Showing 3001 words to 4691 words out of 4691 words

Chapter 2 - Bakar Mace Complete Hausa Novels by Meenatu DMS.txt

koma daga Farouq sai Farida.
Nan suka shiga labari Farouq yana yi yana sako
kalaman soyayyah.
Farida kuwa yana yi tana rufe fuskan ta.
Domim kunyar Farouq take ji sosai!
Ahaka suka sha labari kafin daga bisani suyi
sallama.
Farouq yace baxai ta fiba har saita fada masa
cewar tana son shi.
Farida rufe fuska tayi sannan tace nifa baxan iya
ba gaskia.
Maimaita maganar da tayi yayi. Farida cike da
Shagwaba tace Allah ka daina.
Farouq yace i won't until you tell me that you
love me.
Farida yace i'll but not now. Farouq yace ni kuma
yanxu nake so.
Farida tace i said i'll but not now, i'll tell you but
through the phone.
Farouq yace ok promise? Farida tace yh promise.
Ahaka sukayi bankwana Farouq ya tafi gida cike
da farin ciki marar misaltuwa.
BAQAR MACE!
WANENE FAROUQ??
Farouq shine na biyu awajen mahaifan su kuma
shine last born.
Cikakken sunan sa shine Farouq Sulaiman, sunan
mahaifitar sa Hajia Amina.
Mahaifin sa da mahaifiyar sa sunyi auren
soyayyah.
Mahaifin sa Attijiri ne suna xaune.
Suna xaune a anguwar Rimi gidan su gida je qato
kuma mai kyaun gaske.
Mahaifin sa Senator ne mahaifiyar sa kuma
Lecturer ce.
Amma ahalin yanxu ta ajiye aiki.
Babban yayan sa shine Usman yana da aure
harda yaya 2 duka mata.
Farouq yana da shekaru 38 yana aiki a NNPC
kuma yana business.
Farouq ya kasan ce mutum kirki ga mutane baki
daya.
Farouq dogo je fari yana broad chest, yana da
dogon hanci, cutely lips which are pink.... yana
da manyan idanu.
Sumar kansa kwance take, haka sajen fuskar sa!
Farouq ya hadu iya haduwa, hakan yasa yan
mata ke son sa sosai.
Duk cikin matan Farouq babu wacce ta liqe masa
kamar Salimat qanwa ce ga matar Usman.
Sunan matar Usman Hafsah, Hafsah tana son
Salimat ta auri Farouq domin tasan qanwar tata
xata huta.
Shiyasa Salimat kusan kullun tana nan wajen
Umman Farouq.U DMS!
BAQAR MACE!
22
Farouq koh kalli Salimat bata ishe shiba!
Domin sam ya tsani ya kalle ta, hakan yasa duk
lokacin da ya shigo side din Umma ya ganta.
Saiya bar wajen!
Umma dai bata damu da yadda Farouq yake wa
Salimat ba domin bata son bacin ran autan nata.
Ita kanta Umma yadda taga Salimat na wannan
iyayin hakan yasa Umma bata takura ma Farouq.
Farouq bashi da babban aboki irin Ishaq.
Domin kuwa childhood friend dinsa ne, hakan
yasa suke kamar yan uwa.
Duk wani hali da Farouq yake ciki, Ishaq ya sani
haka kuma Ishaq duk halim da yake ciki Farouq
ya sani.
Ishaq yayi aure harda yarinya daya.
Ishaq yaso ace sunyi aure tare amma tun
alokacin da Farouq ya hadu da Farida when she
was in 200lvl.
Tun daga wannan lokacin Farouq ya leqe mata.
Ita kuma alokacin bata da raayin sa koh kadan.
Shi kuma Ishaq abnda yasa yake qin Farida shine
yadda yaga tana wulaqnta Farouq.
Ishaq adunia ya tsani yaga wani yana debasing
friend dinsa.
Hakan yasa ya dauki kin Farida ya daura shi cikin
ransa.ausa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
23

Tun tashin Farouq ya kasan ce abn so da qauna
awajen al'uma!
Arayuwar sa baya wulaqanta kowa, gashi abn
hannun sa baya rufe masa ido.
Farouq yana girmama yayan Usman!
Domim yana yi masa kallo kmar Abban shine,
kasan cewar Usman yanxu yakai shekaru 44.
Kamar yadda yake girmama yayan nasa haka
yake girmama matar sa.
Sai dai abu guda daya tsana game da matar
yayan nasa shine yadda take turo masa Salimat.
Wannan abu yana cima Farouq tuwo aqwarya.
Gashi baya son shiga harkar Salimat hakan yasa
koh gaishe sa tayi baya amsawa.
Domin ya lura kanta yana yi mata rawa.
Salimat ta kasan ce kamar kaska ga Farouq!
Don akwanakin baya har office ta riqa binsa.
Saida yayi mata dukan gaske cikin office sannan
yayi mata korar kare.
Wannan dalili yasa Salimat jin tsoron Farouq
sosai da kuma ja baya gare shi.
Ta rasa gane dalilin da yasa Farouq baya sonta.
Abu ma farko dai ita tasan tana da kyau domin
koh cikin mata masu kyau toh ta kai.
Gata kuma yar gayu, amma Farouq koh kadan
baya ganin wannam baiwar da Allah yayi mata.
BAQAR MACE!
CIGABAN LABARI!
Kamar yadda Farida tayi alqawarin cewar xata
fadi masa cewar tana sonsa.
Haka kuwa akayi, domin bayan ya kira a waya ne
take qara bashi hakuri akan abnda tayi masa
baya.
Sannan tayi declaring cewar tana son sa.
Murna wajen Farouq baa magana.
Wasa wasa soyayyah tsakanin Farida da Farouq
ta ginu.
Soyayyah suke tsakani da Allah, babu wani aibu
acikin kalar son da Farouq yake mata.
Farida wani lokaci har mamaki take akan yadda
Farouq yake nuna kulawar sa akan ta.
Wani lokaci gani take kamar mafarki taki.
Wani lokaci kuma gani take anya bata cuci
Farouq ba? Domim shi mai kyau ita Mummuna.
Farouq da Ishaq sun shrya domin yanxu Ishaq in
banda yabon Farida babu abnda yake yi.
Hakan yasa suke shiri sosai da Farouq yanxu.
Kuma shi kanshi Ishaq ya gano halin Farida da
yadda take da mutunci.
Hakan yasa ya gane ashe abaya yadda ya dauke
ta ba haka take ba.
Ahalin yanxu Ishaq yana girmama Farida badan
komai ba kuwa sai yadda ya lura da halayyar ta
da dabi'un ta suke.
Maganar aure ta taso gadan gadan domin an
saka ranar biki wata biyu kacal.
Murna wajen Fati da Hindu baa magana.
Haka wajen Farouq da family dinsa Excluding
Hafsat and Salimat.sa Novels
MEENATU DMS!
BAQAR MACE!
25
⃣ Ahalin yanxu an saka ranar bikin su.
Wata uku kawai aka saka... Farouq ne xaune
yana tunanin inda xau samo ma Farida Maganin
aljanu.
Domin yanxu aljanun ta sun cika tashi.
Shirin biki akeyi, sosai domin yanxu baifi saura 3
weeks ba.
Anyi siyama Farida kaya na gani na fada. Amma
still har yanxu aljanun ta suna tashi.
Farouq aduk lokacin da aljanun Farida suka tashi
yana shiga damuwa sosai.
Hakan yasa yake qara sonta sosai domin wannan
lalurar tata.
Akwana a tashi yau baifi saura kwana 8 bikin ba
hakan yasa hidima koh ta ina ta kacame.
Dangi ta koh ina sun iso, Farida sai shiri suke ita
da su Fatima.
Haka Farouq shima duk wanda ya gansa yasan
yana cikin farin ciki.
Salimat tafi kowa baqin cikin wannan bikin.
Hakan yasa ta tattara ta koma Kano.
Domin ita a ganin abn kunya ne ace wanda take
so xai auri wannan BAQAR MACEN. what a big
slap on her face? That's what she thnk.
BAQAR MACE!
Yau Friday aka daura aure Farouq Sulaiman da
Farida Ahmad.
Bayan sallan juma'a, an daura auren ne abisa
sadaki naira dubu ashirin.
Babu wani party da akayi, da dare aka dauki
amarya aka kaita gidan ta dake, Malali.
Gida ne na gani na fada, matar Usman ji take
kamar ta kashe Farida dan baqin ciki.
The next day akayi walima, kowa ya gama gaban
sa tare da neman musu xaman lafia.
BAYAN WATA UKU.
Soyayyah suke tsakani da Allah, Farida tana bin
duk wata doka da umarnin Farouq.
Farouq yana qaunar matar sa koh kadan baya
son abnda xai bata mata rai.
Aljanun Farida suna tashi akai akai, Farouq yana
bala'in tausaya mata.
Ishaq yaxo masa da labarin Arriyad Islamic
Chemist!
Ba tare da bata lokaci ba suka je harda Farida.
Cikin ikon Allah aka basu magani, duk rana kafin
Farouq ya tafi Office sai ya bata tasha sannan ya
tafi.
Haka kuma da yamma.
Cikin ikon Allah yanxu Farida sai tayi... wata 6 ba
tare da aljanun sun tashi ba.e of Hausa Novels
BAQAR MACE!
27
Farida ce xaune bisa qafar Farouq.
Farouq sai jan ta yake yana fadin mai ciki...
Farida sai turo baki take tana fadin wallahi bani
son sunan nan.
Farouq ya fashe da daria, yace Allah dai ya
rabaku lafia.
Farida tace ameen!
Farouq yace inace yanxu cikin 6 months yake
koh?
Farida tayi saurin cewa wallahi, 9 months ne ka
daina maida ni baya.
Farouq ya fashe da daria, yace wai miya baki son
na maida ke baya ne?
Suna cikin maganar suka ji sallama.
Ahankali Farida ke shirin tashi dan bata son
atarar da su ahaka.
Farouq ne ya temaka mata!
Tun kafin su shigo Farida ke fadin Oyoyo ga
sisters.
Bayan sun shigo sun gaisa da Farouq, sun taba
yar fira, kafin daga baya Farouq ya bar gidan.
BAQAR MACE!
Hindu ce ke fadin wallahi sis cikin nan ya miki
kyau.
Nidai Allah yasa idan nayi aure nawa yayi mani
kyau!
Buge mata baki Farida tayi tare da fadin marar
kunyar banxa kawai.
Hindu turo baki tayi, tare da fadin ay gaskia ce.
Fati babu abnda take yi sai daria.
Basu bar gidan Farida ba saida sukayi Magrib
prayer sannan.
Farida ji tayi kamar kada su tafi.
Yau Farida ta tashi da nakuda.
Sun isa asibiti, an shiga da ita labour room.
Farouq sai safa da marwa yake yi.
Kafin kace haka dangi sun cika asibiti.
Farida ta sauka lafia inda ta haifi 'Yar ta mace
mai kama da Farouq.
Murna wajen Farouq baa magana.
Haka both families din!
Bayan an sallame su, gida aka wuce da Farida!
Farouq yaso ace gidan sa xatayi wanka amma
Umma ta hana.of Hausa Novels
BAQAR MACE!
29
Ranar suna yarinya taci suna Aisha!
Farida ta samu abn dunia dai dai misali.
Taron suna ya tashi lafia kiwa yana fadin Allah ya
raya.
Ya kuma maido su wata shekarar suna.
Bayan wata 3 suka koma gida.
Murna wajen Farouq kamar me, more especially
da yaga babyn sa sai qara kyau take gata bulbul.
Farouq yana taking good care of them.
Hakan yasa Farida ta qara kwantar da kanta
wajen mijin ta.
Aljanun Farida suna tashi amma ba sosai ba.
Bikin Fati da Hindu ya matso domin yanxu baifi
saura 14 days ba.
Hakan yasa suke ta shiri basu cika xama sosai
ba.
BAQAR MACE!
Anyi biki an gama lafia amare gaba dayan su
Kano aka kaisu.
Farida sunsha kukan rabuwa da yan uwan nata
ranat walima.
Sun dawo gida ita da Farouq kamar wasu marar
da lafia.
Farouq ne da yaga abn nata yayi yawa yace Allah
idan bata saki ranta ba xai ce bata qara xuwa
Kano.
Hakan yasa Farida ta saki jiki ta koma kamar da.
Amma tunanin sisters dinta cike da ranta.
Xaune take tana tunanin wannan kasalar da take
fama da ita yan kwanakin nan.
Basu bata lokaci ba suka isa asibiti. Gwajin farko
likita ya sheda musu Farida tana dauke da ciki
wata 4.
Farida abn ya bala'in bata mamaki domin
alokacin Mama shekarar ta daya da wata uku.
Farida bata tada hankali ba domin taga yadda
Farouq yake ta murna.
Hakan yasa ita ta taya shi murnan tasa.
BAYAN 6 MONTHS.
Farida ta sauka lafia, ta haifi danta namiji shima
mai kama da Farouq but some how yana kama
da ita.
Yaro yaci sunan Abban Farouq wato Sulaiman,
suna kiran sa da Junior.
Haka rayuwar tacigaba cikin jin dadi da qaunar
juna.
Farouq dai qara samun daukaka yake ta koh ina.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo qarshen wannan littafi mai suna
BAQAR MACE.
Nayi wannan littafin badan komai sai dan na jayo
hankalin marubutan littafin Hausa.
Akan musan cewa bawai macr mai kyau fara
kadai bace in the world.
And ba ita daya bace maxa suke so.
And also ba Farar Mace mai kyau kadai take da
aji ba. Suma BAQAQE MA MATA NE. Kuma masu
Aji.
Masu aji, domin gaba dayan mu babu wanda yafi
awajen Allah sai wanda yafi tsoron Allah.
Na fiddo Star din wannan novel BAQA kuma
MUMMUNA. Kuma mai ALJANU.
Kuma ahaka classic guy ya aure ta. Kuma ya
gwada mata SO DA QAUNA.
No body is better than any one to Allah except
the one who fear him the most.
So ina son musan cewa kyau ba wani abu bane,
domin da wani kyan gara muni.
I Aminatu Dan-Musa dedicate dz novel to all the
BLACK MUSLIMS WOMEN where ever you may
be!
CHEERS TO BLACK WOMEN .

HADAWA BY
MARYAM AMEERA YOLA
RUQAYYA GAMBO AWE
SAKINA USMAN


1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login