Showing 15001 words to 18000 words out of 24998 words

Chapter 6 - MATAR UBA COMPLET BOOK BY MRS ALKALI.doc

17 Oct 2025

893

amari na Mom ya mugun basa mamaki, matsowa yayi yariqe Mom dakyar da kokuwa ya jawota waje.

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*
Page 2?? 4??

Suna cikin kokuwanne ma aikatan asibitin suka iso kiran dady sukayi awaya yace su shigo kawai, karasowa sukayi, Mom dasukagani tana kokuwa da dady suka nufa sai ihu takeyi tanacewa abarta ta kashe shatu, kabeer nata ne ita kadai, daga kabeer har dady mamakin wannan lamarin sukeyi sai dai yanzu ba lokacin magana bane.
Dady ne yabisu , a motar su sukasaka Mom, dady yashiga tasa motar yabisu abaya.
Dr kabeer ne yakoma cikin dakin sai sauke ajiyar zuciya yakeyi toilet yanufa, boddi yagani tana zaune acikin ruwan dumin daya sata harsunyi sanyi amma bata fita acikiba sai zare ido take tayi, tausayi tabashi, nade hannun rigarsa yayi yasunkuya daukanta yayi, yanufi kofa da ita ajiyeta yayi akan kujeran gaban dressing merro zanin gadon daya baci yacire , drower yabude yadauko wani ya shumfuda, tattare kayan da yake kasan dakin yayi ya hada da bedsheets din da yacire .
Toilet yakaisu yasa a washing machine fitowa yayi drower yabude yadauko mata t-shirt dinsa zuwa yayi yasamata, yasaukamata har guiwa haka yasama shi, first aid box dinsa nagida ya dauko jikinta yataba yaji akoi zafi sosai, kallon ta yayi tasunkuyar da kanta kasa.
Ahankali kamar wanda baison aji maganarsa yace" Aish" ina yakemiki ciwo, harcikin zuciyarta taji yadda yakira sunannata, taqasan ido takallesa, ita yazubawa mayun idonsa , shiru tayi, toh ita mai zatace masa , bazata iya bude baki tace masa kasanta ne yake ciwo ba.
Jin shirun nata yasa shi matsowa kusa da ita, da sauri itama ta matsa gefe don ita tsoro ma yake bata, first aid box din yabude alluran PCM ya dauko yaja a syringe tasowa yayi ya tsaya akanta yace toh jara inmiki allurannan na zazzabi ne zakiji sauki, kin jarawa tayi, ganin bata da niyan jarawan yasashi kontar da murya yace Aish ba kyason kisamu lafiya ne a hankali cikin muryan da ta dashe tace ina so hamma ,wani irin bugawa zuciyarsa tayi yadda tafadi hamman cikin sigan shogoba, kauda kai yayi yace to barin miki a hankali bazakiji zafiba, a ah hamma nikam na warke bana son allura kabani magani kawai, ya lura tsoron alluran takeyi da gaske yace to shikenan anfasa miki konta kiyi bacci, a hankali takonta don itama baccin take buqata, bargo yadauka zai rufamata , batare da ta ankaraba ya shammaceta ya sokamata alluran dan qaramin kara ta sake , wayyo hamma zafi , kukan sakalci tafara yi , a hankali ya zauna a bakin gadon hannunsa ya daura a inda yamata alluran a hankali yake mulmulamata wajen wani ajiyan zuciya take ta sauqewa ahankali yaji numfashinta yana sauka .
Fiskar ta ya leka yaga bacci ya dauketa, kyakkyawan fiskanta ya zubawa ido, yarasa me yake ji azuciyarshi game da yarinyar nan, mafarkin da yayi jiyane yafadomasa aransa , wani kawaceccen murmushi yayi da ya tuna ba mafarkiba ne yadda numfashinta yake sauqa a hankali yake kallo, fiskar ta tayi fayau da ita , sai idanunta dasu ka kumbura, gashi ne baki a gaban goshinta ya konta yayi luf luf da shi , tunda yake baitaba zama da mace yaqaremata kallo kamar hakaba, shikanshi yarasa meyasa zuciyarsa ta damu da lamarin yarinyar.

Tashi yayi toilet yanufa wanka yayi ya tsaftace jikinsa , fitowa yayi daga toilet din dressing merro ya nufa mai yashafa ajikin sa ya sa turare, sanna yadauko pyjamas masu taushi yasaka, kan gadon ya nufa kwanciya yayi a gefenta a hankali ya rufe idonsa , Mom ne ta fado masa arai tunani yafara shin me yake damun Mom ne kam, yana son yabisu asibitin amma kuma yana tunanin barin Shatu ita kadai, tunani yayi tunda dady yana wajen Mom din kawai sai da safe inyaga yanayin jikin shatun sai yaje da wannan tunanin bacci barawo yayi awon gaba dashi .

('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page 2?? 5??

Amarya hannatu ne riqe da kunkuminta tana jijjiga sai kace wacce take filin dambe, wlh alhaji bazan yadda kahadani da sauran matanka ba tun farko kasan bazaka iya kashe kudin bane ka aure ni, dame zanji da matanka ko da gaiyar yaranka wlh bazan iyaba ehee.
Hannatu kenan gara ki kontar da hankalinki dan wlh kamar kinkoma wancan gidan ne don bazan iya wannan kashe kudin ba haba sai kace wani ATM, ni bansan ma ya akayi na aureki ba wlh, yar bariki kawai aini rufamiki asiri nayi, kingama yawon tazubardinki, nasan kudina kika aura keda kodayaiyiyar uwarki,
Alhaji cin mutuncin yawuce kaina yadawo kan mahaifiyata to wlh bazan daukaba, inbanda qaddara me zanyi da auren ka dakakecemin yar bariki aitare dakai mukayi yawon tazubar din koma wlh inakan bakata bazan koma wancan gidanba wlh, tunda bazaki koma wancan gidan ba to kije gida sai na nemiki, aida sakeni kayi wlh aikin banza kawai tsaki taja tanufi dakinta gelenta ta dauko da akwatin kayanta kofa tanufa tanata masifa.

Inna Rabi ne tafito daga dakinta tana yan waqe waqenta daganinta kasan tana cikin farinciki,tsakar gidan tagani kacha kacha, tsaki taja tace ko uban me habbi da mairamu sukeyi da basu share gidannanba har warhaka ba ohonmusu, yara sai danbanzan ganda ba aikin fari bare na baki, sallama taji , amsa sallamar tayi, Inna larai ne tashigo, tana cewa yaukeda waye haka nakejin muryan ki tundaga bakin kofar gidannan, kedai bari kawai nida habbi mana yarinya sai yawon tsiya kullum tana kan hanyan gidan su qawarta hansai na rasa uban me take daukowa agidansu gashi har takoyawa mairamu yawon gantalinnata, ba abunda suke tsinanamin ingari yawaye ,

Ko gyaran gidannan dama kinsan Shatu ne meyin komai yanzukuma batanan, Wani shewa Inna larai tayi tace niko kintunamin Shatu ne ko gawa wani dariya su kayi atare, kai qawata baki da dama kinsan ance in mace ta kwana agidansa wlh sai dai gawanta wani shekewa sukayi da dariyar mungunta Inna Rabi tace Allah sarki Shatu warhaka anzama gawa, zanso inga yadda ubanta zai inyaji saqon mutuwar yarshi, hmm kedai bari kawai, ina kudin da jiya yabaki na sadakin shatu, sunanan a daki na boyesu , yauwa dauko su kibani kasona kinsan bazanyi aikin banzaba, haba qawata kinsan ai dole kema nafiddake cewar Inna Rabi,wani murmushin mugunta inna larai tayi wanda ita kanta Inna Rabi bata lura da shiba.
Yauwa dama kinga zankoma gurin malam jafaru don yasake dubamin aikin da akayiwa baffah, kinsan shi da shegen taurin kai,gakuma matsalan habbi da bakin aljani ya aure ta kinga tunda kudi sunsamu gara muje yamin aiki mai karfen gaske ko nasamu arabata da wannan aljanin kinga saiki rakani muje tare, bakida matsala qawata kedai dauko kudin,
Dakin inna rabi ta nufa bude akwatin karfenta tayi chan kasan akwatin ta tura hannunta daurin kudin ta dauko, wanda baffah yabata ajiya jiya na auren shatu,

Fitowa yayi rataye da gelenta a kafada , mikawa inna larai kudin tayi tace gasunan qawata saminsu a jakanki ,washe baki inna larai tayi tace, BISSIMILLAHI- RAHMANIR- RAHIM, kinsan riqe mazajen kudi irin wadannan sai da BISSIMILLAH, dariya Inna Rabi tayi tace barinje dakin su habbi gara tafito tazo ta kula da gidan kafin mudawo.
Dakin ta nufa tura kofar dakin tayi , turus tayi , jin shiru ne yasa inna larai tace ya kika tsaya ko tafita yawon gantalinnata, ai gaskiya dole malam jafaru yama aiki me karfi akan habbi kinsan aljanin ne yakesata yawon gantalinnan, wani irin ihu Inna Rabi tayi tace me zangani haka habbi mairamu me kukeyi haka.
Jin haka yasa inna larai ta rugo aguje tanufo dakin su habbi, salati tayi tace munshiga uku me zangani haka.
Habbi ne konce tsirara haihuwar uwarta ita da mairamu suna lesbian, jin ihun Inna Rabi yasa su ankara neman abunda zasu rufe jikin su sukafarayi.
Inna larai ne tayi karfin halin yin magana , dama wannan shine bakin iskan da ya aureki habbi, ehhh lallaekam munga bakin iska kam babbama kuwa.
Hannatu ne tashigo gidan tana jan akwatin ta nufo inda su inna suke tayi , inna larai ne tace hannatu lafiya, inazakije da akwati haka , sai a lokacin Inna Rabi ta iya juyowa jin an ambaci hannatu, ganin hannatu haka yasa kirjinta bugawa tace lafiya, fashewa hannatu tayi da kuka tace inna alhaji ne yace sai dai inkoma wancan gidan nasa wajen matanshi shine naki,
Yace intaho gida saiya nemeni, wani irin ashar Inna Rabi tasake tace wlh bai isaba, sai nayi maganinsa.

Larai yakamata mutafi gurin malam jafaru yanzunnan don wannan al amarin akoi sa hannu aciki, kinga halin da habbi da mairamu suke ciki ko yanzu kuma ankoromin hannatu wlh bazai yiwuba.
Wani wawan ajiyan zuciya habbi da mairamu suka sake , dama suna makure jikin bango , sunzaci inna rabi zatamusu fada ne yadda sukaga tasaki ihun nan , amma jin zancenta yasasu jin sassauci azuciyar su.

Inna Rabi da aminiyar ta ne suka kama hanya machine suka tara sukayi 3in1 sabida mota bata zuwa rugar su malam jafaru, sun iso rugar bukkarsa suka nufa , suna shiga kamar kullum suka sameshi , bayani Inna Rabi tahauyimasa , bayantagamane , yadauko wasu layu guda biyu yabata yace wannan kibawa hannantu tasashi a farjinta ya kwana sai ta cireshi , inta cire tasamu gawa wanda takwana daya a makabarta sai ta sa layan acikin ramin,indai tayi yadda nace mata toh sai yadda tayi da alhaji issaqa don bai isa ya musata ba koda yake kema shaida ce tunda anmiki irin aikinnan,

Sannan maganar habbi bakin aljanin ne yasata wannan abu amma yau zanraba ta dashi, wani garin magani yamiko mata yace ki kai mata wannan , wanka zatayi na kwana 7 , sannan tayi hayaki da wannan , indai tagama to ta rabu da wannan aljanin,

Sannan ga wannan kicigaba dasawa mijinki a abincinsa kamar yadda akasaba , Inna Rabi ne tasa hannu takarba magungunan tacewa inna larai tabude jakan taciro abun sadaka abawa malam jafaru, haka Inna larai ta irgo dubu dari suka ajiyewa malam jafaru sukamasa sallama suka tafi.


('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*


Page 2?? 6??

Machine suka sake haw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a 3in1 suka kama hanyar gida sun shigo gari mai machine yanata sheka gudu da su, wata trailer tana gabansu bai ankaraba kamar kiftawar ido machine din ta kwace a hannunsa sai kasan trailer, kan kace me su Inna Rabi sunyi mummunan accident,

Dakyar akasamu trailern ta tsaya, mutane ne aka taru , dakyar akaciro su Inna Rabi,
Mai machine kam rai yayi halinsa hakama Inna larai itakam namanta yana manne ajikin titi , inna rabi da sauran numfashinta sai dai batasan inda kanta yake dan tayi doguwar suma , haka mutane suke ta jajanta wannan mummunan al amarin motar asibiti ne tazo tadauki su inna rabi da gawar qawar ta da mai machine.
Asibiti aka nufa da su , isarsu asibiti ne aka qara tabbatar da rasuwar su Inna larai da mai machine, ita kuma inna rabi anshiga da ita dakin theater dan kafafunta gaba daya suntashi a aiki gashi kanta yayi mugun buguwa .

Wadanda suka kawosune suka dauki jakan da suka samu atare dasu budewa akayi wayar inna larai ne da kudi aciki daukan wayan sukayi dake wayar irin burin dangaruwa ne ba password ajikinta, last call dinta suka duba .
Number n suka kira ringing daya aka dauka, inna , ba itabace me wayanne sukayi accident, yanzu haka suna general hospital, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, shine abunda jummai yar inna larai take nanatawa kashe wayan akayi,
Dake inna rabi bata fito da wayantaba , haka police sunzo suna jiran afito da Inna Rabi daga theater room suga halin da take ciki kafin anemi yan uwanta.

Ko minti gama aba ayiba saiga jummai yar inna larai ta iso asibitin emergency tanufa, wasu police tasamu atsaye awajen, nice wacce aka kiradazu da wayan wacce tayi accident, ok toh saidai kiyi hakuri ita Allah ya riga da yamata rasuwa sai dai akoi wacce su ke tare ita da sauran numfashinta, ko ba a fadaba jummai tasan da Inna Rabi suke tare dan haka tana kuka takira number n hannatu tana dagawa tasanar da ita halin da ake ciki ba bata lolaci ta taho asibitin.
Isowarta har anfito da Inna Rabi daga theater room har yanzu bata farfadoba , an gutsure duka kafofin ta sabida sunyi damage dayawa bazasu sake aiki ba,sanna tabugu akanta sosai, haka aka sata a room din da za acigaba da kula da ita.
Jummai takira kawunta sunzo andauki gawan Inna larai ankaita gidan ta anmata sutura anmikata gidanta nagaskiya sai dai muce Allah ya jikanta.

Kuka hannatu takeyi ganin irin halin da inna Rabi takeciki wayanta ta dauka takira bappha tasanarma halin da inna Rabi takeci, baffah ne ya nufo asibitin hanakalinsa atashe ,ganin halin da inna Rabi tashiga yasa zuciyarsa karyewa , police ne suka nemi ganin baffah bayani sukamasa game da abunda yafaru dasu Inna Rabi, mamakine yakama baffah sabida shi baisan yaushe inna Rabi tafitaba amma yanzu lafiyanta ne ake bukata koma mene ne yabiyo daga baya.

Dakin da aka kwantar da Inna Rabi baffah ya nufa hannantu yasamu tana ta rusa kuka, tausayi tabashi sosai hakika wannan babbar jarrabawa ce tasamu Inna Rabi, inta farka taga ba kafofin ta duka biyu yazataji aranta , Amma duk wani bawa baya wuce qaddaransa, hannatu ya kallah yace bari yaje masallaci yayi sallah.

Misalin qarfe 8:00am a hankali boddi take bude idanunta dasuka mata nauyi , saukesu tayi akan Dr kabeer dayake tsaye agaban dressing merro, ta cikin merron yaganta zuba mata nasa idon yayi tacikin madubin , zuciyarsa ce ta tsananta bugawa yayinda yakejin wani nitsuwa na ratsashi.
Ahankali yake takowa harya iso bakin gadon , hannu yamikamata alaman tazo gareshi, noke wa tayi taki zuwa, murmushi yayi wanda yasa zuciyar boddi bugawa, dan abune mai wuya kaga dariya ko murmushin Dr kabeer, shiyasa inyayi yakemasa kyau, don kartayi karya ne da tace ita bata taba ganin wanda yakeyiwa murmushi kyau ba kamar sa, batasan sanda ta kafesa da idoba ko kyafta idon batayi,
Jaran murya Dr kabeer yayi ganin ma batasan tasha'afa ba wajen kallon sa, rufe idanunta tayi da hannunta, dariya shima yayi , kumatunta ya lakuce yace kinga dan saurayi mai kyau kingagara dauke ido ko, sake rufe fiskanta tayi da kyau dan kunyansa takeji , ita kanta batasan ta sha'afa sosai ba a wajen kallon sa ba,
Banason gulma pha gara kibude idanunki ki kalli kyakkyawan mijinki, sanda taji zuciyarta tabuga da mugun qarfi yadda ya ambaci Kalmar mijin, a hankali ta dan bada gaf a tsakanin yatsunta data rufe idanunta dasu , satan kallon sa tayi karaf yakamata tana kallon sa, shi dariya ma tabashi, yace yajikinnaki a hankali tasauke hannayenta data rufe fuskar, tace masa ina kwana Hamma, lafiya ya jikinnaki , dasauki a hankali ya matsa kusa da ita hannunsa yadaura akan wuyanta dan yaji yanayin temperature nata, wani irin shocking yaji haka itama boddi ajiyan zuciya suka sauqe atare, jikinnata bazafi kamar dazu, hannunsa yacire a hankali yace mata ina yake ciwo shiru tayi , ganin bata da niyan magana yasa shi tashi yanufi kofa, kitchen ya je ya hado mata tea me zafi tare da ,
Shigowa dakin yayi hannunsa riqe da kofin tea , wajenta yanufa mikamata cup yayi a hankali ta sa hannu ta karba , juyawa yayi yaje yadauko first aid box din sa PCM tabs yadauko guda biyu yacira ya mika mata karba tayi tasa abakinta cup din ta dauka a hankali ta kurbi tea din, cigaba da shan tea tayi shikuma yana tsaye yana kallon ta sanda ta shanye tas sannan ta ajiye cup din ,zuwa yayi ya dau cup, din yanufi kofa da , juyowa yayi yace mata zanje asibiti Mom bata da lafiya inkina son wani abu kisauka kasa akoi chief a gidannan ko me kike so ki tambayeta, gyada masa kai tayi,har ya juya zai fita , muryanta me sanyi da nitsuwa ne ya doki dodon kunnen sa , Hamma Allah ya tsare a dawo lafiya, murmushi ne ya subucemasa wanda ma baisan yayi shiba a qasan lebe ya amsa da ameen.


('MATAR UBA ('
*Mrs Alkali*

Page 2?? 7??

Asibitin mahaukata ya nufa direct dama yayi waya da dady, aharabar asibitin ya hango dady sai sintiri yaketayi ya gagara zama ,karasawa yayi gaisawa sukayi, ya tambayi dady ya jikin Mom din , alhaji qarami jiki sai dai hamdala, amma tunjiya damukazo nagagara fahimtar me yake damun hajiya luba wasu irin surutai taketayi wanda nagagara gane kansu shiru Dr kabeer yayi,zuciyar sa na rayamasa wasu abubuwa akan Mom din,doctor n dayake duba Mom ne yafito yace wa dady ya biyo shi da sauri dady yace wa Dr kabeer su je,

Bayan sun zauna ne doctor n yadubi alhaji yace kaine mijinta ko ehhh dady yace yanuna Dr kabeer yace wannan kuma danta ne , wani file ya dauka bayan yagama dubawa yace alhaji duk wani bincike da yakamata muyiwa hajiya munmata su sai dai kuma ciwon nata bana asibiti bane dan result din test dinta ya nuna kwakwalwanta lafiyarsa kalau, inaga yakamata amaida ita gida sai ajarraba maganin gida agani,inaga hakan zaifi daga dady har Dr kabeer shiru sukayi suna tunanin wanna lamari na Mom, dady ne yayi qarfin halin cewa toh shikenan doctor ba komai mungode bari muje muganta ,

Dakin da aka kontar da Mom suka nufa harda doctor n, Mom ne daure jikin gadon sai fisge fisge takeyi kana ganinta kaga me ciwon hauka , Dr kabeer ne ya matsa kusa da gadon nata, Mom ne ta dena fisge fisge n da takeyi zuramasa ido tayi tana kallon sa, shima kallon ta yakeyi cikin tausayawa , wani dariya tasake wanda yasa dady matsowa kusa da ita, tsayawa da dariyar tayi chan sai ta saka kuka me sauti , ni ni zakayiwa kishiya wlh bazan yardaba sai na kashe yarinyanan abunda take fada kenan , daga dady har Dr kabeer kallon ta sukeyi cikin mamakin ta shin wannan wani irin ciwo ne haka ,doctor ne yace tunjiya abunda taketa fada kenan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login