Showing 24001 words to 27000 words out of 34864 words
Chapter 9 - Cin Amana Ko Fansa (1 to End) Compelet By Zahra Muhammad Mahmud.txt
da hayaniya wasu nacewa Sun yarda wasu nacewa basu yarda ba.
Abban Khairat ne ya tsawatar musu ta hanyar cewa.
"Ba shawararku muke soba abu d'aya nasani ko duka duniya gatan Khairat ne sena aurawa Hydar Yasmeen yanzu batare da bata lokaciba, ko kunaso ko bakwaso tunda nidasu munaso ya wadatar"yana gama fad'in haka yasa hannunshi a aljihu yaciro bunch d'in d'ari biyar dubu hamsin kenan ya d'aga sama yace.
"Ni Alhaji Mukhtar Abubakar uba ga Hydar ina nemarwa d'ana Hydar auran y'arku Yasmeen abisa sadaki naira dubu hamsin,idan kun amince waliyyin Yasmeen yafito ya bani auranta".
Ihu Khairat tasa ta je ta kama k'afar Abban nata tana kuka tana fad'in.
"Abba karka tarwatsa farincikina wlh bazan iya kishi da Yasmeen ba tafini komai, Abba kishi da ita azaba kawai zansha mace irin Yasmeen aka had'ata da kishiya wlh seta kashe kishiyar da bak'in ciki don Allah karka yimin haka natuba kagafarceni don Allah".wani kyakkawan mari Abba yasakarmata wanda yatilastamata ganin wucewar wutar nefa a waya, agigice tasaki k'afarshi takama ta Abban Yasmeen tana rok'onshi,rasa yazeyi da ita yayi kawai rungumeta yayi yana rarrashinta dan zuciyarshi tafi tata k'una kawai de anfi k'arfinsane.
Abban Khairat ne yasake nanata buk'atarsa tanemawa Hydar auran Yasmeen inda yabuk'aci waliyyin Yasmeen ya fito Amman gaba d'ayansu ba wanda ya motsa hakanne yasa yace.
"Hydar da Yasmeen kuzo muje masallaci a d'aura muku aure nan banida wata darajar daza tasa su bani auran kutaso muje" ya mik'e yana shirin ficewa.
Da gudu Abban Yasmeen yaje ya kama k'afarsa yana fad'in.
"Yaya don Allah karka tonamana asiri kayi hak'uri karkayi fushi damu inde waliyyine gani zanmata walicci don farin cikinka kawai badan suba kayafemana don Allah".
Dakyar Abban ya hak'ura yakoma yazauna nandanan aka fara karanto sharudd'an aure yana amsawa daga k'arshe yamika sadaki aka d'aura auran Hydar da Yasmeen cikin k'ank'anin lokaci.
Khairat tana ganin angama d'aura auran ta yanke jiki ta fad'i k'asa sumammiya da gudu sukayo kanta Zasu Kawo mata agaji Abba yadaka musu tsawa yace.
"Duk Wanda yasake ya tab'ata wlh senayi Shari'a dashi,dukanku ku watse a gurinnan na sallami kowa kubarta ta mutu ma intaso, mugun iri zamu rage" ya fad'i cikin tsananin fushi wanda ke nuni da abinda yafad'a ze iya aykatawa.
Jiki a sanyaye d'aya bayan d'aya suka dunga ficewa a gidan har kowa yafice amman Hydar na tsugunne a gabanshi kallonshi yayi yace.
"kai me kake jira dabaka fitaba?".
Kukane ya kubcewa Hydar sabida yayi imani duk abinda Abba yakeyi dauriyace kawai dason k'arfafa zumunci amman ba wanda za'awa y'arsa haka komai laifin da tayi beji zafiba,cikin kuka Hydar yace.
"Abba kayimin dukkan hallacci kuma nagode kuma zan kasance me maka biyayya akowanne al-amari sede yanzu Abba zuciyata tagaza yimaka biyayya kayi hak'uri wlh bazan iya ganin Khairat cikin wannan yanayin natafi nakyaleta ba" yana gama fad'in hakan ya nufeta d'aukarta yayi kamar gawa yafice agidan motarshi yanufa da ita ya kwantar da ita abaya yashiga yatada motar yanufi asibiti da ita.
Abba ko zuciyarsa da tayi bak'ik'k'irin abisa abun da yafaru tabbas dauriyace kawai yakeyi Amman kulawar da Hydar yanuna ga Khairat a gabansa yasa duk wani b'acin Ransa yanemeshi ya rasa tabbas ya yarda Hydar k'addarace ta fad'a masa nason auran Yasmeen amman bawai dan ya shirya wulak'anta Khairat ba, wani farinciki yaji yana shigarsa tabbas yayi abinda yadace Allah yabasu zaman lfy.
Yasmeen ko duk inda tashiga se gulmarta akeyi ana kyararta,wasu suyi agaban idonta wasu kuma suyi abayan idonta.
To kunsan halin mutuniyar taku ba tsaron kowa takejiba dan haka Bud'ar bakinta se cewa tayi.
"Ayyiriririy ni Amarya a Gidan Hydar tunda bak'inciki yasa kun Kasa yimin y'ar gud'ar da akewa Amarya yayinda aka d'aura mata aure toni nayiwa kaina,kuma wlh komai zakuce daga bayane tunda nariga nazama mallakinsa Wanda ku baku isa ku rababa dan haka kun dade baku zageniba"ta fad'i cikin isa ita duk zatonta iyayenta basa cikin gidan shiyasa tazage ta karkad'awa masu gulmar tata rashin kunya.
Wuf taji an damk'ota ta baya Umman tace kan tayi wani yunk'urin guduwa tariga ta rik'eta nanfa tashiga dukanta kamar zata kasheta dangin suna kallo bawanda yazo ya ceceta ita kuma takasa gudu Umman ko cigaba take da dukanta iya k'arfinta Yasmeen tun tana kuka har muryar ta dusashe da sauri Fatima tazo ta kama Umman Da kyar takaita d'akin da ba kowa tace cikin kuka.
"Haba Umma meyasa kike hakane?dukan dakike matane ze warware auran da aka riga aka d'aura? koko shine ze shafe abinda yafaru,?kidubafa kiga ko kara cikinsu bawanda yamiki kina dukanta amman bawanda ya ceceta wanda aka'ida hakan ba dede bane,Umma duk abinda kayi se anmaka, meyasa baki dauki hakan a matsayin sakayyace Allah yayimin ta wannan hanyarba? nide gaskiya kidena dukanta haka shi kanshi mijinta inyaji kindaketa wlh girmanki ze zube a idonshi tunda son da yake mata banawasa bane Amman kiyi hak'uri inna batamiki rai".
Ajiyar zuciya umman tayi sannan tace.
"Fatima rainane yab'aci badan komaiba sedan ruk'on da Khairat tayimata na tsakani da Allah amman bawai ina Jada hukuncin Allah bane, bakomai bazan kuma dukantaba,matuk'ar batazo inda nakeba".
Kamal ne yace Fatima ta fito su tafi gida Abba yace su wuce gida shiyasa da zasu wuce ta kama hannun Yasmeen suka tafi tare dan bazata barta ummansu ta Illa tata ba itama lokaci yayi dazatawa Y'ar uwarta rana, tunda tasan komai Yasmeen tayi Dan ita tayishi.
wannan kenan
Maman Yusuf.
ππππππππ
*CIN AMANA KO FANSA*
ππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*Nobody is like you Nobody is like u, nobody cares 4 u, nobody misses u, nobody wants to see u good, nobody is ur best fr, nobody is happy with u.... dont cry.......my name is nobody.Rumaysa Lego's am always with you, take care*
*page 59-60*
Ko a mota kamal da Fatima se rarrashinta sukeyi da kalamai masu dad'i a haka har suka iso gidan.
Kaitsaye ruwan wanka me zafi Fatima ta had'awa Yasmeen sabida ta gargasa jikinta abinka da farar mace ko ina shatin dukane ajikinta yayi jawur, Da kyar tasamu tayi wankan kayan Fatima tasa dan ba tazo da kayantaba.
Indomie Fatima ta dafa mata wacce tasha had'in kayan lambu da hanta da kwai,Yasmeen duk soyayyarta da indomie wannan kasa ci tayi tanajin zafin abinda mahaifiyarta tamata wanda take kallonsa amatsayin rashin k'aunane yakawo hakan, tunda ko ita Khairat uwar laifin ay nata iyayen basuyi mata hakaba,kuka tasa sabida abun na cimata rai sosai.
Fatima ce tajiyo sautin kukanta tashigo d'akin da sauri ta dafata tace.
"Yasmeen wannan kukan ya isa haka inde baso kike kirasa hawaye gabad'ayaba, yadace kiyi shuru haka,inma akan abinda umma tayimikine namata magana kuma ta fahimci bata kyautaba Danhaka ki share hawayenki kinji k'anwata".
Share hawayen tayi tana kallon Fatima tausayinta nadad'a kamata,fatima ta fahimci hakan dan haka dariya tayi kawai tajawo kwanon abincin tashiga bata abaki harta cinye.
Hydar suna isa asibiti emergency ward aka kaita likitocine suka rufu akanta seda suka kwashe awa biyu akanta sannan ta farfad'o amman jininta yayi mugun hawa fiye da tunani, kwantar da ita sukayi awani d'aki namusamman anyimata allurar bacci dan haka bacci takeyi anason kwakwalwarta tasamu hutu.
Hydar ganin asibitin akwai kulawane yasa yabaro asibitin yadawo gidansu Khairat d'in anan yamusu bayanin abinda ke faruwa jiki na b'ari Umman Yasmeen ta d'auko mayafinta ita da wasu acikin y'an uwa tabishi zuwa asibitin lokacin dasuka je Khairat ta farka se kuka takeyi Hydar ne yashawarci likitocin akan ko zasu sake yimata allurar baccin ba musu suka sake danna mata wata takoma baccin.
Ganin dare yafarayine yasa Hydar mik'ewa ze tafi gida sabida Umman Yasmeen ce zata zauna da ita a Asibitin,sallama yamata bayan yaajiye mata kud'i koda buk'atarsu zata taso kamin yazo gobe sannan ya wuce.
Se yanzu yatuno da Yasmeen amman d'azu sam yamanta da ita sabida tashin hankalin dayake ciki gameda rashin lafiyar Khairat,waya yaciro yakira number d'inta ga mamakinsa Fatima ce ta d'auka bayan sun gaisa yace mata.
"Ina Yasmeen d'in take?".
"gatanan a gidana bata danjin dad'ine shiyasa"inji Fatima bayan sun had'a ido da Yasmeen d'in dake zaune tana jinsu.
"Oh my God gashi bansan gidanki ba Fatima turomin address Amman de jikin da sauk'i ko?".
"Eh to ba laifi da sauk'in zamuce bari na turo maka address d'in"
Amsawa yayi agaggauce dan gaba d'aya hankalinshi yatashi fiye da wanda yayi alokacin Khairat d'in,kallon wayarshi kawai yakeyi har text d'in address d'in yashigo da sauri ya Karya kan motar yanufi unguwar su fatiman besha wuya ba yagane address d'in,yana isa yakira yashaida musu gashi a k'ofar Gidan.
Yasmeen dariya kawai take kyalkyalawa lokacin da Fatima ke zuba masa K'aryar wai bata da lafiya har zuwa yanzu da Fatiman ke koyar da ita salon siye zuciyar miji.
Kissa da kisisina Fatima tashiga koyawa Yasmeen ta yadda zata zauna Lafiya da Khairat dan tasan Khairat farin sani badaga baya bace wajen wannan fannin,wani abun in Fatima ta fad'i Yasmeen dariya take harda hawaye, itade Fatima bata bi takanta abinda ze fishsheta take koyamata.
Wani turare Fatima ta shafawa Yasmeen sannan ta dunga jaddada mata abinda zata ce in Hydar d'in yashigo dade duk abinda yakamata seda takoya mata sannan tasa ta kwanta akan gadon ita kuma taje d'ayan d'akin inda kamal keta wasa da meemee ta sanar dashi zuwan Hydar yaje yashigo dashi.
Ba musu kamal yaje yashigo dashi cikin gidan kai tsaye har d'akin da Yasmeen d'in take yakaishi sannan suka sake gaisawa da Fatima daganan suka basu guri,a rud'e ya isa kan gadon yazauna rasa me zemata yayi kawai se yamik'a hannu ya d'agota cak yad'ora akan cinyarsa, itako kamar yadda Fatima Ta koyar da ita langabewa tayi ajikinshi tana kuka mara sauti sosai tana wani d'an zazzamewa ajikinshi.
Hankali atashe yasake rungumota yace.
"Babyna meyasameki haka? fad'amin abinda ke damunki"yatambaya cike da nuna kulawa.
Kamar yadda Fatima ta koyamata,narkewa tayi ajikinshi dakyar tace.
"K'irjinane yake wani irin abu nima bansan komeyeba"ta fad'i cikin lafazinta med'auke da tsabagen kissa aciki.
D'agota yayi yana kallon k'irjin yace, "dede inane yake miki ciwon?".
Ho y'ar nema,ay seta nuna masa dede saman na shanunta,da sauri yacire hijab d'in dake jikinta yanak'arewa gurin kallo,hankalinshi ne yafara tafiya ga wani asirtaccen k'amshi dake fitowa ajikinta yana k'ara tadamishi da hankali.
Dakyar ya iya kai hannunshi kan gurin πjinin jikinsu duka seda yadena ayki na wani lokaci bama kamar Yasmeen da tsoro yakamata, dan ita inbanda ita ba wanda hannunshi yatab'a kaiwa wannan gurin se yau Hydar daya kai,ya lura da tsoronnata Amman seyayi kamar be luraba yaci gaba da shafa gurin duk azuwan yana ganin inda ke ciwonne da kyar ya iya d'auke hannunshi,koda yace tazo suje asibiti k'i tayi dan haka shantakewa yayi agidan se shad'aya yabar Gidan.
washe gari da safene yasamu damar yiwa iyayensa bayanin komai murna mahaifinshi yayi masa daga bisani yatafi gurin Abban yasake yin godiyar,gida yadawo yad'auki mahaifiyar Hydar d'in sukaje asibiti gaida Khairat.
Me gyaran amare Fatima ta d'aukowa Yasmeen tashiga gyara Yasmeen gyara bana wasaba dan Fatima cewa tayi ak'ure maneji wajen gyarata, ayko me gyaran ba ha'inci nanda nan Yasmeen tafara haskawa ciki da waje.
Maman Yusuf.
ππππππππ
*CIN AMANA KO FANSA*
ππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*Never cry for those who donot deserve ur tears but who deserve your tears never let you cry,AMINA SANI, MAMAN SAHIBA,MAMAN MUALLIM. am much more appreciate your care and support thanks stay nice.*
*page 61-62*
Kwanan Khairat bakwai a asibiti sannan aka sallameta bayan an kafa mata dokoki game da kula da lafiyarta.
Kai tsaye gidan su Yasmeen Umman Yasmeen d'in ta wuce da ita,jama'a se zuwa gaisheta akeyi gamida kwantar mata da hankali, dayake sanda tana asibitin anhana kowa ganinta shiyasa yanzu aketa tururuwar zuwa ganinta.
Fatima da Yasmeen ma ba'a barsu a bayaba suma sunzo dubata,ko kallo basu ishetaba, da Fatima ta isheta da maganane kawai seta taso mata da masifa.
"Kinga malama banason tsohon munafunci tunda kinsa Yasmeen ta d'aukar miki fansa kuma tayi yadda kikeso ay inaga seki fita harkata haka, kuma wlh daga ke har ita sekunyi danasanin wannan d'aukar fansar,sabida ni Khairat wlh nafi k'arfin irin wannan agurin kowa bare ku,ke kuma Yasmeen I salute you, yardar danayi dakene yasa kikayi nasara Amman wlh dana farga da wuri ke kinsan kinyi kad'an kimin haka, Amman yanzuma ban makaraba muzuba nidake".
Tsananin mamakine ya hana Fatima magana gamida takaici, hawaye ne kawai suka shiga biyo fuskarta, Allah yasani bata da masaniya akan abinda Yasmeen tayi,amman Abu d'aya tasani tunda har Yasmeen ta auri Hydar a matsayinta na y'ar uwarta da bata da kamarta bazata barta tazama bora agidan mijiba, muryar Yasmeen ce takatseta.
"Allah yayi gaskiya dayace inbaka da kunya kayi abinda kaga Dama,yanzu har kece zaki bud'i baki kice anmiki ba dedeba? Dank'ari to kibud'e kunnenki dakyau Khairat nima Yasmeen ba tsoronki nakejiba, muzuba nidake aga wanda ze hak'ura yabarwa wani kuma albishirinki, kishirya zama dani amatsayin kishiyarki ba k'anwa ba dan najima da datse wannan dangantakar".
Da sauri Fatima taja Yasmeen suka fice a d'akin gurin ummansu sukaje suka gaisheta daganan suka shiga gidansu Khairat,a falo suka samu Abba da Umma durk'usawa sukayi suka gaishesu suka amsa cike da walwala Abba yace.
"Ke Fatima waya baki damar fita da matar mutum bada izininsa ba? wannan ay shashancine kibarta anan inzaki tafi sabida asan meza'ayi gameda tarewarta kinjiko?".
Kai Fatima ta d'aga tana murmushi.
Umman Khairat tace cikin dariya.
"Hala koda kika tafi da ita bawani shiri dakika mata dan shashanci?".
Shuru Fatima tayi hakan yasa umman d'auka bata ba Yasmeen magungunaba.
Haka Fatima ta tafi tabar Yasmeen agidan umman Khairat d'in.
Umma wata mata y'ar Sudan ta d'auko tace ta gyara mata Amarya,ayko Yasmeen tasha wuya dansu basu d'auka anmata agidan Fatima ba sosai suke d'irka mata magunguna har kuka take in aka bata wani Maganin ko tsarki zatayi da ruwan Magani take yinshi inde ba sallah zatayiba,ta jima da dena shan ruwa pure sede na Magani shiyasa duk abin ya isheta.
Shiko Hydar ya koma Abuja sabida yanayin aykinshi se ranar Friday zezo domin tafiya da Khairat kamar yadda Abba ya umarceshi.
Ranar Friday ko se bayan an sakko masallaci ya iso kaduna gidan iyayensa yafara zuwa suka gaisa sannan ya wuce gidan su Khairat inda Abba yace yasameshi inyazo.
A sit room Abban ya saukeshi bayan sungaisa nasiha sosai Abban yamasa akan yarik'e musu y'ay'a amana dan duka d'aya suke agurinsu ba banbanci.
"Insha Allahu Abba zanyi iya bakin k'ok'arina wajan ganin ba'a samu matsalaba".
"To Allah yabaka ikon kamanta adalcin, yanzu katafi da Khairat Yasmeen kuma zaka d'an bamu lokaci mud'an kintsa tunda kaga ayadda abun yazo bamu shiryaba".
"Abba wannan bawani abun damuwa bane duk abinda uba yakeyiwa y'arsa yayin auranta nine dama meyiwa Yasmeen koda bani Ta auraba tunda a hannuna ta taso, dan haka bana buk'atar ko tsinke a hannunku ni zanyimata inhar kun amince nan da sati biyu se ayi bikin tarewarta, Abba Tunda budurwace ba bazawaraba be kyautu amata aure bawani biki ba".
Kalaman Hydar sunshigi Abba tabbas abinda Hydar yafad'i gaskiyane dan haka dole itama ashirya mata taron auranta kamar kowacce y'a.
"Maganar ka Hydar gaskiyane kuma naji dad'in wannan shawarar taka insha Allahu kuma nan da sati biyu za'ayi kamar yadda ka buk'ata,maganar kayan dakace zakayi kuwa bazan hanakaba danshima kafimu gaskiya tabbas uba kake a gurinta munbaka wannan damar Allah ya had'a kanku baki d'aya ku zauna Lfy,bari inturo maka Yasmeen d'in kugaisa kamin Khairat d'in tafito ku wuce".
Godiya Hydar yay tayi kamar baze denaba har Abban yafice daga gurin,cikin gida Abban yanufa yakira Yasmeen yace taje sit room Hydar najiranta, Umman Khairat ce tasake gyarata sannan tace taje to,tafiya Yasmeen take jiki a sanyaye dan bak'aramin kunya Umman Khairat take bata ba ahaka har tak'araso k'ofar shiga sit room d'in,kasa shiga tayi ta tsaya tana tunani shiko ya hangota ta labule danhaka sejitayi an kamota anjata zuwa cikin d'akin a tsorace take kallonshi dan ita tsoronshi takeji tun abinda yamata rannan.
"Baby yanzu kuma ni kikejin tsoro har baza'a shigo gurinaba?"yafad'i yana k'ok'arin had'a bakinshi da nata,k'ank'ame jikinta tayi guri guda ta rufe idonta shi abunma dariya yabashi danhaka cakulkuli yashiga yimata ayko takasa daurewa tashiga kyalkyala dariya tana gaggantsarewa seda ya wahal da ita sannan ya kyaleta.
"Baby jikinki yak'ara laushi gawani k'amshi dakikeyi fad'amin meyene sirrin?".
Cusa kanta tayi a k'irjinshi tayi lamo tak'i bashi amsa se murmushi takeyi.
"Baby zanyi missing d'inki wlh yau zan wuce da Auntynki ke kuma senan da two weeks sabida za'ayi taron biki kamin ki tare,yanzude kije ki kawomin passport naki ko guda d'ayane da national I'd card d'inki kinji da indigen d'inki".
Akunyace tashiga cikin gidan dan kayanta duk sunyi squeeze haka ta daure ta shiga taje ta d'auko duk abinda ya buk'ata ta kawomishi.
Mik'ewa yayi suna sallama, ay mutuniyar taku yi tayi kamar zata fad'i hakan yasa Hydar ya rungumeta da sauri ita ko tai amfani da wannan damar Wajan manna bakinta a k'irjinshi jambakinta yafito ajikin shaddar jikinshi kamarde kiss, shiko bemasan tayiba,kwacewa tayi ajikinshi takoma gefe, kud'i yabata masu yawa yace tarik'e kamin yazo next week a haka sukayi sallama yafice itakuma takoma cikin gidan tana dariyar muguntar bomb d'in data had'a.
muje zuwa.
Maman Yusuf.
ππππππππ
*CIN AMANA KO FANSA*
ππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*Only the open heart receives LOVE Only the open mind receives WISDOM,Only the open hand receives GIFTS, and Only the CUTE 1 receive MESSAGES From ME!,MAMAN IZZUDDEEN, MAMAN ABULKHAIR,QUEEN HASSANA GWAMBE,MAMAN HANIF,am really appreciate your support thanks you all*
*page 63-64*
Mota Hydar yaje yazauna yana jiran fitowarta dan tuni ansaka kayanta a booth.
Koda tazo tana shirin shiga motar yadakatar da ita dacewa yakamata taje tawa iyayenta sallama, ko kallo be ishetaba tashige motar abinta tana doka masa harara.
Be kulataba yatada motar suka bar harabar gurin,tafe suke bame cewa kowa k'ala har suka zo unguwar mu'azu junction inda yashiga wani gidan mai domin yak'ara mai,angama zubamasa, mik'a hannun dazeyi cikin aljihu yad'auko kud'in idon Khairat yasauka akan kiss d'in jambakin Yasmeen.
Wohoho bala'i ba'a samaka rana.
Wata kururuwa tayi takaima gurin damk'a dasauri Hydar yabada kud'in yaja motar suka fice daga gidan man dan takusa tara masa jama'a.
Itako ashar data dunga zundumawa Yasmeen bazasu fad'uba kamin daga bisani tadawo kan Hydar d'in.
"Wlh kaji kunya Hydar kazama bunsuru kabi ya kabi k'anwa, wato iskancinnaku yakai hartayimaka kiss a riga dankazo kanunamin? to wlh baku isaba daga kai har itan dede nake daku,cin amanar tawa dakukayi bata ishekuba sekun bini da haka,waya sanima ko tuni kagama saninta awaje watak'ila ma Allah kad'ai yasan yawan cikin dakuka zubar dan amaryar da bata saba da mijin tun awajeba bazatayi hakaba, nide ba abinda zancemuku