Showing 1 words to 2925 words out of 2925 words

Chapter 1 - GOOD EVENING (Dangerous story) Romantic Hausa Novels By Oum Hairan .pdf

19 Sep 2025

1657

arewanovels.com.ng
*GOOD EVENING*
_*(Dangerous story)*_



*OUM HAIRAN*


_Wannan littafin iya arewabooks zaku sameshi Cmplt👌🏽_

*Page One*

"Ke karuwa ce! Bakar ashana kona gari... Da halinki gwamma gobara ran sallah. "
Maganganun saurayin suka ci gaba da yi mata kararrawa a kunnuwanta. Kwakwalwarta ba ta
saba da karbar maganganu masu zafi irin wadannan ba, bayan cakudewar da rayuwarta ta yi
da munanan abubuwa da suka zagaye ta suka hana ta sakewa, a karon farko ta yi nadamar
shigowarta bariki. Barikin boye!
Barikin da iyayenta ba su san tana yi ba, mutanen unguwarsu ba su san tana yi ba, duk da
shigarta barikin da faruwar al'amarin sun kasance ne a cikin kwanaki kadan, amma ji take yi ba
za ta iya bari ba. A mafi yawan lokuta tana fakewa da guzuma ne tana harbin karsana ;ta sha
fakewa da zuwa makaranta tana samun abin da take so daga mutanen da suke karbar abin da
take da shi a wurinta.

Za ta iya tuna ranar farko da mutum na farko da ya fara sanin ta 'ya mace, wato saurayinta
Rabi'u ;wanda ta aminta da shi ta mika masa soyayya ta damka masa amanarta babu haufi, har
ya yi nasarar bata mata rayuwa, bayan ya yi amfani da tsantsar kwadayinta tare da kaifin
basirarsa ya yaudare ta da kyautar sarkar gwal ta mata, wadda kudinta ya kai dubu hamsin. A
karshe tana ji tana gani ya nuna mata sarkar ta bata.
A dole ta hakura bayan ya yi alkawarin sayo mata wata.
Mutum na biyu da take zargi da bata mata rayuwa ;ita ce babbar kawarta kuma aminiyarta
Nusaiba. Ita ta dora ta akan harkar good evening (gaisuwar yamma).
Ah to! Ina ruwan biri da gada?
Wata rana ne Nusaiba ta same ta a dakinta cike da damuwa, domin tun bayan karayar arzikin
mahaifinta gabadaya gidan nasu suka shiga damuwa ; maraici, da kadaici suka dabaibaye su.
Nusaiba ta ba ta shawarar hanya mafi dacewa da za ta warware matsalarta.
"Haba Nusaiba! Ba ki ganin abin da Rabi'u Mangyal ya yi mini? Amma kike gaya minmin
hanyar da zan bi wadda ba bullewa take ba? "
" Matsalarki daya Rabi'atu ; kullum idan ana nuna miki hanyar da za ki rage matsalolin rayuwa
sai ki dinga tunanin abin da zai faru gaba. Ki gaya min idan akwai wata mace baliga da za ki iya
shaidar ta a wannan zamanin, komai kankantar shekarunta kuwa, hatta matan aure da su ake
damawa a ciki. Idan matar aure ta aikata ta aikata ta yi babban zunubi, Amma ke, a karkashin
ikon wa kike da har za ki nemi daga hankalinki? Ki duba yadda rayuwarki ta koma baya, ba

wani wanda zai tallafa miki, karatun da kike yi nema yake ya gagara. Idan ba ki warware
matsalolinki yanzu ba sai yaushe? Ko sai ikonki ya bar hannunki ya koma karkashin wani? Da
sandar da ke hannunka fa da ita kake jifa. Haba Rabi'atu ki dawo daga duniyar dimuwa da kika
jefa kanki ko kya samu sa'ida a rayuwa. Abu ne fa na lokaci kankani, ba shiga sojan badakkare
za ki yi ba."
Rabi'atu ta yi shiru tana sauraren hudubar kawarta, lokaci guda tana hasko yadda ta taso cikin
gata da yadda karayar arziki ta wargaza kwanciyar hankalin gidansu ta yi dai-dai da zumuncin
danginsu da talakawan unguwar ('yan maula).
Rabi'atu ba ta san É—acin talauci ba a farkon rayuwarta, wannan ya sa ta kasa jure masa, a duk
lokacin da bukatar kuÉ—i ta zo mata sai ta ji kamar ta dora hannu a ka ta saka ihu, wannan ya
mayar da ita makwaÉ—aiciya akan mallakar abin duniya, zuciyarta kuma na gaya mata wata rana
arziƙin mahaifinta zai dawo, wataƙila ma ta hanyarta, sai dai har yanzu ba ta ga alamu ba. A da
ta yi tsammanin abin zai kasance ne bayan ta kammala karatu ta samu wani gwaggwaɓan aiki.
To amma ga shi tun ba a je ko ina ba karatun nata ya cije.
Don haka lokacin da Nusaiba ke ba ta shawara, duk da ta jinjina shawarar amma sai take ganin
Nusaiba na da gaskiya, kuma ko babu komai ma wanda ruwa ya ci in ka ba shi takobi kamawa
zai yi. Don haka za ta jarraba ta gani, amma na lokaci ƙanƙani ne, daga zarar ta samu ta
kammala karatunta za ta... "Tunanin me kike yi ne Rabi'ah? Kina da matsala wallahi," Nusaiba ta katse ta,"ni zan É—auki
jakata in tafi idan tunani za ki tsaya yi."
Ta miƙe tsaye bayan ta ɗauki jakarta.
Rabi'ah ta yi saurin riƙe ta, "Kada ki tafi kamata, ta ya ya kike ganin za a ɓullo wa abin?"
"Ba kina zuwa makaranta kullum da yamma ba? " in ji Nusaiba.
" Kina nufin daga makaranta sai mu wuce? "
" Kash! Ba kya gane karatun sosai ;shiryawa za ki yi kamar za ki je makaranta, da zarar kin fita
sai ki yi min waya, zan gaya miki inda za mu haɗu, sauran bayanin kuma ruwa ya fi shi sauƙin
sha. "

Da haka Nusaiba ta shawo kan kawarta suka fara sana'ar da suke ganin ribarta a yanzu, riba
kan riba ;domin suna kashe ƙishirwa da ke damun su sannan kuma ga sinadaran rayuwa (kudi )
Yamma ta yi. Rana ta sunkuya. Zirga-zirga ta yawaita a manyan titunan garin Kano, saboda
dawowar mutane daga wurin harkokinsu, walau na kasuwanci ko aikin ofis. Gosulo ya yi yawa,
kowacce danja ko madakata ta manyan titunan motoci ne jere a tsaye cak! Saboda tsabar
cunkoson ababen hawa. A can titin unguwar Nassarawa inda su Nusaiba ke tsaye ita da kawarta Rabi'atu da sauran
abokan harka ba haka abin yake ba, akwai karancin ababen hawa.
Lokaci - lokaci masu kuÉ—i kan tsaya da manya-manyan motoci domin É—aukar abokan harka.
Idan haka ta faru matan da ke tsaye suna jiran gawon shanu kan rugo da gudu ga duk wadda
motar ta tsaya kusa da ita don zaton saboda ita aka tsaya. WaÉ—ansu daga cikin matan, matan
aure ne da kan baro gidajensu saboda tsabar kwaɗayi, da kuma zawarawa,'yan ƙwalisa, sai
kuma 'yan matan da suka buÉ—e ido irin su Nusaiba.
Nusaiba ta gyara tsayuwarta bayan ta turo É—ankwalinta gaba, "Ina fata kina kula da yadda ake
harka?"

Rabi'ah ta kyaɓe baki. Ita abin haushi yake ba ta ganin yadda' yan mata suka maida kansu
kamar wani tumatirin kasuwa a gefen hanya, amma daga zarar ta tuna ba tsayuwar banza take
ba, domin tana ganin yadda Nusaiba ke facaka da kuÉ—i sai ranta ya yi fari, ta san nan gaba
kaÉ—an ita ma idonta zai buÉ—e. Ta san tana da kyawun dirin da duk wanda ya kalle ta sai ya sake
kallonta. Haka nan matsattsun kayan da ta sa sun taimaka wajen fito da ƙugunta da cikar
ƙirjinta. Ta yi imani babu daɗewa za ta kashe wa Nusaiba kawarta kasuwa, bariki za ta fara
yayinta, domin kuwa ta fi ta kyau nesa ba kusa ba.
"Ina kula. Amma na ga ai ba wasu yara sosai, duk dattawa nake gani. "
Sai da Nusaiba ta yi dariya kafin ta ce," Kada ki zama wata sabon yanka rake mana ƙawata! Ai
wadaynda kike rainawa su ne abokan tafiyar, ba ki ga abin da matasan irin su Rabi'u saurayinki
suka yi miki ba? "
Rabi'ah ta haɗe rai, domin duk sadda aka tuna mata da Rabi'u takan ji tsanar sa ta ƙaru a
zuciyarta fiye da lokacin da ya ci amanarta. Don haka a yanzu da Nusaiba ta tuna mata shi sai
ta ji tana ƙaunar ko ma waye ya dauke ta za ta bi shi a je a shakata, kuma zai rage mata
raÉ—aÉ—in damuwar zuciyar tata.
A hankali wata mota mai tsada ƙirar Anaconda ta tsaya a kusa da su, sannan aka sauke gilasan
motar, wani mutum kakkaura mai tarin gashin baki da gashin kai duguzumzum ya leko ya kare
musu kallo daga sama har kasa, sannan ya yi wa Rabi'ah sigina da ƙwayar idonsa.
Nusaiba ta É—auko madubi tana kallon fuskarta a wani salo na basarwa.
Rabi'ah ta lura da yadda sauran matan da aka dauka a gaban idonta suke yi, kuma tun kafin su
zo nan ƙawarta ta nuna mata babu sanayya a harkar bariki.
Don haka da mutumin ya kira ta ba ta kalli Nusaiba ba kawai sai ta nufi motar kai tsaye ta bude
ta shiga, Mutumin ya ja suka tafi.
Wani hotel suka nufa. Bayan ya ajiye motarsa a wajen adana motoci suka karasa, ya kama
musu daki kwana guda, aka ba shi mabuÉ—i. Suka nufi inda ayarin dakunan ke jere reras!
Lokacin da ya buÉ—e ÆŠakin suka shiga tuni an fara kiran sallar Magriba a wani masallaci da ke
kusa da hotel É—in.
Rabi'ah ta ajiye jakarta a kan wani katon gado mai lallausar katifa.
"Sunana Alhaji Yunusa. Kuma ni É—an kwangila ne, "dattijon mutumin ya ce mata," in dai har na
samu yadda nake so a wurinki to kina da naira dubu hamsin. "........





*GOOD EVENING*
_*(Dangerous story)*_

*Oum Hairan*


_Wannan littafin iya arewabooks zaku sameshi Cmplt 👌🏽_

*Page two*


Ya nufo ta sanye da tawul a jikinsa yana murmushi, Rabi'ah ta yi mutuwar tsohuwa, zuciyarta
cike da fargabar kada ya gane abin da ta yi masa.
'Da ma ke barauniya ce?' Ta so ta ji kamar haka yake ce mata, amma sabanin haka sai ta ji
yana cewa.
"Bebina me ye matsalarki? Ya kamata ki yi wanka don mu nishadantu."
Yin wankanta na nufin tonuwar asirinta. Don haka a take sai kwakwalwarta ta soma aiki.
"Ba ka gamsu da kwalliyata ba ke nan?"
Ta kalle shi da murmushin 'manta sunanka'
"Ni na isa in ce haka? " ya zauna kusa da ita tare da dafa kafadunta," ai irin ku ba make up
(kwalliya) kyau kukeyi. Da ma na ga kamar kina gumi ne."
Sai a yanzu ta ankara da gaban rigarta da ya soma jikewa.
Ta dube shi, "Babu komai. Na dan wanke fuskata kawai... Mhm! Darling ka cika tambaya da
yawa," ta dan kwanto jikinsa.
Ya shafi fuskarta, "Ki yi hakuri Bebina ban san ba kya son tambaya ba. Kina jin yunwa?"
"Ga shi ka kuma tambaya ta! "
"Na damu da ke ne shiyasa daga yanzu duk abin da kike so ki gaya min, zan yi miki daga nan
zuwa safe tun da kwanan gida na dauke ki. Matsalata daya; na tsani munafunci ko sata, da
munafuki da barawo ba abokaina ba ne. Zan iya kashe mutum idan ya yi min daya daga cikin
halayen nan." Gaban Rabi'ah ya fadi, "Kisa? Kisa fa ka ce?" ta fada a razane.
Ya shafa kanta, "Bebita ke nan, kina mamaki ke nan, to ki daina, domin mutanen nan biyu su ne
matsala a rayuwata. Mhm! Mu share wannan zancen Bebi. Ya kamata mu fara ko?"
Rabi'ah ta miqe cike da mutuwar jiki, ta fara cire kayan dake jikinta, har sai da ta koma daga ita
sai pant da bra
Tun da Alhaji Yunusa yake bariki bai taba ganin yarinyar da ta tsuma shi da kyawun surarta
kamar Rabi'ah ba. Sai da ya yi kokari wajen daidaita luguden kirjinsa da saitin kwakwalwarsa
sannan ajiyar zuciya ta biyo baya. Tun kafin ta gama nutsuwa ya rungumo ta jikinsa hadi da
sumbatarta cikin salon jan hankalinta. Yana shafa bayanta cikin nutsuwa ya haÉ—e bakinsu yana
wani tsotsar lips É—inta da salon da yasan dole tayi amanna dashi, cikin Nutsuwa ya É—ora
hannunsa bisa bra É—inta ya É—an É—ago yanda idanunta yake a kunshe ne ya bashi damar zagaya
hannunsa bayanta ya cire mata bra ɗin. “Wow! Masha Allah" ya furta cikin wata irin murya ganin
cikakku kuma tsayayyun nonuwanta masu É—aukar hankali, a nutse yakai yatsarsa saman
nipples É—inta ya É—an jashi a hankali ya kuma Kallonta ganin yanda ta sallama masa jiki ne ya
bashi damar É—ora bakinsa saman nipples É—inta ya fara tsotsa, baija wasan da nisa ba
kasancewar a asalin buƙace yake domin kuwa daga tafiya ya dawo yaje gida ya tarar da
matansa sunata bala'i ya buƙaci me girki tazo gareshi sun tsaya yi masa haka wannan tana ita
ce da girki wannan tana itace, shi kuwa da yaga bazai iya ba ya sanya kayansa yayo waje
abinsa domin nemawa kansa mafita.

Ba su rabu da juna ba sai da suka gamsu. Alhaji Yunus yana ji a ransa yarinyar ta gamsar da
shi, kuma ba ya zaton zai iya rabuwa da ita matukar yana raye.
A bangaren Rabi'atu kuwa har yanzu ba ta gama sakin jikinta da shi ba, illa dai ta ba shi dama
ya sarrafa ta yadda yake so, in son samu ne ta rabu da shi tun kafin ya waiwayi lalitarsa. Lokaci
- lokaci tana waiwayarsa bayan da wani bacci mai nauyi ya dauke shi.
Ta dauki wayarta ta duba agogo. Ashe har dare ya yi nisa haka? Karfe uku na dare ana abu
daya aikuwa taji a jikinta duk da ba asalin gajiya tayi ba amma har yanzu akwai rashin sabo a
tattare da ita, Alh Yunus shine mutum na uku daya ratsata É—iya mace, wannan rayuwa bata
mata daÉ—i saidai ya zataci tunda tanason kuÉ—i. A hankali ta sauka daga kan gadon ta lalubi kayan sawarta ta saka, cikin sanda ta nufi bakin
kofa ta ja. Sai a sannan ta tuna ya kulle kofar kuma ba ta san inda ya jefa mabudin ba. Shin
tashin sa za ta yi ta ce ya ba ta mabudin ko kuwa lalube za ta tsaya yi har ya farka ya tambaye
ta inda za ta je? Tana nan tana dawurwura ita kadai har ta ji motsinsa, a zatonta farkawa ya yi, amma sai ta ga
ya gyara kwanciya har da minshari.
Rabi'ah ta tsaya cik! Gabanta na dukan tara-tara. Idan ma ta fita ba ta san inda za ta je ba. Ya
kamata ta bari ya farka ya nemo mabudin da kansa ya ba ta.
Zuciyarta ta tuna mata da maganarsa ta dazu.
'matsalata daya, na tsani munafunci da sata... Da munfuki da barawo ba abokaina ba ne... Zan
iya kashe mutum idan ya aikata min daya daga cikin halayen nan...

Rabi'at ba ta ankara ba sai ta ji agogon dakin ya fara bugawa, alamun Karfe biyar ta yi.
Karar agogon bangon ya farkar da Alhaji Yunus, lokaci guda gaban Rabi'ah ya yi mummunar
faÉ—uwa, duk da haka sai ta basar ta matso kusa da shi.
"Darling ka farka? "
" Bebita me kike yi a tsaye ne?" ya tambaye ta.
Ba ta ba shi amsa ba illa kyakkyawar sumba da ta ba shi.
"Kada ka damu Darling, ina dan motsa jikina ne kawai kasancewar na saba yin haka duk dare...
Jiya kuma ka hana ni," ta karasa cikin shagwaba mai wuyar kamantawa.
"Okay Kafin ki gama motsa jikin bari in dan watsa ruwa mu koma aiki. Kin san bana tashi sai
Karfe tara, idan na je na sallami iyalina sai in wuce ofis."
Ya sauko daga kan gadon babu ko wando a jikinsa ya nufi bandaki.
Sai a sannan ne ta kula da kan siririn mabudin ya leko ta karkashin fulon da ya kwanta a kansa.
Sai da ta fara jin sautin zubar ruwa daga bandakin sannan ta kaiwa key É—in sura, ta yi sauri ta
dauki jakarta da duk wani abu da ta san nata ne ta bude kofar dakin ta yi waje da gaggawa.




Lokacin da Alhaji Yunus ya fito daga wanka bai san dalili ba sai ya ji gabansa ya fadi. Da farko
bai kula da cewa kofar dakin a bude take ba sai da ya kalli gadon ya ga babu ko dankwali balle
wata mace da ke amsa sunan Rabi'atu.

Idanuwansa suka yi bulaguro zuwa inda ya ajiye walet dinsa sannan suka kankance saboda
ganin bakin walet din a bude. Bai tsaya mamaki ba ya fara kwala mata kira.
"Bebina ina kika shige ne?" yayin da hannunsa ya dadumi walet din yana fatan ba ta yashe shi
ba.
Zatonsa bai tabbata ba, domin ya yi imanin Rabi'ah ta sace masa kudinsa. Ya dan yi jim! Kafin
ya danna kararrawa.
Wani siririn farin ma'aikacin otal din ya fado dakin, "Oga me kake so?"
Alhaji Yunus ya dube shi da idanuwansa da suka rikide suka zama jajaye, kamar idanuwan
mayunwaciyar damisa a cikin tsohon dare.
"Yarinyar da muka shigo da ita jiya tare, ba ka ga fitar ta ba? "
Sai da ma'aikacin ya ja baya saboda hada ido da Alh Yunus da ya yi kafin ya ce,"Wacce
yarinya? Ai ni yanzu na karbi duty, sai dai a tambayi Misbahu, shi ya yi aikin kwana jiya. Yallabai
wani abu ya faru ne?"
"A'a babu komai, je ka kawai. Ina jin ta shiga wanka."
Alhaji Yunus ya juya ya saka kayansa cikin hanzari sannan ya lalubi wayarsa wadda ke kashe
tun jiya (kasancewar ba ya son kira da daddare) ya kunna ta. Ya yi kamar zai kira wata lamba
sai kuma ya fasa. Ya koma bakin gado ya zauna, zuciyarsa tana kuna. Sai da kyar ya samu ya
karasa saka kaya. Bai tsaya karyawa ba ya suri key É—in motarsa ya yi waje.



*Contact me 09031307566*


*Oum Hairan*





*Oum Hairan*

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login