Showing 3001 words to 5296 words out of 5296 words

Chapter 2 - SA MAZA GUDU BOOK 1 BY ABDULAZIZ MADAKIN GINI.txt

zaki
iya kare kanki alhalin baki iya yaki ba?Dajin
haka,sai Malika ta mike tsaye taje ta zaro
wadansu takubba guda biyu dake jikin bango a
rataye ta jefawa sarki guda ya cafe,tace,tashi
ka
jarraba jarumtakar 'yarka yau kasha
mamaki.Koda jin haka,sai sarki Sharkuf ya mike
tsaye yana murmushi gami da yi mata kallon
mara hankali yace,haba 'yata wai shin anya kuwa
yau ba Aljanu bane suka shafeki acikin daji?Ta
yaya kike tunanin zaki iya tarata da yaki alhalin
ko yayanki Yarima Lahaman da yazamo jarumin
da babu kamarsa a wannan nahiyar,ya kara dani
baiji dadi ba.Malika ta maidawa masa da
Martanin murmushin tace,ai sarko goma zamani
goma,ni yanzu karfina ya kawo kuma na dade ina
yiwa kaina tanadi.Tana gama fadin haka sai ta
juya tayi tafiya gaba daku goma da yake
turakace
mai girma da fadin gaske.Daga inda ta tsaya sai
kawai sarki yaga Malika ta dako tsalle a sama
tamkar an harbata daga cikin baka,kafin ya
ankara ta kawo masa wawan sara aka.Cikin
bakin
zafin nama sarki sharkuf ya yunkura ya daga
takobinsa dake hannunsa ya kare saran amma
saboda karfin saran da nauyinsa sai da ya dan
durkushe kasa rawaninsa ya tuje.Al'amarin da
yayi matukar bashi mamaki kenan ya mike tsaye
ya koma gefe daya yana mai motsa dukkan
gabban jikinsa domin shirin fara yakarta.Nan take
murmushi ya subucewa sarki sharkuf ya juya ya
fuskanci malika yace,yaya akayi kika koyi yaki
amma bansani ba?Kabari sai mun gama motswa
jikin na baka labari.Kawai sai Malika ta sake
rugowa izuwa kan sarki suka sake ruguntsumewa
da masifaffan yaki tamkar sun kasance tsofaffin
abokan gaba ya zamana cewa suna kaiwa
junansu
SARA DA SUKA cikin zafin
nama,juriya,bajinta da jarumta.Nan da nan
suka
fara lalata duk kayan kawar dake cikin
turakar.Karar takubbansu kuwa ya firgita
dakaru,suka rugo da gudu izuwa cikin turakar rike
da makamai tsirara domin zatonsu wasu 'yan
simame ne suka hauro cikin gidan
sarautar.Amma
duk wanda ya shigo cikin turakar sai yaga ashe
sarki ne da Malika suke yaki.Sai ya kamu da
tsananin Mamaki ya koma gefe daya ya rakube
yana kallon ikon Allah,amma da yakin ya sake
nutsuwa sai kallon ma ya gagara ,kuma hankali
ya dugunzuma domin tun suna gumurzu a cikin
kuryar daki saida suka dawo babban falo,daga
nan suka fito waje,sai gasu a cikin harabar.Ba
komai ne ya dugunzuma hankalin gaba daya
jama'ar dake cikin gidan sarautar ba face ganin
yadda sarki da Malika ke kaiwa junansu mugayen
hare hare irin na abokan gabar dake son hallaka
juna farat daya.Lokacin da aka shafe rabin sa'a
ana wannan dauki na dadi,sai sai salon fadan ya
sauya domin a sannan ne gimbiya Malika ta gane
cewa ruwa ba sa'an kwando bane saboda ji tayi
alamun ta fara gajiya har takai cewa da kyar
take
iya tare saran sarki saboda Karfinsa da
nauyinsa.Duk sa'adda ya kawo mata saran ta
tare
sai taji kamar katon dutse ya kwado mata.Amma
saboda bakin naci da muguwar juriya taki yarda
ya fadi kasa kuma bata daina yunkurin maida
martani ba.Duk da cewa wani lokacin har
durkushewa kasa take bisa guiwarta amma sai
kaga ta mike zumbur a haka.Saida suka sake
shafe wata rabin sa'ar bataje kasa ba,amma
kuma ta gaji likis.Ana cikin haka ne sarki ya
shammaci Malika ya kwarfi kafafunta a tayi
sama
da baya taje ta gwara bayanta a jikin katangar
gidan sarautar ta fado kasa a mutukar galabaice
ta kasa tashi.Koda faruwar hakan,sai sarki
Sharkud ya sauke takobinsa kasa yayi jifa da ita
sannan ya kama yiwa Malika tafi.Nan fa gaba
dayan Jama'ar gidan sarautar suka kama yiwa
Malika tafi.Sarki Sharkuf ya nufo Malika fuskarsa
cike da murmushi yazo daf da ita ya mika mata
hannu ta kama,ya tashe ta tsaye suka rungume
juna,sannan ya janye jikinsa daga cikin nata ya
dubeta yace,Ina tayaki murna saboda kece
jaruma ta farko wacce ta iya jure yin gumurzu
dani har tsawon sa'a guda.Hatta yayanki Yarima
Lahaman da kyar ya jure tsawon rabin sa'a.Bani
labari yake 'yata yaya akayi kika iya yaki haka da
jarumtaka?Koda jin wannan tambaya,sai Malika
tayi Murmushi sannan ta zaiyana masa a
wuraren
da ta koyo yaki kamar yadda ta gayawa Yarima
Lahaman,lokutan da take fita ziyara kasashe.A
karshe ta kara da dace batun Jarumtaka kuwa ai
kaima kasan cewa barewa batayi gudu ba danta
yayi rarrafe.Na gaji sadaukantaka ne a wajenka
da wajen kakana na uwa.Koda jin wannan
batu,sai Sarki Sharkuf ya kyalkyale da dariya
yace,Tabbas maganarki dutse ce,to naji wannan
yaya kuma batun wannan rauni dake hannunki da
kuma batun dakarun da suka yi miki rakiya izuwa
farautar?Koda jin wannan tambaya,sai Malika
tayi
ajiyar zuciya tace,'yan fashi ne suka kawo mana
harin bazato kafin muyi wani yunkuri sun kashe
gaba daya dakarun nawa.Ni kuwa saina afka
musu muka ruguntsume da azababban yaki.Da
suka ga nafi karinsu,sai suka girgiza suka bace
bat
na nemesu na rasa.Lokacin da Malika tazo nan a
zancenta,sai taga sarki yayi mata wani irin kallo
na rashin yarda sannan yace,yake 'yata ta yadda
naga irin jarumtakarki a yanzu babu wasu
'yanfashi a wannan nahiyar da zasu tareki da
yaki
batare da kin samu nasarar kashe koda mutum
dayaba daga cikinsu a cikin dakiku kadan bare
harma wani daga cikinsu ya sami nasarar yi miki
wannan raunin.Shin yanzu idan akaje wajen da
kukayi gumurzun za'a sami gawar koda mutum
daya daga cikinsu?koda wannan tambaya sai
Malika ta gyada kai tace,Ai muna fara yakin suka
bace kawai sa'a ce tasa shugabansu yayi
nasarar
yimini wannan rauni.Sarki Sharkuf yayi dan
guntun murmushi mai nuna alamun rashin
yarda,sannan ya dubi Malika yace,A nahiyar nan
gaba daya mutum daya ne zai iya fafatawa dake
ya samu nasarar yi miki wannan rauni,kuma ba
wani bane face dan'uwanki Yarima
Lahaman.Fada
min gaskiya shine Lahaman yakai miki harin
bazato ne?Malika ta girgiza kai tace,
Ina mai tabbatar maka da cewa a nahiyar nan
tamu kaf babu wata bafatakiya data kaini arziki
da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar
fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano
cewa
fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin
fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji
labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake
ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa
ga kasashen dake yakar juna kuma bani da
bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin
yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA
GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku
kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba
dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude
rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman
wadanda dole saida su za'a iya budewa komai
jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa
ban tara dukiya domin komai ba sai domin na
kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda
nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana
cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin
wulakantani ko cutar dani da sauran
talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin
shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya
kare
kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen
gari nasa a gina mini fada ta musamman inda
zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da
mahaifiya da sauran masoyana har izuwa
karshen
rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa
jawabinta,sai
mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu
da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke
yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda
ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar
nami ba'a taba samun mai basira da hangen
nesa
kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai
amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk
wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin
cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba
cikin
kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a
inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya
taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai
kowa yasan wannan dukiya da kuma inda
take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman
ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake
ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai
iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron
kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya
kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta
bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman
zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi
duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan
sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine
har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku
bisa
wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar
wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka
ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu
idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai
gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki
Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan
ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna
tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu
yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da
wanda ya dace ya zama ya gajeni daga
cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan
gidan
sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne
wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu
aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin
nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun
sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka
warware wannan matsalar ba tunda da akwai
alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin
hakan?
Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda
bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema
bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin
sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na
gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki
sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake
kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga
matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman
ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan
batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki
nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan
dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki
zauna tare dani in yaso ki tura amintattun
yaranki
su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta
dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me
yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba
yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin
haka,sai sarki Sharkuf ya mik
By Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634
SA MAZA GUDU
LITTAFI NA DAYA 1
Ina mai tabbatar maka da cewa a nahiyar nan
tamu kaf babu wata bafatakiya data kaini arziki
da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar
fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano
cewa
fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin
fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji
labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake
ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa
ga kasashen dake yakar juna kuma bani da
bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin
yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA
GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku
kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba
dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude
rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman
wadanda dole saida su za'a iya budewa komai
jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa
ban tara dukiya domin komai ba sai domin na
kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda
nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana
cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin
wulakantani ko cutar dani da sauran
talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin
shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya kare
kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen
gari nasa a gina mini fada ta musamman inda
zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da
mahaifiya da sauran masoyana har izuwa
karshen
rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa
jawabinta,sai
mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu
da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke
yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda
ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar
nami ba'a taba samun mai basira da hangen
nesa
kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai
amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk
wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin
cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba
cikin
kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a
inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya
taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai
kowa yasan wannan dukiya da kuma inda
take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman
ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake
ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai
iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron
kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya
kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta
bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman
zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi
duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan
sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine
har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku
bisa
wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar
wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka
ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu
idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai
gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki
Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan
ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna
tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu
yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da
wanda ya dace ya zama ya gajeni daga
cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan
gidan
sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne
wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu
aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin
nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun
sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka
warware wannan matsalar ba tunda da akwai
alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin
hakan?
Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda
bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema
bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin
sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na
gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki
sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake
kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga
matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman
ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan
batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki
nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan
dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki
zauna tare dani in yaso ki tura amintattun
yaranki
su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta
dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me
yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba
yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin
haka,sai sarki Sharkuf ya mike tsaye yayi tafitaku
uku,yana mai juya mata baya,sannan yace yake
'yata kiyi sani cewa ni fa yanzu girma ya fara
kamani tunda yanzu shekaruna sunkai sittin da
takwas a duniya bana son naga kina yin nisa dani
tunda kullum lokacina karewa yake,kuma har
yanzu akwai sirrikana da dama wadanda baki
sansu ba,asali ma dan'uwanki Yarima Lahaman
ya fiki saninsu saboda ya girmeki sosai kuma na
jashi a jikina daga kuruciyarsa kawo izuwa
girmansa kafin na fahimci cewar shi azzalumine
wanda baya kishin talakawansa na
gujeshi.Lokacin
da Sarki Sharkuf yazo nan a zancensa sai
hawaye
ya subuto masa gimbiya Malika ta sake dafe
hannun sarki akan cinyarta ta dubeshi tace,ya kai
abbana kamar yadda bakasan rabuwa dani
daidadi da rana daya haka nima na
kasance,amma ina rokonka alfarmar nayi wannan
tafiya domin itace tafiyata ta karshe akan
harkokin kasuwancina kuma acikin tane nake so
na cika wani buri nawa wanda bani da kamarsa a
raina.Kayi hakuri bazan iya gaya maka wannan
sirrin ba kamar yadda kaima bazaka iya gayamin
hawa KARAGAR MUKIN kasar nan ba,amma zaka
san nawa burin da zarar na dawo kuma nayi
maka alqawain cewa bazan fi wata uku ba zan
dawo.koda jin wannan batu,sai shima sarki
Sharkuf hawaye ya zubo masa ya kamota ya
rungumeta a kirjinsa suka dan jima a kankame da
juna.Suna cikin wannan hali ne Malika taji an
kirawo sunata,a tare suka waiga baya.
SHIN WANENE WANDA YA SHIGO MUSU
BATARE
DA NEMAN IZINI BA?
SARKI SHARKUF ZAI BAR GIMBIYA MALIKA
TAYI WANNAN TAFIYAR?
YARIMA LAHAMAN ZAI BATA WANNAN BAWAN?
INA LABARIN BAWAN DA YARIMA LAHAMAN YA
KAMO?
TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA
LAHAMAN WAYE ZAI GAJE KARAGAR MULKIN
SARKI?
MU HADU A CIKIN LITTAFI "SA MAZA GUDU"
LITTAFI NA BIYU(2) DON JIN WADANNAN
AMSOSHI.
AMMA MENE HASASHEN KU?.
By Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login