Showing 30001 words to 33000 words out of 71576 words
Chapter 11 - MAZAN JIYA 4 Rubutawa By Abdulaziz Madakin Gini.txt
cikin gagarumar shigar Yaki, ga wasu manyan Dakarunta su goma suna take mata baya.
Zubaina ta dubi matar da kyau a cikin nutsuwa ta ce, "Ya ke YALDISA ina wannan bakon saurayi?"
Yaldiṣa ta risina cikin girmamawa ta ce, "Ya Shugabata, rabo na da bakon saurayi tun da muka fito tare daga gidan abinci ya tambaye ni hanyar kasuwa na nuna masa anan muka rabu".
Koda jin wannan batu sai Sarauniya Zubaina ta yi murmushi mai nuna alamun rashin yarda sannan ta hankade Yaldisa ta fadi gefe guda.
Kai tsaye Zubaina da Dakarunta suka kunna kai izuwa cikin falon.
Sarauniya Zubaina ta zauna akan kujera sannan ta umarci Dakarunta da su caje ko ina na gidan.
Lokacin da Yaldisa ta taso ta zo gaban Zubaina ta durkusa tana mai sunkui da kanta kas ba tare da ta nuna wata alama ta tsoro ba ko rashin gaskiya.
Zubaina ta sake duban Yaldisa ta yi murmushi a karo na biyu sannan ta ce, "Ya ke Yaldisa yau shekara bakwai ke nan kina aiki a karkashina. Na san dukkan halayenki, ke karuwa ce wadda in dai za ta sami kudi babu abin da ba za ta iya yi ba. Ki gaya mini gaskiya tun kafin lokaci ya kure miki. Idan na gano cewa kina da hannu akan ɓoye wannan bako daga baya, kin san halina, ba sani ba sabo. Ban san tausayi ba kuma ban san hakuri ba, kashe ki zan yi kawai".
Yaldisa ta dago kai ta dubi Zubaina ta ce, Ya Shugabata tsawon shekaru bakwan da nake aiki a tare da ke ban taba yi miki karya ba, wannan ya isa ki aminta da ni.
Zubaina ta jinjina kai gami da ajiyar zuciya ta ce, tabbas abin da kika fada gaskiya ne, amma ai a wajenki kudi su ne gaba da komai. Ni na abbatar da cewa za ki iya siyar da iyayenki ma muddin za ki sami kudi.
Gama fadin hakan ke da wuya sai ga Dakarun Zubaina sun dawo gabanta.
Shugabansu wanda ake kira SADAR ya risina ce, "Ranki ya daɗe, babu kowa a cikin gidan nan".
Koda jin haka sai Zubaina ta mike tsaye ta nufi bakin kofa, Dakarun nata na biye da ita.
Har ta sa kafarta guda a waje sai ta juyo ta dubi Yaldisa ta ce. "A ko yaushe za mu iya kawo ziyarar bazato, Kar ki manta hukuncin kisa ne a kanki idan na kama ki da laifin boye mai laifi".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Sarauniya Zubaina da Dakarunta suka fice daga cikin gidan. Yaldisa ta mai da Rofar ta rufe sannan ta jingina bayanta a jikin kofar tana mai yin doguwar ajiyar numfashi cikin tsananin tsoro.
Ba ta matsa daga inda take tsaye a jikin Rofar ba sai bayan lokaci mai tsawo bayan ta tabbar da cewa su Sarauniya Zubaina ba sa kusa sannan ta nufi dakin barcin nata.
Tana shiga sai ta iske Shaddadu a kwance akan gadonta har ma ya kama barci abinsa tamkar ba shi aka zo nema ba.
Cikin fushi ta girgiza gadon, Shaddadu ya mike zaune ya dube ta cikin mamaki ya ce, "Lafiya za ki katse mini barcina alhalin a cikin gajiyar tafiya nake?"
Koda jin haka sai Yaldisa ta sake fusata ta ce, "Au! Kai ta barci ma kake ba ta raina ba? To tsaya ka ji, ga kudinka da ka ba ni, ba zan iya siyar da rayuwata ba a kan dirhami ashirin kacal da ka ba ni".
Koda jin haka sai Shaddadu ya yi murmushi, nan take ya janyo jakar guzurinsa ya bude ya sake debo dirhami ashirin ya mikawa Yaldisa ya ce, ga wannan ki kara. Ni dai ki kyale ni na yi barcina.
Yaldisa ta tankwaɓe hannun Shaddadu dinaren ya zube kasa ta yı masa tsawa ta ce, "Ran nawa zan siyar maka akan dinare arba'in? Ka ga ni ba na bukatar kudinka kawai ka tashi ka bar mini gida don ba za ka janyo mini hukuncin kisa ba a banza".
Maimakon Shaddadu ya yi fishi sai ya yi dariya kuma ya dauko kullin dinarensa gabadaya ya cilla wa Yaldisa ta cafe ya ce. "Gashi nan gabadayan abin da na mallaka ke nan in kin so ki kyale ni na kwana. Na yi miki alkawarin babu abin da zai taɓa lafiyarki koda asirinki ya tonu, kuma gobe da safe zan bar miki gidanki".
Koda gama fadin hakan sai Shaddadu ya koma ya kwanta akan gadon yana mai juya mata baya.
Kafin cikar dakika dari da ashirin ya fara munshari. Al'amarin da yai matukar bai wa Yaldisa mamaki ke nan kuma ya ba ta dariya.
Nan dai ta sunkuya ta tsince ragowar wannan dinaren da ya zube kasa ta zuba a cikin kullin wanda aka ba ta ta boye, sannan ta je ta ci gaba da dan aiyukanta na gida.
Har dare ya yi Shaddadu bai farka daga barci ba. Lokacin da Yaldisa ta ji ta soma jin barci har ma tana gyangyadi daga zaune sai hankalinta ya tashi domin dama can tsoro ne ya hanata zuwa ta kwanta, saboda tana ganin cewa a kodayaushe Dakarun Sarauniya Zubaina za su iya kawo ziyarar bazato. Da dai ta ga tana jin barcin sosai sai ta mike tsaye ta nufi cikin dakin barcin. Tana shiga ta ga har a sannan Shaddadu barci yake yi.
Koda ta kura masa idanu ta dube shi sama da kasa ta ga irin tsananin kyawun fuskarsa da kyawun surar jikinsa, sai nan take ta ji ta kamu da tsananin sha'awarsa.
Sai a sannan ne ta gane cewa ashe da can tsoro ne ya sa ta kasa yi masa kallon nutsuwa bare ta san cewa kyakkyawa ne.
Nan dai Yaldisa ta kautar da tsoro ta cire tufafin jikinta ta sanya na barci sannan ta kwanta a bayan Shaddadu.
Koda ta kai hannu ta tabo Shaddadu sai ya mike zumbur! A fusace ya dube ta ya daka mata tsawa da karfi.
Yaldisa ta razana ainun har sai da hantar cikinta ta kada. Shaddadu ya ce. "Na gaya miki ba na bukatar mace a kusa da ni. Ki sauka daga kan gadon nan tunda dai biyanki na yi kudin komai a gidan nan".
Cikin alamun tsananin mamaki Yaldisa ta sauka daga kan gadon ta dauki matashin kai guda daya ta dawo falo ta kwanta a kasa.
Nan fa Yaldisa ta ci gaba da mamakin wannan bakon saurayi har barci ya sace ta ba ta sani ba.
SHADDADU FA YANA DA GASKIYA. DOMIN KOMAI TUMBATSAR SADAUKI MATUKAR YA HADA SHAGALA DA MACE SAI AN YI NASARA A KANSA. SADAUKI HANTARU IZINA A GARE MU.
Lokacin da gari ya waye sai Yaldisa ta ji ana tashinta daga barci. Koda ta farka ta bude idanuntasai ta yi arba da wata mace tsohuwa tukuf! Zaune gabanta.
Cikin alamun tsananin tsoro ta mike zumbur! Ta koma jikin bango ta takure jikinta tana mai kallon tsohuwar a firgice ta ce, "Wace ce ke kuma yaya aka yi kika shigo gidan nan? Shin kin samu wani ban da ni a cikin gidan nan ne?"
Koda jin wannan tambaya sai tsohuwar ta bushe da dariya, nan take ta rikide ta zama Shaddadu. Mamaki ya sake kama Yaldisa ta ce, "Ashe ma kai ne? Mene ne dalilin da ya sa ka rikide izuwa siffar wannan tsohuwa".
Shaddadu ya yi ďan guntun murmushi a gare ta sannan ya ce, "Ai jiya bayan kin yi barci ya yin dà dare ya raba sai na tashi na rikide izuwa siffar wannan tsohuwa na ci gaba da barcina. Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai ga wadansu hadimai na Sarauniyarku sun shigo cikin gidan nan da karfin sihirin tsafi, suka kama bincike.
Koda suka shigo cikin dakin barcinki sai suka ga tsohuwa akan gadonki tana shara barci har da munshari, sai suka juya suka fice daga gidan gabadaya.
Wannan shi ne dalilin da ya sa na sauya kamannina don kada a zo a gan ni na shafa miki kashin kaji.
Sa'adda Shaddadu ya zo nan a zancensa sai Yaldisa ta cika da tsananin mamaki da murna. Shaddadu ya dube ta ya ce, to ni yanzu nan zan tafi neman abin da ya kawo ni garin nan don haka sai dai na yi miki bankwana.
Yana gama fadin hakan sai ya koma cikin dakin da yai barci ya dauko Mashinsa na GALILUL HARAS wanda ya rataye shi a jikin bango sannan ya dauko karamin Tsuntsun nan nasa na tsafi ya dora shi akan kafadarsa.
Koda ya fito falo Yaldisa ta yi arba da Mashin da kuma wannan Tsuntsu sai ta dube shi cikin mamaki ta ce, "Yaushe kuma ka sami wanna Mashin da wannan Tsuntsun? Ni dai a sanina jiya ba ka tare da su".
Koda jin wannan tambaya sai Shaddadu ya yi murmushi ya ce, "Ai babu mai ikon ganin wadannan abubuwa nawa face da amincewata."
Yana gama fadin hakan sai ya sake rikidewa ya zama wannan tsohuwa wacce saboda tsananin tsufa sai da ta rankwafa ta yi doro.
Shi ma Mashin Galilul Haras sai ya rikide ya zama sanda. Tsohuwar ta dogara sandar ta nufi bakin kofa za ta fita, sai Yaldisa ta ruga ta sha gabanta ta ce, "Haba ya kai bako, yaya za ka kwana a gidana na ba ka abinci kuma na ba ka makwanci duk da dai siya ka yi amma za ka tafi ban san koda sunanka ba? Ka yi sani cewa ina da wadansu 'yan tambayoyi guda uku rak a gare ka wadanda na ke son amsarsu kafin mu rabu.Tambayata ta farko ita ce, Mene ne dalilin da ya sa kake neman wata Jaruma mai suna ZIYA'UL HAK?
Tambaya ta biyu, ina son na sani idan kai namiji ne cikakke, ko kuwa ba ka da lafiya?
Tun da na fara karuwanci ban taba haduwa da namijin da bai yi sha'awata ba sai kai saboda kyawuna da kyawun surata.
Tambaya ta uku ita ce, Yaushe za ka bar wannan garin namu?"
Sa'adda Shaddadu ya ji wadannan tambayoyi sai ya yi murmushi mai taushi ga Yaldisa ya ce, Game da tambayarki ta farko, amsarta ita ce, ina neman Jaruma Ziya'ul Hak ne saboda ta kásance babbar abokiyar gabata a duniya, muddin zan yi arba da ita sai na hallaka ta.
Amsar tambayarki ta biyu kuwa, ni namiji ne cikakke mai lafiya, amma mahaifiyata ta cire mini sha'awar 'ya mace da karfin sihiri, kuma ta hore ni da kaidinku tun ina karami don haka, a rayuwata babu abinda na tsana kuma nake tsoro sama da mata.
Game da amsar tambayarki ta karshe ita ce ba zan bar wannan gari naku ba har sai na tabbatar da cewa abokiyar gabata Jaruma Ziya'ul Hak ba ta cikinsa. Na barki lafiya sai watarana idan da rabon mu sake saduwa.
Koda gama fadin hakan sai tsohuwar ta je ta bude kofa ta fice daga cikin gidan.
Ita kuwa Yaldisa sai ta ji ta kamu da tsananin damuwa da bakin ciki tamkar wacce ta rabu da wani dan uwata shakikinta kuma rabuwa ta har abada wacce ba za a sake saduwa ba.
Kawai sai Yaldisa ta ji idanunta sun ciko da kwalla har hawaye ya subuto ma ta.
A sannan ne ta gane cewa lallai ta kamu da son Shaddadu ne, kuma a sannan ne ta tuna cewa ai bai gaya mata sunansa ba.
Nan take Yaldisa ta ruga da gudu izuwa kofar gida. Tana fita ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa amma ba tá ga alamar Shaddadu ba, ya 6ace ɓat! Tamkar daukewar ruwan sama, kawai sai ta yi ajiyar zuciya ta juyo ta koma cikin gidants zuciyarta na cike da damuwa da takaici.
(KE YALDISA. AI WUTSIYAR RAKUMI TA YI NESA DA KASA)
****
Lokacin da Shaddadu ya fito daga cikin gidan karuwa Yaldisa a cikin siffar wannan tsohuwa yana dogara sanda sai yai tsafi wani dan koko ya bayyana a hannunsa.
Nan take ya kunna kai izuwa cikin gari yana bara tamkar tsohuwa ce mai neman abin da za ta ci. Sai da ya shafe sa'a guda yana yawon bara bai hadu da wanda ya ba shi koda ruwan sha ba bare abinci ko durhami guda. Al'amarın da ya ba shi mamaki ke nan, duk da cewar shi rayuwarsa a can Birnin Kufa bai taba yin bara ba asali ma a gidan Sarauta ya taso cikin gata amma ai ya san cewa mutanen gari suna taimakon Almajirai.
Abin da bai sani ba shi ne, game da al'adar mutanen wannan gari ba a yin bara a ko ina sai dai Almajiri ya je ya sami wuri a bakin hanya ya zauna ya yi bararsa in yaso masu wucewa mai niya ya ba shi.
Shaddadu na cikin yawon barar tasa ne ya hango Almajirai a gefen hanya kimanin su goma maza da mata a zaune sun yi layi mutane masu wucewa suna ta ba su sadaka.
Cikin murna Shaddadu ya karasa inda Almajiran suke a cikin siffarsa ta tsohuwa tukuf gami da dogara sanda da kyar.
Yana isa gare su sai ya tsaya ya fara kokarin zama kusa da wani tsoho wanda ya fi shi tsufa nesa ba kusa ba.
Amma bisa mamaki sai ya ga tsohon ya mike da sauri cikin kuzarinsa tamkar ba tsohon ba ya taimaka masa ya zaunar da shi kuma ya mika masa sandarsa ya rike.
A sannan ne suka dubi juna cikin murmushi sai tsohon ya dubi tsohuwar ya ce, "Ya ke wannan almajira in ce ko ke bakuwa ce a garin nan? Na ga kina bara akan hanya alhalin ba haka dabi'ar g garin nan take ba?"
Koda jin wannan tambaya sai Shaddadu ya ji bai amince da wannan tsoho ba don haka sai ya ɓoye masa gaskiyar al'amari ya ce, "A'a ni ba bakuwa ba ce a wannan gari amma dai daga kauye na zo nan. Wannan ne dai karon farko da na fara yin bara anan.
Koda jin haka sai tsohon ya sake yin murmushi ya ce, "To ai a nan ba a yin bara a ko ina sai a gefen hanya don haka sai ki kula saboda gaba".
Da jin haka sai tsohuwar ta maidawa tsohon martanin murmushi kuma ta yi masa godiya.
A daidai wannan lokaci ne suka hango Sarauniya Zubaina ta tunkaro su bisa doki tare da Dakarunta su ma bisa dawakai kimanin su dari biyu.
Da isowar Sarauniya Zubaina gaban Almajiran sai ta sauko daga kan dokinta ta shiga rabawa Almajiran sadakar dirhami guda-guda.
Duk wanda ta zo kansa sai ta kura masa idanu ta yi wani surkullenta na tsafi domin ta gano akwai bakon saurayin nan a cikinsu wanda ya karya dokarta ya shigo gari ba izini ya ɓalla kofar garin kuma ya yi wa Dakaru duka. Haka dai Sarauniya Zubaina ta ci gaba da bai wa almajiran sadaka har ta zo kan wannan tsoho wanda ya taimaki tsohuwa.
Da zuwanta kan tsohon sai ta tsaya cak! Ta dade tana kallonsa kuma tana surkullenta a kansa har sai da gumi ya tsattsafo mata amma ba ta gano komai ba.
A sannan ne ta yi ajiyar numfashi ta dubi tsohon ta ce, "Ya kai wannan almajiri shin ba ka ga wani bakon saurayi ba a cikin garin nan wanda ya shigo mini gari ba izini kuma ya balla mini kofa?"
Dattijon ya gyada kai ya ce, "Ban gan shi ba amma dai na ji ana zanċensa a cikin nan kuma da zarar na gan shi zan gaggauta zuwa fada na sanar".
Koda jin haka sai Sarauniya ta yi murmushi sannan ta matsa gaba wajen tsohuwar ta ba ta sadaka tana mai kura mata idanu gami da yin Wannan surkulle.
Ai kuwa sai da ta ɓata lokaci fiye da sa'adda ta tsaya a gaban wannan tsoho har ya zamana cewa ta jike sharkaf da gumi.
Sarauniya Zubaina ta sa hannu ta share guminta tana mai ajiyar zuciya sannan ta dubi tsohuwar ta ce. "Ya ke wannan almajirila yaushe ki ka zo garin nan? Tabbas ban taba ganinki a cikin wannan birnin ba.
Koda jin wannan tambaya sai tsohon almajirin ya tari numfashin tsohuwar almajirar ya ce, "Ai wannan Almajirar bakuwa ce daga kauyen LAIRUF, ba ta ma saba yin bara a nan ba.
Dazun nan muka hango ta tana yin bara a cikin gari sai da ta zo nan muka yi mata bayanin al'adar garin nan".
Sa'adda Sarauniya Zubaina ta ji wannan batu sai ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta mike ta dubi Almajiran da ke zaune a wajen gaba dayansu ta ce "Duk sa'adda dayanku ya ga wani bakon Jarumi saurayi ya hanzarta zuwa fada ya sanar da ni, zan ba shi lada na adadin dukiyar da har ya mutu ba zai iya cinyewa ba".
Koda jin wannan batu sai gabadayan Almajiran suka kama shewa suna yi wa kansu fatan su dace da samun wannan lada.
Nan dai Sarauniya Zubaina ta je ta kama dokinta ta hau ta wuce gaba Dakarunta na take mata baya. A lokacin ne wata rundunar daban ta Dakarun Sarauniya Zubaina suka shigo cikin garin suka barbazu a ko ina lungu-lungu, sako-sako suna neman bakon Jarumi.
Koda wannan tsohon Almajirin ya hango abin da ke faruwa sai ya dubi tsohuwar Almajirar ya ce, "Kai al'amarin nan da ban mamaki yake. To wai shin shi wannan bakon Jarumi wane irin hatsabibi ne haka? Tun jiya ake nemansa a garin nan amma an rasa inda yake.
Anya kuwa shi ma bai kasance hatsabibin matsafi ba?"
Koda jin haka sai tsohuwar ta ce, "Ai kai ma ka san ruwa ba ya tsami banza.
Duk yadda aka yi wannan bakon Jarumi shi ma ya taka babban matsayi a tsafi da jarumtaka, in ba don haka ba da tuni Sarauniyar garin nan ta kamo shi tunda na ji an ce ita ma shahararriyar matsafiya ce kuma Jaruma".
Tsohon Almajirin ya gyada kai sannan ya ce. "Tabbas zancenki dutse ne. Yanzu dai ga shi mun sami babbar dama bisa tayin da Sarauniya ta yi mana.
Ya ke wannan Almajira tunda dai na ga kina da kokarin yawo a garin nan sai ki zuba ido da kyau da zarar kin ga bakon Jarumi ki hanzarta zuwa nan inda muke zama ki zo ki sanar dani tunda kin ga ni na fiki kwarin jiki sai na garzaya fada na sanar da sarauniya.
Na yarda ki sam mini ladan da Sarauniya za ta bayar ba sai mun yi raba dai-dai ba.
Ni burina kawai shi ne, a kama wannan Saurayi saboda ya ci mutuncin garin nan kuma ya keta alkadarin Sarauniya. Sa'ad da tsohuwar Almajirar ta ji wannan batu sai ta numfasa ta ce. "Babu komai lallai zan yi kamar yadda ka bukala.
Amma ina