Showing 1 words to 3000 words out of 71576 words

Chapter 1 - MAZAN JIYA 4 Rubutawa By Abdulaziz Madakin Gini.txt

MAZAN JIYA
Littafi na hudu 4
Part A
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

Sai da sarki dujalu ya shafe sa.a shida cif yana baiwa hursiya lbrin sadauki shaddadu na birnin kufa, amma ba ta kosa ba da jin labarin har ya zamana cewa dare ya raba amma ko gyangyadi bata fara ba. Shi kuwa sarki dujalu a wannan lokaci bakinsa ya gaji da surutu kawai so yake yayi shiru don ya huta.
Dama ga tsananin gajiyar yaki gami da tsamin jiki da radadin raunikan jikinsa sun dameshi.
Kwatsam! Sai Hursiya taji sarki dujalu yai shiru ga barin zance..
Cikin tsanani damuwa ta dubeshi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin yin shirunka? Ina mai rokonka bisa girman iyayenmu daka cigaaba da bani wannan lbr mai dadi domin ina son naji yadda karshensa zai kasamce kamar yadda na ji na JARUMI HANTARU.
Koda jin wannan batu sai sarki dujalu yayi doguwae hamma gami da murmushi sannan ya dubi hursiyya yace haba yake yar uwata ai idan kika ce na ci gaba da baki wannan lbr har sai na je karshensa ba kiyi min adalci ba sbda koda zamu kwna muna yi ba zai kare ba.
Ki sani cewa duk a cikin labaran uku babu Hikaya mai tsawonta tunda gashi dai har yanzu ba ta kammalu ba.
Kiyi hakuri idan mun yi tsawon rai nan gaba bayan wanna yaki na karasa miki wannan labari. Lallai akwai bukatar na kwanta domin na sami isasshen hutu da bacci domin na sami kuzarin domin iya ci gaba da yaki. Idan gari ya waye.
Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya kwanta akan shimfidarsa yaja mayafi ya lulluba.
Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya sace shi, koda ganin hakan sai itama Hursiyya ta kwanta akan tara shimfidar taja mayafi kuma ta rintse idanu domin ta yi barci, amma sai barcin ya gagara sakamakon tunani da fargabar yadda makomar wannan gagarumin yaki zai kasance idan anci gaba dashi a gobe ba ta sami damar rintsawa ba sai da suba ta kusanto..
Sai da gari ya waye rana ta take amma sarki dujalu da yar uwarsa gimbiya Hursiyya ba su farka ba daga barci...
A wannan lokacin gaba dayan mutanen nasu
da ke sansanin tuni sun farka daga barci an yi
kalaci kuma an gama shirin ci gaba da yaki
sahun aljanu dabam da na mutane..
A wannan lokacin manyan dakarun sarki dujalu
matinu da ratiju sun tsaya a gaban rundunar
tasu suna jiran fitowar sarki dujalu domin ya
bayar da umarni....
Tsakanin rundunar sun sarki dujalu da ta su
sarki Hamraz bai wucce taku dari biyu ba sbda
dama dukkaninsu abakin kogin na bahar
sufiyan suka yada sansani., kowanne bangare
suna hango abokan gabarsu...
Lokacin da matinu ta hango abokan gaba sun
gama nasu shirin tsaf kuma sarki maharaz
sadauki inmal da sadauki hibru na tsaye
agaban rudunar tasu sun zobo ido izuwa ga
nasu matinu kawai jira suke suga sarki dujalu
ya baiyana agaba,,.
Cikin tsananin damuwa matinu ya dubi dan
uwansa ratiju yace ja ruga izuwa tantin sarki ko
lpya..
Kafin matinu ta gama rufe bakinsa tuni ratiju
yaruga izuwa can tanti sarki yake..
Yana isa ya dubi dakarun da suka
Kewaye tantin don tabbatar da tsaron yace kuyi
min iso a wajen sarki.
Kafin daya daga cikinsu tace kala sai suka jiyo
gyaran ,muryar sarki...
Nan take sarki dujalu ya fito daga cikin tantin a
cikin gagarumar shigarsa ta yaki kuma
fuskaraa cike da annuri ya dubi rantiju cikin
murmushi yace ya kai babban jarumi ka
kwnatar da hankalinka kayi sani cewa yau ba
rana bace ta gaggawa domin kuwa a yau ne za
ayi tata kare!
Ko dai muyi nasarar wannan yaki ko kuma mai
abonka gabar mu su samu wata kila ayi ragas
ina mai tabbar muku da cewa yakin da muka yi
jiya share fage ne ko kuma wasan yara akan
wanda za ayi yau.:
(TAB IJAM! DUK BAKAR GUMURZUN DA
AKAYI KUNJI PA WAI WASAN YARA YAKI
CEWA TO KUBIYO NI MUJI YAWANNAN NA
YAU ZATA KASANCE KENAN TIN DA YACE
WANCAN WASA YARAN NE SULEIMAN
ZIDANE KD.)
Yaune maza zasu gane kurensu. Yau ne kasa
da taiku zasu sha jini suyi gyatsa, kuma a
yaune tarihin jarumta zai kafa kansa a bakin
teku. Maza ka koma can bakin filin daga ka
gayawa rundunarmu cewa gani nan tafe yanzu
kuma ina zuwa za a fara wannan yaki.
A jirani zan gana da yar uwata Hursiyya.
Koda jin haka sai ratiju ya juya da sauri kuma
ya falfala da matsanaicin gdu domin yaje ya
isar da wannan sako.
Tafiyarsa ke da wuya sai sarki dujalu ya juya ya
fuskanci yar uwarsa Hursiyya suka kurawa juna
idanu.
Nan take duk biyun idanunsu suka ciko da
kwlla.
Hawayen sarki dujalu ne ya fara zubowa
sannan nata. Sarki dujalu ya sa hannu ya share
hawayen nasa yace yake yar uwata kiyi sani
cewa wannan hawayen nawa bai zubo ba
sboda tunanin zamu rabu ba. Tabbas ni na san
ba zan mutu ba a wannan yaki to amma taki
rayuwar ce bani da tabbacin zata tsira.
Babu mamaki wannan gani da nake yi miki shi
ne na karshe.
Hanya daya ce nake zaton zan iya tserar da
rayuwarki wato nasa a dauke ki yanzy a mayar
da ke cikin birninmu domin ciki gaba da tafiyar
da mulkin kasata.
A hakan ma bani da tabbacin birnin nawa zai ci
gaba da wanzuwa..
Koda sarki dujalu yazo nan a zancesa sai wani
sabon hawaye yasake gangarowa daga cikin
idanu Hursiyya ta dubeshi tace haba yakai dan
uwana ashe har ka manta da bayanin da nayi
,maka kenan a jiya da daddare??
Nifa bazan iya rabuwa da kai ba a yanzu sai dai
a ci gabada wannan yaki a gaban idanuna idan
ma mutuwa zaka yi mu mutu tare domin
muddin bana tare da kai ba zan taba samun
sukuni da kwnaciyar hankali ba...
Koda jin hakan sai sarki dujalu ya juyawa
Hursiya baya a lokacin da shima hawayen ya
sake subuto masa ya ce ai kuwa sai dai kiyi hkr
domin rabuwarmu a yanzu ta zama dole..
Yana gama fadin hakan yaka tafiya ya nufi inda
sansanin dakarunsa suke..
Koda ganin hakan sai goimbiya Hursiyya ta
yunkura da nufin ta bishi ta gudu kawai sa taji
an sureta an yi sama da ita tamkar shaho ya
dau shirwa.
Wata irin iska mai karfi taji tana busota a
sama. Koda ta dga kanta sama sau ta ga ashe
wani aljanu ne mai suna BARZARU ya dauketa wanda ya kasance
babban hadimin sarki dujalu.
Koda Hursiya taga barzaru ya juya da ita baya
don barin sansanin yakin gaba daya sai ta kwlla
ihu, ta fashe da matsanaicin kuka cikin sbda ta
gane cewa dan uwanta sarki dujalu ya
shammace ta ne ya sa a mayar da ita can gida
domin ta tsira da ga masifar wannan yaki.
Haka dai Hursiya ta ci gaba da ihu tama rusa
kukan bakin cikin har aljani barzaru ya luluka da
ita a cikin gajimare suka kule aka daina
hangosu..
* * *
ACAN Sansanin yaki kuwa lokacin da sarki
dujalu ya iso filim dagar ya tsaya a tsakiyar
matinu da ratiju sai aka fara kallon kallon
tsakanin rudunar tasu da ta su sarki Maharaz.
Kowanne bangare yana da jinsin mutane da na
aljanu dukkaninsu a cikin gaagarumar shigar
yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro.
Wasu aljanun ma ko kallomsu mutum yayi nan
take yake iya samin tabin hankali mai
dakakkiyar zuciya zai tsure da gudawa ya cika
wandonsa da iska.
A dai dai wannan lokacin ne mulaifa ta matso
gaban inmal ta tsaya tana mai rike da takobi, cikin tsananin mamaki inmal ta dubeta yace
yake masoyiya mene ne yakawo ki nan filin
yakin alhalin sarki ma yace ki yi zamanki a cikin
tanti har izuwa karshen Yakin?
Sa.adda mulaifa taji wannan tambayan sai tayi
murmushi tace ai idan har na zauna a cikin
tanti na bar masoyina yana fafatawa anan filin
daga kuma na bar mahaifina yana
gwagwarmaya ban cika jinin sarauta ba kuma
ban yiwa soyayya adalci ba.
Idan har a wannan yaki zaku mutu to ina fatan
na mutu tare da ku.
Koda Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta sai
sarkin yaki hibru ya taho gareta domin ya
rarsheta ya mai da uta can baya inda tantin
sarki yake amma sai sarki Maharaz ya sha
gabansa yace ka kyaleta.
Ai yana da kyau ta nuna gadon gidansu.
Cikin alamun tsananin mamaki da fargaba
Hibru ya dubi sarki Maharaz yace haba ya kai
abkna akan wane dalili za ka bar yarka gda
daya jal a duniya tayi wannan yaki mai tsananin
hadari alhalin ko sarrafa takobi bata iyaba?
Kuma bata da wani sihirin tsafi da za ta iya
kare kanta.
Dajin wannan batu sai sarki Maharaz yayi
murmushi gami da yar guntuwar dariya sannan
ya ce abinda nakeso da kai ya kai abkna ka
zuba ido kawai zaka sha mamaki.
Sannan ina son ka gane cewa muddin mulaifa
tana tare da inmal babu abinda zai sameta.
Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki
Maharaz ya wucce gaban rundunar da kimanin
tafiya taku goma sanan ya tsaya.
Koda ganin hakan sai shima sarki dujalu ya
wucce gaban tasa rundunar da kimanin tafiya
taku goma sannan ya tsaya..
Ya zamana cewa tsakaninsa da sarki Maharaz
bai wucce taku arba.in ba amma sbda karfin
sihirinsu kowannesu na iya jiyo numfashin
dayan.
Nana fa suka fara yin kallon kallo na yan dakiku
sannan sarki Maharaz yai ajiyar numfashi yace
ya wanan sarki kayi sani cewa yakin da muka yi
asarar
Miliyoyin rayuka.
A yau kuwa idan muka cigaba zamu iya kawar
da dukkkaninmu a karshe duk mu tashi a tutar
babu zamana cewa babu wanda ya sami
nasarar dauko TAKOBIN SAIFUL LUJARA da ke
karkashen wannan teku na bahar sufiya dake
gabanmu.
Wai shin me zai hana mu fito da wani tsarin
dabam a wannan yaki wanda zai kawo karshen
rigimar da ke tsakaninmu.
Abinda nake nufi shi ne mu ware jarumai uku
uku daga cikin mu su yaki juna.
Idan nawa jaruman ne suka kashe naka sai ka
hkr ka bar mini takokobin SAIFUL LUJARA.
Idan kuma naka jarumai ne suka kashe nawa
sai na hkr na bar maka.
Ba don komai na yi wannan tunanin ba sai
domin mu rage asarar miliyoyin rayukan da za
ayi anan gaba.
Sa'ad da sarki Maharaz yazo nan a zancensa
sai sarki dujalu ya tuntsure da mahaukaciyar
dariya kolacin guda kuma ya turbure fuska
tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace ya
kai maharaz na ji duk abinda kace kuma na
aminta da shi.
Amma bisa sharadi guda biyu.
Sharadi nafarko shine jaruman uku uku da
zasuyi wannan fafatawa ba zasu yi amfani da
karfin sihiri ba kuma sai kowa ya rantse da abin
bautarsa cewar ba zai yi yaudaraba sai dai ya yi
amdani da tsagwaron karfensa da kwarewarsa
ta yaki....


Zan ci gaba.

Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.

MAZAN JIYA
Littafi na hudu 4
Part B
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

Sharadi na biyu shine babu wanda zai zabi
abkin gwaminsa da kansa sai dai ayi kuria a
rubuta sunanyen jarumai shida a jikin duwatsu
a gwamutsasu a zubar a kasa kowa ya dauki
dutsen daya dauka shine abkin gwaminsa.
Yayin da sarki dujalu yazo nan a zancensa sai
sarki maharaz yai shiru yana tunani da nazari.
A wannan lokacin gaba dayan jamaar dake
sansanin yakin hakalinsu ya dugunzuma ainun
sbda sun san cewa idan har aka bi wannan
tsari wanda sarki dujalu yazo da shi dole ne ayi
asarae manyan abban dogaro na kowanen
bangare.
Bayan sarki Maharaz ya gama nazari da tunani
sai ya dubi sarki dujalu yace ina bukatar nayi
shawara da mutanena....
Sarki dujalu yayi murmushi yace na baka har
tsawon rabi sa a kaje jayi shawara bisa abinda
zai fisheju jai da jama arka...
Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya juya
da baya ya koma cikin ayarin rundunarsa ya ja
sadauki ratinu da Matinu gefe daya domin
suma su yi shawara.
Sarki Maharazya durfafi inda su Hibru ke tsaye
jikinsa a sanyaye fuskarsa cike da alamun
tsananin damuwa.
Da isarsa garesu sai suka kebe suka zauna a
gefe daya suka shiga tataunawa sarki Maharaz
dubi Hibru sannan ya dubi inmal yace me kake
gani dangane da shawarar da nazo da ita bisa
rage yawan a sarar miliyoyin rayukan da za a yi
nan gaba?
Hibru da inmal suka junansu suka sunkui da
kansu kas sai ga mataimakin hibru ya taho
gareshi barde KURSHAM.
Kursham ya zauna daf da sarki maharaz ya
risuna cikin girmamawa yace ya Shugabana ka
zo da shawara mai kyau amma kuma itace mafi
hadari idan ka yi la.akari da sharuddan da sarki
dujalu ya kafa.
Ka sani cewa kai kanka baka da wani abin
dogaro wanda yafi karfin sihirin tsafi kuma
gashi
An ce baza ayi amfani da tsafin ba sai dai
mutun yayi amfani da tsagwaron karfin sihirin
tsafi kuma gashi ai amfani da tsagwaron karfin
dantsensa, lallai kuwa in dau hakan za ayi to babu kai a
cikin wanna fafatawan da za ayi mutum uku
uku koda jin haka sai sarki maharaz ya dakawa
barde kursham tsawa yace wnann wacce irin
maganar banza kake yi haka?
Ka sanin cewa yadda nake kishin jamaata da
kasata bana kishin tawa rayuwar don haka
lallai dani a cikin mutane ukun da zasu yi
wannan fafatawa.
Kafin sarki maharaz ya gama rufe bakinsa tuni
sarkin yaki Hibru ya taru numfashinsa a
fusatace cikin daga murya yace dakata ya kai
abkna ka yi sani cewa wani lokacin ran mutum
daya yafi na mutane dubunanai muhimmaci.
Shin baka tunanin cewa idan aka kasheka a
farko wanna yaki jama armu zasu sami karayar
zuciya su kasa aiwatar da komai a wanna yaki?
Shin baka tunanin cewa kai bango ne babban a
filin yaki wanda idan ya fadi bamu da kwnacin
hankali a can gida da nan waje.
Kuma makiya zasu sami karfin guiwar daza su
dada zage dantse akanmu domin ganin sun
gagauta shafemu.
Abin nake so da kai shine ka amince mana mu
uku nan ni Hibru da Inmal mu wakilceka a
wannan Gumurzu da za ayi.
Koda jin haka sai sarki mahaza ya yunkura a
fusace yace ba zan taba yarda ba ayi hakan ba.
Ai mutuwa tace maza ta dada kara muku fishi
da kwarin guiwa a wannan filin daga kuci gaba
da ragargaza abokan gaba har ku karar dasu..
Da jin haka sai sarki yaki Hibru ya matso gaban
sarki Maharaz ya kusanceshi ainu yadda har
suna iya jin numfashin juna yace ya kai abkina
ka sani cewa tsawon shekaru ina bauta a
karkashinka kuma ina yi maka biyyya ban taba
kin bin umarninka ba amma a yau baza ka bi
umarnin naka ba kuma zan yi maka dole akan
ka hakura da shiga wannan yaki idan kuma kaki
to zan kashe kaina.
Koda gama fadin hakan sai hawaye ya zubiwa
Hibru aL.amarin da ya karya zuciyar sarki
maharaz kenan nan da nan shima idanunsa
suka ciko da kwallah ya rugunme Hibru yana
mai cewa hakika yau ka nuna mini cewa bani
da wani masoyi da ya fika a doron kasa don
haka na janye nawa nunfi.
Ku tafi ku ukun ku wakilceni a wannan yaki.
Zan ci gana da hangenku daga nan inda nake.
Ubangiji Durbuza ya baku nasara koda gama
fadin hakan sai sarki maharaz ya janye jikinsa
daga cikin na Hibru.
Shi ku,ma hibru sai yadubi inmal da barde
kursham yayi musu inkiyar su bishi izuwa can
filin daga.
Nan take kuwa suka bishi da sauri suka nufi
can tsakiyar filin suka tsaya.
Suleiman zidane kd)
A sanna ne sarki dujalu Matinu da Ratiju ma
suka tunkarosu.
Sai ga ya rage saura bai fi taku goma ba a
tsakaninsu sannan suka tsaya aka yi mugun
kallon kallo yan dakiku.
Nan take sarki dujalu yasa aka kawo tsakuwoyi
guda shida masu dan fadi aka rubuta sunan
kowannesu jikin tsakuwa guda sannan aka
zuba tsakuwunyi duka shidan a cikin wani
kurtu aka karkada suka hautsine a cikin sannan
aka ajiye a kasa.
Sarki dujalu ya bushe da dariya mugunta kuma
ta turbune fuska yace kowannemu daya bayan
daya zai zura hannusa ya dauko tsakuwa guda
a cikin kuttun nan.
Duk tsakuwar da mutum ya daulo to sunan
wanda ke jikin tsakuwar shine abkin gwaminsa.
Suwaye zasu fara zabar tsakuwar mu ne ko
kuma kune?
Sariki dujalu ya tambaya yana mai kallon fuskar
inmal.
Inmal yayi dan guntun murmushi mai nuna
dakewar zuciya da jarumta ya ce kune zaku
fara zaba sanna mu.
Sarki dujalu ya bushe da dariya yace ai komai
nisan jifa kasa zai fado.
Yaro yau zan kasan cewa dujalu murucin kan
dutse ne bai fito ba sai da yashirya kuma zaku
san cewa kun tabo tsulliyar dodo.
A yau ne zan karar da dukkanin wannan
runduna taku sannan na shiga cikin karkashin
kogin BAHAR SUFIYA na dauko TAKOBIN
SAIFUL LUJARA daga nan naje na dauko
MASHIN GALILLUL HARAS da HULAR
LAMSARA wato na hada MAKAMAN da zan
gagaru duniya gaba dayanta na zama sarkin ko
ina da ina.
Ka sani cewa birninku shi ne na farkon wanda
zanje na mallakeshi.
Waccan yarinyar kuwa Gimbiya Mulaifa wacce
kake tsananin so zan masheta baiwa na
wulakantata tamkar Akuya..
Kafin sarki dujalu ya gama wannan furuci tuni
zuciyar inmal ta kufulo jikinsa ya kama tsuma
don haka sai ya daka masa tsawa yace
karyarka ta sha karsha yakai wannan sarki.
Kayisani cewa nine mai yanka maka dukkan
wannan burin naka kuma bani da wani buri
wanda yafi ya zamana cewa kaine abkin
gwamina ayanzu.
Idan kowa ya dauki tsakuwarsa domin na yi
maka kisan Gilla!
Koda jin wnan batu sai sarki dujalu ya takarkare
ya bushe da dariyar mugunta sannan yace ai ni
da kai KAR TA SAN KAR ne tunda mun hada
jiki ka ji.
Ni babban bakin cikina shine rashin ganin sarki
Maharaz a cikin ku ukun nan.
Ko dayake na san bai isa ya shiga wannan
gumurzu ba tunda shi jarimtakarsa ta karfin
sihiri ce kawai...
Na so ya zama abkin gwamina na yi masa
mugun kisa a gaban yarsa da sirikinsa domin
na kunsa muku gagarumin bakin ciki.
Koda jin wanna batu sai Hibru da Inmal suka
fusata ainun suka ji kamar su zare takubbansu
su afkawa dujalu amma sai suka daure suka
tsaya suna kallonsa kawai cikin hahara jikinsu
na tsuma.
Nan take sarki dujalu ya dubi Matinu wanda ke
tsye a hannun hagunsa yace.
Maza ka sa hannunka a cikin wannan kurtu ka
zabo avkin yakinka.
Cikin hanzari Matinu ta cika umarnu ai kuwa
yana dauko tsakuwar sai aka duba aka ga
sunan sarkin taki barde kursham.
Matinu da kursham suka zubawa juna idanu
suna yiwa kansu kallon raini sbda kowannensu
gani yake zai iya gamawa da dayan a cikin
kankanin lokaci.
ABIN DA SUKA MANTA SHINE SAI AN GWADA
AKAN SAN NA KWARA!
sarki dujalu ya dubi su inmal yayi murmushin
mugunta yace yanzu kuma kune zaku zaba ko
mu?
Da jin haka sai inmal ya yunkura domin ya
sanya hannunsa a cikin wannan kurtu amma
sai Hibru
Hibru yai sauri ya sha gabansa yace dakata
ya kai dana ai nine yakamata na zaba yanzu
kuma da izinin ubangiji garzuba sarki dujalu
zan zabo a matsayin abkin gwamina.
Cikin alamun firgici da tsananin tsoro inmal
ya dubi Hibru yace haba ya kai abbana ina
kai ina tarar sarki dujalu alhalin ka sancewa
ya fika jarumtaka nesa ba kusa ba?
Page 18
ni kaina da nake da kuruciya a jikina na
tsorata da shi bare kai da yanzy girma ya
fara riskarka..
Yayin da yazo nan a zancensa sai Hibru ya
numfasa yace yakai dana ai ni burina ke nan
na kara da shi domin ya kasheni ba tare da
naga yadda zai kashe kaba.
Domin mutuwar tawa ta fiye mini sauki da
ganin taka.
Koda sarkin yaki Hibru yazo nan a zancensa
sai Inmal yaji ya kamu da tsananin kaunarsa
gami da matukar tausayinsa don haka bai
san saadda hawaye ya subuto masa ba.
Hibru yai sauri ya kau da fuskarsa ga barin
kallon inmal don haka shima ya zubar da
hawayen kawai sai yaje inda wannan kuttu
mai tsakuwoyin yake ya zura hannunsa a
cikin ya dauko tsakuwa guda koda ya fiddo
tsakuwar aka duba sai aka ga sunan sarki
dujalu ne.
Nan fa sarki dujalu ya kamu da tsananin
farin ciki yayi kururuwar murna.
Shi kuwa inmal sai yakamu da tsananin
bakin ciki ya cigaba da zubar da hawaye
sbda ya sancewa lokacin rabuwarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login