Showing 15001 words to 18000 words out of 23100 words

Chapter 6 - HABIBI DA'IMAN Book Hausa Novels by Aufana

mune ake kyamata".

Humaida ce tamik'e tsaye dasauri tarik'o hanun mami cikin kuka tana fad'in "dan Allah mami kiyi hkr, mami dan Allah kibari" hanash ma tasowa yai yazo yarik'a hanunta yafita da'ita woje.

HUDAYYA kuwa bedroom d'insu tafice dagudu tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu, hunayya kuwa kamar wocca aka kafe anan, sai kuka take tana share kwallah,.

Woni mugun kallo da wota kanwar momy saudat tamata ne yasa dasauri tamik'e tabar parlon itama.


Cikin tsintsar masifa da balbalin bala'i momy bako mayafi tafita woje tabi bayansu mami, tana zowa bayanda su mami suka shiga side d'in hajiya kawai saita fara cin mutunci da masifa,

"Babie Abbu kuna inane kufito yau wlh ko ni kokuma ku agidannan" cikin mamaki mama da ummi suka fito saiga hajiya itama tafito sbd ganin yanayinda mami tashiga side dinta dashi, shine ta tambaya humaida tafad'a mata dik yanda akayi,

Su babie ma fitowa sukai kasancewar tin bayanda aka kare baikon da sadaki basu sake fitaba suna a parlon abbu suna fira da wosu abokanansu, hakama sauran abokanan baba moallayid'i basu woceba suna gunsa a parlonsa suna cin abinci, cikin tsintsar masifa da rashin kunya da fitsara momy tafara balbala masifa,


"Wato kunmayardani sha-sha-sha shine kuka kyaleni kukace kuma kar wonda yabari nasan HUDAYYA itace wocca HINASH yazab'a ba hamida ba sbd tsabar mugunta da cin amana, to wlh gidannan ko ni kokuma ku, matuk'ar HINASH bai auri hamida ba to wlh baku ba zaman lfy a gidannan, saina sab'awa kowa a gidannan saina nuna maku ruwa ba sa'an kwando bane, haka kuma rijiya ba wurin wasan makaho bane, saina nuna maku ni basa'anku bace sainaku yin nadamar aurawara HINASH HUDAYYA, wulakantaccin banza, mayaudara, maciya amana, azzalimai".

Cikin zafin nama da tsintsar b'acin rai yaya hisham yazo yad'aga hanu danufin zai kai mata mari, dasauri Abbansu HUDAYYA yarike masa hanu cikin b'acin rai,

"Ai da kabarshi yamareni abban hamida, wlh dasaikayi nadamar zowanka duniya hisham da bazaka sake marin kowaba" cewar momy saudat.

Cikin b'acin rai Abban su HUDAYYA yake fad'in "hisham kanada hankali kuwa, matar tawa zaka daka" cikin tsintsar b'acin rai hanash yace "haba uncle woce irin maganace wonnan baka ganin yanda take zagin mutane dakuma kalamanda take furtawa izuwaga iyayenmu da kakanninm...." bai k'arisaba Abban yawonkesa da mari,

Cikin zafin nama yanunasa da yatsa yace "karka sake kace zakaman rashin kunyarda ka koyo a abuja, kuma tinda iskancin naku yakai har haka kuyi gaggawar barin gidannan tinkan wlh nasaka afitar man daku, sha-sha-shun banza da wofi".

Cikin b'acin rai mami tamatso kusa da abba tana fad'in "yaya yanzu akan wota banza kake korar y'ayana acikin gidanka, hmm bazanyi mamaki ba tinda yanzu nagani a idona bare kuma abayan idon??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a, natabbata wota rana gaba d'aya zamakace bakataba saninsu ba, shikenan amma inaso kasani namaka alk'awarin bazaka sake ganin k'afata data y'ayana acikin gidanka ba daga yanzu kuwa har abada" tana gama fad'ar haka tajuya kwallah nazuba daga idanuwonta tana sharewa.


Hakama abbu da babie dasu hisham harma dasu hassan da hussain dasu Affan dik kuka suke ssi,.

Dasauri mami taje tadakko mayafinta tana sharan kwallah tacewasu hisham "kufice muje" dagudu Affan da Ammar sukazo suka durk'usa agabanta cikin yanayin magiya da zubda kwallah sukace,


"Dan Allah mami kiyi hkr karki tafi karkiyi fushi karkice zaki hanamu mu'amala da y'an uwanmu" suka juyo gunsu babie sukace "babie, abbu dan Allah kubata hkr".

Kasa cewa uffan sukai sai zubda kwallah suke kamar mata, mami ma kasa yin magana tai kawai tafice su hisham ma sukabi bayanta.

Cikin rashin sanin abunyi abba yace "to saime dankin hana y'ayanki da kanki zuwa gidana, kujecan kuk'arata Allah iraka taki gona" tsaye mami tai cak jin kalaman abba izuwa gareta saikuma tajuyo takallesa tai d'an murmushi batareda sake cewa komaiba,

Itafa a zuciyarta mamaki take, anya kuwa wonnan d'an uwonta ne, anya hassan dinta ne kuwa, wonda yakasance baya k'aunar ganin kwallah sun zubo daga idanuwonta, wanda yakasance yana k'aunar ganin farincikinta, dikda tai aure amma hakan baihanasa nunamata gata da k'auna ba, yakan kai mata ziyara har abuja yaga lafiyarta data zuriyarta, amma woi yau itace yake fadawa waennan kalaman harda korarta da y'ayanta acikin gidansa.

Kowa tsit yai aka rasa maiyin magana ga bak'inda sukazo ko gama ficewa basuyiba kowa sai mamaki yake da al'ajabi, bawonda yace uffan momy tafice fuu izuwa side dinta.


Har mami tajuya zasu fice kawai basu ankaraba kawai sukaji hajiya tazube akasa wonwar somammiya, cikin tashin hankali sukai kanta, shikuwa Abba ficewarsa yai yabi bayan momy waishi adole ya rarrasheta yabata hkr ranta yabaci, cikin sauri hisham yad'auki hajiya sukai ciki da'ita Ammar kuma yakira family doctor nasu yazo cikin gaugawa.

Tana shiga tin a k'ofar shiga tafara kwallawa HUDAYYA kira harta k'arisa k'ofar shiga bedroom d'insu, cikin masifa idanuwonta kamar zasu fito woje tabude k'ofar tashiga.

Tana a kwonce kan bed d'insu taji shigowarta ba shiri aikuwa dasauri tamik'e tsaye kanta bako d'an kwali, ganinta a tsaye tana huci tamkar kumurcin maciji yasa tsoro yamamayeta, cikin ina ina tafara cewa "mo.....mom...momy lfy".

Cikin zazzaro idanuwa tafara tinkararta tace "wato sbd tsabar kin rainani shine kikaje kikabi baya kika karbewa hamida saurayi ko sbd kinganshi d'an gaye mai kud'i kyakkyawa, kinga kuma ita ba irinku bace mai bak'in jini, ku kunrasa mashinshini shine kukebin bayan fage kuna kwacen samari ko, to yau ni zanyi maganinki tayanda gobe sauran bazasu sake aikata irin lefinda kika aikata ba".

Dasauri HUDAYYA tafara fad'in "dan Allah momy kiyi hkr, wlh ni bance inason HINASH ba, shine yace dole saina aures...." rufeman baki y'ar iskar banza wulak'antacciya" tafad'a tareda damko sumarta dakarfin tsiya,

Wota iriyar k'ara HUDAYYA tai sbd azabarda taji, ba tausayi ba tsoron Allah momy tabuga kanta a bango sannan tasaka hanunta tashake wuyanta, idanuwon HUDAYYA sun firfito woje sbd azaba.

Hanunta takai tana neman ta cire hanun momy sbd numfashinta dataji yana nema ya d'auke, tana kallonta ta zaro idanuwonta cikin tsintsar mugunta, can tasaketa tafadi kan tiles tana tarin wohala a kakari, sake damkota tai tabuga kanta akan tiles d'in nantake jini yab'alle mata tahanci da baki goshinta yafashe da jini,.


K'ara tai mai k'arfin gaske "Wayyo Allah na, kutaimakeni zata kasheni" takuma sake damko sumarta tana zare idanu "ai tukuna banma maki komaiba wlh" tafad'a tana kaimata naushi abaki yasake fashewa da jini hak'oranta d'aya yafita.

Sake damko sumarta tai zata kaimata woni dukan cikin ikon Allah tasamu takafamata hakora ta cijeta a hanu hakan yasa taji zafi tasaketa dasauri, hakan yabata damar samun d'an k'arfi dasauri tana dafe bango tafita izuwa parlor kasancewar k'ofar ma abude take, tana ganin tafita tasake bin bayanta domin tacigaba da dukanta kwatsam saiga hamida tashigo,

Hanu HUDAYYA tadinga mikawa hamida sbd bazata iyayin magana ba ahalinda take ciki saiga momy tafito dafe da hanu gunda HUDAYYA tacijeta d'in, ganin abunda ke faruwa yatabbatarwa da hamida abunda take zargi acikin zuciyarta sbd haka bama saitayi tambaya ba.

Dagudu hamida tazo tareda fashewa da woni irin kuka cikin tashin hankali tarik'o HUDAYYA, momy nazowa tai facali da hamida tadinga marin HUDAYYA tareda kaimata naushi a fuska da ciki,.

Dukanta take ba kakkautawa kuma takoina, hamida tasake tasowa tarike momy tana fad'in "momy kibari dan Allah kibari karki kasheman y'ar uwa, wlh batada lefi acikin wonnan al'amarin" ko sauraronta batayi idonta ya rufe da tsabar mugunta.

Tini numfashin HUDAYYA yad'auke sbd tsabar mugunta, hamida ganin bazata iya hana momy cigaba da dukan HUDAYYA ba yasa dagudu tafita woje, side d'in hajiya taje bako mayafi bare d'an kwali barekuma takalma dagudun tsiya, tana zowa cikin haki da shesheka dakuma kuka muryanta ko fita bayayi sosai tace,

"Dan Allah kutaimaki HUDAYYA momy zata kasheta, kutaimaketa" cikin tashin hankali Affan dasu hisham suka fita da gudu da mami sukai side d'in.

Koda sukaje HUDAYYA na a konce wanwar tamkar gawa Abba na tsaye tareda momy sai huci take tamkar kumurcin maciji,

Cikin b'acin rai da takaici mami batasan lkcn da takaiwa saudat kyawawa marika ba har biyu alokaci d'aya, itama cikin zafin nama da masifa tace "kutmar uban can, Aysha ni zaki mara" mami tace,

"Har abonda yafi mari zanmaki yanzu sbd kin can-can ceshi wlh kedai saudat kinyi asara kin tabe, ke kinyi asara wlh, saudatu ina jiyemaki tsoron karshenki dakuma lahirarki sbd na tabbata bazasuyi kyauba, kincuci yarinyarda bataji ba bata ganiba, wlh sai Allah yasakamata, sannan kisani auren HINASH da HUDAYYA kamar anyi angama, ke kima kaddara anyisane gobe gobe insha Allah HUDAYYA zata zama mallakin HINASH matarsa ta sinnah kuma uwar y'ayan sa insha Allah, kaikuma hassan".

Saita juyo ga abba sannan tacigaba.

"Indai wonnan ce kaje wotarana saikayi kuka da idanuwonka saika nemi y'ayan ka dakanka saikuma kayi nadama alokacinda nadamar batada amfani, kabi duniya ahankali tinkan tamaka fitsarin fako, tinkan tamaka daurin huhun goro".

Tabe baki momy tai tace "atafi, atafi atafi Allah raka taki gone, dama miye amfanin haihuwar yaya mata banda bak'ar wohala da tarin dana sani, wlh y'ar kwaya d'ayar nan danakeda ji nake kamar nai sadaka da'ita".


Bawonda yasake cemata uffan mami tace dasu HINASH dasukai tsaye cikin tashin hankali tace "hisham kaje kafitar da mota muje hospital mukaita".

Cikin sauri kuwa hisham yafice inda mami da hamida suka kama HUDAYYA zasu dauketa, salatinda humaida tashigo tanayi ne yasa suka daga suna kallonta.

Daga ita har hunayya da Amira dasuka shigo a yanzu hankalinsu yamatukar tashi, hunayya da humaida fashewa sukai da woni matsanancin kuka sukazo dagudu suka rungume HUDAYYA dake kwonce somammiya, kuka sukeyi ssi kamar ransu zai fita sbd tsintsar tashin hankalinda sukaga y'ar uwarsu aciki,


Momy da abbu ficewa sukai izuwa bedroom d'in momy, mami kuwa ko kallonsu batayiba sbd basune agabanta ba,


Cikin tashin hankali mami tace "haba wonnan abun baidaceba, ba kukane yadace kuyiba kutashi muwuce izuwa hospital domin aceci rayuworta.

Mami da hamida da Amira ne suka kama HUDAYYA suka fita da'ita inda su humaida keta kuka mai ban Tausayi, bayan sunsakata a mota sannan su humaida suka shiga suka rungumata sbd sunki su zauna a gida mami kuma tashiga kujerar gaba takusa da driver,


Su Amira kuwa motar yaya Affan suka shiga su da Ammar dasu babie, kai tsaye wota special private hospital suka fice mai suna equity hospital dake kusa da mak'abarta..


Manage plss.......

#/Vote
#/Share
#/Comment
#/AUFANA for life

_*HABIBI DA'IMAN*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

_*Page 19~20*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Suna isa cikin gaugawa Affan yashiga cikin hospital d'in inda su mami kuma suka fito sukai cirko cirko fuskokinsu d'auke da tsintsar tashin hankali daka gansu kasan suna cikin tashin hankali.

Cikin gaugawa harda d'an gudu gudu Affan yadawo tareda nurse's har hud'u da woni doctor da keken d'aukan marasa lafiya,

Cikin sauri aka fito da HUDAYYA wocca har yanzu hancinta da bakinta basu daina zubda jiniba, fuskarta kuwa gaba d'aya tasauya tai zajir koina alamar tambarin duka ce.


A gaugauce aka fice da'ita emergency inda su mami kebin baya su humaida kuwa har yanzu kuka sukeyi ssi,

Saida aka shiga da'ita woni daki danaga anrubuta I.C.U sannan aka dakatarda su mami domin idan aka barsu zasu iya shiga sbd halinda suke aciki.

Tsawon awonni biyu da rabi likitoci sukai akan HUDAYYA suna kokarin ceto rayuworta daga hallaka.

Sunsaka mata oxygen sbd yataimaka mata wojen dawo da numfashinta sannan suka cigaba da nasu kokarin domin ganin numfashinta yadawo amma har yanzu shuru abun yaci tira,

Ganin hakane yasa mami takira dadyn su HINASH tafad'amasa abunda ke faruwa sannan takira HINASH shima tafad'a masa,


Aikuwa cikin gaugawa HINASH ya'iso hospital d'in, koda ya'iso kuwa gaba d'aya baya acikin hayyacinsa, ta window yalek'a yahango yanda manyan kwararrun likitoci keta fafutika domin ceto rayuwor masoyiyarsa.

Nantake zuciyarsa ta tafarfasa ransa yakara baci gangar jikinsa tafara rowa sbd tsintsar b'acin rai, idanuwonsa suka sauya kala daga farare tas izuwa ja zajir tamkar barkono.

Juyowa yai gun mami jikinsa har rawa yake sbd tsabar b'acin rai yace "mami wanene ya'aikatawa HUDAYYA haka, wanene yakeso yakasheman y'ar uwata kuma masoyiyata, wanene nace mami....!!!" yafad'a cikin kakkausar murya harsaida su humaida suka razana corridor d'in wojen yai amsa amo,

Mami tasan halin HINASH sarai, mutum ne mai zafin nama, mai zuciya, wonda baya d'aukan raini kuma bayason cutar talaka kokuma cin zarafin woni, mutum mai tsintsar tausayi, kawaici yakana da son zumunci da mutane, mutum ne kuma mai matuk'ar tausayi,

Mami tasani sarai matuk'ar HINASH yasan wonda ya aikatawa HUDAYYA haka kodama ace baitace HUDAYYA akayiwa hakaba zaiyi dik yanda zaiyi har saiya hukunta wonda a aikata wonnan lefin, saiya kwatarwa wocca aka zalinta hakkinta.

Sanin hakan yasa dasauri mami tamatso dab dashi tasha gabansa sannan tace "Please come down my son, relaxe....relaxe....relaxe HINASH, ka kwontarda hankalinka tukuna harmuga tadawo hayyacinta tukuna, banaso ka daga hankalinka ssi, insha Allah komai zaizo dasauki".

D'ago rinannun idanuwonsa yai yakalli mami yace "haba mami kidubafa kiga yanda yarinyar nan akaci zalinta, ni kawai dan Allah kibari naje nadaukar mata fansa" yai maganar kamar zaiyi kuka,

Shuru mami tai tareda sauke nannauyan numfashi batareda tace komaiba, hamida ce tashare kwallanda suka zubomata sannan takallesa tace,

"Yaya HINASH, koda kasan wonda ya aikatawa y'ar uwota wonnan aika aikan ba abunda zakayi saninma bashida amfani agareka gwandama karka sani, tin farko dama akan gudun faruwar irin wonnan matsalarne yasa HUDAYYA taki amincewa dakai sbd tasan matuk'ar ta yarda ta amince da kai amatsayin masoyi to tabbas ta tarowa kanta da y'an uwonta ne arado da bala'i,

Shiyasa taki amincewa dakai tace kuma kabarta ka amince dani kawai tinda dama guna aka turoka, amma badon bata sonkaba, a,a saidai gudun irin wonnan matsalar, saidai kuma kash dikda haka bata tsiraba, hakan baihana aka nemi a kasheta arabata da rayuworta ba".

Tak'arisa tareda fashewa da kuka, share majina tai da kwallah sannan takalli HINASH tace "Shin kasan wocca ta aikatawa HUDAYYA wonnan zalincin?" HINASH ya girgiza mata kai alamar a,a, saitai murmushi sannan tacigaba,

"Momy saudat ce mahaifiyata, kuma tayi hakan ne sbd tahuce takaici da haushin abunda kuka mata na hada aurenka da HUDAYYA ba niba".

Mamaki da al'ajabi ne suka kama HINASH "momy saudat" yasake maimaita sunan hamida tace "Eh, wlh nidai nayi asarar uw...." dasauri humaida tarufe mata baki tana zubda kwallah tace "kidaina fad'an haka hamida, dik lalacewar momy ita mahaifiya ce agareki".

Cikin kuka tace "dole ne nafadi haka yaya humaida, nikam kamar ninafi kowa, Allah yahadani da wonnan uwor wacca bata k'aunar zumunci da y'an uwana".

Mami ce tace "ya'isa haka hamida kiyi shuru kidaina kuka, adduah ce kawai yadace kiyiwa mahaifiyarki Allah ya shiryata kan tafarki madaidaici" suka amsa da ameen.

_____________________

Su mami nafita da HUDAYYA zuwa hospital momy tashirya tsab takira driver dinta yazo suka kama hanyar garin Lego's,

Tsawon awa hud'u suka dauka suna tafiya kamin da suka iso garin lego's,

Kai tsaye katafaren gidansu suka fice inda suka tadda dalla dallan motoci anyi parking nasu aharabar gidan.

Hakan ya tabbatarmasu da abba haliru yai manyan bak'i tabbas, kodai gomnoni kokuma senatoci da dai sauran irinsu da kamarsu manya dake zowa gunsa domin yamasu magani.

Ganin haka yasa tawoce cikin gida gun umman su, kwatsam umma taganta sbd saudatu bata fiye zowa gida haka kawaiba batareda tanada bukata agun mahaifinsu ba, sai kuwa wota babbar lalurar haihuwa ko biki ko mutuwa,

Bayan sun gaisa ne ta tambayi mahaifin nata sai umma tace "ai dama tatsuniyar gizo bazata woce ta kokiba, tinda naganki a wannan lokacin nasan da akwoi abunda yakawoki sbd nasan rowa baya tsami banza" b'ata fuska tai gashi kuma dama tanacikin yanayi mara dadi tace,

"Haba umma na, ni shikenan dik lokacinda nazo saikice baganinku nazoba wota buk'atata ce takawoni" murmushi umman tai tace "yo nasan halinkine shys saudatu, mahaifinku yanaciki yanada manyan bak'ine shys, kijira harya sallamesu sannan kishiga" tashi tai tashige ciki tabar umman anan parlon.

Sai kusan 10pm sannan yagama yashigo ciki, bayan yaci abinci yagama abunda yake ne umma tafad'a masa zuwan saudatu, dariya yai sannan yace,

"A,A y'ar Abban ta tasamu kenan, to kije kicemata tasameni a parlor na sai muyi magana acan" ummah tace "to" tana murmushi sannan ta tashi tafita shikuma yafice izuwa parlon nasa.


Bayan ummah tafad'a mata sannan ta tashi tafice izuwa parlon.

Fuskarta ba annuri tashiga parlon, abban ta na ganin yanayinda yashigo dashi sai yai murmushi yace "y'ar Abban ta waya tab'aminke?" zama tai kusa dashi sannan tafara gaidashi ya amsa sannan tafara magana,

"Abba aikinda kaman akan yaronnan d'an kanwar abban hamida baiyiba, sam baiyiba, a maimakon yace yanason hamida sai yace HUDAYYA yakeso y'ar mak'iyiyata wocca natsana a duniya fiye da komai, gsky Abba asake woni aikin mai nauyi".


Dariya yai sannan yagyara carbinsa mai kama da k'uli dan shima kansa tafi karfinsa sbd girmanta sannan yace "saudatu dama nagani acikin dubanda nai, hamida baitace wocca aka rubuta zai auraba, y'ar uworta ce kuma abun k'addararren abune kuma rubutacce, kawai dai nab'oyemaki ne sbd banason ki tada hankalinki" ran saudat ne yakara baci tace,

"Tinda hakane abba gsky to yakamata kayi woni abu akai, ahana yiwuwor auren, kodai akashe ita yarinyar kokuma shi yaron akashesa, kokuma asaka woni shamaki a tsakaninsu wonda zaihana yiwuwor auren" gyara zamansa yai tareda gyara zaman k'atuwor carbinsa sannan yace,

"Saudatu indaifa batun hana auren HINASH da HUDAYYA ne kisani ba abubane mai yiwuwoba, sbd anriga an kaddara itace matarsa, amma akwoi wota hanya dazamubi guda d'aya" dasauri tace,

"Woce hanyace abba, indai zata hana ahalin farida jin dadin duniya da zama acikin kwonciyar hankali to koma woce irin hanyace abi kawai" murmushi abba yai sannan yacigaba.


"Hanyar itace, zamu jira har ayi auren, bayan anyi auren ne zamufara gudanarda aiki akansu, zamu hanasu jin dadin zaman auren tayanda acikin k'ankanen lokaci shi mijin zai gaji da zama da matar, daganan zai saiketa sakinda babu gyara acikinsa, kinga daganan saimu hadasa da hamida suyi aure mukuma tirasasa masa sonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login