Showing 36001 words to 39000 words out of 43747 words

Chapter 13 - Zumuntar kenan 2 Hausa Novels by Takori Kabara.txt

na linke na goge leshin na boye can kasan kayana.
Ina da takalmi da jaka 'yan (Thailand) suma mahadin leshin duk ban taba sanyawa ba. Abinda yayi mani cikas inda zan samu goggoro ba tare da na kula wadanda muka yi amfani dasu a yau ba.
A take na dau mayafi na fita, naje saloon aka gyara min kai da (setting) na burgewa na kuma je aka nado min goggoron yadda nake son shi (light pitch) aka yi min gyaran akaifa da wankin kafa nayi sumul da ni. Na dawo gida na kulle kaina cikin kallabi kai ba zaka ce an taba shi ba na hada kayan da goggoron na boye a sif din Aunty Zainab.
Wurin sha biyun dare barci ya soma fizgata sannan su Ummi suka shigo ina kwance a gado, ta cire goggoronta ta kwado min, shi kansa goggoron kamshin turaren Bashir yake yi.
Na ja wani wawan tsaki na ture goggoron daga kusa dani, ko me zan jiwa haushin oho! Tana so ta gaya min ne ta hada jiki da namiji, ko me zan jiwa haushin oho!
Banza an bata sidin turawa shi ne zata zo ta yiwa mutane fiffika, har warin tabar da aka ce yaya Bashir yana sha take yi.
"Banza mahaukaciya".
Ban san sanda furucin ya amayo daga cikina ba.
Tayi dariya ta ce, "Duk haukana ai ban kai ki ba. Yaya Bash ya ce a gaya miki kada ki samu damuwar rashin (partner) gobe don 'couple evening' ne za'ayi miki mijin roba da yaya Sa'id Ibrahim Bamalli".
Ashariya naso danno mata, amma sai na fasa. Ta cancanci bakar magana itama, don haka nayi gyaran murya daga kwance.
"Babban hauka ya wuce ka kaiwa miji kanka a soron gidan iyaye? Don haka ban fiki hauka ba, ke naki salon na zamani ne, nawa kuwa (old-fashioned) ne. Ni kam ku bar mijin robar ku na yafe ba a matse nake da namiji ba da har sai nayi riga malam masallaci. Party ba don kowa zani ba, sai don kar ku dauka wulakancin ku da cin fuskar ku ya hana ni sakewa ne ko ina bakin cikin rashin miji har hakan ya hana ni shiga mutane, ina fatan kin gane?"
Ummi ta tafa hannu tayi dan fitoo, ta ce.
"Yeho! Yarinya wallahi kinci a baki kyautar amsarki. Indai wannan shi ne hauka, don Allah a nada min sarautar mahaukatan duniya akan umarnin iyayena nake ba kuma zan taba ganin ba dai-dai ba, tunda na bisu, su nakewa biyayya.
Ke kuma mai hankalin da yafi na kowa da kika tasarma kisan kai fa? Waima tukunna ina hankali ga matar da ta titsiye mijinta da duka da zagi ya saketa? Matar da ta dauki kwalba ta rotsawa mijinta ai ta tabbata tsinanniya".
(Baki kasan me zaka fada baka san me za'a mayar maka ba-TAKORI).
Zaneerah ma aka cire mayafi aka jefo min. Eh naji kamshin (212) din yaya Aliyu kam babu shakka amma itama ta cancanci a tanka ta duk dai da ban san ita din dame zata mayar min ba.
"An dai ji kunya wallahi, tsofai-tsofai ga goyo ga tirtsetsen ciki amma ba'a fasa jaraba ba, shima Yaya Aliyun...".
Daga labulen dakin yayi yana fadin.
"Zaneerah ina wayata da na baki ki sa min caji?"
Dif! Kake ji na dauke wuta, kamar ba ni ce mai magana ba. Ya dube mu suna ta sheka dariya kamar sun samu motsatstsiya ya ce.
"Me take cewa ne?"
Na mike gaba-gadi na dauki dankwalina na daura na bar musu dakin. Ina jinta tana cewa dashi.
"Zaginmu take yi".
Ya ce, "Baya tsiro ai, da tuni jikin nata mijin ba masaka tsinke".

***
Washegari tun safe su Ummi ke shirin wucewa Kaduna liyafa, sai shirya kaya ake ana zuge (troller). Motocin da za su kwashe su zuwa Jabi Road basu zo ba sai bayan azahar suka shiga suka tafi da kawayenmu duka daga can ne za su shirya zuwa wajen da aka tanada don yin liyafar.
Ina kwance a doguwar kujera ban ko motsa ba ina kallon fitarsu daya bayan daya. Yaya Aliyu ya shigo yana balle 'links' din hannun rigarshi ya ce da Zanirah.
"Madam, muje ko?"
Ta tashi wata tikisa da ita kamar alkubus, shi kuma aka sakalo hannu kugunta aka tallafeta, a haka suka fice ko kallona basu yi ba, suka fice. Inda ya bude mata gaban 'Porsche' dinsa ta shiga, ya rufe ya zagaya shima ya shige. Bashir aka kama hannun amarya mai kama da Princess Diana don kyau da daukar ado suka fice. Har sun kai kofa ya juyo yana ce da ni.
"Af, gwauruwa, mijin robarki fa yana jiranki a waje Yaya Sa'idu, an baki kaya don kidifiri kin ki amsa. No worries, na jikinki ma inaga ba laifi, kya samu waje ko tebirin iyaye da su".
Wani gululu yazo ya tokare ni yaki wucewa, ya tsaya min a makoshi, amma Fa'izah (is always) Fa'izah, ina da 'ki-fadi' sai na ce.
"Allah Sarki Yaya Bashir ka sallami mijin robar Fa'izah ko babu shi Fa'izah (can survive), kasan mace Allah Ya yi mata juriyar iya rayuwa ba tare da namiji ba, namijin ne bai iya rayuwa mai dadi sai da mace. I.e namiji zai saki mace, ta zauna gidan iyayenta ba tare da ta yi wani auren ba kuma ta zauna lafiya. Amma shi namiji a ranar da yayi sakin ma zai iya kawo wata, ka gane?"
Ya ce, "Ohonki kuma! Tsoron shan kunya ya hanaki zuwa (party) baki da sauran bakin surutu". Da haka ya fice.
Na mike tsam bayan fitarsu nayi wanka, na dauko lesi na na sanya, na saki dogon gashina a gadon bayana, na karkata goggoro na tsayar dashi dai dai goshi na. Na janyo takalmi da jaka na cikin kwalinsu mai tudun dunduniya siririya da siririyar igiyar daurewa na fitar na sanya, na rike 'purse' din mahadinsa wadda kudin mota kawai na zube a ciki. Nan da nan na hau walkiya kamar wata dan daren goma sha hudu.
Na kawo (fashion earing) kalar adon lesin na daura (shimmering pearls) hannu, wuya, kunne da idon sawu sai walainiya nake duk motsin da nayi. Ni kaina yau nayi mamakin yadda nake, ban taba tunanin haka Allah Ya kyautata surata ba sai yau.
Na fito harabar gidan Baba Na'ibi babu kowa don haka na tura wani almajiri yayo min hayar taxi kafin minti goma sai gashi ya dawo cikin motar tare da mai taxin.
Na ce da mai taxin ya yi duk iya gudun da zai iya ya kaini (Indoor-sport hall) na garin Kaduna cikin awa daya, ko nawa ne zan biya shi. Nan da nan ya ce in shigo mu tafi.
Dakin taron ya cika ya batse babu masaka tsinke da kyawawan iyalin A.B tabbacin a yau mallawan na biki kasurgumi da basu taba yin kwatankwacinsa ba. A cikin tafiyar nutsuwa na shiga ratsa taron jama'ar suna kallona tabbacin basu tsammaci zuwana ba ma balle wannan shiga ta firgitarwa. Ashe wajen cike yake da abokan Fa'eez na Kad-Poly irin su Surajo Nuhu wanda a halin yanzu ma'aikaci ne a Central Bank da wasu daga cikin abokan su da yawa suka mike suka tarboni muka jero tare sai tafi suke yi da dariyar farin ciki, yayin da Sa'adu Bori dake cin kasuwarsa a wajen ya karkatar da akalar wakarsa gareni ya kyale su Ummi, cewa yake.
"TAKAWARKI LAFIYA GIMBIYAR ABUBAKAR FA'IZU GIWA... AMARYA FA'IZA AMANAR FA'IZ GIWA...".
Suraj tunda na tako kafata cikin (hall) din yake min (spraying) da dollers madadin Fa'izun su kenan.
Ni kam ko a jikina, a raina fadi nake wahala ce bata ishe ku ba, ko kallo basu isheni ba.
Wajen ya hautsine da kirarin abokan Fa'iz masu video da masu camera suka juyo da akalarsu kanmu gaba daya abokan Fa'iz daukana suke hotuna wasu vedio da wayoyinsu. Ina kallon bakin su Yaya Aliyu dake (high-table) yaki rufuwa, haka Mama da tarin hamshakan matan Kaduna da ta gayyato.
Anan Yaya Rabi, Aunty Hauwa da Mama da kanta suka taso suka tarbeni suka hana ni isa ga mazaunin su Ummi.
Girgiza kai nake cikin son kecewa da kuka ina yi musu nuni da ka su barni in wuce, amma sunki hakan. Mama ta rikeni gam-gam, haka Ummi da Bashir, Zanirah da Yaya Aliyu tasowa suka yi daga mazauninsu ya saura babu kowa a gaban Sa'adu bori cikin filin sai mu 'ya'ya da jikokin Hajjah da kawayen Maman Kaduna sai ko Surajo da ya rufa min asiri suka shiga yi mana "spraying" ni da Surajo sai ka rantse da Allah shi ne angon nawa, kazalika Ummi da Bashir, Zanira da tirtsetsen cikinta da Yaya Aliyu rungume da ita, duk suka bude bakin jaka suka shiga yi mana 'spray' tako'ina. Dadi ne ko mene ne ya yi min yawa, sai gani kuka ya kece mani.
Tausayin Mama har kokon raina da jinjina kaunar da take mani na kasa jurewa nima ban san dalilin tausayin nata da ya rufeni ba, na zame da gudu na karasa mazaunin su Ummi na zauna na kifa kaina a tebirin na shiga kuka mai yawan gaske wanda ni kaina bansan dalilinsa ba.
Suraj ne yazo ya zauna a kujerar Yaya Bashir ya ce.
"Fa'izah, Fa'iz bai kyauta ba na sani, don me ya yi mana haka? Rana irin wannan mai dumbin tarihi ka tsallake ka tafi wani aiki kai kafi kowa aiki?"
Haushinsa ya kara kamani da shisshigin da yake ta yi mini tunda na sako kafata a filin wajen nan shi bai yadda ba asiri ya rufawa abokinsa, kuma abin kirki yayi.
Na dago idanuna jike jagab da hawaye,
"Kada ka kuma yi min zancen wani Fa'iz, nazo (partyn) nan ne don Ummi da Bashir, don me zaka zo kana tambaya ta wani Fa'iz bayan mun rabu tuntuni?" Dariya Surajo ya yi, "Aradu bonono Fa'iz yayi miki wai rufe kofa da barawo, waye ya ce miki Fa'iz zai iya sakin ki? Ko jiya shi ya kirani daga England ya ce in taimake shi inzo in tsaya tare da ke, bai yarda da kowa ba cikin abokanmu sai ni. Wane irin saki babu ko dadin ji? Kina hauka ne?"
Wani irin rugugi naji cikin kwanyar kaina, da kyar in ba motsin kwakwalwa bane. Na zazzaro ido ina duban Surajo ina auna abinda yake fadi cikin hankali da tunani. Nasan Surajo mutum ne mara wasa, na sanshi da can don ya so Ummi aka nuna ba za'a bashi ba ya hakura.
Abubuwan da suka faru suka shiga dawo min sabbi kar, wato yanayin Fa'iz bai nuna damuwa ko bacin rai ba a sanda yake min rubutun cikin takarda, babu wata alama ta nuna damuwa a fuskarshi. Me ya hana Baba bai lallasa ni ba, kuma su Aunty Rabi babu wanda ya yi fushi dani a lokacin? Sai ma cewa da tayi in taso mu tafi bikin Ummi Giwa? Me ya hana ni karanta takardar da kaina abin kamar tsafi?"
Raina ya yi mugun baci, hankalina ya jirkice, idanuna suka kada suka yi jawur suka wani irin cicciko da kwalla.
Suraj Nuhu, ya yi danasanin karambaninsa, ya tabbatar ya yi babban kwafsi, kuma abinda ba'a aike shi ba don son ya burge. Ya shiga in-ina yana fadin.
"Fa'izah da gangan nake, na rantse miki bamu yi maganar komi da Fa'iz ba, ni na kawo kaina...".
Ina! Surajo ya barota domin kuwa mikewa nayi gaba dayana tsam nayi hanyar fita, yayin da ya biyoni yana magiyar in saurare shi, amma kurar da ta debo shi ban kalla ba.
Su Ummi suka dakata da abinda suke yi suka biyo mu da idanu. Aliyu ya saki hannun matar shi ya biyo bayanmu, ya riqo hannun Suraj ya ce ya rabu dani, kana ya haushi da fadan.
"Don me yasa ka gaya mata Surajo? Wa ya aike ka yi mata zancen Fa'iz? Ka san haukar Fa'iza kuwa? Muna zaman zamanmu lafiya ka sayo mana tashin hankali".
Surajo cikin matsananciyar nadama ya ce.
"Ni ina na sani? Na gaya mata ne kawai Fa'iz ne ya yi min waya cewar yana Wales inzo in tsaya da ita, shi kenan abinda na fada".
Yaya Aliyu ya dafe kai yana fadin, "Shi kenan Surajo ka baro mana likin, sai gyaran Allah. Wallahi ko lallashi ba zan je ba ta je can duk inda zata je zata dawo da kafafunta, ai ba yau ta fara ba”.
Da daren washegari aka raka Ummi gidanta a Kabala Custain. Washegari Zanirah da Aliyu da ‘yarsu Fa'izah suka wuce Lagos, na Giwa suka nufi Giwa, na Zaria ma haka, haka na Kaduna.
Miftahu da Ya Rabi suma suka dauki hanyar Kano da yaransu biyu, amma Ya Rabi ta ce da Yaya Mufty su tsaya Zaria su ga halin da nake ciki.
Hajja kam ta ce da su don Allah kowa ya kyale ni inyi kida na da rawata ni kadai, kada wanda yaje inda nake balle ya wani lallasheni in bata masa rai a banza. Amma Ya Rabi ta kasa jurewa. Ko cikin 'ya'ya Fa'iza ta daban ce a wurinta, tana da matsayin da babu mai shi cikin tarin 'ya'yan nata.

***
Da na baro Indoor Sport Hall Zaria na nufa a taxi bana ko ganin abinda yake gabana don tsananin takaici da tashin hankali. Fatana inga takardar sakin nan nawa da idanuna in karanta abinda ke ciki. Har aka zo kofar gidanmu ban sani ba ina sharar hawaye da dankwalin leshi na, sai da mai taxi ya ce.
"Hajiya, ba nan ne gidan ba?"
Na bude na fita na fiddo kudin da ban tsaya kirgawa ba na dai tabbatar yafi abinda zai nema na zube mishi a kujerar gaba nayi ciki.
Na danna kararrawa (door bell) Momi ta zo ta bude duka hannuwanta cude da fulawa ina jin alkubus take yi. Ganina haka hajaran majaran fuska babu alamun rahama ta tabbatar cikin ranta da kyar in ba (bomb) din ne ya tashi ba. Ta matsa min hanya na shige, ta koma kicin ta ci gaba da aikinta.
Gidan babu kowa sai Walid autan Momi, duk suna Kaduna cin biki. Na fadi nan bisa carpet na shiga kururuwa kamar na rasa iyayena biyu a lokaci daya.
Momi bata ce min cikanki ba, haka ko lekowa bata yi ba. Wannan ya kara kunna ni, na mike na shiga tamaula da kayan falon su filillikan kujera, flower rose. Ganin ina shirin yi mata ta'adi da kayan kallonta ta fito a fusace ta nuna ni da yatsa.
"Wallahi-wallahi ki kiyayeni cikin gidan nan, kinga dai babu kowa, babu mai kwatar ki don haka sai inyi miki dukan tsiyan da zai taimaka ya dawo dake cikin hankalinki, don da alama Fa'izah ke dabba ce, dabbar ma ta daji wadda bata san ciwon kanta ba. Allah Yasa Fa'izu yankan kai yake yi, ya yanke naki kowa ya huta wannan bala'in".
Na hade kaina cikin gwiwa bayan nayi fatali da goggoron.
"Momi bai kamata kice min haka ba, duk abin nan da nake yi saboda in kare mutunci da martabar ki ne daga idanun wanda bai san kina da su ba, don ni ta tawa mai sauki ce ban dauki kaina a bakin komai ba balle in dauki wulakancin da Fa'iz ya shekara yi mini abinda zai hana ni shakar numfashi a duniya.
Ba zan taba son shi ba Momi, ba zan taba ganin farinshi ba tunda ya wareki daga cikin iyayensa. Duk abinda yayi min a baya kin manta Momi...".
"...Na manta don ubanki, sai ki sani in tuna! Wallahi ki ka sake yi min kururuwa a gida sai na kakkarya ki, kin kuma koma inda ki ka fito kinji na gaya miki".
Sai na tura kai cikin kafafuna nayi ta rasgas kuka a hankali, babu mai lallashi balle wanda zan yiwa in huce. A kuma yanayin Momi na na tabbata zata aikata abinda ta fadi na sake na sake daga mata sauti.
A haka Babana ya taddani, ya zauna cikin kujera yana fadar.
"Kiyi kukanki mai dalili, yi kukanki da babbar murya Fa'izu bai sake ki ba! Da yake shi ya haifu cikin uwa da ubanshi ya san darajar iyayenshi da karfin ikon su a kansa. Allah Ya dawo dashi lafiya kafarki kafarsa, inda duk ya sanya kafa na rantse da wanda raina yake hannunsa".

***
Kwana biyu aikina kenan ina abinda naga shine rangwame a gareni wato (kuka) duk na koma jemammiyata ta baya a dakin Abdallah. A haka ne Ya Rabi da Ya Mufty, kan hanyarsu ta komawa Kano sai gasu a Zaria, Aunty Rabi ta shigo ta iskeni dakin Abdallah, ta aje mayafinta da babynta akan gadon Abdallah, ta ce.
"Kai! Fa'izah bakya gajiya, zuciyarki bata gajiya da kuntatawa kanta a banza a wofi alhalin hakan ba zai sa ba, kuma ba zai hana ba! Shin duka wannan na kiyayyar ne, ko na haushin Fa'iz dan albarka bai yi saki ba?"
Nayi banza da ita, can kuma na ce.
"Ki bani takardar in gani da idanuna".
Da murmushi fal a fuskarta ta ciro takardar a jakarta ta ce.
"Gata".
"Don haka in zaki hutar da kanki da zuciyarki to ki hutar, in kuma kina ganin kukan ki da tayar da hakarkari da hankalin ki shi zai sa Fa'eez ya yi saki to anan kam kinyi kuskure. Haka in ma duka da kwalba ne shima aikin banza za kiyi tayi don kuwa Fa'iz jinin Hajjah ne, rabin zuciyarta, magajinta. Idan ya ce 'eh' baya taba dawowa ya ce, 'a'ah'.
Shin don Allah in tambaye ki, meye abin ki ga Fa'iz?"
Na dago sharkaf da zufa, kashirban da hawaye da majina bayan na karanta takardar.
"Ai ba zaku taba gano aibunshi dani nake hangowa ba tunda danku ne, ba kuma ka taba ganin aibun danka komin muninshi ko munin halinshi. To tunda ba zaku gani ba da duk hujjar da na kawo to ni na tsane shi ne, bana sonsa, fakat! Da inyi zaman aure dashi gara min zama a dokar daji da bakin-kumurci. Allah da Ya halicce ni Shi Ya daura min kiyayyarsa da duk wani mai irin halayyarshi.
Yadda kuma ake ikirarin shi jinin Hajja ne baya magana biyu sai a gaya min in ni tawa uwar shege na tayi ta kawo muku".
Ya Rabi ta jinjina kai cikin kidima tana fadin.
"Babbar magana. Ni na kawo kaina, dama ba yadda Hajja bata yi dani ba kar nazo ke mahaukaciya ce amma banji maganar uwata ba dole naji wohoho! Sai ki mutu kuwa! Muddin Fa'iz ya dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login