Showing 3001 words to 6000 words out of 8387 words
Chapter 2 - SAKAMAKON ZUNUBI Book Complete BY ZAHRA ROYAL.txt
dan a rana sai suyi abinci ya kai kala goma koma fin haka, mutunan gidan suna ji da milki da isa suna gadara da kud'i.
A can parlon su kuwa Emily dake kallon Asma tana murmushi ta ce "hey sister kinyi dai-dai wallahi, ai ki barni da ita, saina gyara mata zama ne, shegiya kodan ta ganta da kyau?"
Wani yatsine baki Asma tayi tana amsa da cewa "har wani kyau ne da ita ni banga kyan ba gaskiya mi take dashi?"
Duk abunda suke Ayat na kallo tana sak'a wani abu a ranta, wani murmushi ta saki tana tono yadda zatai rink'a anfani da Amali tana k'unsa ma Asma bak'in ciki akan Henry, tabbas zatai anfani da ita, kodan ta jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya, zata sa a k'ara tsanar Amalin, sai kuma Asma da zata rink'a kwasar bak'in ciki.............
*💫SAKAMAKON ZUNUBI*💫
(THE RESULT OF SIN)
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Dedicated to BOSS BATURE💋
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
FREE PAGE 5-6
Tab'a tan da akai ne yasa da sauri ta tashi tana share hawayenta matsowa kusa da ita Hannah tayi tana sa hannunta ta dafa kafad'arta, cike da tausayin su ta ce "Amali lafiya dai na ganki a haka, ko dai mutanan gidan nan ne suka yi miki abunda suka saba yi ne?". Wani murmushin k'arfin hali Amali tayi tana duba agogo, da sauri ta mik'e tana cewa "karka damu Hannah bari na je wajan Emily tana jira na, kinsan lokaci take badawa idan banje akan time komi zata iya min"
"Ai nima bari mu tafi tare zanyi mata wankin kaya"
Da sauri suka fice suna jawo k'ofar d'akin nasu.
Suna shiga kai tsaye part nata suka nufa, koda suka shiga tana waya ne da wani saurayinta, samun waje k'asa sukai suka zauna suna faman jiranta tana waya tana kurb'ar shayi.
Sai da ta d'au kusan minti 40 tana waya tukun ta aje wayar a nan ma sai da ta nuna kamar ba mutane bane a gabanta, sai da ta mula ta munl-mule. Ta d'ago tana binso da hararara. Suko dama duk zaman ya gunduresu babu yadda zasuyi ne.
Wani tsaki ta saki mtswwww tana ya tsine baki, a tsawace ta ce "ubanmi zanyi muku?, kuka wani zo kuka zaunawa mutane a nan, sai wani wari kuke kun cika min d'aki da wari". Da sauri Amali tayi k'asa da kanta tana duba jikinta harda d'an shinshina jikinta koda wai zataji warin da aka ce suna yi, amma itakam bata ji wani wari ba. Tsawa ta kuma buga masu ta ce "keee Amali dubanni nan". Da sauri Amali ta d'ago tana kallon Emily, sai dai d'ago war da zatai taji saukar ruwan shayin dake hannun Emily ta watsa mata shi a fuska. Runtse idonta tayi tana jin wani rad'ad'i na ratsa mata fuska. Wasu hawaye ne suka shiga zarya akan fuskar tata. Hannah dake kusa kuwa da sauri ta zaro ido, tana sa tafin hannunta ta tushe bakinta. Kallonta Emily tayi tana cewa "kee Hannah tashi ki bar wajan nan munafaka, kin wani zauna min a nan baki san aikinki bane?". "Amma ranki ya dad'e ke ce kika ce idan na zo na rink'a tsayawa harsai kin ban umarnin farawa tukun sabo.... Katseta tayi a tsawace ta ce "dalla can rufe min bakinkin nan mai wari, munafuka kawai bagidaji zaki tashi kibar wajan nan ko sai na zamga miki mari?".
Da sauri Hannah ta mik'e har tana tuntub'i tayi wajan b'an d'aki domin yin aikinta, jikinta duk a sanyaye tana waigen Amali dake zaune kanta a k'asa.
Emily ta dawo dubanta ga Amali ta ce "kee kuma yau ina so ke kad'ai zakiyi min abincin mutum ashirin da biyar, idan kin gama ki gyara Babban parlon gidan nan, zaki iya tashi kiban waje".
Wata irin zabura da zare ido Amali tayi ta ce "ranki wannan aikin banzan iya yinsa ba ni kad'ai, ki tausaya min dan Allah". "Ke rufe min baki zaki tashi kibar wajan nan ko saina miki shegen duka, kuma nanda minti goma idan na sakko baki fara aikin dana saki ba to tabbas horon da zan miki sai ya fi wadda nayi miki yanzu, dalla tashi kiba mutane waje".
Emily ta idasa maganar tana bin Amali da wani banzan kallo na k'as-k'anci. Da sauri Amali ta tashi jikinta a sanyaye tayi waje.
Koda ta shiga k'aton kitchen d'in part d'in nasu Emily, tsabar girma da da fad'i kamar wani d'aki guda, bin kitchen d'in tayi da kallo kamar ganin babu kowa kenan duk an kori kowa ana nufin yau ita d'aya zatai duk wani aiki daya shafi abinci.
Da sauri ta fara aikin, tun tana yi da marmari, tana yi ta sauke wannan ta d'ora wancan, kanta harya fara juyawa tsabar yadda ta jigatu tasha bak'ar azaba kamin ta gama abinciccikan nan. Wani irin jiri take ji da kyar ta lallab'a ta fara gyaran k'aton parlon da kai girman wani gidan. Tana idasa kyaran ta zube, wajan a sume saboda wani irin bala'in jiri dake d'ibarta ga yinwa bata ci komai ba.
Emily dake sakkowa taci uban wanka an zubo gashin doki har gadon baya, ansha k'ananun kaya ana cin chingum ana taku d'ai-d'ai.
Jan birki tayi tana duban Amali dake yashe a k'asa, duk taga kamar ba k'alau take ba amma hakan baisa ta tausaya mata ba, da wata irin tsana ta nufi firiza tana d'akko ruwa mai sanyi tana zuwa kan Amali ta b'alle murfin ruwan ta fara kwarara mata shi a jiki. Wata irin zabura tayi har lumfashinta na shid'ewa tsabar yadda ruwan sanyin ya shigeta. Da sauri ta mik'e da kyar ta tsaya kan k'afafunta saboda kwata-kwata bata da k'arfi a jikinta. Emily tayi mata wani d'an iskan kallo tana cewa "uban mi kike a nan?". Amali ta had'e wani abu mai d'aci a mak'oshinta ta ce "ranki ya dad'e babu komai banma san na fad'i a wajan ba", "yen yen yen da anyi magana kin iya munafurci da iya zaro zance kega tsohowar munafuka, and kin gama aikin dana saki ko kuwa?"
Da sauri Amali ta ta bata amsar ta gaba d'aya, amsar data bata ce ta bata haushi ta ce ma Amali "kin taimaki kanki and zakiyi kwana uku kina min abincin nan fatan kin gane?"
Wasu hawaye ne suka cika idon Amali tana amsawa a ladabce. Tana tsaye saida tayi kusan minti biyar tukun Emily ta bata umarnin zata iya tafiya.
ISAAC AND NOAH POV
Zaune suke a wani lanbo dake cikin estate d'in nasu suna shan lemo, Julia ce take ta sintirin kawo masu kayan ciye-ciye, tana yi tana gyara suturar dake jikinta domin ta lura da wani d'an iskan kallo da suke binta dashi. Allah-Allah kawai take ta gama aikinsu ta tafi, karda suyi mata wani mugun abun. Sai dai tana gaf wucewa har tana murnar ta gama basu mata wata maganar banza ba. Kawai taji muryar Isaac yana cewa "kee Julia kike ko kowa dawo nan". Wani irin miyau Julia ta had'iye , ta juya ta nufi inda suke zaune ta duk'a k'asa, kanta a k'asa zuciyarta na wata irin bugawa tsabar tsoron daya dirar mata. Batai aune ba kawai taji Isaac ta jawota, sai ganinta tayi zaune akan cinyarsa yana k'ok'arin sa hannunsa a cikin rigarta. Da sauri ta rik'e hannunsa tana girgiza mai kai hawaye nabi mata fuska, kallonta yayi da haushi ya fisge hannun nasa yana kifa mata wani mari mai zafin daya sa ba shiri ta sakar mai hannun nasa. Bai tsaya komai ba yasa hannunsa biyu yana kamo gaban rigar Julia yajata da mugun k'arfi ji kake feeeet ta yage gida biyu. Wani irin marayan kuka ta saki tana sa hannunta domin k'are k'irjinta, sai dai Noah daya taso ya rik'e hannun nata ya jasa baya ya bank'are mata hannu ya jasa baya har sai da ya bada wani sauti k'as. Wani kuka ta sake saki. Wani kyalli Isaac ya d'akko ya d'aure mata baki dashi, sana Noah ya sureta yayi part d'insu da ita Isaac na biye dashi.
Koda suka shiga a tsakar parlon su suka ajeta suka cire kaya a gabanta su duka sai da sukayi anfani da ita, harda inda ya kusan sa zuciyarta bugawa, saboda harta duburarta saida sukayi anfani da ita, bak'in ciki ya cika mata zuciya kukan ma ta kasa sai sauke ajiyar zuciya take. Suna gamawa Noah ya tashi yana tufa mata miyau a fuska. Da sauri ta runtse idonta hawayen bak'in ciki da tsananin tsanar su na zubo mata ta gefen idon ta. Tsawar da suka buga mata ce yasa da kyar ta mik'e. Wurgo mata kayanta da suka keta su, sukayi masu fata-fata. Isaac ya ce "dallah tashi daga nan, kuma ki tabbatar kin kyara mana parlo ki tabbatar kin kyara wannan k'azantar". Binsu kawai Julia tayi da kallo har suka haye sama, da kyar ta samu da d'angyanshi da rarrafe ta d'an gyara parlon, tasa kayanta ta nufi k'ofar fita idonta jawur da kyar take tafiya k'afafuwa duk a gwale..........
*💫SAKAMAKON ZUNUBI*💫
(THE RESULT OF SIN)
ZAHRA ROYAL STAR
08130479973
Dedicated to BOSS BATURE💋
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
FREE PAGE 7-8
"Adam wato ba zaka daina shiga harkar da babu ruwanka ba ko?"
"Amma Mami kina ganin irin cin fuskar da suke ma wannan yarinyar Amali kuma ace ba wadda yayi magana"
Kallon sa Mami tayi tana k'ara cewa "to ina ruwanka a ciki?, miye matsalarka da ita?, hakan ai shine ya dace da talaka tunda dama bauta ce ta kawota dole kuma tayi hakuri tunda a k'ark'ashin wani take, kaga kuwa dole a juyata". Zai sake magana ta d'aga mai hannu ta sake magana ta ce "kaga dakata Adam daga yau duk abunda zai faru bana so kana tsuma bakinka, indai abu bai shafeka ba". Ba yadda ya iya kawai ya fice daga part d'in nasu yana jin wani iri a ransa.
Yana fita Mubeena tayi sallama tare da k'awayenta su uku suna tafe suna rufa mata baya Mami ce tayi murmushin ganinsu, Mubeena ta d'an tsaya tana kallon Mami ta ce "Mami yana ganki haka?" "Uhmm" sauke lumfashi Mami tayi tana jawo hannun Mubeena ta zaunar da ita ta ce "nida Yayanki ne mana ya cika shiga abunda babu ruwansa a ciki"
Tab'e baki Mubeena tayi tana mik'ewa ta ce "ai Mami indai Ya Adam ne ya saba da hakan dan haka ki daina ma damun kanki, amma nidai kam dama kowa ya sani bana shika shirgin family d'in Estate d'in nan tamu kowa yayi harkarsa, sai idan kaine ka shiga tawa harkar nanne fa za'a sha kallo danni kinsan Mami bana son raini a rayuwata"
"Ai Mubeena ke ni ce kika biyo duk wasu halayanki amma banda Adam sai kace an canza min shi wallahi"
Kiss kawai Mubeena ta kai mata ta juya ita da k'awayenta da suka gaida Mami ta amsa fuska a sake, suka fara haurawa sama Mubeena na tafiya tana cewa "Mami wai yaushe su Abbiey zasu dawo ne sunfa dad'e?"
"Eh kinsan dama idan suka tafi harkar kasowancinsu da harkar siyasar nan sai a hankali amma cikin satin nan zasu dawo shima naji Sir Benjamin sai tafi k'asar India cikin satin nan"
Da sauri Mubeena ta waigo inda Mami take ta ce "shin wai shi Daddyn su Henry ba zai hakura da siyasa ba wannan zab'enma sai ya ce saiya tsaya takara, da alama neman asiri zaije India dan kinsan ba wadda ya kaisu iya asiri da sihiri wallahi"
"Kinci gidanku ina ruwanki idan basa irin haka an gaya miki zasuci zab'en ne ki wuce kawai ku shiga ciki, wannan zancen ba naku bane"
Shuru Mubeena tayi tana d'an d'aga kafad'arta irin ko a jikinta d'in nan.
Ayat dake zaune akan kujerun parlon su tana kallon wani film, taji Amma ta tab'a ta tana cewa "da alama ba kallon nan kike ba, domin tun d'azo nake ta miki magana amma baki ji ba hankalinki na wani waje, mi yake damunki ne?"
"Tabbas Amma akwai matsala ina son Captain Henry amma Asma tana shigarmin hanci da k'udundine wallahi"
"To kina buk'atar fiddota kenan?"
"Tabbas Amma haka ne, ina so na shirya mata wani tugun da zata rink'a kwasar takaici"
Murmushi Amma ta saki tana k'ara dafa k'afadar Ayat ta ce "karki damu mudun ina lumfashi Asma ita da uwarta bazasu tab'a mallakar wani abu mai daraja ba, ke dai kawai ki cigaba da k'ulla masu munafurci ni kuma zanje ga boka na d'an mukyakis zai min wani aiki akansu"
Wani tsalle Ayat ta saki tana rungume Amma tana cewa "shi yasa a bana jinki Amma, Amali zan had'ama tarko domin itama na tsani yarinyar da ace nan part d'inmu take aiki da tuni nasa an koreta daga estate d'in nan, domin idan kika lura yarinyar nada wata baiwar kyau mai fisgar mutum, tare da wata baiwa duk namijin da yayi katari da ita dole sai ya kalleta ya sake kallo, wai a haka ma cikin wahala take inaga ta samu waje, ai ba'a san yadda zata koma ba"
"Kashhh wannan ma ki daina tunaninta, domin bazata bamu matsala ba, idan kuma zata bamu ai baza tai wahalar kawar da ita bama a duniyar gaba d'aya, wa take da shi?, waye gatanta a duniya?, waye ubanta? bata da kowa bare har ta d'au kanta wani abu baiwace kuma y'ar aiki kuma a haka zata cigaba da zama".
Murmushi kawai Ayat take saki tana sauraran Amma.
Tashi kawai Ayat tayi ta d'au wani k'aramin mayafi tana nufar k'ofar fita daga part d'in, da sauri Amma ta ce "ina zuwa kuma Ayat muna magana kawai zaki tashi?" "Karki damu Amma yanzu zan dawo kinsan da zafi-zafi ake bugun k'arfe ina zuwa". Tana idasa fad'ar haka tayi waje.
Fitowarta kuwa ta hangi Amali dake fitowa daga part d'in su Emily, wani murmushi cin nasara tayi tana kwalama Amali kira. Amali dake tafiya a hankali saboda aikin da Emily ta sata da kyar take tafiya, tana k'araso, ta ce "ga ni ranki ya dad'e"
Wani banzan kallo Ayat ra wurgama Amali kamin ta ce "ina kiranki kina min wata yanga, ubanwa zakiyi ma yanga a nan wajan iyeee?". Wani abu mai d'aci Amali ta had'iye a mak'oshinta cike da takaicin mutunan gidan gaba d'ayansu ta ce "kiyi hakuri bana jin dad'i ne". Tab'e baki Ayata tayi tana cewa "ki biyo ni".
Tana fad'ar haka ta juya tayi cikin part d'in. Bin bayanta Amali tayi, har suka shiga cikin parlon gidan basu tsaya parlon Amali taga sun nufi kitchen, tana zuwa taga Ayat ta d'akko wani lemo da wasu kayan ciye-ciye tasa a faranti tana mik'ama Amali ta ce "ungo nan kije part d'in Henry ki kai mai"
Zaro ido Amali tayi tana kallon Ayat ta kasa amsar farantin, wani banzan kallo ta bita dashi tan cewa "kee ni sa'arki ce zance kiyi kaza, ki tsaya kina bina da kallo, zaki amsa ki wuce kije ko kuwa sai na ci miki uwa?". Wani irin abu taji ya rik'e mata k'irji dan taji zagin da Ayat d'in tayi mata ta tsani a zagar mata iyaye, cike da jin haushin Ayat d'in ta amshi farantin bata k'ara cewa komai.
Ta juya zata tafi taji muryar Ayat na cewa "saura kuma idan kika je baki gansa ba ki juyo ki taho baki basa ba, ki tabbatar ya ganki ya amsa da kansa, kinji na gaya miki?" Wasu hawaye ne Amali taji sun tarar mata a cikin ido, da sauri kuma ta mayar dasu, bata dai ce komai ba ta fice kawai.
Tana fita daga part d'in ta tsaya cak tana duban masu tsaro kota ina a cikin estate d'in sai shawagi suke bare a k'ofar part d'in Sir Benjamin, shine yafi kowane part girma a gidan, da tsoro da komai ma, duk da yana d'an siyasa bai zauna gidan gwammanati ba, yafi son zama a cikin estate d'in, tana tunani tasan idan ba tana y'ar aikin gidan ba ita ai bata isa koda taka inda d'an president yake ba bare harta sa president d'in a idonta tasan komai sanadi ne, ji yadda ake basa tsaro shida y'ay'ansa kai duk wadda ke cikin estate d'in ma idan zai fita cikin gari haka zakaga ana mai jiniya tare da motoci nabin bayansa.
Tana tunani harta k'arasa inda part d'in Henry yake, duk haka sai da masu tsaron part d'in suka dakatar da ita suka duba abunda ta d'akko tare da dubata ko ta taho da abun cutarwa, duk sunsanta sun san ma'aikaciyar gidance, amma haka k'a'idar take, idan shiga goma zakai sai an cajeka.
Koda ta shiga k'aton parlon, wani k'amshi yayi mata d'irar mikiya daya sa sai da ta lumshi idonta tsabar yadda k'amshin turaran ke shiga ta k'ofar hancinta. Sauke ajiyar zuciya tayi, tana tsaye ta rasa inda zata nufa da kayan dake hannunta.
Gargad'in da Ayat tayi mata, ba yadda ta iya ta haura sama inda take d'anjin motsi.
Koda ta shiga yana zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya, yana aiki a computer sai wani mutum dake tsaye gefensa yana masa bayanin wasu takardu yana nuna mai. Jin shigowar mutum da sallama yasa mutunan dakatawa da yimai bananin, tunda ya kalleta sau d'aya ya maida dubansa ga computer, sai mutunan data ji ya kira da suna Osman, ne ya kalle ta yana cewa "ranka ya dad'e kaine kasa a kawo ma abinci ne?".
Sai da aka d'au minti talatin kamin yad'an motsa bakinsa kamar baya son magana ya ce "No, I don't know about him, to be honest",
Shine kawai ya ce ya tsuke bakinsa, wani haushi ne ya cika Amali jin yadda ya amsa, to ita ina ruwanta dashi cewa akai ta kawo mai kawai.
Osman ya ce "zaki iya ajewa ki tafi"
Da sauri Henry ya dakatar da ita, shuru sukai Amali ta cigaba da tsayuwa su kuma suka cigaba da aikinsu. Amali tun tana tsayuwa da marmari harta gaji ta rasa ta inda zata fara magana ma. Har sai da Osman ya gama mai