Showing 9001 words to 12000 words out of 45461 words

Chapter 4 - NISFUL HAYAT Book Complete by Mimi queen.txt

19 Jun 2024

7727

suke gabansu sunkai shida.


Sosai ake ganin sun dace, wani babbane cikin sojijin ya tashi yafara magana cikin harshen turanshi, yafadin irin murnan da suke taya Aadil tareda fadin dacewan da sukayi.bayan yagama ya zauna.




Wani sojan ya mike, tareda cewa za'ayi game tsakanin Ango da Amarya, amarya zata zabi bindiga daya cikin bindigogin dake gabansu Ango ze setawa amaryarsa bindiga zuwaga kwalban dake sama rataye idan ta harba daidai kenan tana cikin zuciyan mijinta in kuma ta kuskure kenan bata ciki.


Ido aka zuba musu, a hankali ya dagota ido ya zuba mata, idanta ya cika da kwalla zatai kuka kai ta girgiza mishi, lumshe ido yayi a sanyaye yace. "Please choose..." ganin ya tsureta da firgitattun idanunshi yasata rintse ido a hankali tayi pointing bindiga na uku, iho taji ansa, bude ido tayi a sanyaye yace."Wow perfect Grade one.."


A sanyaye ya mata alama data dauka, hannunta na rawa takai hannu ta dauka ihu tasa cikin tsoro tana kokarin sakin bindigan da sauri ya tamke hannunshi da nata da bindigan,


Tsakiyan gurin suka sauko ta kasa, bottle din nacan nesa sosai dasu, sosai hannunta ke rawa sama ya dago hannun nasu yakai kanshi setin kunninta a sanyaye ya rada mata. "Ki natsu..."
Ijiyan zuciya ta saki ta lumshe ido, tana tunanin tayama zataci bayan tasan bata zuciyan Aadil.


Seda yaji numfashinta ya daidaita hannunta yadena rawa sannan yaseta bindigan setin kwalban yakai hannunta setin inda ake harbawa da kyar ta daura hannun yakai hannunshi saman nata cikin kunninta yake counting "5,4,3,2,1 shuttt" tareda harbawa,


Tafiya bullet din yafara, tsakiyan kwalban yafasa kwalban ya tarwatse ihu gurin akasa yayinda Aadil yayi murmushi, ido ta bishi dashi ta kasa koda motsi ganin yanda murmushi kemai kyau.


Nan akace saura second game sun yi winning na farko, kaman tayi kuka.


Wata baturiyan macen sojace ta kariso gabansu ta amsa bindigan hannun Aadil ta ijiye a kan table, blindfold din dake hannunta takai da nufin kullewa Aysher ido da sauri Aysher tajuya tana kallon Aadil.


A sanyaye yace. "Ki bari mana zasu gwada sanda kike minne indai har kika iya ganoni a cikin sojoji ishirin...."


A hankali ta saki kuka mara sauri, naga ta kaina" blindfold din ta rufe mata idon dashi, ya zamana bata ganin komai se duhu,


Ko minti goma ba'ayiba taji matar taja hannunta binta tayi, harta kaita wani guri me dan tudu, a kunni ta rada mata. "Oya select ur husband...."


Kaman Aysha zatasa kuka a hankali tadan matsa inda taji alamun mutum, a sanyaye tafara matsawa gaba harta wuce mutane uku duk tana lura dukda bata tab'a ko mutum daya a cikiba, harzata wuce mutum na shida kamshin turaren Aadil da yake addabanta da kamshi koda yaushe yashiga kofofin hancinta.


Tunani tafara kodai bashi bane, kuka tasaki a hankali kobashi bane gara na fadi tunda nasan baya cikin raina.


Kirjin mutumin ta fada tareda sakin kuka, jinta tayi ta hade da kamshin Aadil har wani shidewa takeyi sobada kuka,


Ihu gurin ya dauka tareda tafi, hannayenshi ya daura a bayanta ya rungumeta tareda kwance blindfold din a sanyaye yace. "It's okey kinyi winning....."


Ido ta lumshe takara kamkameshi hakanan taji wani nutsuwa yazo mata, rabata yayi da jikinshi jin ana ana fadin saura third game wanda shine last.


Kuka ta kara saki, itadai ta gaji kaman Aadil yasani a hankali yace. "Wannan ni kadai zanyi, zaunawa kawai zaki ki kalla. " Kama mata hannu yayi yakaita sit dinsu ya zaunar sannan yakoma kasa.


Ido ta zuba tana kallon abinda akeyi, butun butumi aka kawo mace cikin shigen Amarya aka kaita can nesa da Aadil dan tsakaninsu ze kai 10km aka ijiye,


Wani sojane yashiga tsakiyan Aadil da Amaryan ya saita bindiga zuwaga amaryan,


Counting wani soja dake gefe yafara. "5,4,3,2,1 shutttt....."


Harba bindigan wannan sojan yayi da yayi setin amaryan nan, da gudu Aadil yatafi domin inya riga bullet din zuwa yatare amaryarshi yana santa kenan sosai kuma ze iya bada rayuwanshi akanta,


Duk da sosai bullet din ya wuceshi.


Befi saura kamu daya bullet din ya sauka jikin amaryan nanba Aadil ya ture amaryar gefe bullet din yafada cikinshi, zubewa yayi a gurin,


Da sauri Aysher ta mike ganin yanda ya fadi ta dauka bullet din gaskene, se taga ya tashi gurin akasa ihu, dagowa yayi yana kallon Aysher yana mata murmushin data rasa gane nameye,


Karisowa yayi kusa da ita seda yajata sannan ta zauna se kallonshi takeyi, nan ma'aikatan hotel suka fara raba abubuwanci yayinda komai daya faru se dauka akeyi a gidan t.v, ko wani soja zaune yake shida matanshi wanda basuda mata kuma budurwa ko su kadai kaf gurin ba ba'ka'ken fata daga indiyawa, larabawa se turawa inma da en Nigeria to fararen fatane en hutu.


Aadil ko a jikinshi bude ciki yayi yanata cin abinci itako ba abinda ta iyaci domin bata wani saba sosai dacin abincin US ba, bakin ciki kaman ya kasheta danta gaji sosai,


Cake aka gunguru zuwa gabansu wuta na tashi a jikin cake din kalan kayan sojoji, duban Aysha yayi tareda kashe mata ido da sauri ta sunkuyar da kai kasa, se ji tayi yariko hannunta kallanshi tayi taga yana nuna mata cake alaman suje su yanka da ido, ba musu ta mike, hannunshi ya daura saman nata ya dauki knife din, counting aka fara, 1,2,3.


Yanka cake din yayi wanda yana yankawa wasu flowers suka zubo akansu wuta yafara tashi kaman an kunna bob aka saki harbin bindigogi da seda Aysha ta tsorata, sakin hannun nata yayi ya dauki cake din yakai bakinta, a hankali ta amsa, ido ya zuba mata yana jiran ta bashi ganin taki yasashi sa duka hannayenshi biyu ya cagwalgwalo saman cake din tareda kaiwa fuskanta ya shafa mata.


Baki ta fara ta'bewa tareda fashewa da kuka, takai mai duka a kirji tana kuka lakuto cake din itama tayi ta shafamai a fuska tana dukanshi a kirji, dariya mutanen gurin suke cikeda sha'awa, janyota yayi jikinshi a hankali tareda daura hannunshi a bayanta cikin sigan lallashi yana murmushi, tafi aka saki nan aka shiga musu hotuna.


Bayan an gama shugaba ninsu suka yi jawabai akaba su Aadil kyautuka tareda kara mishi babban matsayi daga captain zuwa commandos (wato soja na musamman).


Sunsha kyautuka, en jaridane sukazo suka ishesu da tambayoyi kawai se Aysha tasa kuka domin ta gaji sosai, hakan yasa ya rungumota jikinshi ya kauce musu ta baya da baya,


Se around 11 sannan taron ya watse.




Ido ta zuba mishi a cikin mota, kaman yasan abinda take tunani yace. "Mamaki kike yanda duk mukai winning game dinnan bayan bamu son juna ko....? "
Da sauri ta daga kai, yadanyi murmushi. "Nima nayi mamaki kuma a ka'idan game din gaskiya yake nunawa nayi mamaki da akanmu ya sa'ba amma kinsan ba abinda ubangiji baya canzawa ko, nidama gwanine a iya harbi da iya tsere da gudu dama nasan ta bangarena inada hope Allah ze bani nasara kecedai nai mamaki da kika ganeni cikin 20 soldiers....."


Jingina tayi da jikin kujeran tareda lumshe ido danta gaji sosai, a haka suka karisa gida.




Commens if you like 🤷‍♀️.


Mimi queen ✍️.
2022-06-21, 7:05 a.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*


13&14.




Muryan Aabid ta jiyo yana waya harda dariya abun ya bata mamaki, jin da Aadil yake wayan yasa bata waniyi mamakiba domin baka cikajin dariyan Aabid ba idan ba yana tareda dan uwanshi bane, mami ko Abie.


"Congratulation Dil 4 d extra position, nayi murna sosai....."


daidai lokacin ya shiga dinning room din inda zarah take, murtuke fuska yayi a dan dake yace. "Am coming Dil...."


Dif ya katse wayan, ledan dayake hannunshi ya mik'a mata tareda fadin. "Yanzu kudinki da suke hannuna saura I think 4million ne nayi using 1million na siya miki phone."!


Baki ta saki tana kallonshi wayan 1million, tab lallai wannan ai albazzaran cine, seda yadan daka mata tsawa sannan a firgice ta amsa wayan shikuma ya kara gaba.


Ledan ta bude ta ciro wayan ta bude iPhone 13 ne, wayan ta hadu irin wacce Aadil ya siyawa Aysherne, ba abinda babu kuma full take kuma harda power bank hakan yasa da sauri ta saka sim dinta tayi downloading WhatsApp ta seta,


Kiran Aysher tayi suka hau yin waya, cikin kewan juna.




****
Magana Aysher tayiwa me dafa musu abinci akan ta dena ta dinga bari ita zata dinga dafawa dukda bata wani iya girka abincin kasarba dan ba abincin Nigeria a gidan amma ta kudirta indai sukaje seta taho dasu, yaune suka fara girki itada kuku zata fara koya mata kala kalan abincin kasar harse ta iya.






Bayan sun gama ta haye sama ta shirya dan yau ta gaji sosai dan sunyi abincina kusan kala biyar,




Muryan Aadil ta jiyo a kasa da alama bashi kadai bane , tabe bski tayi dan wani bala'in haushinshi takeji kwalliyanta taci gaba dayi, kafin taji yaturo kofa ya shigo a bakin kofan ya tsaya tareda dakewa . "ki sauko kasa munyi baki...."


Yana fadin haka ya fice, hararan kofan tayi sama da kasa kafin a hankali taja brezia hijab black ta zura tareda saukowa,


Wani mutum wanda yafi kama da balarabe tagani zaune kan three siter, se wata kyakykyawar mace da alama balarabiya ce da kyakykywan yarinyarsu.


Cikin fara'a da sakin fuskah Aysher ta sauko, nan taba masu aikin gidan umarni suka hau jera musu abinci....


Zama tayi a can gefe tana wasa da yatsun hannunta, Aadil yace yace. "Ga khaleesat matar abokin aikina captain Ashraf, zata dinga kawo miki ziyara domin anan take itama kaman ke batasan kowaba sedai batajin hausa domin er kasar madina ce sedai tanaso ta iya dafatan zaki koya mata...."


Duk cikin turanci yake wannan maganan, Murmushi tayi tareda d'aga kai, hakan yasashi duban khaleesat yace. "To ki murna yanzu kinyi kawa se a dena rigiman za'a koma gida. "
Murmushi tayi, yarinyarsu me suna Ummusuleim bazata wuce 4 years ba hakan yasa Aysher ta dingi wasa da yarinyar domin tana kewan Amira yayinda su kuma suketa firansu, basu jimaba suka tafi bayan Aysher sunyi exchanging contact da khaleesat.






*****
Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya ba wani jituwa tsakanin Aabid da Zarah dan ko kadan be sakin mata fuska,
Haka bangaren su Aysher da Aadil tanayin girki dai yaci domin izuwa yanzu ba abinda bata iya girkawaba na kasar kuma tasaba da cin abincin kasar.


*******
Yanzu kam zarah na sakewa tafito taita ganin gida kuma tana sakewa ta shiga duk inda taga dama domin yanzu Aabid becika kwana a gidanba saboda aikinshi dukda be fada mataba ji tayi yana waya .




Hakanan taji tanaso taga yanda dakin aabid yake, a hankali ta murd'a handle din takoci sa'a a bude kofan take, mutuwan tsaye tayi data bude dakin domin bata taba ganin hadaddan daki irin wannanba se taga duk kayan alatun da suke gidan ba komai bane akan wannan dakin.


Kwas kwas takun takalmin Aabid ta jiyo yana hawowa yana waya seda gabanta ya fadi dan batai tsammanin yananan ba,


A rude tafara waige waige tana kuka sosai jikinta na rawa tana neman inda zata 'buya, wani babban had'add'en flower verse silver tagani gefen kofar ga hadaddun flowers a ciki da sauri taje bayan verse din ta tsugunna ta la'be ta daga kanta ta flowers tana kallon hanyen stairs din.


Muryan mace taji cikin kuka tana fadi da alama wayan a free take.


. "U got married after professing to me that u loved me......."


Cikin daga murya yace."what do you mean jamima.....did I covenant marry to you....."




Daidai lokacin ya ida hawowa yana sanye cikin wani Fendi white t-shirt daya kama jikinshi sosai, hanun rigan are dark brown, yana sanye da dogon brown pant yasanya white sneaker na Fendi, wrist dinshi daure da agogo na rolex gashin kanshi a kwance yana kara bubbude manyan idanunshi yana kallon door din, wani hadadden kamshi na tashi ajikinshi, ja yayi yatsaya bakin kofan batareda ya shigaba,


. "Ni zaka yaudara Aabid ni zakawa haka, seda ka gama lalata min rayuwa yanzu kuma zakace haka wallahi baka isaba....."


Wani irin shu'umin Murmushi ya saki. "Do what ever u can do jamima....tayama zakice ni zan iya aurenki bayan nasan kin gama lalata rayuwarki nd secondly we're not desame religion."!


"ba addinin da yace dan ina christian bazan iya auren musulmiba, amma zanyi as u said zaka gani....."


Dogon tsaki yaja ya katse wayan. "Worthless....", murda handle yayi ya shige.


Fitowa tayi daga bayan verse din tana kuka sosai ta tsaya bakin kofan tana kallon kofa jikinta bata inda baya rawa.


Dama Aabid mazinacine, innalillah wa'innan ilaihir raji'un kuka sosai take tanajin tsananshi na shiga zuciyarta..


Jin alamun ze fito yasa da gudu ta fada dakinta tana kuka.




Comments if yhu lyk 🤷‍♀️.


Oum Humaira ce ✍️.
2022-06-21, 7:05 a.m. - ~Mimi 🥰🥰: *NISFUL HAYAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
*Sadeeyah Isah (Mimi Queen)*


*Marubuciyar:*
_Son zuciya_
_Rayuwa sai da ke_
_Barista Shulaifat_
_Labarina_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


_Sadaukarwa ga My twin sis (Dr. Meenart Umar Usman) Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance._

Ba wanda baya kuskure ko wani dan adam ajizi ne idan har nayi kuskure a cikin rubutuna karda ka zageni kamin addu'a Allah ganar dani.
Duk wacce ta zageni nidai nayafe mata🤷




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*




15&16.




Yau kwanan zarah biyu kwance batada lafiya, amma Aabid ganin baya ganinta kwana biyu ko ya nemeta, itama a nata bangaren bata bu'katan ganinshi domin ba abinda ta tsani gani sama da Aabid yanzu kuka kam tayishi batasan adadin shiba.




******
US.


Hadarine ya had'u sosai gari yayi mugun duhu duk da bawani dare bane sosai amma garin yayi mugun duhu, a gurguje Aadil ya shiga mota ya nufi gida.


Yanayin parking yafito sanye yake cikin kayan ruwa na coast guard domin basu jima da fitowa daga ruwaba, iska aka fara had'e da 'kura, 'kuran na dakan hancinshi yafara tari domin bayasan 'kura ko kadan, da sauri ya nufi cikin gidan yanaci gaba da tarin.




Aysher na raku'be a falo dan yanda taga garin yakoma yasata fara jin tsoro domin kam ita kadaice a cikin gidan in Aadil yafita dan masu aiki bangaren su daban.




Shigowa yayi yanaci gaba da tarin sama sama, ido ta bishi dashi harya shigo tsakiyan falon yaji numfashinshi yasoma sar'kewa sakamakon asmanshi batasan 'kura shafa aljihunshi yayi da sauri ko zeji enheler dinshi wayam yaji hakan yasa ya tuna ya barshi a mota,


Juyawa yayi da sauri ze fita daidai lokacin aka tsugage da ruwa, zabura Aysher tayi ta 'kara ra'bewa jikin kujera,


Kai ya rike tareda karisawa kan kujeran ya zauna domin indai ruwan sama ya dakeshi tofa seyayi ciwo yana shiga ruwa sosai amma indai na sama ya ta'bashi shine da matsala.




Tarbe kanshi yayi yanajin numfashinshi na sarqewa domin yasan indai be shaqi inhela ba numfashin shi ze iya daukewa.




Ido Aysher ta bishi dashi dan bata fahimci halin da yake cikiba, sama sama taji nishinshi da sauri ta 'kura mishi ido se lokacin ta lura da zufan dake zuba a jikinshi.


A rude ta karisa daurewa tayi tace. "Ya Aadil....."
Shiru taji, seda ta kirashi sau biyar taji ba amsa hakan yasa da karfi ta dagoshi, tsorata tayi ganin yanda yake numfashi da kyar yasa hannu ya rufe hancinshi da bakinshi yana janyo numfashi da kyar.


Rudewa tayi a rude take fadin. "Meke damunka ya Aadil......"


Waje kawai yake nuna mata da d'ayan hannun yanaso yace, ta dauko mishi inhela a motanshi.


Kawai fadi yake. "Car.... Car......"
Wajen da yake nuna mata tabi da ido, a rude ta mike tanufi hanyan fita dan taga meye a motan daidai lokacin aka saki tsawa, da gudu ta dawo ta 'kan'kameshi, numfashin shi taji yafara daukewa idanunshi sun fara rufewa rasa yazatayi tayi kawai se dibawa ta fado mata.


Riko kanshi tayi da sauri ta had'a bakinta da nashi tafara hura mishi iska, in banda kuka ba abinda takeyi.
Sama sama ya bude idanshi dukda baya cikin hayyacinshi yafahimci abinda takeyi dan numfashi bakinta shiya hana nashi daukewa.


Ba tareda dama tafahimci abinda take aikatawa ba ita burin daya ta temakeshi, haka ta dingi hura mishi iskah, idanshi nadan lumlumshewa yana kallonta, a hankali yaji numfashinshi na daidaituwa.


Tari ya danyi hakan yasa tayi saurin raba bakinta da nashi ta d'ago.


Ido ta bishi dashi ganin numfashin shi yadawo amma ba normal yake fitarwaba.


Lumshe ido yayi a hankali ya daura kanshi kan cinyanta, ba 'bata lokaci bacci ya d'aukeshi, Aysher jin shiru yasa tadan leka fuskarshi, idanshi a rufe innocent face dinshi me kyau tayi haske yana sauke ijiyan zuciya a hankali daga ganin yanda yake baccin ta fahimci yanajin dadin baccin hakan yasa ta daura kanta hannun kujeran ta lumshe ido itama ba 'bata lokaci bacci yayi gaba da ita.






Cikin dare Zarah ta farka yunwa takeji sosai, tashi tayi da kyar ta kunna bob fuskarta takara karama saboda raman da tayi idanunta sun cicciko sun fito waje, amma tayi haske sosai.
Da kyar ta iya fita falon, Aabid dake zaune ya baje system yana aiki kallo daya ya mata ya dauke kai
Itako kota kanshi bata biba, ta nufi dinning flasks ta bud'e ta tsiyayi ruwan zafi tasaka Lipton tea tasa shiga tafara sha, lumshe ido tayi har wani kuka cikinta keyi domin tunda tafara ciwo bata samu taci abinciba, shanyewa tayi domin kadan ta zuba jin har lokacin cikinta na mata kukan yunwa yasa ta shige kitchen fridge ta bude, ta dauko Pepe chicken ta bude sosai taci tasha ruwa ta ijiye sauran kan table ta fito,
Amai taji yana zuwan mata, kanta farga taji ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login