DALILAI 5 DA KE HAIFAR DA CIWON MARA A MATA
Mansur Usman Sufi
02 Aug 2025
368
DALILAI 5 DA KE HAIFAR DA CIWON MARA A MATA
___________________________________________
1. Fitowar Kwai daga Ovary (Ovulation Period – yayin da kwai ya tashi fitowa daga jakar kwai zuwa bututun falofiya ana samun matsakaicin ciwon mara.
2. Ciwon Al’ada (Menstrual Cramps) – Tsokokin mahaifa suna matsewa domin fitar da jini, hakan na jawo ciwon mara.
3. Sanyin Mara (PID) – Cuta ce da ke kama mahaifa da ovaries, galibi sakamakon kamuwa da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.
4. Fitar Kumburi ko Kullutu daga Mahaifa (Fibroids) – Ƙwayoyin nama da ke girma a mahaifa, suna iya jawo zubar jini da matsanancin ciwon mara.
5. Cyst a Ovaries – Ruwan da ke taruwa a ovary, idan ya fashe ko ya girma sosai, na iya haddasa ciwon mara mai tsanani.
6. Ciwon Ƙoda ko Mafitsara (UTI) – Cututtukan mafitsara na iya jawo ciwon mara, jin zafi yayin fitsari da yawan yin fitsarin.
___________________________________________
SHAWARA:
Idan ciwon mara yana yawan damun ki kar kiyi shiru domin alama ce ta wani abu na faruwa. Ki nemi kulawar likita domin gano musabbabin ciwon dan magancewa cikin gaggawa.
___________________________________________
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(3)
-
(6)
-
(2)
-
(4)
-
(19)
-
(3)
-
(25)
-
(1)
-
(2)
-
(1)
-
(1)
-
(10)
-
(21)
-
(14)
0 Comments