Showing 30001 words to 33000 words out of 55369 words

Chapter 11 - MAZAN JIYA Book 1 Na Abdul'aziz Madakin Gini.txt

na rikeda takobi wannan birran dai sunfi shekara arba'in acikin wannan dajin idan maza suka kama take suke kashe su inko mata ne sai su tafi dasu cikin gidajensu suna lalata dasu koda birurrukan suka tasan ma hantaru sai shima yayi kansu yana mai saransu yana bangajesu da kafa suna zubewa kasa bisa mamaki sai hantaru yaga ai takobi bata tasiri acikinsu duk sa'adda ya sara sai yaji kamar dutse ya sara nan fah birran suka fara kokarin su hallakashi amma sai yazamo musu alakakai yayinda hantaru ya gano nufin birran nan kuma yasan takobinsa batada wani amfani sai zuciyarshi ta harxuka yayi jifa da takobinsa cikin zafin nama ya goya shamilat a bayansa sannan ya diro kan dokin aka cigabada gumurzu mai ban alajabi domin duk inda hantaru ya kai duka saidai kaga birurrukan sun zube a kasa duk yawan nasu sai yaxamo na banza domin sun kasa koda lagutar jikinshi da faratunsu babban abinda ya tayarwa hantaru hankali dazarar ya zubar da birurrukan a kasa sai sumike zunbur su sake afka mishi runa masu kai mishi cizo da yakushi suko birurrakan sunyi matukar mamaki domin basu taba haduwa da shaidanin mutum irin hantaru ba, haka dai aka cigabada wannan fafatawa har tsawon sa'a daya shibai nakasa suba kuma bai kashe koda daya daga cikinsu ba ka suma basu hallakashiba tuni shumilat ta acikada tsananin mamakin bisa ganin jarumtakar hantaru domin bata taba tsammanin yakai hakaba babu abinda ya bata mamaki kamar yadda birurrukan nan suka kasa kai shi kasa wani lokacin har dandaxo sukeyi waje guda su tafo da gudu domin su hallakashi amma sai kaga ya tokare su ya watsasu. lokacin da hantaru yaga cewa lallai idan kara sa'a daya ana wannan gumurxun zasu iya samun nasara akanshi saiya chanza salon fadan kawai sai ya dinga kama hannayensu da kafafunsu yana cisgewa saidai kaga jini na tsartuwa na feshi nan birurrukan suka dinga kururuwa suna zubewa kasa a mace.. wohohoho!! maza maganin maza hakika birurrukan nan sunga bala'i domin kafin su ankara hantaru ya kashe samada guda duba biyar daga cikinsu saida takai birurrukan sun fara jada baya kai da sukaga abin yafi kafinsu rugawa sukayi cikin kogunan koda ganin haka hantaru ya yunkura da nufin yabisu cikin kogon dutsen sai shamilat ta gargadeshi kada ya bisu cikin kogon dutsen nan domin kowa a gidashi sarki ne, ka kyalesu kawau mu cigaba da tafiyarmu ai nasan ba zasu sake biyomu ba domin sun tsaga basuga jini ba.
Hantaru yayinkwafa sannan ya ce kash! Ummina naso ki kyaleni na cigaba da yaki da burirrikan nan har sai naga babu dayansu da ya rage mai numfashi.
Shamilat ta yi murmushi ta ce na gaisheka dana, hakika ina farin ciki da samunka domin ayau ne nasan cewa ina da namijin duniya kuma jarumin jarumai.
Hantaru ya ce ai dukkan godiya ta tabbata a gareki da kika zama uwata na sha nononki har ya zama garkuwa a gareni. Hakika dole ne nayi alfahari da zuri'arki domin ina ganin cewa sadaukarnan tawa a wajensu na gadota.
Shamilat ta sake yin murmushi ta ce tabbas mahaifina gawurtaccen jarumi ne na gaske mai tarwatsa maza a filin daga ina ganin cewa shi ka gado kuma gashi har ma ka fishi yarinta.


**********************
Mazan Jiya Part 16

Labarin Sadauki hantaru mai takobin #saiful lujara na mazan jiya

#Cigaba

Kafin shumilat ta rufe bakinta sai sukaji sautin taku daga cikin kogon dutseo nan tamkar sawun giwa koda hantaru da shamilat suka waiga nan take hantaru yayi arba da abinda yarazanashi yayi matukar firgitasu ba wani suka ganiba sai wani katoton gwaggon biri wanda girmarsa ya ninka na wadannan birurru kan sau biyar katon goggon birin nan ya dunfafo inda su hantaru ya yana tafe yana nishi da gurnani takun tafiyar tasa na haddasa karamar girgixar kasa koda ganin haka sai shamilat ta kara rudewa tana mai jan hantaru tana cewa zomu gudu yakai dana tabbas bazaka da wannan birin ba hantaru ya cije ya tsaya cak sannan ya dubi shamilat yace ai faduwar gaba asaran namiji ce kede kijada baya ki zuba ido kiga abinda zai faru a rude shamilat ta juya ta labe a bayan wata bishia tana leke sukuwa birurrukan sai suka haukan duwatsu suka zuba idanu domin suga abinda zai faru tsakanin hantaru da shugabansu asannan ne hantaru ya gane cewa wannan narkeken birin shine shugabansu kuma yaransane sukaje suka kirawo shi a fusace shugaba birurrukan yayi kan hantaru lokacin da sauran yaran nashi suka fara wani irin gurnani runa mai mishi kirari kawai sai hantaru ya dunkule yan yatsunsa ya gyara tsayuwa, cikin shammaci birin ya gabzawa hantaru naushi a fuskanshi saboda karfin daushin saida hantaru yayi sama ya fado kasa kuma jini yayi tartsuwa daga bakinshi har hakorinshi guda ya fadi akasa take hantaru ya tashi a fusace zuciyarshi ta fara tafarfasa koda ganin haka sai sauran birurrukan ruka fara ihu suna shewa saboda nasarar da shugabansu yasamu akan hantaru alamarin daya kara fusata hantaru kenan baxato ba tsammani hantaru ya daka tsalle ya gabza mishi naushi a kasan cibiya kawai sai akaga birin ya kame kamar an zare duka lakar jikinsa nan take kuwa ya sulale kasa ko shurawa bai sakeyi ba hantaru ya daga kai sama ya dubi birurrukan na ya kwarara uban ihu nan take suka tarwatse suna masu fantamawa cikin daji batareda sanin inda xasu tsayaba, Kaicon inbada wuyya ta kai wuya ya za ayi wadannan muggan burirrikan har su guje wa biladama guda daya jal.
Bayan birurrukan sun gudu sai shamilat ta fito daga bayan bishiyarda take ta rugo da gudu cikin farin ciki tana mai cewa hakika yau kayi bajintar da bayantaba mancewa da itaba suka rungume juna daga can sai shamilat da dauki takobin Hantaru ta sare kan wannan birin ta cire a cikin wani icce.
Koda ganin haka sai Hantaru ya dubi mahaifiyar ta shi ya ce da ita ya ke ummina me kuma zakiyi da kan wannan birin?
Shamilat tayi murmushi ta cw da shi ai d shi zan tafi, kuma zanyita ajiyar kokon kan wannan birin har iya tsawon rayuwata, domin abun tarihi ne wanda har abada bai kamata a manta da shi ba, ya dana kayi sani cewa kayi gagarumar bajinta wajen kashe wannan buri.
Nan de hantaru da shamilat suka yada zango suka kunna wuta suna jin dumi saboda sanyin dake kadawa. kashegari da safe suka kada rakumansu sukayi gaba su hantaru suka cigaba da ratsa dazuzzuka iri iri a ranar kwana na goma sha biyar ne suka shigo cikin daji mai girman gaske abinda ya fara daukan hankalin hantaru shine gaba daya harabar dajin komai tsab yake babu kazanta a ko ina, sannan ga kuma wata irin iska mai ni'imah na kadawa koda ganin wannan wuri sai murna ta kama hantaru ya yunkura zai sauko daga kan dokinsa ba caraf! sai shumailat ta rike hannunsa tace kadaka sauka yakai dana wannan daji baza'a rasa aljanu acikin saba hantaru yayi murmushi yace yake ummina inaso kisani cewa wahala ga da namiji ibada ce, haka kuma tsoro tsanani ne na hallaka da rashi.
Koda gama fadan haka sai hantaru ya sauko daga dokinsa ya xare takobinsa ya rike linzamin dokin ita kuwa shamilat saita dinga binsa abaya a hankali tana wauge-wauge kwatsam sai hantaru yaga wani katon lambu a gabansa wanda ke cike da yayan itatuwa iri-iri kamar su tuffa, inibi, fasa dabur dadai sauransu, bazato ba tsammani sai yaga wata yarinya budurwa kwance akan wata shimfida tana cin tufa fuskan a cike da annuri a iya rayuwar hantaru bai taba ganin mace mai kyan taba amma abin takaici daya dubi kafarta sai yaga kofato koda kyakyawar ta kalli hantaru rai ya kauda kai yaje ya sai ya kaufa fuska yaje ya tsinki tufa guda daya ya fara ci, alamarin dayabawa budurwar mamaki kenan ta bishi da kallo cikin takaici ta kuma shumailat rai taki shiga cikin lambun alokacin da hantaru yagama cinye tafar kawai sai yaji an rike hannunsa bawata bace face wannar budurwar daya wuce kwance,budurwar ta dubeshi cikin fushi tace haba bil'adama ka shigo lambu na babu sallama ka tsinki tuffata ka cinye. sa'adda hantaru yaji wannan sai kunya ta kamashi domin yasan baiyi da'a ba kuma bai nuna shi dane mai tarbiyya ba, cikin sanyin murya ya dubi budurwar yace yake wannan ma'abociyar kyau ki gafarceni hakika nayi kuskure amma ki sani kayan marmarin dake cikin lambun sunada daukan ido. budurwar ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace hakika kude bil'adama da rashin hakurh kuke to kasani cewa kaciwa kanka bala'i domin abune mawuyaci ka tsira da rayuwar ka ina yimaka albishir cewa ka fado cikin tarkon uwar mayu ta aljanu koda gama fadin hakan sai budurwar ta rikide ta dawo wata tsohumaw mummunar aljana mai matukar ban tsoro hantaru ya yunkuri da nufin ya kaimata sara sai yaji cikinsa ya murde ya fara ciwo kafin cikan dakika biu ya fara aman jini nan take fadi kasa sumamme. Koda shumailat taga abinda ya faru da hantaru sai itama ta fadi kasa sumammiya. lokacin da shumila ta farfado daga dogon suman datayi saita tsinci kanta acikin wanin irin gida an daureta da wata katuwar sarka shide wannan gida an gina shine da zallan duwatsun wuta kuma babu komai acikinsa face wata katuwar tukuba wacce aka hada guma guman itatuwa suna taci da wuta saman wutar an daura wani gado yayi jawur. kwatsam sai shamilat ta jiyo hayania daga can bangaren yammacin gidan sannu a hankali ya ringa karuwa yana cika dodon kunne daga can saiga dandazon wasu yayan aljanu sama dasu million 40 sun taho da gudu suna tsalle a tsakiyar su wannan mummunar aljanan ne dauke da hantaru su duka suka tunkaro inda tukubar wuta take koda ganin haka sai shamilat ta fahimci cewa cikin wannan gadon wuta aljanar nan zata daura hantaru shamilat ta kurma ihu tana kuka tana mai rokon aljanar kadata kona mata danta aljannar bata dubi shamilat ba saida suka iso dab da wutar sannan ta tsaya cak tana kyalkyala daria tace yake wannan bil'adama kiyi sani cewa idan ban gasa wannan danaki ba na baiwa yayana sunci duk mutuwa zasuyi ayau. kuma basu iya haura kwana 40 batareda sunci naman bil'adama ba kinga kuwa da bai fi ɗa ba.
Kodajin haka sai shumilat ta fashe da kuka, aljanar ta sake bushewa da dariya a karo na biu tace ai gara kisha kukanki ki more kafin na dawo kanki domin idan na gasaki ni kadai zanyi walimanki domin yayana basa cin nama mace cikin tsananin fushi shamilat ta dubi aljanar tace tir dake wannan la'ananniar maiya inda dana acikin hayyacinsa yake dakin raina kanki domin baki isa kiyi masa komai ba sa'adda aljannar taji haka sai ta bushe da daria sannan ta dakawa shamilat tsawa tace ke bil'adama kiyi sani cewa agaban sarauniyar mayun aljanun duniya kike babu wani mahaluki daya isa ya hallakani sa'ar ki daya mijina baya nan ya tafi farautar bil'adama dayanzu kema mun gama dake dolene na hakura sai yadawo domin akwai yajin dazai tafo mana dashi wanda muke jin dadincin naman bil'adama dashi.
********************
Mazan Jiya Part 17

Labarin Sadauki Hantaru mai takobin saiful lujara na Mazan Jiya

#Cigaba

Gama fadin hakan keda wuya sai uwar mayu ta yunkara zata daura hantaru akan gadon wutan bazato ba tsammani sai sukaga hantaru ya mike zumbur ya daka tsalle sama daga kan tafin hannun ta kafin takai masa cafka cikin zafin nama ya gabza mata naushi a idon ta take hannun nasa ya burma cikin kwarmin idanun nata, koda ya zaro hannun nasa saiga kwayan idanun nata ya fado kasa nanfa jini ya kama feshi uwar mayu takama kururuwa tana katan tanwa saboda tsananin zafi da takeji a cikin idanun ta yayin da yayan uwar mayu sukaga abunda yafaru da mahaifiyarsu sai sukayi caa akan hantaru da nufin su yayyaga shi su cinye shi danye abinda basu saniba sun gamu da gamon su maimakon sadauki hantaru yayi amfani da takobin sa wajen yakar su sai yayi wurgi da takobin sa ya afka musu yadinga cafkar wuyan su yana gwara kawunan su nanfa kafun a jima hantaru ya hallaka sama da guda dubu dari a daidai wannan lokaci ne uwar mayu tadawo hayyacin ta koda taga mummunar barnar da hantaru yayi mata saita fusata ta runtuma sabon ihu da kukan bakin ciki shi kansa hantaru saida ya razana sakama kon jin sabon ihun datayi suko sauran yayan nata dasuka rage sai suka ruga izuwa bayanta suka tsaitsaya uwar mayu ta tunkari hantaru da mugun nufi shima sai ya tunkaro ta bada jin tsoron komai ba koda ya rage baifi taku goma su gamu sai hantaru ya ruga da gudu yayi tsalle sama yakai mata wawan naushi da nufin ya fasa daya idon cikin zafin nama uwar mayu ta kade shi da hannunta take hantaru ya maku da dirkar gini ya fado kasa a matukar galabaice koda uwar mayu taga hantaru a kasa ya kasa tashi saita rugo da gudu ta daga kafar ta sama ta kawo masa wawan taku da nufin ta mutsuke shi cikin zafin nama hantaru ya goce saboda karfin takun saida kafar uwar mayu ta nutse cikin kasa har gwuiwan ta uwar mayu ta zare kafar da sauri ta cigaba da kaiwa hantaru taku yana gocewa kafun ajima harabar gidan ya cika da ramuka ita kanta uwar mayu saida ta gaji ainun takama haki a sannan ne hantaru ya samu ya mike tsaye aiko sai suka kasa tsere ta dinga binsa tana kai masa cafka tana wangame baki domin ta hadiye kansa gabadaya aduk sa'adda ta karta mashi farata a jikin shi saidai taji kamar ana karta takobi akan dutse kuma ko korzanewa bayayi cikin dakika kadan gidan ya hautsine hankalin kowa ya dugunzuma domin gunguma gunguman duwatsu ne na wuta ke fadowa kasa su kansu yayan uwar mayu saida suka firgice suna neman mafaka itako shamilat tuni dirkar da'aka daure ta a jiki ta karye ta fadi sannan wani katon dutse ya fado akan dirkar lokacin da hantaru ya waigo yaga halin da shamilat ta shiga sai hankalin sa ya dugunzuma sabona yasan cewa idan ta dade a kasan wannan katon dutse na wuta kasa zata iya zaftarewa a wannan lokaci ne hantaru ya fusata don haka saiya daina gudun yama tsaya cakk awaje daya yana sauraron isowar uwar mayu gareshi koda uwar mayu taga hantaru ya tsaya cak ya daina guje guje sai murna ta kamata domin tasan cewa yanzu zata hallakashi bada bata lokaci ba kawai saita durfafe shi da dukkan karfinta cikin bakin zafin nama da isowar ta dabb dashi saita kawo masa wawan cafka da hannayen ta guda biyu cikin tsananin zafin nama hantaru ya sunkuya kasa ta kama iska kafun ta sake kai masa hari tuni daka tsalle ta cikin karkashin kafafun ta ya zagayo bayanta ya sake daka tsalle kafun ta waigo ya dira akan kafadar ta ya gabza mata naushi acikin kunnen ta aiko sai hannun nashi ya lume acikin kunnen ya futo ta cikin daya kunnen yana zare hannun jini yakama feshi take uwar mayu ta sulale kasa matacciya a matukar galabaice hantaru ya durshe kasa bisa gwuiwoyin sa saboda tsabar wahala a sannan ne ya lura cewa guma guman duwatsun wuta dasuka yita fadowa daga saman ginin sun hallaka gabadaya yayan uwar mayu dayan su bai tsiraba da rayuwarsa hantaru na durkushe yana haki sai kawai yajiyo ihun shamilat daga can kasan wannan katon dutsin daya danne dirkar ginin da'aka daure ta a jiki cikin zafin nama hantaru ya yunkura da saurin gaske ya ruga wajen ya kaimata dauki wani irin takun sawu mai karfi da hantaru ya jiyo a bayansa shine tsaida shi ya juya a firgice aiko sai yayi arba da wata jibgegiyar halitta mai tsananin kwarjini daban tsoro da muni bakomai ne wannan halitta ba sai mijin uwar mayu ya dubi yadda gidan sa ya rugurguje sannan ya hango gawar uwar mayu a can gefe daya can kuma saiga gawarwakin yayan sa kota ina kawai saiya takarkare ya kwarara ihu karar ihun tamkar ana ruwan kwaran kwatsa daga sama ak'amarin daya kara razana hantaru kenan musamman daya karewa mijin uwar mayu kallo sama da kasa ya tabbatar dacewa ruwa ba sa'an kwando bane a wannan lokacin ne kuma shamilat ta cigaba da kwala ihu ashe dutsen daya danne dirkar da take jiki ne yake kara dannawa kasa nan fa hankalin hantaru ya rabu gida biyu ya rasa abinda ya kamata yayi shin mijin uwar mayu zai fuskanta suyi yaki koko wajen mahaifiyar sa shamilat zaije ya ceto rayuwarta harya yunkura zai ruga wajen shamilat sai yaji an shako wuyan sa ta baya koda ya kama abun daya shake shi sai yaga ashe wata irin doguwar bulala ce mijin uwar mayu ya jefa mishi ta shake shi a wuya kuma ta shake shi ne ainun ya kasa cire ta mijin uwar mayu yafara janyo bulalar nan domin ya kawo hantaru gaban sa shiko hantaru saiya fara cijewa da dukkan karfin sa domin yasan cewa muddin ya kuskura yaje gaban sa ya damke shi saidai kuma mahaifiyar sa ta haifi wani amma shi tasa ta kare hantaru ya cigaba da cijewa amma saboda mijin uwar mayu yafi shi karfi nesa ba kusa ba saiya dinga jansa gabadaya al'amarin daya dugunzuma hankalin hantaru kenan ya saduda domin yasan cewa kwanan sa yazo karshe.
******************
Mazan Jiya Part 18

#Cigaba

A lokacin daya rage baifi saura taku biyar ba mijin uwar mayu ya cafi hantaru da hannun sa sai wata dabara ta fadowa hantaru ya tuno da wata wuka dake sakale a bayansa cikin hanzari ya zaro wukar ya yanke wannan bulala data shake shi ya fada baya koda mijin uwar mayu yaga bulalar sa ta yanke sai yayi jifa da ita ya zare wani katon sungumi dake sakale a cinyar sa ya ruga izuwa kan hantaru suka kacame da sabon azababben yaki mai ban tsaro da ban al'ajabi wohoho!! tashin hankali ba'a saka maka rana saida hantaru da mijin uwar mayu suka kwana suka tashi suna fafata yakin bala'i hatta kasa tasha azaba domin saida mijin uwar mayu ya ratattaka komai dake cikin gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login