Showing 75001 words to 78000 words out of 153964 words

Chapter 26 - BAYAN NA MUTU! Complete Book Writing By Aisha Shafii.doc

ma a tak'aice amma ta yaya zasu iya rufe idonsu su dinga fad'ar wadannan abubuwan akan 'yar d'anuwansu? Gashi sun k'i yarda su gaya masa komai akanta balle ma ya sami wani abin.

"Haka ne, Na fahimta kuma Nagode."

Ya yanke shawarar barinsu kawai don babu amfanin zaman, amma sai d'ayan daya fahimci sunansa Sulaiman ya tsaida shi.

"Idan zan baka shawara ka d'auka Alhaji Ahmad, ka rabu da case d'in yarinyar nan kawai, don kamar yadda ka fad'a ka tsince ta ne da girmanta da kuma wayonta, kuma d'an mutum a yanzu ko kai ka raine shi baka shaidarsa. Mu san Bintu tun tana tsumman goyo don haka mun fika sanin abinda zata aikata da wanda baza tayi ba."

Idan har ya d'auki wannan shawarar suka rabu da al'amarin Fadeelah, to a baiyane yake cewa rayuwar gidansa baza ta tab'a dawowa daidai ba, don ya tabbata bashi kad'ai ba, har Mami da take Uwa banbancin da take ganin Fadeelah da Zahra na haihuwa ne kawai amma sun riga sun karb'eta cikinsu, don wasiyyar mahaifiyarsa ta k'arshe a duniya zancenta ne, ta yaya kuwa zai dauki wannan shawarar su hakura da ita suna ji suna gani?

Tunda Daddy yake a rayuwarsa bai tab'a alfaharin rashin samun 'yanuwa ba sai a lokacin da Kawu Ibrahim ke wannan zancen, don ji idan har d'anuwa zai rufe idonsa ya dinga irin wannan abin akan d'iyar d'anuwansa da baya duniya a lokacin, to meye amfanin 'yanuwantakar?

Gaskiya ne da ake cewa DANGI suna suka tara!

Lokacin da ya koma cikin asibitin da a yanzu ya zama matattarar iyalinsa, ya tarar Hadiza, yayar matarsa tazo tare da su Zahra da a yanzu suke wajenta, a hannunsu kulolin abinci ne kala-kala amma 'yansandan nan uku da aka sa gadi sun hana su k'arasawa ma d'akin da Fadeelan take balle su sa ran basu.

Tun daga ranar Kamun nan taron bikin ya tashi gabad'aya, mutanen da suka zo washegari d'aurin aure haka akayi ta binsu da hak'urin cewa ga abinda ya faru an fasa sai komai ya lafa tukunna, don Al'ameen ya tubure cewa bai yarda a d'aura auren da Fadeelah a cikin wannan halin ba.

"Barka da zuwa Daddy."

Muryar Al'ameen d'in dake sanye cikin wata doguwar jacket ta fad'a daga gefe. Ga duk ya sanshi kallo d'aya zaiyi masa ya lura cewa ya canja, idanunsa sun zurma kamar zasu koma raminsu saboda tashin hankalin da ya ke ciki kala-kala, bayan wannan al'amarin na Fadeelah daya faru, a can America ya san mahaifiyarsa na dab da tsine masa albarka ta kuma yakice shi daga inuwar 'ya'yanta in har ta san ba ta'aziyya suka zo yi Nigeria ba, watakila harda wannan dalilin ne ya bashi k'arfin gwiwar cewa a dakatar da d'aura auren sai taji sauki tukunna.

Sauk'in da a yanzu bayan ya fahimci komai yake hango wahalarsa, don tun sanda ya fara sanin Fadeelah, ya santa da son warkewa daga ciwonta har ta tuna rayuwarta ta baya wadda ta had'a da 'yanuwanta. Ashe reshe ne zai zo ya juye da mujiya, maimakon 'yanuwan nata su karb'eta a yanzu da komai ya baiyana, sai suke kokarin cutar da ita da kansu.

"Barka dai Al'ameen, ka dawo?"

Daddyn ya tambayeshi don sunyi waya a d'azu yace dashi zaije raka mahaifinsa da sauran 'yanuwansa da suka zo d'aurin aure airpot zasu koma, don yau kwanansu biyu kenan a garin, yanzu daga shi sai abokinsa Kamal ne kawai suka rage.

"Eh na dawo Daddy, ka same su d'in?"

Kafin ya bashi amsa, su Aunty hadizan suka k'araso inda suke tsaye, bayan 'yar gajeriyar gaisuwa, Aunty Hadiza tace.

"Wata Nurse ta shaida mana cewa Fadeelan ta farka har likita ya shiga wajenta."

Hakan labari ne mai dad'i, amma ga Daddy bai masa dad'i ba, don daga yadda ya lura da mutanen nan, ya san da zarar Fadeelah taji sauk'i baza su b'ata wani lokaci ba zasu tafi da ita.

Bayan su Aunty Hadiza sun koma sun zauna ne ya kalli Al'ameen yace.

"Basu saurare ni ba kamar jiya Al'ameen, sunce an riga an shigar da zancen kotu da dad'ewa don haka sai dai mu d'auki lauya kawai."

Ga mamakinsa sai kawai yaga Al'ameen ya gyad'a kansa yace.

"Kar ka damu Daddy, na san hakan zasu ce dama, muna ta fafutukar licence din Nigeria ni da Kamaal, sannan za'a turo min da takarduna nan da kwana biyu insha Allah komai zai daidaita."

Da mamaki Daddy yace.

"Al'ameen kai fa lauyan kamfani ne kawai, ta yaya zaka d'auki shari'ar kisa?"

"Kowanne lauya ya iya komai Daddy, zab'ar b'angaren aiki ra'ayi ne kawai, kuma na tabbata case d'in nan ba zaiyi wuya sosai ba zamu tsayawa Fadeelah ni da Kamal insha Allah."

A lokacin da yake fad'in hakan ne gefen idonsa ya hango masa wannan matar mai kama da Fadeelah sak! da aka ce dashi yayarta ce, tana zaune a can kujerar data zama makwancinta tun kwanaki biyun da aka kawo Fadeelah asibitin, ya lura bata taka k'afarta waje ko sau d'aya ba, anan take kwana take tashi tare da d'anta, sai dai mijinta yazo da d'aya 'yar ta su ya kawo mata abinci, da daddare kuma su koma, a yanzun ma yana zaune a gefenta rik'e da d'an nasu yayin da ita kuma take cusa abincin da ya zuba mata a bakinta.

Tace musu ita mai laifi ce a cikin DANGINSU, shi yasa ko da suka zo ba wanda yabi ta kanta, tun kallon farko da suka yi mata a harabar asibitin ita da mijinta, basu k'ara bi ta kanta ba, ta bi su a ranar duk inda suka sa k'afa sannan ta rok'e su kamar mahaukaciya amma wallahi cikinsu ba wanda ya kula ta, ya rasa a duniya wane irin mutane ne DANGIN Fadeelah don haka suka tsallake ta a harabar asibitin nan suka tafi.

A take kwakwalwarsa ta gaya masa cewa yayar Fadeelah ita zata zama tsaninsu wajen ceto ta, ta san rayuwarta ta baya ta san komai, zata basu cikakken bayanin abubuwan dasu basu sani ba!

***

A D A M

Ya dace da mafarkin 'yanmata, ya dace da irin mazan dake nik'e zuciyar mata su fad'a cikin tarkonsu a d'an kalilan lokaci, sannan ya dace da irin mazan da wata macen zata kusan bauta musu don samun hankalinsu zuwa gare ta kawai.

Yana zaune cikin d'akin daya mayar office d'insa a gida, ya kurb'i tean dake tiriri cikin kofin hannunsa a hankali, idonsa na manne kan screen d'in labtop d'in dake gabansa, wasik'ar da matar da ya girma yana mata kallon mahaifiyarsa yake karantawa, kamar koyaushe rok'o take kan ya bata adireshinsa anan Nigeria zata zo ta ziyarce shi, ya san k'ulafuci irin na uwa akan d'anta, ya san irin yadda ta sawa kanta damuwarsa sannan ya san cewa ita a wajenta har yanzu tana masa kallon D'a ne, amma zuwanta wajensa yayi wuri yanzu, so yake ya manta da komai na waccan rayuwar ya saba da sabon kewayensa da kuma mutanen cikinsa tukunna, don haka zuwanta zai iya dawo masa da komai baya ne, zata canja masa tsarinsa.

K'ofar d'akin ta bud'e a lokaci d'aya, Sa'id ne ya shigo rik'e da waya a hannunsa.

"Yaya wayarka a kashe take?"

Ya tambaye shi cikin harshen hausa, don tun farkon zamansu baya tab'a bari yayi masa turanci, shi yasa yanzu sosai ya iya yaren, 'yan kalmomin da bai sani ba kad'an ne.

Ya cije gefen lebb'ensa na k'asa a hankali, don a lokacin ba zai ce ga inda wayar tasa take ba, wannan satin akayi zaman k'arshe na wani case d'in siyasa da yayi mutuk'ar wahal dashi, saboda da kyar ya samu b'angaren da yake wakilta suka yi nasara, shi yasa wular da ita bakid'aya, ba zaice ga inda take ba.

Cikin kasalalliyar muryarsa ya kalle shi yace.

"Sa'id ai na manta ma ina da waya ni."

Sai ya k'araso cikin d'akin yana fad'in.

"Shi yasa ake ta nemanmu ba'a samu ba, ashe su Kawu yahya sun zo garin nan har kwana biyu bamu sani ba."

"Kai ina wayar taka?" Ya tambaye shi yana k'ifta idonsa a hankali.

"Na canja layi tun last week, kuma na manta ban kira su ba sai yanzu dana kira Mama (yana nufin mahaifiyarsa)
take gaya min, yanzu munyi magana da Kawu Ibrahim yace in baka wayar."

Haka kurum sai yaji gabansa ya fad'i amma ya ture hakan ta hanyar gyad'a kansa a hankali.

"Kira shi." Ya fad'a kamar da kyar maganar ta fito.

"Baba muna lafiya?"

Ya gaishe shi cikin gurb'atacciyar hausar sa da ba kowa ke ganewa ba. Ya zab'i ya kira shi Baba don ya yarda cewa shi kad'ai ne a duniya mafi kusanci da mahaifinsa.

"Lafiya k'alau Adam, ya ibadun naka?"

Gaisuwarsu kenan a kullum sai ya tambaye shi game da addininsa, don yafi kowa tuna cewa shi bak'o ne a addinin kuma yafi kowa damuwa da ya san abubuwan cikinsa.

"An gaya maka su Yahya suna garin koh?"

Kawu Ibrahim d'in ya tambaye shi bayan sun gama gaisawa.

"Eh, yanzu nake ji a wajen Sa'id."

"Ai ana ta kiran naku ba'a same ku ba, yanzu dai sunce zasu turo muku da inda suke sai kuje ku same su, wani tsohon case ne na gida ya taso, har Kawu Danjuma ma yace bai sani ba ko kana da aiki da ba sai an d'auki lauyan gwamnati ba."

Ya cusa yatsunsa biyu cikin sumar kansa ta baya sannan yace.

"A'ah, Baba bani da wani aiki dana karb'a yanzu."

"To maganar bata waya bace ba, idan kaje wajensu Yahyan zasu fara yi maka bayanin komai, in kaga zaka karbi shari'ar, sai a sanar da kotun da al'amarin yake hannunta anan."

"To Baba, zamu je wajen nasu yanzu insha Allah."

Ya amsa a hankali kafin suyi sallama. A cikin ransa ya k'udirce cewa dole ne ma ya karbi wannan case d'in, dole ne yayi abinda zai faranta ran DANGINSA ko ya k'ara samun yardarsu, ba tare da tunanin komai a ransa ba ya kudirce cewa zai karb'i case kuma Allah zai taimake shi yayi nasara kamar sauran duka cases d'insa da baya tab'a faduwarsu a baya.

***

Kuna tunanin Adam zai karb'i case d'in bayan yaji komai? Ya kuma ga BINTUN da har yau baya iya bacci sai da idanunta a cikin nasa?

Kuna tunanin Al'ameen zai samu license har ya karbi case d'in Fadeelah? Ya kuma kara da Adam d'in dake mutuk'ar burge shi a matsayin takara?

Fadeelah zata ga Adam a matsayin d'anuwanta?

Me yasa danginta suka kasa yafewa shari'arta tsawon wannan lokacin?

Ina Habiba? Taji labarin ganin Bintu?

Wane tunani Mairo ke yi game da mijinta? Shin zata had'a hannu da Al'ameen su karbi case d'in Bintu?

Wace k'addara ce ke shirin sake faruwa tsakanin Fadeelah, Al'ameen da kuma Adam?

Akwai tambayoyi da dama da zamu cigaba da kwance su.=??


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

26

(&_&)

I K A R A.

Salisu ya shigo cikin d'akin da sallama sannan ya nemi waje ya zauna jiran fitowar Kawu D'anjuma daga k'uryar d'akinsa. Safiyar ranar lahadi ce saboda haka kamar koyaushe ya kan jinkirta fitowa don samun hutawa.

Ba'a fi k'arfin minti goma ba kuwa,? labulen d'akin nasa ya d'age sannan ya fito.

"Salisu kaine? Har ka dawo kenan?" Ya tambaya sanda ya lalubi wajen zamansa ya hard'e, kafin Salisun ya amsa, sai da ya sunkuyar da kai ya gaishe shi cikin girmamawa sannan ya mik'a masa envelope d'in dake hannunsa.

"Gashi Kawu, ranar goma sha biyar ga wata suka tsayar, nan da kwanaki goma sha d'aya kenan."

"Yawwa to, sannunka da kokari."

Ya fad'a bayan ya karb'i takardar, ya juya ya d'auko glass d'insa dake tare da 'yan tarkacen su Robb a gefen kujerar da yake kai ya sanya a idonsa, layi bayan layi sai da ya karanta takardar da ta fito daga Babbar koton birnin Zariya kan shari'ar da suka shigar ta zargin 'yar d'anuwansu Bintu da kashe mahaifiyarsu ta hanyar sanya mata guba a abin sha da kuma guduwar da tayi bayan hakan, a wancan lokacin sun shigar da k'arar ne musamman saboda tunanin hukuma zata taimaka musu wajen gano inda take cikin sauk'i, amma a yanzu sun maida k'arar ne da fushin cewa da gaske Bintu ta gudu daga gare su ne don wannan laifin har ta bud'e sabuwar rayuwar da take ganin baza su gano ta ba.

Sai da ya gama karantawa tsaf! Sannan ya? juyo ya kalli Salisun da a lokacin shi nasa tunanin na takaici ne kan yadda manya irin su Kawu D'anjuma ke shirin aikata abin kunya a zuri'arsu, ta yaya zasu yi shari'a da 'yar d'anuwansu? ya san laifin kisa musamman na mahaifiya yafi k'arfin komai da kuma tunaninsa, amma wannan abinda ya dad'e me yasa baza su manta shi ba musamman akan yarinya k'arama irin Bintu? Matsalar ma shine irinsa masu wannan tunanin a Babban gida kad'an ne, don kusan kowa yana goyon bayan yin shari'ar ne duba da yadda matsayin Bintun yake a wajensu tun farko.

"In ka fita ka kira min kawunka Ibrahim." Muryarsa ta katse gajeran tunanin da yake yi. Sai ya sunkuyar da kansa kad'an sannan ya amsa da.

"Insha Allah Kawu, na barka lafiya."

Lokacin da Kawu Ibrahim ya shigo cikin falon, fuskarsa bata nuna yanayin kammaninsa na kullum. Damuwa ce fal a ransa game da abinda yake shirin faruwa yana ji kuma yana gani.

"Wallahi bani da shakka akanka Ibrahim, na san koda na mutu zaka kare min iyalina ba zaka tab'a bari su tozarta ba."

Wad'annan kalman na d'anuwansa marigayi su ke ta yawo akansa tun daga lokacin da Sadiya ta dawo da shelar ganin Bintu kuma Kawu D'anjuma ya bada umarnin tuntub'ar kotun da case d'in ke hannunsu tsawon wannan lokacin, sannan kuma aka tura yayyensa biyu da 'yansanda hud'u daga kotun don su taho da ita.

"Wallahil azeem Kawu, na san darajar?rai kuma na san laifin kisa, ba zan tab'a iya cutar da hajiya ba kome take min kuwa, ina sonta a matsayin kakata da kuma mutum mafi kusanci da nake dashi na b'angaren Baba, na san hukuncin kashe mutum wallahi Kawu ba zan tab'a iya kashe ta ba, wannan tunanin ma bai tab'a zuwa kaina ba...."

Kalaman da Bintu ta gaya masa a daren da zata gudu suka amsa a cikin kansa, zuciyarsa na gaya masa cewa da gaske ne Bintu ba zata iya kisan nan ba, amma daga ranar da yayi k'okarin furta hakan yaga b'acin ran Kawu D'anjuma, ya tabbatarwa kansa cewa bashi da iko a al'amarin.

"An tsayar da ranar shiga kotun, nan da kwanaki goma sha d'aya, ina son ka sanar da Habiba da kuma duk wanda zai iya zama shaida cewa su zama cikin shiri, don na tabbata su Yahya ma zasu taho da yarinyar kafin nan."

Ya jinjina kansa a hankali yana kallon takardar sanda Kawu D'anjuma ke masa wannan bayanin, kwanaki goma sha d'aya rak suka rage k'addara ta yanke wannan yardar da d'anuwansa marigayi ya bashi ita.

"Kunyi magana da Adamun?"

Sanda Kawu D'anjuma yayi masa wannan tambayar, a sannan kwakwalwarsa ta haska masa cewa idan ba zai iya juya su Kawu D'anjuma ba, to tabbas zai iya juya Adam d'in da suke saka ran samun taimakonsa!

***

"Wai me zai tashi hankalinki ne?"

Salame, aminiya ga Habiba ta tambaya sanda suke zaune tsakar katafaren d'akinta da yasha gyara ya kuma banbanta dana kowacce mace a Babban gida.

Habiba ta ja tsaki k'asan numfashinta sannan tace.

"Dole ne muyi tunani akan lamarin nan Salame, wallahi jiya ko runtsawa banyi ba saboda tsananin mamaki, ace wai har ni zan yiwa Malam magana yasa k'afa ya tsallake ni ba tare da amsa ba, gashi labari ya baza koina cewar kotu za'a shiga.

Ni na rasa wane irin k'ulafuci ne da duk wad'annan shekarun bai ci ace sun hak'ura da mutuwar wannan tsinanniyar tsohuwar ba, Shu'aibu jiya har wani d'aga jijiyar wuya yake a tsakar gidan Asibi wai a daman ba tsayawa akayi da nemanta ba, kuma su Kawu D'anjuma basu janye shari'ar ba don haka dole ne aje kotun."

Salame ta tab'e bakinta.

"Wallahi har da ke kanki kika jawo wannan matsalar Habi, a daren da akayi abun wane irin baki ne ban baki ba kan muje a kashe yarinyar itama, amma kika tsaya cewar?da matsala za'a iya ganinmu, sai gashi ita ba wanda ya ganta ta samu hanya ta salallab'e ta gudu. Sai a yanzu da kike tunanin zaki fara cin duniyarki da tsinke an gano ta komai ya dawo sabo."

"Ajiye batun cin duniya da tsinken nan Salame, kina gani Malam tun yanzu ya fara canja min fuska, tuntubarsa na fara yi kan maganar janye shari'ar nan amma wallahi 'ta tafasa, sauke' bai ce dani ba, kuma ke kin san uwar wahalar da muka sha zuwanmu Niger kafin a iya sake d'aure tunanin sa da na su Kawu D'anjuman amma ace shekaru basu rufa ba lamari ya fara rawa? yanzu ko yaya aka samu matsala a wannan gab'ar yaya kike gani? Kin san dai bani da damar komawa Niger a wannan rikicin."

"Babu ma zancen komawa, don na gaya miki da idona naga aikin da Jaribi yayi kuma har gobe yana ci, don haka kautar da batun Malam a gefe, ina ga kai tsaye wajen Kawu D'anjuman zaki je mu san yadda akayi yasa baki don a janye shari'ar."

Habiba ta shiga kad'a kafafuwanta da d'aya ke kan d'aya sannan ta girgiza kanta, idonta na kallon jikin had'add'en labulen falon nata tace.

"Kayya Salame, wannan ba mafita bace don a tunani na fa har an basu rana, yaushe zai saurare ni."

"An saka rana? Bayan yanzu haka ma ance ita yarinyar tana asibiti?"

"Eh, tana asibiti, haka su Yahyan suka ce da suka yo waya, tana can tare da wannan banbad'addiyar 'yaruwar tata da kuma mutanen da suka rik'e ta."

"Yo wai daman tare suke a can da Mairon?"

"Haka dai Sadiya da ta dawo take fad'i, amma su su Yahyan da suka je sunce tace wai itama a ranar da Sadiyan ta ganta itama taje nemanta, amma Kawu D'anjuma ma yace kar su bi ta kanta, don har yanzu ba gida ta dawo ba."

Salame ta girgiza kanta.

"Al'amarin ne a cakud'e wallahi, don kin san abinda yafi d'aukar hankalin mutane a zancen ma da akace wai har an fara yinin bikinta a can Habujan."

"Yo yarinyar da akace har k'asar waje ta taka tare da marik'an nata me yafi wannan mamaki? Sannan wanda zata aura d'in ma sunce Balarabe ne daga dangin marik'an nata."

"Wannan ba mamaki yaga yaluwa mai irin nasu yalolon gashin ne, amma su dai masu rik'e tan ne suka yi kokari, ka tsinci d'a a titi ka jashi jikinka haka?"

Ganin hirar tasu na shirin karkata kan wani abun da ba shine a gabanta yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login