Showing 39001 words to 42000 words out of 84238 words

Chapter 14 - ROYALTY (YAN SARAUTA) by Mrs Alamin.txt

d'in Abbansu ba shiga tai da sallama acan ta sameta bayan sun gaisa ta gaisar da Abban ma ta mi'ke tana yi musu sallama ta fito babu alamar Khairat maybe tayi part d'in Momy books d'in data aje akan hannun kujera ta d'auka tana gyara ratayawar handbag d'inta ta fita a part d'in zata tafi sashin Momy taga prince Hamid dama kuma shi zataje nema da mamaki ya kalleta yaga shirin school tai amma sai yanzu...........................

"Yaya Abdul-Hamid ina kwana"? Ta fad'a tana katse masa tunani qara kallonta yai yana cewa "lafiya amma me kike har yanzu baki tafi school d'in ba wato saboda kinsan Ahmad baya gidan ko"? Ya karasa maganar da murmushi kai Baby ta girgiza tana cewa "a'a badan baya nan bane lokacin tafiyar tawa ne bai karaso ba shiyasa ban tafi ba sai yanzu sha biyu muke da class".

"Ok yayi aina d'auka ko dalilin kinga gwani baya nan ne" ya fad'a yana shirin wucewa da sauri Baby tace "Yaya Abdul-Hamid" dakatawa yai yana juyowa yace "aha meya faru"? Langwa6ar dakai tayi tana qarqar da murya tace "dama cewa zanyi dan Allah ka kaini school yau idan baka da uziri"? Kallonta yayi sosai yasan abinda bazata iya cewa Ähmäd ba kenan ko iya tsayawa ta kalleshi batai balle ta iya bud'e baki ta fad'a masa cewa ga abinda take so ya tabbata da ace shima Ahmad d'in yana janta jiki ya daina had'e mata fuska ya ri'ka sakewa ko kad'an ne da ita dan ta saba dashi amma ina ya kasa yai hakan.......................

"Ya Abdul-Hamid".
Maganar datai yasa ya dawo daga tunanin da yake ya kalleta zaiyi magana tace "ko kana da aiki"? Kaiya jinjina yana cewa "eh akwai amma muje na kaiki yau ba hospital zanje ba airport zanje karfe biyar da rabi".

"Airport kuma yaya Abdul-Hamid wa zaka d'auko".

"Wani ne muje na kaiki kekam ba ruwanki da wanda zanje d'aukowa" dariya Baby tai tana cewa "to kodai budurwarka zaka d'auko shiyasa baka so mu sani"? Kaiya d'aga yana murmushi yace "eh kamar kin sani ita zan d'auko" ya fad'a yana wucewa gaba tabi bayansa tana sake tambayarsa.

"Yaya Abdul-Hamid baka fad'a min a ina take ba mene sunanta"? Daidai sun isa wajen da motocin masarautar suke yasa key yana bud'e murfin motar ya shiga zagayawa itama tai tana shiga ya tada mota suka bar masarautar Baby kam bata ha'kura ba a hanya ma saida ta sake tambayarsa "Yaya Abdul-Hamid baka fad'a min a ina take ba mene sunanta"? Jin abinda ta sake fad'a yasa ya kalleta yana murmushi yace "sunanta mele" a shagwa'be Baby tace "kai Yaya dan Allah ka fad'a min".

"Amma baby zaki iya tarar Ahmad da irin wannan maganar ko ki tambaye shi kamar yadda ni kike min yanzu"? Zaro ido tai tana girgiza kai tace "niii wanne tsautsayin ne zaisa na tari ya Ähmäd da irin wannan tambayar humm aiko ranar dana kwana a asibiti dan nasan bazai ta'ba 'kyale niba".

"Ok ashe kura tasan gidan me babban sanda kenan saboda kinga ni bana fad'a shiyasa kika dameni da tambayar ko "?.

"A'a kawai dai naji dad'i ne da naji kana da budurwa muma kwanan nan zamu samu Aunty mu ri'ka zuwa gurin ta ziyara".

"A'a ba kwanan nan ba Baby sai nan gaba sosai ba yanzu zanyi aure ba dan sai Ahmad ya rigani ma".

Da mamaki Baby tace "Ya Ahmad kuma shi d'in yana da budurwa ne dama bamu ta'ba sani ba"?.

"Eh yana da ita man baki sani ba"? Kaita d'aga tana cewa "nikam ban sani ba saifa yau taya zan sani bayan ko fuskar gaida dashi bama samu sosai fad'an sa yafi shirunsa yawa amma koba komai nasan yanzu zamu huta da yayi aure shikenan zai d'auke hankalinsa a kanmu ya mayar kan matarsa" kai prince Hamid ya jinjina a ransa yana hasko daya za'ai ta sani zaman me ake dahar yanzu ba'a fad'a mata ba to sai yaushe ya kamata ace lokaci yayi da zata sani shi kansa Ahmad daya fahimci tasan cewa shi yake sonta zai aureta maybe daga ranar zai daina mata abubuwan da yake mata.....................

"Yaya Abdul-Hamid yaufa banyi breakfast ba dama nace sai zaka kawoni ka sai mun wani abu" daina tunanin da yake yayi yana kallon ta yace "ok me kike so"?.

"Ina son ice cream da chocolate kawai idan na dawo gida naci abinci".

"Amma da kin fad'i wani abu me kyau kyace a siya miki kayan sanyi bakya tsoron mura ta kamaki"? Fad'i wani dai amma Banda wannan a marairaice Baby tace "dan Allah Yaya Abdul-Hamid shi nake so please" parking yai yana cewa "ok jirani" ya fad'a yana fita tana zaune ya sayo mata ya dawo suka karasa school d'in ya sau'keta tai masa godiya sosai cikin jin dad'i saidai tayi mamaki da bataga Ayrah ba kardai bata zo ba meyasa yau tayi fashin school kalle kalle ta fara ganin babu alamarta yasa ta karasa shiga cikin class d'in nasu a zaune taga Ayran da book a gabanta tana karatu sauke numfashi tai tana karasawa ta dafata tana cewa "Ayrah Abdul-Kharim yakike kwana biyu"? D'agowa Ayrah tai ganin Baby yasa tai murmushi tana ri'ke hannunta tace "kai oyoyo Zuhra Ashraf Sharfaddeen ai tun d'azu nake jiran zuwanki naga shiru baki zo ba ya akai"? Zama Baby tai tana aje littafan hannunta da ledar da prince Hamid ya sayo mata kayayyi tace "humm kedai bari kawai Ayrah inacan a gida Ina shirgar barci saboda boss baya nan yabar gari".

"Kema yayanki yabar gari Ashraf Sharfa kice hutu kike abinki"?.

"Uhm nikam hutu nake wallahi ranar daya tafi kamar sallah har party muka had'a nida Aunty Khairat da Sultan" kai Ayrah ta jinjina tana cewa "nikam nawa Yayan daya tafi ranar wuni nayi ina kuka karshe har zazza'bi nayi gashi 'yar wayar da zamu ri'ka magana ma bani da ita".

"Ok ayya yayanki Aiman kema ya tafi ne"? Kai Ayrah ta d'aga Baby taci gaba "wacce qasa ya tafi"?.

"Beijing" .

"Allah ya dawo dashi lafiya".
"Amin Zuhra na gode" ta fad'a jiki a sanyaye bud'e ledar shopping d'in da prince Hamid yai mata l kallon Ayrah tai ganin yadda tai shiru kamar tana cikin damuwa tace "Ayrah meya faru naga fuskarki kamar da matsala"? Murmushi Ayrah ta saki wanda iyakacin sa kan le6enta saboda kartasa Babyn a damuwa tace.

"Babu komai Zuhra kawai ina tunanin tafiyar ya Aiman ne shiyasa".

"Uhmm 'kwarai kekam har jin kewar yayanki kike banda mu mukam farin cikin fecewarsa muke".

"Aini dole nayi kewarsa saboda shine komai nawa shine yake kula dani" tashi Baby tai tana cewa "ok ayya Allah sarki Ayrah karki damu insha Allahu zai dawo ai kamar yaune taho muje waje musha wannan dan haka na taho banci komai ba" mi'kewa Ayrah tai suna fita inda suka saba zama anan suka zauna sunaci gaba da hirarsu har lokacin shiga lecture d'insu yayi suka shiga awa uku bayan sun fito Baby taiwa Ayrah sallama driver yazo d'aukarta suka tafi Ayrah itama ta kama hanya da yake kullum a kafa take zuwa ta koma a kafa Hajiya Khubura bata ta'ba bari Daddy ya baiwa Ayrah kud'i wanda zata hau napep koda naira biyar ne bs ada kuma kafin ya sauya driver ya aje mata yake kaita wani lokacin kuma da kansa yake kawota har cikin school lokacin tashi ya baro office d'insa yazo ya d'auketa ya mayar da ita gida tsabar gata baya bari tai tu'ki da kanta amma yanzu ko kallo bata ishe shiba saidai tasan ba laifinsa bane tabbas akwai lauje cikin nad'i shiyasa ta daina damuwa da halin ko in kula d'in da yake nuna mata tasani wata rana sai labari komai zaizo ya wuce kamar ba'ai ba.

Baby ta riga Khairat dawowa gida dan ita sai jikin magriba sosai ta dawo direct part d'in Mami ta wuce dan a 6angaren Mamin suke yanzu kafin su koma na Momy tana shiga taga Baby a zaune ita kad'ai a bedroom zama tai cike da gajiya tana cire hijab d'in jikinta ta aje a gefe kafin ta sauke numfashi tana kallon Babyn tace "Baby kinsan wana gani a harabar gida yanzu sun tafi masallaci da yaya Abdul-Hamid kuwa"? Khairat ta fad'a tana zaro ido tare da ri'ke baki" kai Baby ta girgiza tana cewa "a'a waye a wajen dama Yaya Abdul-Hamid d'azu yace min budurwarsa zaije ya d'auko a airport".

Gwalo ido waje Khairat tai tana cewa "wacce irin budurwar tasa hum'um to wallahi ya Ahmad ya d'auko ba wata budurwa Yaya Abdul-Hamid d'in ne yake da budurwa boss ne ya dawo"? Zaro ido waje Baby tai itama jin abinda Khairat tace harda zabura tana mi'kewa tsaye tana cewa "Aunty Khairat kikace Ya Ahmad ya dawo kuma dama ba dad'ewa zaiyi ba ko kuwa hukunta ni ya dawo yi"? Ta fad'a tana d'ora hannu aka.

"A'a akwai abinda yazo yi inaga karma ki d'orawa kanki wata damuwa ko tsarguwar danke ya dawo ko d'aya ba lallai hakan bane tunda naji Abba suna maganar da Momy dazu bayan tafiyar ki school naji abbanmu yana cewa zai dawo yau akwai abinda zaiyi bazai wuce sati biyu ba zai koma" sauke numfashi Baby tai jin abinda Khairat tace tana cewa "kai Masha Allah har naji dad'i wallahi Allah yasa idan mun had'u karyai min magana akan abinda ya faru".

Da sauri Khairat tace "Allah yasa kar yai mana magana dai kin manta Nima harda ni".

"Uhmm Aunty Khairat naki me sau'ki ne nifa kinsan abun biyu ya had'e mun yace idan ya dawo saina gane Allah da girma yake nidai na shigesu na da azaba ya Allah ga baiwarka tana cikin matsala ka cireta daga tarkon bawan nan naka" ta fad'a tana bud'e hannu Amin Khairat tace tana dariya ta mi'ke tana shiga toilet zatayo alwala yayin da Baby tai zaman dirshan tana rafka tagumi kafin Khairat d'in ta fito.

A ranar basu yarda sunje part d'in Momy ba saboda kowa tsoron had'uwarsa da Ahmad yake musamman Baby a ankare take ta kasa sakewa hatta abinci da Khairat ta fita ta d'ebo musu da'kyar taci baifi spoon biyar ba tasha ruwa kawai ta sakawa kofar bedroom d'insu lock suka kwanta duk da haka saida Khairat ta riga Baby barci saboda yadda ta saka dawowar Ahmad d'in a ranta kasa runtsawa tai data rufe ido take ganinsa saidai ta bud'e da sauri ta kama waige-waige har jikin asuba idonta biyu barci 6arawo shiya d'auke ta batare data sani ba kuma da asuba ta riga Khairat tashi tai sallah bata iya komawa ta kwanta ba taci gaba da zama akan sallaya tana addu'a har Khairat itama ta tashi ta sallar saidai ita tana idarwa ta mi'ke ta koma gado kallonta Baby tai tana cewa "Aunty Khairat kin manta ya Ahmad ya dawo wai barci zaki koma"? D'agowa Khairat tai zatai magana ganin yadda idon Babyn yake yasa tace.

"Baby kiga yadda idonki yayi ja baki samu isasshiyan barci bane kome hakan" kai Baby ta jinjina tana cewa "Humm Aunty Khairat kedai bari kawai ban samu na iya barcin ba sai wajen asuba shiyasa kika ganni haka" da mamaki Khairat tace "saboda me"?.

"Kin manta ya kashe min warning kuma yace idan ya dawo zamu gauraya tuna hakan yasa na kasa sukuni har karfe uku da rabi bansan sanda barcin ya d'auke ni".

Murmushi Khairat tai tana cewa "ai kuma kinsan duk rintsi ya Ahmad bazai shigo mana ba bedroom da dare ba dakamar da safene da yanzu kin ganshi idan yayi niyya Baby ki cire wannan tsoro da damuwar a ranki ki sallama kinsan ya Ahmad idan yai ra'ayin abu sai yayi dan haka ni banga wani abun ki d'aga hankalinki ba tunda kinsan kome zaki idan yaga damar ya hukunta ki zaiyi toni anan banga abinda zaisa ki takurawa kanki ba" sauke numfashi Baby tai tana kallon kofar bedroom d'insu kafin ta d'an girgiza kai tana cewa.

"Shikenan Aunty Khairat nagode zanyi kokari naga nayi yadda kikace min da ace abinda kika fad'a min zan iyayi dani kaina na huta amma zan gwada" kallonta Khairat tai tana sakin dariya tace "to indai haka ne tashi muje part d'in Momy nasan yana can ki dake karki nuna wani abu kamar yadda nima zan tsume idan yaga haka ina mai tabbatar miki maybe bazai tada mana wancan zancen had'a partyn da mukai ba.

"To Kuma Aunty Khairat kin manta nifa yanzu ba wannan ne a raina ba cewa dayai zan gane ya aje waya na ta'ba masa wannan shine matsala ta".

"Ki had'a harda wannan laifin da kikai masa duk ki share muje kawai Khairat ta fad'a tana ri'ke hannunta alamar ta tashi su tafi Baby batako motsa ba sai tambaya data jefo mata "anya kina ganin zan iya kuwa"? Kai Khairat ta d'aga tana cewa "kwarai zaki iya saidai idan bakiga dama ba shimafa mutum ne kamar mu taso kawai kinsan indai Momy ko Yaya Abdul-Hamid wani yana nan bazasu bari ya dakemu ko yasaka mu wani abu me wuya ba" shiru Baby tai kamar zatai kuka tace.

"Nidai kawai kije banda ni basai naje ba".

"Ban gane basai kinje ba? Please Baby taso muje nayi miki alkawarin koda ace zaiyi tambaya zan bashi amsa kozai dakeni zan shiga cikin zancen ku inyaso ya had'a mu tare yayi mana komai" jin abinda Khairat tace yasa baby d'agowa ta kalleta sosai tana cewa "Aunty Khairat da gaske bazaki barni ni kad'ai ba"?.

"Da gaske man Baby taso muje" mi'kewa Baby tai zuciyarta na harbawa tana dar-d'ar suka nufi 6angaren Momy suna shiga kuwa dashi suka fara had'a ido yana zaune kusa Momy suna zance tsaye sukai a kofar shigowa aka rasa wacce zata fara shiga kowa sai raba ido take kamar Ahmad bai gansu ba ya sharesu yaga iya gudun ruwansu aiko kusan awa guda suna tsaye kaiya jinjina a ransa yana fad'in lallai yaran nan basu sanni ba har yanzu amma zanyi maganin ku d'agowa yai yana kallonsu daidai Momy ta mi'ke ta shiga bedroom sakamakon wayarta da aka kira kusan numfashin sune yaso d'aukewa ganin wacce zata taimakesu tasa baki tabar gurin su juya yaci ubansu su karaso nan yaci ubansu ko'ina basha..................

"Kai tsaiwar me kuke anan ku karaso min kafin sakan daya bana son taku duk wacce ta taka zan take ta" tun bai gama magana ba da gudu suka karaso kowa jiki na 6ari musamman Baby da taga ita yafi kallo tasan yau kam Allah ne kad'ai gatanta...........

Saukar muryasa sukaji yace "Baby da Khairat wato saboda na tafi shine kuka had'a party ko harda gabatarwa da DJ nagode gani na dawo ba tafiya nayi har abada ba saidai ku sani yau kun shiga uku sai kun sake had'a min valentine day kamar yadda kuka had'a ranar ku tashi ku nemo cake duk inda yake da balloons sannan ku aro mp dakuka aro nima ina so kuyi min a fili In gani" ya fad'a fuskarsa a had'e yana kallonsu babu ko d'igon murmushi da ganin yanayin sa babu sau'ki tsabar yadda suka rud'e babu wacce fuskarta babu hawaye jiki kuma na rawa ganin halin tashin hankalin da suke ciki yace.

"Ko ban kai matsayin da zakuyi min ba"? Duk shiru sukai wanda zai girgiza kai ma a cikinsu rasawa akai sai kuka da yazo musu shima kuma an rasa wacce zata fara fito da nata fili ganin sunyi tsit yasa cikin tsawa yace "ko baza kuyi ba yanzun nan jikin ku yai tsami wallahi yau sai naci ubanku" jin abinda yace yasa Baby kukanta ya fito fili dan tasan duk tsiya kome zaiyi musu saiya fara 'kyale Khairat kafin ita....................

"Ke wato harkin samu bakin kuka ko? Yayi kyau ku tashi ku fara kar'bar hukunci zakuga karshen azabata yau ku fara zaga min parlon nan da frog jump" yana rufe baki da sauri suka tashi kowa ta ri'ke kunne suka fara duk girman parlon da yawan kujerun sai sun zagaye su kuma babu hutu yana kallon su da yadda suka gaji amma yai banza dan yasa a ransa daga yau bazasu sake marmarin koda dariya bane idan ya tafi, suma a nasu 6angaren sun d'auka abun nasa da sau'ki amma sai sukaga baida alamar cewa su tsaya gashi Momy kamar bata part d'in har lokacin bata fito ba tsabar wahala kukan ma sun daina idonsu ya bushe.

"Ku tsaya".

Yana fad'a da sauri kowa ta tsaya a inda take tare dayin zama da6as suna mayar da numfashi tabbas sun sha wahala ko yanzu ya barsu sun azabtu mi'kewa yai batare daya kalli inda suke ba ya nufi hanyar fita yana cewa.

"Ku biyo ni".

Zaro ido waje sukai musamman Baby da taji cinyarta kamar ba'a jikinta take ba gashi harya fita mi'kewa Khairat tai da'kyar hajijiya na d'ibanta ta kalli Baby tana cewa "Baby taso mu tafi kinsan ya Ahmad yana da sauri maybe yanzu yaje part d'insu fa karmu jawowa kanmu duka bayan wannan azabar" numfashi Baby ta sau'ke hawaye na zubo mata zurr kafin itama ta rarrafa ta dafe kujera tana runtse ido da'kyar ta samu ta mi'ke kowa tana jan'kafa suka fita yadda suke jin ciwon jikinsu babu me iya sauri a cikin su dole sai a hankali suke tafiya har suka shiga part d'in nasa yana zaune sukaje da suka karasa inda yake kowa kasa dur'kusawa tai.

"Bazaku iya zama bane? Ya tambaya yana kallon su "ai bakuji komai ba kuma bakuyi nadama ba tunda har zanyi tafiya bayan kunsan waye ni dan rainin hankali har ku zauna kuna d'aura balloons da sayo cake kuyi party saboda mugu yabar gida ko? Yau kuwa zakuga mugu zanyi maganin ku" ya karasa maganar yana mi'kewa yace "ku biyo ni" kallon juna sukai a matukar razane yaufa sukam sun shiga uku ina kuma zai kaisu ina zasu sake binsa.........................

Sautin bud'e kofa ne ya dawo dasu hayyacinsu ganin ya bud'e ya fita suma suka bi bayansa garden ya shiga yana tsayawa a gurin fountain bai juyo ya kallesu ba yace "Khairat d'auko min boket guda biyu a bathroom d'ina minti d'aya na baki" jin abinda yace yasa Baby sake susucewa mezai saka su badai d'iban ruwa ba Allah yasa Khairat ta had'u da prince Hamid ya tambaye ta me zatai da boket ko Allah zai taimake su................

Ganin Khairat d'in ta dawo da botikan biyu a hannunta yasa Baby ta fahimci basu had'u dashi ba kawowa tai tun kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login