Showing 111001 words to 114000 words out of 227252 words
Chapter 38 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
rayuwa ita kuwa wani irin BALA'I ya fado mata rayuwa a daidai wannan lokacin bata san mai za ta ce ba bata san ya za ce da wannan ƙaddarar ba ta sani rayuwarta ta kare komai nata ya sauya zuwa tashin hankali da bala'i ta sani tayi bankwana da farin ciki tayi bankwana da kwanciyar hankali ta rabu da iyayenta har abada ga shi yanzu ita kuma ƙaddararta ta jona ta da wannan bala'in wanda ba ta san ya zata kwatantashi ba.
Gyada kai ta shiga yi idanuwanta na fiddo da wasu hawaye masu tsananin zafi da kokarin yayyaga mata fatar fuska duban sa take yi da wani irin yanayi mai girman gaske tana ayyanawa a ranta wannan mutumin mai rai daya a jikinsa shine ya addabi miliyoyin mutane ya hana su kwanciyar hankali bata san ya zata kwatatta wannan lamarin ba.
"Karki yi tunanin sake wata rayuwa kawai ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid".
Wani zafi taji kirjinta nayi kafun wani abu mai girman gaske ya zo ya tokare mata kirji dago idanunta tayi tana duban Baaba BG wanda tun da aka kawo su duniyar BALA'In nan ta lura dashi a durkushe har izuwa wannan lokaci tsoho ne sosai wanda wahala da bala'i suka dakusar dashi wajan kara zama tsoho na karfi da yaji fuskarsa kawai ta kalla ta gane bala'in da yake ciki idanuwansa a kasa ko motsin kirki ba yayi wani irin tausayin sa taji ya tsirgar mata da sauri ta kau da kai kafun ta dubi Malik wanda har lokacin yana rankwafe a gabanta.
Kallon sosai tayi masa lokaci guda ta ji zuciyarta ta kekeshe da duk wani tashin hankali da take ji komai taji tsaya mata na tsoro kallon sosai da sosai tayi masa kafun ta kau da kai tana jan tsaki can kasar makoshinta.
Wani wawan Mari da sanya ta sakin fitsari da ganin taurari taji ya gilma a kuncin ta lokaci guda ta baje a kasa gami da kurma uban ihu.
Mikewa yayi zuciyarsa na wani irin tukuki da zafi bindigi ya ciru daga kugunsa karama lokaci guda ya saita ta sosai idanuwansa na bayyanar da wani tashin hankali mai girman gaske runtse idanu tayi tana jiran saukar alburushin domin ta gama sadakarwa ba za ta sake ko da minti daya a duniya nan ba.
Tun tana jin tafiyar numfashinta da sauri-sauri gabanta na wani bugu mai girman gaske a hankali ta fara kiran sunan Allah kafun taja numfashi mai girma ta buɗe idanuwanta tsaye ta hangeshi har yanzu bindigar na saitinta amma bai harba ba.
Mamaki ya cika mata zuciya sosai ganin yanayin da yake ciki gabadaya idanuwansa na kanta ga bindiga a hannunsa amma ya kasa harbawa kuri tayi masa da idanu tana mai sakin ajiyar zuciya sunayen Allah a laɓɓanta ba ta san ma mai za tayi ba komai take jin yana zama al'ajabi da mamaki a gareta ba ta ankara ba kawai taga ya cafko hannunta ya mikar da ita cikin wani irin yanayi na mazantaka ya shiga jan ta ciki hanzari kamar zai kifata da kasa ita kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah lokaci guda fargaba da razana da tsoro suka shiga tsalle -tsalle a zuciyarta har lokacin da suka iso wajan da Baaba BG yake yashe idanuwa ya dago a cikin galabaitaccen yanayi ya dubeta ita ma shi take duba cikin wani yanayi na tsanani sadakarwa sosai suke kallon juna cikin yanayi na tashin hankali mai girman gaske tana kallon shi yana kallonta har zuwa lokacin da taji Malik ya fizge ta zuwa cikin tamfol din sa yayi cilli da ita a ciki ba komai a cikin tamfol sai hargitse wanda sam ba su dakyan gani bindigogi da alburusai can gefe kuma wata yakunaniyar shimfiɗa ce mai dauke komaitsai da sauri ta dago kai gabanta na cigaba da bugawa tana dubansa shima ina ya ke duba kafun ya ajje kallonsa ga kan shimfiɗarsa.
"Zaki kasance dani kamar yarda na sanar dake ki shirya zama dani ki saka a ranki kina tare da Malik Bin Yazid".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una".
Abin da zuciyarta ta shiga fadi kenan cikin kyarma da tsoro lokaci guda ta shiga matse jikinta waje daya duban sutturar jikinta take yi yarda aka kekketa ta sosai ana hango wasu sashi na jikinta ya bayyana a fili runtse idanu tayi wasu hawaye su ka balle mata.
Ta sani shikenan rayuwarta ta kare shikenan duniyarta ta gama k'awa da tashin hankali wnda ba ta san ran fita daga cikin sa
A Hankali taji ya fara takowaa kusa da ita gabanta yana tsananta faduwa jikinta sai kyarma yake yi lokaci guda numfashin ta ya fara sama da kasa lokaci guda ta saki razananniyar kara cikin firgici da tashin hankali komai taji ya tsaya mata cak! duniyar tana juya mata bata san abin da ke faruwa ba idanuwanta dai na kansa har lokacin da iso gareta ya rankwafa yana mai kamo hannayenta duk biyu yana mikar da ita a hankali idanuwanta suka shiga rufewa kafun taji jikinta na narkewa lokaci guda tana watsewa a kasa....
😘😘 *_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA UKU
Huce mai zafi yake fesarwa kamar wani kumurci. tashi yayi tsaye daga kan kujerar dayake zaune yana bugun Table din dake gabansa idanuwansa sunyi jajir kamar wanda aka yiwa sirace da barkano.
"Alhaji Abdulwahaab na fada maka ka fice mani daga cikin Office in kuma ba haka zan yi maka abin da baka taba zato ba".
Ya fadi yana mai kara turbuɗe fuskarsa kamar zai cinye shi danye.
Murmushi Alhaji Abdulwahaab yake saki mai cike da bakin ciki da takaici wai yau har shine Dr.Erena zai dubi tsabar idanuwansa yana fada masa magana son ransa kamar wani wanda ya zo maula wajansa numfashi ya ja kafun ya dubi Dr.Erena sosai yana mai gyaɗa kai wani irin tukuki yake ji zuciyarsa nayi ba abin da yafi bata masa rai kamar yarda Dr.Erena ya zage yana keta masa rashin mutum bai taba tsammanin haka ba bai taba kawo wa kansa haka ba bai yi tunanin duk rashin mutuncin Dr.Erena zai iya yi masa.
"Dr.Erena ni...".
"I Say get out now i don wanna see you in my Office".
Dr.Erena ya fadi a zafafe yana kara so wa wajansa har yana tunkuɗashi.
"Ka je kayi abin duk da zakayi kudi ne na cinye in akwai wanda ya isa ya kwatar maka ka turo shi tunda naga abin naka hauka ne har nawa ne kudin naka da zaka zo kana yi mani ihu kamar wani kare a cikin Compay".
Mamaki ne ya sake kume Alhaji Abdulwahaab jin zuciyarsa yake yi kamar zata faso kirji tayo waje gabadaya saboda tsabar tsananin bakin ciki dake nukurkusar sa hannunsa ya kai ya saukar da na Dr.Erena dake kafadarsa fuskarsa da wani murmushi kafin ya fara taka kafafuwansa a hankali har ya isa bakin kofar hannunsa saman Handle din ya juyo ya dubi Dr.Erena cikin wani irin kallon wanda shi kansa Dr.Erena sai da yaji wani iri a zuciyarsa amma bai bari hakan yayi tasiri a fuskarsa ba sai ma wata uwar harara da yake cilla masa.
A daidai lokacin da ya tura kofar domin fita ita kuma Areefa ta sanyo kai cikin Office din saura ka dan suyi gware dashi amma tayi saurin kauce wa don a tunanin ta Dr.Erena ne.
"Yaa Allah".
Ta furta tana duban Alhaji Abdulwahaab da wani irin yanayi mai kama da tuhuma kafin ta dubi Dr.Erena da yake faman cika yana batsewa kamar zai tarwatse ganin Areefa ya sanya shi ware idanuwansa sosai mamaki na kokarin ka kashe shi ganin Areefa yau a cikin Office din sa How Comes yace ya manta rabon da ya ganta ko sashin sa ta zo amma yau ita ce a bangaren sa abin mamaki lokaci guda jikin sa ya shiga rawa ya fara takowa izuwa gareta a daidai lokacin ta juya ta dubi Alhaji Abdulwahaab yanayin da ta ganshi a aciki ya tabbatar mata akwai abin dake faruwa bata karasa tsinkewa da lamarin ba sai da ta ga Alhaji Abdulwahaab ya kashe mata idanu daya hakan ya kara jefata cikin wani irin yanayi mai girman gaske na mamaki.
"Nace ka fice mani daga Office, ko sai na saka an fitar da kai a rashin mutunci ne?".
Dr.Erena ya sake fadi a zafafe ganin irin kallon da Areefa ke yi masa juyawa yayi ya dube ta yana faman sakin Murmushi kamar tsohon da aka bashi kyautar budurwa.
"Areefa ban yi zato ba...".
Hannu ta daga masa alamun bata so fuskarta a tsuke.
"Haba mana Dr.Erena me haka kayi wanda sam bai dace ba abokin ka ne fa wanda bai kamata ace irin haka ya faru a tsakaninku ba".
Ta fadi tana mai dubansa kafin ta dubi Alhaji Abdulwahaab wanda a daidai lokacin yake ficewa daga Cikin Office idanu ta kashe masa kafin ta juyo da kallon ta zuwa wajan Dr.Erena fuskarta da alamun damuwa.
"Ban san haka wasu in suka gani ai sai su yi muku dariya".
Wani gundumeman tsaki ya ja gami da kau da kansa.
"Bar ni kawai Areefa raina min hankali zai yi ni kuma a rayuwa ta abin da bana so kenan komin kusanci na da kai in har kace zakayi mani akuyanci to wallahi ba zan kyale ka".
Sosai ta gano in da lamarin ya dosa amma cikin basarwa da kin ba wa zancen muhimmanci ta dube shi.
"Good and Fine ina son mutum haka mai ra'ayi irin naka na rashin son daukar raini".
Ai ji yayi kamar ta cilla shi a gidan aljanna haka ya shiga yashe baki kamar wani bugun shaho da sauri ya dube ta cikin rawar jiki yana yi mata nuna da ta zo ta zauna a hankali ta fara taka kafafuwanta idanuwanta na kansa kallon sa take yi da wani irin kiyayya mai girman gaske dubansa take yi da wani irin haushi da takaici zuciyarta take ji tana wani irin kartawa kamar zata faso kirjinta ta fito saboda tsabar tsanar sa da take ji a duk wani sashi na zuciyarta.
'Ni yake so wai da aure'
Ta ji wani sashi na zuciyarta na fadin haka ji tayi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu don bakin ciki amma ina bata so ta bata shirinta ba ta so ta bata salon da Hajiya Layla ta karanta mata tayi amfani dashi bata so ta samu wata ɓaraka daga wannan KUDIRIN nata da take kokarin cin masa.
Isa tayi cikin takunta wanda yake kara fizgar Dr.Erena yana jefashi cikin wani irin hali na matsanancin son ta sosai ya firgice cikin lokaci kalilan sai kai kawo yake yi yama rasa abin da ya dace yayi sai kai kawo yake yi yana dube-dube sannan ya juya ya janyo kujera kamar zai zauna sai kuma ya fasa ya shiga sakar mata murmushi ita kan ta sai da taji wani iri na daban da yanayin da yake nuna wa amma zuciyarta wani irin kunci take jefa ta a duk lokacin da ta kalle shi ji take yi kamar ta tashi ta shake shi ya mutu kowa ya huta sai dai wani sashi yana gargadin ta da wannan kudirin nata na kisa wanda sam bai dace ace tana sanyo shi a lissafin ta ba.
"ka zauna mana gabadaya duk ka wani rikice sai kace wanda aka kama da satar butar masallaci".
Sai a lokacin ya tsaya da kai kawon da yake yi ya janyo daya daga cikin kujerun dake girke a gaban Table din ya zauna yana fuskantar ta.
"Nayi mamaki matuka da ganin ki Areefa na dauka har yanzu ba a yafe mani gingimeman laifin da nayo ba".
"wa yace kayi laifi?".
Ta tare shi tana mai sakin wani yake da BAI KAI ZUCI BA.
"Uhmm dole nace haka mana Areefa yaushe rabon da ki tsaya ki saurare ni yaushe rabon da ko alfarmar kallon arzuki na samu a gareki muna Company daya amma har ki shigo ki gama abin da zaki yi ba ki dubana da kallon arzuki in ma nayi miki magana sai ki nemi dizga ni don kawai na nuna ina son ki ban san laifin da nayi har ya kai haka ba ban san me nayi miki da kika tsanani har haka".
Runtse idanu tayi jin ya ambaci kalmar 'ina son ki' wani takaici da makakin bakin ciki taji sun taho sun tsaya mata a zuciya wani abu mai nauyin gaske taji ya zo saitin kirjinta ya zauna numfashin ta taji yana sama da kasa kamar zai katse.
Sosai taji ba za ta iya cigaba da zama cikin Office din nan ba sosai take ba za iya kara ko da minti guda bane tare da Dr.Erena komai zai iya faruwa sosai zuciyarta ke tururi sosai take ji kwanyarta na juya wa.
A hankali ta mike kan kafafuwan ta tana jin yarda kanta ke sarawa da wata irin tsana ta Dr.Erena bata zaton zata iya juri zuwa gareshi bata zaton zuciyarta za ta barta tayi abin da ya dace sosai take jin ina ma ace ta kashe shi shine kawai hanya guda da take zaton samun nasararta a akansa amma ina hakan sam bai dace ba bai dace ace zuwa wannan lokacin ace ta kashe shi ba ba ita kadai ke bukatar Dr.Erena ba ba ita kadai bane a filin duniyar nan take son daukar fansa akan sa mutane da yawa wanda ba ta san a dadin su ba suna BURI da KUDIRI mai girman gaske akansa sai dai rashin WATA DAMA da ba su samu ba amma gata ita ta samu amma tana kokarin ruguza komai.
"Areefa ya dai ba dai tafiya zakiyi ba?".
Muryar Dr.Erena ta doki kunniwanta ba ta san ma ta fara tafiya ba sai da taji amonsa sanna ta dawo hayyacinta har ta kai bakin kofa da sauri ta juya ta dube shi fuskarta da wani irin murmushi wanda ita a karan kanta ba ta san ma tayi ba sam! ba tare da tace dashi komai ba ta buɗe kofar ta fita.
Fitar ta ke da wuya Dr.Erena ya mike cikin hanzari fuskarsa na kara haɗewa waje guda wayarsa ya janyo ya shiga danna kira yana mai kaita saitin kunnuwansa sai faman numfashi yake ja.
"Bobby".
Ya fadi da wata irin murya kafun ya dora da fadin.
"Ina son ganin ku anjima a gida".
Daga nan bai sake cewa komai ba ya sauke wayar yana mai sakin wani murmushi na mugunta yana murza gashin gemunsa.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ya furta yana mai hade hannayensa waje guda yana lankwasawa.
******
"Meye amfanin haka da kayi Alhaji Abdulwahaab baka tsoron Dr.Erena ya turo a kashe ka don karka kawo masa tsaiko cikin lamarin sa kai fa da kanka ka fadi mani ko waye ya zo masa da rainin hankali ko yana kokarin tona masa asiri kashe shi yake yi amma kai kayi gangancin tunkaransa akan wani dalilin?".
Areefa ta fadi tana mai duban Alhaji Abdulwahaab da takaicin duniya ya ishe shi sai faman huci yake yi kamar wanda zai hadiyi zuciya ya mutu.
Mikewa yayi tsaye ya shiga kai kawo sai faman kai wa iska naushi yake yi kamar da ita cikin wanda suka bata masa rai juyawa yayi ya dubi Areefa ita ma idanuwanta na kansa hannun ta rike da Glass Cup a hankali take kurbar lemon da yake ciki.
"Areefa ya kamata ki san wani abu wannan abin da ki ga nayi masa so nake yi na kara tunatar dashi cewar ina nan fa ban matan abin da ke tsakaninmu ba don na lura sam ya mance wani abu da ya shiga tsakanina dashi ba wai nayi bane don neman hakki akan sa a,a nasan ma ba samu zan yi ba nayi hakan ne don ya sani ina nan kuma komai daren dadewa sai ya bani hakki ba zai ci bulus ba".
"Wannan ba magana bace Alhaji Abdulwahaab".
Areefa ta katse shi da fadin haka kafun ta dora da cewa.
"Ko Shakka bana yi yanzu haka nasan yana nan ya na kokarin bin hanyar da zai kawar da kai a filin duniyar nan kar kayi tunanin ABOTA da ta ratsa tsakaninku zatayi wani tasiri a gareshi na rantse maka da Allah yarda da lura da Dr.Erena duk da dai kafi ni saninsa amma ina da zaton ko kaninsa ne zai kawo masa wasa zai iyayi masa komai Dr.Erena MUGUN ABOKI ne a gareka domin kuwa ba ya bukatar ace ka samu cigaba yarda yake yi maka yana nuni da cewa da ma can abin ka yake so".
Runtse idanu yayi yana kai komo zuciyarsa yake ji tana zafi bai taba zaton Dr.Erena zai masa haka ba bai taba zaton ko da a mafarki ne haka zata faru ba.
"Shikenan Areefa amma don Allah ya kamata ace zuwa yanzu kin san komai game dashi lokaci tafiya yake yi a ko wani lokaci zai iya gano ke wacece tsoron abin da zai je ya dawo bana so ayi BIYU BABU ba wan ba kanin karatun dan kama".
Wani murmushi ta saki kafun ta juya idanuwanta.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ta fadi cikin wani irin yanayi tana mikewa kan kafafuwanta da wani irin ƙarfi da take ji yana taso mata tun daga zuciya da rushi ajiya Cup din dake hannunta tayi kafin ta dauki jakarta dake kan Table din da suke zaune a hankali ta fara taku kamar ba zata ce dashi komai ba juyawa tayi a hankali har zuwa lokacin da murmushi a fuskarta da BAI KAI ZUCI BA amma yana tattare da abubuwa masu yawa.
"Yanzu za a fara Alhaji Abdulwahaab ka shirya zaman kallo".
Ta fadi tana mai kashe masa idanu kafin ta juya ta cigaba da tafiyarta cikin sassarfa.
Hannu ya daga ya jinjina mata yana hango gaskiya a batunta yana hango kudiri da buri da ta dauka akan Dre.Erena abin da yake so kenan dama kuma tsaf ya shirya duk yanayi sai ya ga yarda wasan nan zai kare kamar yarda ta fada amma kuma dole ya ja baya da Dr.Erena kamar yarda Areefa ta fadi ya san dole ya farauce shi a ko wani yanayi zai iya yi masa bazata.
*******
Kai kawo kawai take yi cikin tsakiyar falon gabadaya kanta ya gama kullewa tunaninta take ji ya cak! ya daina tafiya yarda ya kamata numfashi take ja a hankali tana dukan hannunta da dayan idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin damuwa matsananciya da tarin KALUBALE.
Sosai take ji