Showing 9001 words to 10127 words out of 10127 words
Chapter 4 - Sulthan Aneem Complete Hausa Novel By Mujaheeda Matar Malam.txt
ba k'aramin k'ara k'ona ransa yayi ba shi yarinyarnan zata yarfa cikin mutane, hakan yasa yashiga gabansu fuska D'aure yace "ke bakida kunya ko ina Magana shine zaki shareni,"?
Itama tokar Tasha tace"Auncle banaso kadaina"
"Keee ni" d'aga Hannu yayi yawanketa da Mari saida tasunkuya
"Haba bawan Allah meta maka zaka daketa,"?
"Nadaketa kozaka rama mata ne,"
"To ai Dan kana d'an uwanta bashi zaibaka damar cin zarafin taba,"
"Eh lalle ba laifinka bane yaro laifintane domin itace da bak'in kwashe kwashe harzaki kwasamuna mara kunya Agida Kuma yayi k'ok'arin fad'amin Magana wllah idan baka bar gidannanba yanzu zansa Amaka walak'aci mafi Muni domin bakasan ni waye ba zansa Amun maganinka Kuma kada kasake dawowa Kai ko Kiranta kasake saina saka Anyimin maganinka Wllh,"
Sai Alokacin tad'ago fuska jawuri idanuwanta na zubda hawaye cikin dakiya tace"Eyeee sannu Ubana nace sannu Uba dahar zaka saka order Akaina Kuma wllh Auncle nagayamaka kadaina koramun samarina ni karabu dani nayi Rayuwata mana Nishi kad'ainakeso kuma Babu Wanda zai rabamu dashi domin dukanmu Munason junanmu shi zan Aura Kuma....." Wani gigitaccen Mari dataji Wanda yafi nada zafi yasayin Shuru tareda kallonsa idanuwansa sun kad'a sunyi mugun ja tamkar barkono itakanta saida ta tsorata ganin yanayinsa hanyar shiga part d'insu yanuna mata da Hannu ganin yanayinsa yasa tawuce dagudu tana kuka, Maida kallonsa yayi ga guy Wanda Shima yasha jinin jikinsa domin tsantsan kishi da Soyayyar da yahango cikin idan Sulthan sune suka k'ara kashemasa jiki bugu da k'ari ganin yanayinsa,
"Kafice daga gidannan yanzu Kuma idan kabari nasake ganinka tareda k'anwata wallahi sainayi mugun sab'amaka kamanni idan bakasan wayeniba ka tanbaya waye *SULTHAN ANEEM*," yanakaiwa Nan yajuya yabarshi tsaye cikin mamakin irin kishinda yahanga cikin idansa kan Amrash
Wani security yazo yace "mlm kashiga motarka kawuce Kuma y'allab'ai yace kada yasake ganin k'eyarka gidannan Maza kafita kamun mufitar dakai da k'arfin tsiya,"
Baice musu komai ba yashiga motarsa cikin takaici yabar gidan,
Tana shiga parlour tafad'a kan Mommy tasaka kuka
"Wai meke faruwane ina bak'on naki yatafi ne,"
"To umma yakoreshi waini menaka Auncle ne kullum nayi bak'o saiya koreshi Ada kunce saboda nayi k'aramane saboda gyaramin tarbirya yasa yake Hakan to yanzu fa ai na mallake hankalin kaina Mom kisaka baki kan Lamarin yabarni nahuta nasamu Wanda nakeso ni wllh nagaji," k'arasa maganar tayi cikin kuka
"Ya isa Hakan Amma ai yayankine dole kimasa biyayya tayu yaron bashida kirki shiyasa yakoreshi,"
Mik'ewa tayi zaune tareda zubawa Mommy Ido tace"wai Mommy ko yanzu Hakan zakice kullum shine keda gaskiya nibani ba to shikenan tunda Hakan kukeso sainayi tazama ba Wanda zaizo inda nake," tana gama maganar tabar parlour cikin fushi
Murmushi Kawai Mom tareda godewa Allah kan hak'anta Yana dafda cinma ruma dama tuni tana zargin Sulthan Yana d'auke da son Amrash Amma sai yanzu tak'ara tabbatar da hakan,
Yana shiga d'akinsa yawatsarda kayan hannunsa yashiga toilet ko kayan jikinsa baicireba yasakarwa kansa ruwa, shidai yasan basonta yakeba Amma Kuma baison ganinta tareda ko wanne Namiji Watak'il saboda tana k'anwarka ne shiyasa , da wannan dalilin yafake..
Bikin saidad'a matsowa yake inda Ammy tadawoda ita gurinta sai gyaranta take tako ina itadai da Ido kawai takebinsu domin batasan meke faruwa Kuma tayi fushi da Mommy gashi tanajin kunyar Ammy balantana tatanbayeta Kuma su yashina ma talura basusan komai ba dole tazubawa ikon Allah ido,
Zaune take parlourn duk tagaji da zaman Gidan Kuma tana kallosu Yashina suka fita Amma ita dole tazauna duk k'ad'aici yadameta Yanzu idan kowa kanta yake tarasa dalilin hakan, wayarta tad'auka tana d'an dannawa tunkan ya iso k'amshin turarensa ya iso parlourn da sallamarsa cikin K'asaita yashigo parlourn bata d'agoba Kuma bata Ansaba kamar batasan da halittar mutum Hakan tayi Kawai tacigaba da danna wayarta
Shikuwa Ido yazuba mata tunsanda yakore saurayinta baisake ganinta ba sai yanzu saiyaga kamar ba itaba tayi kyau sosai tacanza
D'aure fuska yayi yace "ke waike bakijin Magana ko? Baki iya Ansa Sallama da gaida manya ba,"?
Tamkar Yana Magana da icce domin ko d'ago kanta batayi ba balantana yasaka ran Samun Ansa,
Wayarta tasoma ringing tad'aga cikin shagwab'a tace "Haba my dear wllh Gidan kamar kurkuku nikaina bansan meke faruwa ba nayi missing d'inka sosai Dan Allah kazo naganka,"
Wani irin bak'inci yaji Yana tasomasa tindaga cikin mak'oshinsa harzuwa bakinsa kanta yanufa cikin masifa yace"Badai ke bakida kunya ba ko? Bazaki daina mu'amala da wannan d'an iskan ba zanyi maganin kine,
Ganin yayo kanta yasa takashe wayar tamik'e tareda fasa ihu ta tuma kan kujeran itana Kiran "Wayyo Ammy zai kasheni wayyo,"
Tsaye yayi cak yana kallonta ganin yarda take wani dira kamar k'aramar yarinya komai najikinta sai motsawa yake bakin gaskiyarta Kuma sai birgima take tana kuka tamkar yadaketa d'in,
Tanajin Alamun saukowar Ammy daga benan tafad'i k'asa takuwa sake fashewa da wani sabon kuka harda matso hawaye,
Da Sauri Ammy tazo gareta tareda kamata tace"Kai maikamata ne? Wai Bana hanaka sakawa duka yarana Hannu ba indai bawani babban dalilin ba,"
"Wllh Ammy nidai nabar garin Nan nagaji kullum cinzalina yake yanzuma dashigowarsa komai bance dashiba shine yamareni"
"Mari Kuma Sulthan yaushe zaka daina dukantane wai, nagaya maka banaso idan kasake d'aga Hannu kadokarmin y'a wallahi ranka zaiyi mummunan b'aci, Kinga muje ciki Yi hak'uri barshi dani yake zancen,"
Tsaye kawai yake sororo yana binta da kallon mamaki,
Saida sukayi nisa Asaman step d'in tad'an juyo tareda Masa gwalo gamida nunashi tanuna kanta Alamar zaka sanine takashe Masa Ido d'aya tasake Masa gwalo tashige ciki da Sauri,
Murmushi Kawai yasaki tareda girgiza kansa,
Dukansu sun hallara parlourn domin komai yakankama na Auran
Papi ne yayi gyaran murya yace"Dalilin taraku duka Anan shine saboda Kusani mungama yanke hukunci Kuma munshirya komai Sannan ba shawaran ko neman Amincewar wani muke buk'ataba kawai zamu Fad'a mukune Domin kunada hakke Kuma Kuma kushirya tareda yin naku shagali Nanda sati d'aya Za'a d'aura Auren *SULTHAN ANEEM* DA *AMRASH*"
Tamkar Saukar Aradu haka taji Maganar shikanshi saida yagirgiza Domin maganar tazomasa A bazata
Amrash kuwa jitake kamar cikin mafalki take runtse idanuwata tayi tasake bud'ewa bafa mafalki bane zahirine tabbas ita papi yace za'a Auran wannan mugun mik'ewa tayi tsaye cikin tashin hankali gamida ficewar hayyaci Tace..........................
```KASH GASHI DAI LABARIN YAKORO SAIDAI KUMA LOKACI YAMANA HALIN NASA DOMIN KUWA LOKACIN KARANTA FREE PAGE YAK'ARE YANZU ZAMU SHIGA LOKACIN KARANTA NA K'UD'IN NE 300 KAWAI ZAKI BIYA DOMIN K'ARASA TAFIYAR DAKE, AMMA FA KUSANI AKWAI RIGIMA GAMIDA CHAKWAKIYYA AKWAI TASHIN HANKALI GABA HUNMMM TSAYAWA FAD'A B'ATA LOKACI DAMA CIKA GURI KAWAI MUHAD'U A NEXT PAGE KUMA TAREDA 300 KAWAI DOMIN SANIN YAYA ZATA KAYA.......
SABUWAR SHEKARANDA ZAMU SHIGA JIBI INA ROK'ON ALLAH YASA MUSHIGA A SA'A ALLAH YASA TAZO DA SAUYI ALLAH KABAMU ZAMAN LAFIYA DA ARZKI MAI AMFANI., AMEEN....... TAKU HARKO YAUSHE MAISON GANIN FARINCIKINKU ✍️ MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER'S HAUSA NOVEL'S 📚📖📚 AND DESIGN GRAPHIC'S 🎉```
_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_
Whatsapp Number 07064904617 or 07031012948