Showing 6001 words to 6919 words out of 6919 words
Chapter 3 - JARUMA YAZILA Book 2 by Abdulaziz Madakin Gini.txt
sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan. " Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!". Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!". Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu ya raunata. Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na musamman. Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira. Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci. Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita. Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum, harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau. A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar karamar kofa ta shiga. A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar kullum. Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin yake. Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka rufe kofar kejin. A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma Dabira da Jaruma YAZILA. Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya. Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi dogaro?". Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin addininku ne ya bani ita bayan an bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ". Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen, domin su biyun babu wanda ke da alamun samun nasara akan abokin gwaminsa. WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR HADUWA DA AKAI ? SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA? IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ? YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR BIRNIN KISRA DA RUN DUNAR BIRNIN MISRA? A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE CIKI? SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR? Muhadu a littafi mai suna BAKIN ARTABU don jin cigaban wannan kasaitaccen labari Alham dulillah a yau na kawo karshen littafin jaruma yazila 1-2-3 kamar yadda nagaya muku tun farko shine a hannuna ban sami cigaban saba amma idan na sami cigabansa zan kawo mukushi. JARUMA YAZILA Littafi na Uku Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- SSuleiman zidane kd. WhatsApp 09064179602