ɓalle murfin motar ba ya fita, sai ganinsa yay kawai a gabansu. Yaron sojan ya ƙame da sauri yana salute nashi, sai kuma ya nuna matar cike da takaicinta zai fara masa bayani kawai sai yaga ya ɗan duƙa a gaban matar. Ba shi dake tsaye inda suke ba har waɗan da ke mota sai da suka firgita, ai tuni suka shiga rige-rigen fitowa a motocin harda Imran, yo oga kwata-kwata ya fito su ubammi zasu jira yi kuma. Zak-Shadow dake a gaban matar cike da tsigunnon ƙasaita kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya ce, “Kiyi haƙuri”. Da wani kalar sauri ta ɗago tana kallonshi, dan gaba ɗaya ta gama ƙarasa susucewa tunda ya duƙunnu gabanta, sai taji ma ai gara na farkon da wannan mai kama da mala'ikan ɗaukar ran. Kalmar ‘Kiyi haƙuri’ daya ambata ta matuƙar jijjiga mata zuciya kwarai da gaske, dan ba abinda tai zato ba kenan. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma cikin sanyin murya da rawar baki ta ce, “Ku su waye dan ALLAH? Dan bamu taɓa ganin irinku a wannan yankin ba shiyyasa sauran ƴan uwana suka firgita”. 

    Kallonta kawai yake baice komai ba, fin minti ɗaya kafin ya furta amsar da kowa baiyi zaton zai batan ba. “Mu sojoji ne, masu bada garkuwa ga al'umma da ƙarfin ikon ALLAH.”

     A mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai ƙayatarwa tana ƙara sauke ajiyar zuciya da sharce zufar data jiƙeta da mayafinta. Ta ce, “ALLAH sarki, lale marhabun da shigowarku wannan yankin namu, dama haka sojojin da muke ji ana faɗa a redion Tanimu suke?. Lallai yau na yarda SOJA MAZAN FAMA, SOJA GA WUTA GA YAƘI. ALLAH ya ƙara kareku bisa ƙyawawan aikin ku, ya baku nasara da kariya daga duk wasu mugaye. Tunda na fara jin labarin aikin ku nake fatan ALLAH yasa na haifi ɗa namiji idan Tanimu zai tafi birni yaje da shi ya saka shi a makarantar sojoji shima ya zama soja. Amma tunda yau har gaku a wannan yanki namu in sha ALLAHU in dai namijin na haifa zan nemoku a wannan jejin ko badaɗe ko ba jima na baka amanar yarona ka koya masa wannan aiki na jarumai. Dan daga ganinka kai mutumin kirki ne jarumin kwarai ɗan gaske”.

      Karo na farko ya kai idanunsa akan cikin nata da yay girma sosai, sai kuma ya kauda kai batare daya ce komai ba, anutse ya miƙe gaba ɗaya yana mai tura hannayensa cikin aljihun wandon kakinsa na soji, daga sama kuwa riga ce baƙa t-shirt data kama ingarman jikinsa, yanda yay zanzaro da belt ya bama shafaffen cikinsa bayyana kwance a rigar luf. Tabbas suffarsa itace ta asalin Zaki da ake faɗa.

      “ALLAH ya saukeki lafiya, mun gode da addu'ar ki garemu. Zan zo da kaina amsar amanarki! Ku bata ruwa, a ƙarbi address ɗinta”. Yay furicin ƙarshe da umarni yana barin wajen. Ba ƙaramin mamaki abin ya bama sauran sojojin ba, hatta da aminin nashi Imran kuwa. Duk da dai kowa yasan Zak-Shadow a kallon nesa ne zakai masa ganin mugu, dodo mai firgitarwa koda a kallo ne, amma yana da tausayin na ƙasa da shi da sassauci ga mata, dan ko macen soja ce tai masa laifi yanda yake mata hukunci ba daidai yake dana namiji ba. Kamar yanda ya bada umarni sun bata ruwan roba da aka ɗakko a mota, sun kuma tambayeta garin da take ta faɗa suna rubutawa. Sannan suka taimaka mata ta tashi daga faɗuwar da tayi na firgita. Sojan da yay rubutun address ɗin nata ya miƙawa Imran cike da girmamawa, amsar takardar Imran yayi ya saka a aljihu kawai, sannan yay ma yaran umarnin su koma motoci, dan tuni shi mai gayya da aikin ya koma ciki abinsa. Haka suka wuce suka cigaba da tafiyarsu suka bar wannan mata mai tsohon ciki nabin motocinsu da kallo har sai da suka ɓace mata. Tun daga ranar bai sake bi takan zancen ba, sai dai a daren kwana goma sha shida da haɗuwa da su yay mafarkin ta haihu tana miƙo masa jaririn. Abin kamar wasa ya cigaba da maimaita wannan mafarki akai-akai, kuma koda yaushe irinsa yake maimaitawar babu canji. Gashi a ƙalla yanzu shekara bakwai kenan da wata har biyu..…

_______________

 

FAZANAMS MULTIPURPOSE PLC.

    *_Ina masu neman ayi musu souvenirs Na bukukuwan su dana shagalin bikin birthday da dukkan wasu taruka?_*

 

*_Ina masu son ayi musu abinci Na gargajiya da abin sha Don farin cikin taronku?_*

 

 

_________________

 

       Ɗan motsin da wayarsa tayi ne ya sashi sake furzar da huci, sai kuma ya sauke hannunsa dake cikin dawar nan ya cirota daga aljihu yana dubawa. Kallon wayar kawai yake babu wani yanayi dake nuna kirane ke shigo masa ya kamata ya ɗaga, harta gama ta yanke, sai kawai yay ƙoƙarin maidata aljihun, amma hanzarinsa ya katse saboda sake motsawar data shiga yi a karo na biyu. Yanzu kam hannu ya kai ya wani murza goshinsa, kafin ya sake ɗaure fuska babu alamar wasa sannan ya kai wayar kunne alamar dai da gaske kiran nashi akeyi..

             “Hallo. My D!”.

Wata zazzaƙar murya mai sanyi da kwantar da kai ta faɗa daga can. Shiru babu alamar zai tanka, da sauri ta ce, “Oh I'm sorry dear. Assalamu alaikum”.

        “Wa'alaikissalam”.

   Karo na farko jarumar muryarsa ta bayyana cikin buɗaɗɗen sauti da ƙarfin lafazi irin na maza marasa son wasa da lokaci. Itama sai ta ɗan ƙara kwantar da murya ta gaisheshi. Maimakon amsawa tambaya ya jeho mata a kausashe.

      “Kiran na miye?”.

Yanzu kam murya ta raunana kamar zatai kuka, ta ce, “Haba My D. Shike nan abu baya wucewa a wajenka, na baka haƙuri, na tura maka saƙo amma duk ka share ni. Dan ALLAH kayi haƙuri, nayi kuskure kuma na yarda nayi ina sake neman afuwa. Wlhy ni kewarka ma nake yi dan ALLAH kazo gareni, wata biyu fa ba sati biyu bace.”

      Shiru yayi bashi da alamar tanka mata, har sai da ta fara kuka ƙasa-ƙasa tana cigaba da roƙonsa da ban haƙuri sannan ya motsa lips da ƙyar ya furta, “Naji”.

       Baiwar ALLAH, dariya ta farayi cike da farin ciki, sai jera masa kalaman soyayya take masu zaƙi da taushi dake nuna tsananin kewa da begensa da take ciki. Shi ko yaƙi ya ƙara cewa komai. Cike da sake kwantar da kai ta ce, “Na faɗama Ummie?”.

      “No!”.

  “Ammafa itama tana kewanka D. Haka ma su Biebah kullum zancen ka ne a gidan nan, yau tunda na shiga hiranka kawai mukeyi”.

       “Uhmm!”

  Kawai yace. Bata damu ba ta cigaba da masa labarin ƙannen nasa, sai kuma ta koma na yaran dake tare da ita. Shi dai nashi saurare kawai, sai dai fuskarsa ta ɗan sassauta kaɗan ba kamar farko ba. Hakan na nufin koma wacece tana da muhimmanci a gareshi. Ya jima suna wayar kafin network ya fara rawa, kasancewar inda suke sai a hankali dama. Wayar ya maida aljihu, sai kuma ya ajiye robar dan dawar ta ƙare duka. Jejin ya shiga bi da kallo irin na nazari, kafin ya bar wajen gaba ɗaya ya koma cikin tantin da ya fito ɗazun..........✍🏼

 

 

 

1 Comments

24, October 2025
Husaina Ibrahim

Nice

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
KIDA A RUWA PART 3 BY BILLYN ABDULL
KIDA A RUWA PART 3 BY BILLYN ABDULL
Read MoreKIDA A RUWA PART 3 BY BILLYN ABDULL
KIDA A RUWA PART 2 BILLYN ABDULL
KIDA A RUWA PART 2 BILLYN ABDULL
Read MoreKIDA A RUWA PART 2 BILLYN ABDULL
KIDA A RUWA PART 1 HAUSA NOVELS BY BILLYN ABDULL
KIDA A RUWA PART 1 HAUSA NOVELS BY BILLYN ABDULL
Read MoreKIDA A RUWA PART 1 HAUSA NOVELS BY BILLYN ABDULL
Top 10 Best Travel Destinations to Visit in 2025”
Top 10 Best Travel Destinations to Visit in 2025”
Read MoreTop 10 Best Travel Destinations to Visit in 2025”
Top 10 Profitable Online Business Ideas in 2025 You Can Start with Low Investment”
Top 10 Profitable Online Business Ideas in 2025 You Can Start with Low Investment”
Read MoreTop 10 Profitable Online Business Ideas in 2025 You Can Start with Low Investment”
The Rising Importance of Mental Health Awareness in 2025
The Rising Importance of Mental Health Awareness in 2025
Read MoreThe Rising Importance of Mental Health Awareness in 2025
The Importance of Preventive Health Care in 2025
The Importance of Preventive Health Care in 2025
Read MoreThe Importance of Preventive Health Care in 2025
Real Estate Investment in 2025: Best Strategies and Opportunities for Global Investors
Real Estate Investment in 2025: Best Strategies and Opportunities for Global Investors
Read MoreReal Estate Investment in 2025: Best Strategies and Opportunities for Global Investors
Best Investment Opportunities in 2025: Where to Put Your Money for Maximum Returns
Best Investment Opportunities in 2025: Where to Put Your Money for Maximum Returns
Read MoreBest Investment Opportunities in 2025: Where to Put Your Money for Maximum Returns
Top 10 Types of Insurance You Need in 2025
Top 10 Types of Insurance You Need in 2025
Read MoreTop 10 Types of Insurance You Need in 2025