Showing 1 words to 3000 words out of 5296 words
Chapter 1 - SA MAZA GUDU BOOK 1 BY ABDULAZIZ MADAKIN GINI.txt
SA MAZA GUDU
littafi na daya(1)
Na Abdul Aziz Sani madakin gini..
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude
a
cikin daular larabawa a zamanin da babu wata
huldar kasuwanci wacce tafi cinikin bayi, anyi
wani babban birni mai suna Madinatul Zauwara.
Birnin Madinatul Zauwara na karkashin mulkin
wani gawurtaccen sarki ne ma'abocin jarumtaka
wanda ya zamo gwarzon mayaki kuma dodo ga
dukkan sarakunan dake nahiyar,ana kiran wannan
sarki da suna Sharkuf bin Aufan. Duk wani abu
najin dadin duniya Allah yabawa sarki
Sharkuf,yanada 'ya'ya guda tara amma
dukkaninsu mazane,sai mace guda daya.Babban
dansa kuwa shekararsa talatin da takwas,ana
kiransa da Lahaman.
Lahaman ya gado maifinsa a sadaukantaka da
jarumta kuma shine yake jagorantakar dakarun
sarki a duk sa'adda za'a fita FARAUTAR BAYI.
A tarihin fitarsa farautar bayi sau sittin da uku
bai taba dawowa gida cikin rashin nasara
ba,kuma
duk sa'adda ya fita baya dawowa da kasa da
bayi dubu uku,sau tari idan yarima Lahaman ya
fita farautar bayi baya dawowa sai bayan wata
biyu ko wata uku.
Kashi daya cikin kaso uku na ribar bayin idan an
siyar na yarima Lahaman ne,ragowar kason biyun
kuwa na sarki Sharkuf ne.Saidai duk dakarun da
aka fita wannan farauta dasu akan basu kyautar
bayi bibbiyu.
Bisa wannan dalili ne a gaba dayan 'ya'yan sarki
Sharkuf babu mai kudin Lahaman,kuma wanda
wanda mutane ke sa ran cewa za'a bashi gadon
KARAGAR sarki to amma shi sarki Sharkuf yaki
fadar wanda zai gajeshi. A gaba daya 'ya'yan
sarki Sharkuf su tara babu wanda yafi soyuwa a
cikin zuciyarsa sama da
gimbiya Malika,duk abinda gimbiya Malika ta
furta tanaso indai akwai shi anan duniyar sai
sarki Sharkuf ya bata,kuma babu wata alfarma
da
zata nema wajensa ta rasa.Kai saboda tsananin
kaunar da Sarki Sharkuf ke yiwa gimbiya Malika
ko Fada zaije tare da ita yake zuwa,su zauna
tare
bisa KARAGAR MULKI,kuma duk taro mai
mahimmanci idan bazai samu damar halartar
ba,ita yake turawa ta wakilceshi.Sukan su
ragowar 'ya'yan sarki idan suna son wani abu a
wajen mahaifinsu saidai suyi kamun kafa da
Malika,in ba haka ba kuwa bazasu
samuba.Wannan dalili ne yasa dukkanninsu suke
yi mata biyayyar dole duk da cewa sun girmeta.
Yarima Lahaman ne kadai baya saurarenta kuma
sai kiyayya da hassada ta shiga tsakaninsu,sabo
da ganin kamar sarki zai iya hanashi karagar
mulki
ya bata.
In badon Yarima Lahaman yana matukar tsoron
sarki Sharkuf ba,da tuni yasa an hallaka Malika a
asirrance,domin ya huta da fargabar dake
zuciyarsa da kuma tsananin kiyayyar dake
tsakaninsu,babban abinda yake kara baiwa
Yarima Lahaman haushi shine duk abinda yake
iyayi da kudi itama Malika tanayi,har ma tana
iyayin abinda shi ba zai iyaba,saboda komai
tsadat abu tana iya sayansa,saboda tanayin
kasuwanci a boye ba tareda dashi kansa sarki ya
sani na.
Saida ya zamana cewa fiye ta rabin fataken
birnin
nata ne,kuma saida ya kasance a nahiyar gaba
daya babu 'yar kasuwar da tafi Malika safarar
kayan abinci da makaman yaki
Bisa wannan dalili ne tayi sabo ainun da
sarakuna da kuma manyan attajirai,ababan
misalai.Da
yawa daga cikin sarakunan da attajiran basa
ganinta sai a karshen shekara.a wannan lokacine
take kai ziyara kasa kasa tana karban cinikin da
aka tara a hannun wakilanta dake tapiyar mata
da kasuwancinta.Sarki Sharkuf duk bai san
wannan kasuwancin da take yiba,abinda yasani
kawai
shine duk karshen shekara tana shirya tafiya ta
kai ziyara izuwa manyan kasashe hudu,don
ziyartar manyan dakunan bauta dake birnin
Kisra,Farisa,Yemen da kuma Misra.
A wannan lokacin ba'a barin kowa ya shiga cikin
wadannan dakunan bauta face sarakai,manyan
attajirai,manyan jarumai,da kuma kasaitattun
bokaye.Duk sa'adda gimbiya Malika zata fita
izuwa wannan gagaruman tafiya sarkin yakin
birnin Madinatul zauwara ne yake yi mata rakiya
tare da dakaru dubu uku domin tsaron
lafiyarta,dama babban boka na kasar wanda ake
kira Muzambil bin Samrad.
Wannan gawurtaccen shiri da ake yiwa Gimbiya
Malika na tsautsauran matakan tsaro,shi yasa
Yarima Lahaman ya kasa kai mata hari,saboda
ya
tabbatar da cewar shi kadaine zai iya tarar sarkin
yakin nasu da kuma bokansu kuma in dai ya tare
su sai sun gane shi tunda sun san irin yanayin
yakinsa da irin sihirn tsafinsa,idan kuma yaransa
ya tura sai asirinsa ya tonu an gane shi ya tura
su.
Burin Yarima Lahaman shine sarki ya mutu ya
gaje karagarsa,to abinda ya aiyana a ransa shine
a ranar zaisa a kama Gimbiya Malika da uwarta a
kaisu kurkuku,bisa hukuncin daurin rai batare da
sun aikata laifin komaiba,sauran kannensa kuwa
zai tursasasu suyi masa biyayya,duk wanda yaki
dole ne cikon biyu abu guda ya sameshi,kodai a
batar dashi ko kuma shima a kaishi kurkuku ya
karasa rayuwarsa a can.
A ranar da ya rage sauran kwana uku kacal
Gimbiya Malika ta tafi ziyartar da ta sabayi a
karshen shekara ne,yarima Lahaman ya dawo
daga farautar bayi.A wannan karon wata nahiya
daban suka je suka riski wata karamar kasa
kawai
sai suka afkawa kasar da tsakiyar dare sukayi
mummunar barna.
A daren ne sarkin garin yayi sabon aure yana
tare da amaryasa suna shirin more amarcinsu
kenan
Lahaman ya bayyana tsulum a gabansu.Nan take
aka kama sarkin aka daure shi a gaban idanunsa
yanaji yana gani kuma yana kuka Yarima
Lahaman ya yiwa matarsa Fyade kuma yana
gamawa da ita ya zare wuka ya lumamata a
ciki,take ta sulale kasa matacciya.Koda sarki
Hilairu yaga na kashe masoyiyarsa sai shima ya
sulale kasa sumamme,Lahaman ya bushe da
dariya,ya dubi yaransa yace"ku kama shi ku saka
masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai
mayar da sarki nawa.
idan baku mantaba kwanakin baya mun fara
littafin sai muka tsaya kasancewar sa incomplete
ne. Banaso sai ya dauko dadi kuma a katse shi
babu dadi shiyasama na daina post din sa.
Ammana yanxu alhamdulillahi yasani complete
din sa har karshe yadda zamuji dadin sa. Nafara
post ne daga farko saboda nasan mostly ba'a
karanta ba saboda daukan lokaci. Da fatan
littafin yayi...
Suleiman zidane Kd
Whatsapp no 08161272634
SA MAZA GUDU
littafi na daya(1)
Part B
Lahaman ya dubi yaransa yace "ku kamashi
kusaka masa sarka ya zama bawana,nine bakin
dare mai mayar da sarki bawa,kuma nine
GUGUWAR ANNOBA mai zuwa babu
sallama.Haka
dai yarima Lahaman yayita yiwa kansa kirari,har
suka gama kama bayin dasuke bukata kimanin
dubu hudu maza da mata a cikin wannan karamin
gari,bayan sun kone gidaje da yawa sun kwashe
dukiyoyi da yawa,nan take suka tusa keyar bayin
harda sarki Hilairu suka fice daga birnin mai suna
Baitul Laharas suka juyi suka nufi kasar
Madinatul Zauwara.
Bisa al'adar yarima Lahaman duk macen da
yayiwa fyade take yake kasheta,har a birnin
Madinatul Zaurawa kowa ya sanshi da wannan
muguwar dabi'a.Saida sarki Sharkuf ya kafawa
Yarima Lahaman doka cewa idan ya sake yiwa
wata 'ya mace fyade ko ya kasheta zai cireshi
daga matsayin yarima kuma ya yanke masa
hukuncin daurin rai da rai a kurkuki,sannan matan
birnin suka samu nutsuwa da kwanciyar
hankali.Bakomai ne yasa Yarima Lahaman ya
tsani mata ba yake yi musu fyade kuma ya
kashe
su ba,sai saboda kiyayyarsa da da 'yar uwarsa
gimbiya Malika itama tasan hakan kuma yin
hakan da yake yi ne yasa taji ta dada tsanarsa
fiye da kowa a duniya.
Da yammaci ne sakaliya Yarima Lahaman ya
shigo
cikin birnin madinatul zauwara tare da
rundunarsa ta mayaka da kuma bayin daya kama
a daure cikin sarka nan bugunsu da bulala ana
ingiza su,kai da ganin bayin kasan cewa sunja
bakar wahala,domin duksun rame akwai alamun
sunsha yunwa a wanannar doguwar tafiya da
sukayi,shi kuwa sarki Hilairu sau uku yana
yunkurun kashe kansa saboda bakin ciki amma
dakarun Lahaman na hanshi da karfin tsiya su
tattakashi cikin wulakanci da muzantawa ,duk
sa'adda sarki Hilairu ya tuna cewa an kashe
masa matarsa Zailat wacce yake matukar SO DA
KAUNA,kuma ya tuna cewa an rabashi da
mulkinsa,dukiyarsa,kuma shi da jama'arsa da
yawa an maishe dasu nayi,dakarunsa na yaki
kuwa kusan gaba dayansu aka kashe.ko ina a
cikin birnin nasa gawarwakine da jini,sai ya fashe
da matsanancin kuka yaji ya tsani kansa da
rayuwarsa gaba daya.
Sarki Hilairu ya kasance Kyakkyawan saurayi
abin kwantance mai kwarjini da haiba irin ta
sadaukai
amma ko kadan bai kasance jarumi ba,kuma bai
taba yin yakiba a rayuwarsa,sarautar ma
tsintarta
yayi a sama ba gado yayi ba.Sarkinsu na da
bashi
da 'da ko jika,kuma bashi da wani dan'uwa face
Hilairu.Mahaifiyar Hilairu ta kasance Kuyangar
Sarkin da ya mutu,don haka shi dan baiwane,ba
dan wata 'yantacciya ba,ta haka ne ya gaji
wannan sarauta.
A daidai wannan lokaci yarima Lahaman ya shigo
cikin birnin madinatul zauwara sai akayi akasi
gimbiya Malika ta fito rangadi zata fita izuwa
bayan gari domin yin parauta a daji.A wannan
lokaci tana tare da tsirarun dakaru wandan basu
fi su arba'in ba.A daidai kofar shiga cikin birnin
sukayi kicibus.A wannan lokaci yarima Lahaman
na cikin tsananin farinciki bisa ganin dinbin
dukiyar daya samo wacce baitaba samun
kamartaba,gami da lafiyayyun bayin da yasan
cewa zai siyar dasu da darajar gaske.Koda
yarima
Lahaman da gimbiya Malika suka hadu sai
kowannensu ya murtuke fuska suka bata rai
kamar an aiko musu da sakon mutuwa,da ko
magana basayi da juna.Koda Gimbiya Malika ta
dubi tarin dukiyar da Yarima Lahaman ya samo
gami da tarin bayi,sai takaici ya kamata saboda
tasan ce Allah ne kadai yasan irin mugun
zaluncin da akayi wajen samosu,
Kwatsam sai idanun Malika suka kai kan sarki
Hilairu,tana hada ido
dashi sai zuciyar ta ta buga da karfi nan take a
karon farko a rayuwarta taji ta kamu da tsananin
son 'da namiji don haka batasan sa'adda ta kura
masa idanuba har suka gifta juna tana
waigensa.Abinda ya kara mata sonsa mashi ne
shima ya kura mata idanu,cikinalamun tsananin
kaduwa da mamaki,har ya tsaya cak ya daina
tafiya sai da aka buga masa kulki aka hankadashi
gaba yana turjewa na dada bugunsa sannan ya
janye.Ashe ba wani abu ne yasa Sarki Hilairu ya
kura mata idanu ba face kamanninta yazo iri
daya sak da matarsa wacce yarima Lahaman ya
kashe tamkar an tsaga kara.Dama tun acan
birinin na sarki Hilairu yaran Lahaman suka yita
tsegumin suna cewa matar sarki Hilairu tana
kama da Gimbiya Malika.Yana daga cikin dalilin
ma da ysa Yarima Lahaman ya kasheta,tun da ya
tsani Malika,Ya tsani duk mai kama da ita.Har su
yarima Lahaman suke kule gimbiya Malika bata
daina waigensu ba,kuma zuciyarta bata daina
bugawa ba,da zafi,nan dai ta kudurci aranta
cewar ta kowanne hali sai ta mallaki wancan
bawa wanda ita yanzu ta kamu da tsananin son
sa farat daya a farkon haduwa.Babban tashin
hankalin ta shine tasan cewa ko nawa zata
siyeshi
yarima Lahaman bazai siyar mata ba,saboda
kiyayyar dake tsakaninsu.
Al'amarin Yarima Lahaman kuwa lokacin da yaga
gimbiya Malika ta fito rangadi daga cikin gari
tare
da tsirarun dakaru,sai wani abu ya fado masa a
rai.Nan take yayi tunanin ya batar da
kamanninsa
ya dawo cikin dajin ya afkawa masu
tsaronta,amma sai wata zuciyar tace dashi
a'a,yin
hakan abune mai matukar hadari,domin idan
asirinsa ya tonu ba zatayi masa kyauba.Domin
akwai lokacin da kwatankwacin hakan ta faru da
kyar ya samu kubuta daga zargin sarki.
Al'amarin ya faru ne wata rana sa'adda ana
zaune a
fada,duk su biyun shida Gimbiya Malika suna
zaune a fadar tare da sarki,Malika na daman
Sarki shi kuwa yana hagunsa,sai ga wani mai
gadin kofar gari ya shigo cikin fadar a guje cikin
gigita,da zuwansa sai ya zube kasa gaban sarki
ya
kwashi gaisuwa,muryarsa na rawa kuma kansa a
sunkuye ya bude baki yace,"Ya shugabana,kayi
sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar
gari kawai sai muka hango ......
By Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634
SA MAZA GUDU
Littafi na Daya(1)
Part C
Yace,ya shugabana kayi sani cewa muna kan
aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka
hango wadansu bakin dakaru acikin shigar
bakaken kaya,bisa dawakai sun rufe fuskokinsu
sun nufo kofar gari,koda muka hango su muka
yunkura zamu busa kahon yaki,sai suka ja baya
suka nausa cikin daji suka bace bat tamkat basu
taba wanzuwa ba.Bisa wannan dalili ne yasa
muka kasa samun nutsuwa da kwanciyar
hankali,shi yasa muka ga ya dace muzo mu
sanar
da kai domin kasan matakin da ya kamata a
dauka.Kodajin labarin,sai sarki Sharkuf ya bushe
da dariya,sannan yace,ai kuwa tasan gidan mai
babbar sanda,tsoro suka ji shi yasa suka juya da
baya.To amma akwai wani boyayyan al'amari a
tare dasu,domin ko da wasa ba'a taba samun
'yan fashi ko 'yan harin da suka taba kusantar
kusa da kofar garin nan ba,saidai suyi shawagi a
can wajen gari ciki dazuzzuka,lallai ruwa baya
tsamin banza,kuma da dan gari akanci gari.Akwai
wani munafuncin da ake shiryawa tare da
waninmu.Koda gama fadin haka,sai sarki ya dubi
yarima Lahaman yace,ya kai yarima,maza ka dibi
dakari dubu kuje ku bi sawun wadannan dakarun
sumame,idan sun fice daga yankin kasata ku
kyalesu,idan kuma suna ciki ku yakesu ku kashe
su,kada kubar mutum daya ya tsira da
rayuwarsa.Koda jin wannan umarni,sai yarima
Lahaman ya mike tsaye zumbur da nufin yaje
yayi shiri,amma sai Gimbiya Malika ma ta mike
zumbur tasha Gabansa tace,ya akai da'uwana ina
rokonka ka tafi tare dani,domin idanuna suna son
ganin ko suwaye wadannan marasa kunya da
rashin tsoro har suke tunanin zasu iya kawo
mana hari.Koda jin haka,sai kowa ya cika da
mamaki a fadar musamman ma sarki Sharkuf
wanda a saninsa ko magana Yarima da Gimbiya
basayi,amma yau wai itace ke rokonsa akan ya
tafi da ita wajen gari don yakar abokan
gaba.Lokacin da yarima Lahaman yaji bukatar
gimbiya,sai ya dubi sarki domin yaji ta bakinsa
ko
zai amince ya tafi da itan,Bisa ga mamaki sai
gashi sarki ya Amince.Abin ya baiwa kowa
mamaki a fadar,soboda ansan cewa a duniya
babu abinda sarki Sharkuf ke so sama da
gimbiya Malika,kuma baya yarda taje wani wuri
mai
hadari,kuma yasan irin kiyayyar dake tsakaninta
da dan'uwanta Yarima Lahaman,to amma me
yasa yanzu ya amince ya tafi tare da ita izuwa
yaki?Ita kanta Gimbiya Malikan saida ta yiwa
kanta wannan tambayar a cikin zuciyarta,nan dai
Malika tabi Yarima Lahaman a bya cikin farinciki
suke fice daga cikin fadar.Suna fita Lahaman
yayi
shigar yaki ya tara dakaru dubu sukayi hawa
itama Malika sai aka kawo mata nata dokin ta
hau
suka fice daga cikin gidan sarautar suka nausa
cikin dajin suna masu bin sawun dawakan da
suka gani.Koda suka iso wani wuri inda hanya ta
rabu biyu,sai Lahaman yaja limzamin dokinsa ya
tsaya cak yayi nazarin hanyoyin sannan ya juya
ya
dubi gimbiya Malika yace,Daki tsaya anan ke da
rabin dakaruna dan tabbar da tsaron lafiyarki,ni
kuma da sauran dakarun zamu shiga ciki harsai
mun isa inda wadannan abokan gaba suka
buya.Kodajin wannan batu,sai Malika ta ce a'a ba
haka za'ayiba,ai yanzu baka da tabbacin cewa
hanyar da zakabi can abokan gabar suke,saidai
muma mubi daya hanyar idan muka riske su,sai
mu yakesu,in kuma kaine ka riskesu ka
yakesu.Sa'adda yarima Lahaman yaji wannan
batu,sai yayi murmushi yace ,idan wani tsautsayi
ya sameki kada kiga laifina tunda dai ni ga inda
nace ki tsaya kuma kika ki.Malika ta maidawa
Lahaman martanin Murmushin tace,Saki ranka
tamkar tsumma a randa domin shi kansa
tsautsayin baya zuwa kusa da Malika,in kuwa
yazo saidai ya shafi waninta amma ba ita
ba.Anyi
gumurzu a cikin dajin an kashe gaba dayan
dakarun dake tare da Malika amma ita ta tsira da
rayuwarta da lafiyarta,aka dawo gida da kyar
yarima ya kubuta daga zargin sarki,bayan yasa
tambayoyi har yana hada gumi duk da yarima
yayi wannan tunanin sai ya kudirce a ransa sai
ya
dawo cikin dajin ya kashesu farat daya,sannan
itama ya kasheta,kuma ya alakanta mutuwarta
da
'yanfashi ko miyagun dabbobin daji.
Abu na biyu kuma da ya fado masa a rai shine
koda bai kasheta ba,to lallai bazai bari ta mallaki
wannan
bawa nasa ba wato sarki Hilairu saboda ya lura
da irin kallon da take masa ya gane cewa ta
kamu
da sonsa.Lokacin da yarima Lahaman ya isa gida
sai ya ware bayi maza guda saba'in mata guda
talatin wadanda sune mafi lafiya,da kwarjin da
kyawu.Yasa aka kaisu can wani gida nasa na
musamman wanda ba kowa bane yasan da
shi,aka boye su a can da zummar cewa baza'a
sake fitowa dasuba sai ranar da babbar kasuwar
birnin take ci,domin ya sayar dasu da daraja ga
manyan attajirai.Daga cikin bayin gudu darin
kuwa harda sarki Hilairu.
Sa'adda aka kai su Hilairu wannan gida aka
watsa
su izuwa cikin daki,sai suka ga an kawo musu
abinci da abin sha lafiyayye,wanda rabonsa da su
ci irinsa yafi kwana arba'in tun kafin akawowa
birninsu Hari.Nan fa bayin suka rude suka kama
wawason abincin suna ci kamar dabbobi,mazansu
da matansu har suna kokawa.Shi kuwa sarki
Hilairu sai ya zuba musu idanuwa kawai yana
kallonsu shashashu.Ya rike kimarsa ta sarki
kuma
yaki neman abincin dukda yunwar yakeji.Kawai
sai ya koma gefe daya ya zauna ya daga kansa
sama yana tunani.Ba komai yake tunowa ba face
fuskar gimbiya Malika.Take ya tambayi kansa a
cikin zuciyarsa yace,wai shin matata bata mutu
ba
ko kuwa wacce na gani dazu aljanace,da har
zata
biyo ni tana dada yaudarata?Ashe yarima
Lahaman yasa dakarunsa su zuba ido sosai akan
sarki Hilairu saboda kada ya kashe kansa ko yayi
yunkurin guduwa ko kuma a turo a sace shi.Sarki
Hilairu na zaune cikin wannan hali na tunani sai
daya daga cikin bayin wani katon matashi
mai......
By Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634
#SAS
SA MAZA GUDU
Littafi na daya(1)
part D
Sarki yasan wannan takobi sosai tunda shi ne ya
baka ita da hannunsa lokacin daya raba mana
takubba gaba dayanmu mu tara.Ko ka manta
ne,shaidata ta biyu shine raunmin dake jikin mu
ni dakai,idan na fadawa sarki cewar mun fafata
kayimin rauni a hannu ni kuma nayi maka a
kafada.Za'a duba aga raunin namu kaga kenan
dole ya gamsu cewa kayi kokarin hallakani.Idan
haka ta faru kuwa kasan cewa sarki zai cire ka
daga matsayinka na Yarima kuma sai ka tafi
kurkuku.Koda Malika tazo daidai nan a
zancenta,sai hankalin Lahaman ya dugunzuma
ainun gashi a wannan lokaci jiri ya fara dibarsa
sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa.Ita kuwa
nata raunin karami ne jinin da ya zuba kadanne
don haka ya tabbatar cewa idan suka cigaba da
yakin cikin kankanin lokaci zata sami nasara
akansa.cikin mugun Takaici Lahaman ya dubi
Malika yace,mene me abinda kike bukata a
wajena?Malika tayi murmushi a karo na biyu
tace,A cikin bayin daka zo dasu akwai wani
saurayi wanda babu kamarsa a kyau da kwarjini
yana da siffa irin ta sarauta.Ina son ka siyar mini
da wannan bawa,idan kayi haka zan rufe asirinka
bisa wadannan dakarun da ka kashe,nace 'yan
fashi ne suka kawo mana hari na
fatattakesu.Koda Malika tazo nan a
zancenta,sai
Yarima Lahaman yayi shiru yana tunani da
nazari,ba komai yake tunani ba face hanyar da
zai bi ya yaudari Malika ya nuna ya amince
amma yabi hanyar da a karshe zai hanata
mallakar wannan bawa,amma sai ya kasa samun
mafita.Kawai sai ya dago kai ya dubi Malika a
karon farko a rayuwarsa yayi mata murmushi
yace,To kanwata yau kinyi nasara akaina amma
ki
saurari ranar da zan dauki fansa.Ki sameni a
gidana na can bayan gari da yammaci muyi
cinikin wannan bawa ki biya ki tafi dashi.Koda jin
wannan batu,sai Farinciki ya kama Malika ta ruga
ta kama wani doki ta zabureshi da gudu ta nufi
cikin gari.
A can kuma gidan sarauta kuwa,koda sarki
Sharkuf yaga lokacin da Malika ta saba dawo
gida
daga farauta ya wuce sosai,sai Hankalinsa ya
tashi,nan take ya tura aka kirawo sarkin yaki,ya
tambayeshi yace dakaru na wane suka yiwa
gimbiya rakiya izuwa farautar?Cikin Alamun
damuwa sarkin yaki ya sunkui da kansa kasa
yacemya Shugaba ai dakaru Arba'in ne
kacal.Koda
jin haka sai sarki sharkuf ya dakawa sarkin yaki
tsawa,ya rufe shi da fada,yana mai cewa ai
wannan ganganci ne kabar gimbiya ta tafi daji
farauta tare da dakaru Arba'in kacal.Alhalin
kasan
cewa wasu lokutan 'yan fashi na iya kawo harin
sumame.Cikin tsananin fishi sarki sharkuf ya dubi
wani hadiminsa yace,yaje ya dauko masa kayan
yakinsa da dokinsa da kansa zaije ya dubo
gimbiya.Koda jin haka sai sarkin yaki ya zube
kasa
bisa guiwowinsa ya kama tuba yana mai rokon
sarki ya hakura shi zaije ya dubota yanzu.Gama
fadin hakan ke da wuya sai sukaji sukuwar
doki,suna waigawa suka hango gimbiya Malika ce
ta shigo cikin gidan sarautar ita kadai bisa doki
kuma ga rauni akan damtsen ta na hagu.Cikin
firgici sarki sharkuf ya ruga gareta ya ruke mata
dokin ta sauko ya rungumeta sannan ya goyata a
bayansa ya ruga da ita zuwa cikin gidansa yana
mai kwalawa likitansa kira,kai kace wani mugun
raunine a jikin nata.Sarki sharkuf bai sauke
Malika a ko ina sai akan gadonsa cikin kuryar
turakarsa,nan take likitansa yazo ya duba raunin
nata,ya dubi sarki yace,ya shugabana ai raunin
ma karamine ba sai anmata dinkin ba,mahani
za'a samata.Nan take likitan ya gama aikinsa ya
fice.Fitarsa ke da wuya Sarki yasa aka kawowa
gimbiya abinci da ababan sha na alfarma.Da
hannunsa ya shiga ciyar da ita har ta
koshi,sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake
'yata bani labari mene ya faru gareki har kika
sami wannan raunin kuma ina dakarun dake
tsaron lafiyarki,su arba'in?Koda jin wannan
tambaya,sai Gimbiya Malika tayi Murmushi
tace,kwantar da hankalin yakai abbana,kayi sani
cewa duk irin hadarin da zan shiga zan iya kare
kaina koda kuwa bana tare da dakaru.Koda jin
haka,sai mamaki ya kama sarki yace,tayaya