Showing 3001 words to 6000 words out of 57539 words
Chapter 2 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
ya je ya zauna don nan ne wajen shi, Kallon shi ta yi tace "se yanzu Kuka dawo?" "Ehh", kawai yace mata, muryar lecturer su ka ji yana cewa, submit your Assignment, Safwan ne ya ta shi ya nufi wajen kamal don jakar shi yana hannun shi, Safnah kuwa se yanzu ta tuna ma da Assignment d'in don ya dad'e, muryar mallam d'in ta ji yana cewa Duk wanda be yi ba ya fita kuma shine CA d'in ku, Safnah sosai hankalin ta ya tashi, wa su ne da basu yi ba su ma su ka fara ba shi hakuri Yace su fita kawai, hakan yasa Safnah mi'kewa don fita dai-dai lokacin Safwan ya dawo da takardar Assignment d'in shi yace "Safna ina zaki?" "Nabar Assignment d'ina ne a gida gashi ance a fita", mi'ka mata takardar hannun shi ya yi ta 'kar'ba sannan yace "ki saka suna a wannan ki bada, kije ki zauna kawai",
"amma Safw..... "shiiiii!" yatsan shi ya d'aura a baki alamar ta yi mai shiru, juyawa ta yi ta zauna shi kuma Safwan ya fita waje, Safnah ta shi ta yi ta kai nata.
Safwan ko da ya fita sauran sunyi mamakin ganin har da shi be yi ba yace musu ya bar shi a gida ne, Bayan ya gama 'kar'ba ne ya fito waje, wajen wad'an da ba su yi ba, sosai shi kan shi ya yi mamakin ganin Safwan be yi ba,
"Muhammad!!" Safwan da yasan Lecturer ne kawai ke kiran shi da haka ya ta so tare da zuwa wajen shi, yace "muhammad ya akayi ba ka yi ba", sunkuyar da kai ya yi yana murmushi sannan yace "Sir na bar shi a gida ne", "ok to gobe kazo min da shi" "to thank sir" yace sannan ya nufi aji, su na had'a ido da Safnah murmushi ya sakar nata ita ma murmushin ta mayar mai sannan ya 'karaso ya zauna, tace "ya akayi ka shigo kuma" dariya yayi yace mata, "ke dai kawai kibar maganar ta wuce amma gobe ki zo da nakin se ki bani" "to" ,tace don ganin lecturer ya dawo karatu ya yi musu sannan ya fita yace anjima ze dawo ya basu takardun su.
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_5&6
Ko da ya fita lokacin 'karfe 9:30 surutu wasu ke yi, wasu kuma su ka fita don su sha iska Kasancewar se 10:00 za su 'kara yin karatu, Safwan ne shima ya tashi ya fita ba tare da yayi wa Safnah magana ba ita ma ba ta ce mai komai ba.
Su kamal da ke bayan su ne su ke fira gaba d'aya sun cika mata kunne, Kamal ne ta jiyo ya na cewa
"ai gobe akwai shan shagali a club kun san birthday d'in Malika 'yar chairman d'in anguwar mu ga kuma na Zulaihat, ai akwai Holewa"
Salman ne yace
"ai kuwa fa, amma kasan Boss fa da'kyar ya je kuma kasan idan be je ba abun ba ya dad'i"
"haka ne amma kabar min komai kawai zan san yanda zanyi na jawo mana shi"
shewa su ka yi na jin dad'i gaba ɗayan su.
Safnah ce ta mi'ke ta fito waje can ta hango Safwan zaune a kasan wata bishiya akan kujerar da ke wajen, 'karasawa ta yi ta zauna be kalle ta ba hakan yasa tace
"Safwan!"
Juyowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba,
"Safwan me yake damun ka naga kamar yau ran ka a bace ya ke"
murmushi ya yi yace
"ba komai Safnah kawai anty ne ta 'bata min rai kome ma ya wuce"
"to shikenan, Safwan ka ci gaba da hakuri wata rana se labari"
"to" kawai yace.
"Safwan yaushe ne birthday Malika?"
Kallon ta ya yi cikin zare idanu da mamaki yace
"waye ya fad'a miki za'ayi",
"ba ka amsa min ba",
"gobe ne", yace,
"kuma zaka je ba?"
"Ehh mana",
Hararar wasa ta yi mai tace "har kana 'kara fad'in Ehh ko!, to shikenan se ka dawo",
"to ke ma za kije kenan? Kuma yadda kike mummunan nan, ƙila ki samo saurayi"
Kallon shi ta yi ba tare da tace komai ba kawai ta tsira mishi idanun ko kyaftawa wa bata yi, Safwan ku wa Jin ta yi shiru ya juyo ya ga tana kallon shi, d'an matsawa baya ya yi yace
"Wayyo!, nace ki daina min irin kallon nan ko", kawar da kai ta yi tace
"zaka je, ko ka fasa"
"zan je mana, 'yar kauye kawai ke yaushe za ki waye ne ke baza ki je ba amma ki hana mutum zuwa kuma"
murmushin jin dad'i ta yi don tasan halin Safwan sarai Idan ya yi mata maganar nan to ba ze je ba ne. amma duk da haka se ta ƙara cewa
"Tambayar 'karshe zan maka zaka je ko baza kaje ba",
"se na je"
yace mata ya na murmushi, mi'kewa ta yi ta nufi aji a zuwan ta yi fushi, kuma ba hakan ba ne don tana da tabbacin ba ze je d'in ba, amma idan yaga ta nuna ta yi fushi Ko da kuwa an zugashi baze jeba.
Shi ko koda ta tafi mi'kewa ya yi yana murmushi don wataran ma dariya Safnah ta ke ba shi.
Ajin ya shiga don lokacin ma har an fara karatu magana ya yi wa Safnah ta yi banza da shi, kawai se ya kyale ta, don karatu ma ake yi.
Yau se 'karfe 2:00 su ka ta shi makarantar yau ita kad'ai ta fito don maryam bata zo ba.
Har ta fita bakin gate Safwan da sauri ya shiga motar shi kamal ne ya biyo shi da sauri don wataran Safwan na d'aukan shi Safwan har ya kunna mota kamal ya zo, Hannu Safwan ya saka a aljihun shi ya ciro dubu uku ya mi'kama kamal yace "ga shi ka hau mota yau zan d'auki Besty ne" murmushi kamal ya yi don shi gaba ta kai shi ma don ya samu kud'i.
Da sauri Safwan ya ja mota ya fito don yasan halin ta zata iya hawa napep ta ta fi koda ya fito kuwa ya hangota har ta tsayar da Napep d'in, da sauri ya fito ya bawa mai Napep d'in hakuri ya tafi sanna yace
"wuce muje",
bata yi musu ba ta wuce motar ta bud'e ta shiga, shima shiga ya yi ya fara tafiya bata yi mai magana ba shima haka, ganin shirun yayi yawa ne yace "Haba anty na ki yafe ni kinsan zan iya jure komai amma banda fushin ki a gare ni haba 'yar kanwata anty na kuma" dariya ta yi don yayi ne dama don yasa ka ta dariya, bayan ta gama dariyar ne tace
"Safwan kace se ka je ko?, To indai kaje bani ba kai"
dariya ya yi sannan yace
"to ba shikenan ba waye ze damu, ke za ki damu don ni ko ajiki na ma, don ko school ne ban zo ba kin dinga kira kina cewa yau baka zo ba, tsabar baza ki iya jure rashi na ba, shiyasa ma baki son naje, nasan duk kishi ne kar na je na samo santaleliyar budurwa ko?",
Safnah sakin baki ta yi ta na kallon shi se yanzu tace "Allah ya kyauta me zan yi da kai, ba ka san saurayi na ba ne, idan ka gan shi se ka raina kan ka don ya fi ka had'uwa ma sosai, amma jika fa mummuna da kai",
Dariya Safwan ya yi yace, "lallai yarinya, kin ga had'ad'ad'en saurayi, ke ba ki ga 'yan mata na ba, ko school guda nawa ne su ke so na, ga anguwan mu ma, ke ko a club ma......"
Shiru ya yi ganin ta juyo ta na kallon shi jin ya ambaci club,
"ko a club ma miye?" Murmushi ya yi yace
"ba komai dai"
"shikenan zaka ga saurayina duk lokacin da ku ka had'u ko!, se ka rai na kan ka" Safnah tace
Dai-dai lokacin kuma Yayi perking kasancewar an iso gidan su Safnah, dai-dai lokacin mai napep d'in su Khalil shi ma ya kawo su gida Khalil na sauka da gudu ya 'karasa wajen Safwan, Safwan bud'e motar ya yi khalil ne ya 'karaso yace
"yaya Safwan ina wuni",
"lafiya lau khalil" dai-dai nan su Halima ma su ka 'karaso su ma gaishe shi su ka yi, yace "Sannun ku ya karatu?", "Alhamdulillah" su ka ce atare.
Motar shi ya koma ya ciro mu su sweet da coculate, da biscuit da yawa a leda yace
"gashi ku je ku ci"
'kar'ba su kayi su ka shiga gida don lokacin ma Safnah har ta shige gidan, koda su ka shiga Safnah na Sallah, Gaishe da anty su ka yi, su ka cire uniform suma su ka yo alwala khalil ne ya mi'kawa Momin su ledar da Safwan ya ba su, yace
"momii kin ga yaya safwan ya bamu",
"to an gode, Safwan kamar baya nan kwana biyu ko zuwa ma baya yi",
"ai yace mu gaishe ki" cewar Afrah
"to ina amsawa".
Sallah su ka yi sannan su ka zubo abinci su ka fara ci.
Waye Safwan waye kuma Safnah.
Ku biyo ni don jin labarin su.
Taku har kullum
Khadeejerh Ishaq ce
Comment and share pls
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*7&8
SAFNAH
Mallam Suleiman ya kasance haifaffen garin kano ne yana da matar shi guda d'aya Fatima, yaran shi biyu, Al-amin se shamsiyya, su biyu Allah ya ba su.
Neman kud'i da karatu ne su ka kawo Al-amin Zaria inda ya ke karantar Doctor, ita kuma Shamsiya, wani mai suna Abdullahi ya fito neman auren ta amma shi d'an katsina ne kuma d'an dangi ne don shine ma auta a d'akin su yana da yayyi maza da mata, Salihu shine Babba ad'akin su akwai zafi sosai don duk ana shakkar shi 'ya'yan 'yan uwa da sauran su, se Aminu, Bashir, sagiru, Mudassir, se kuma mustapha wanda shine autan maza daga shi sai Abdullahi, se kuma matan Aisha saudatu, maryam, ban da wad'an da su ka ra su, su goma ne cif a ɗakin su,.
Kasancewar Abdullahi shine auta shiyasa akafi ji da shi ga shi kuma shine ya yi karatu mai zurfi har ya samu aikin gwannati hakan yasa nan da nan kuma ya fara juya kud'in shi nan da nan yayi kud'i sosai duk da Familyn dama da kud'in su don ko wa yana fa sana'ar shi.
Ba'a d'auki lokaci ba aka saka ranar Shamsiya da Abdullahi, ba dad'e wa aka yi bikin, aka kaita katsina ba laifi dangin Abdullahi su na son ta amma akwai wad'an da ba su son ta, da ma ba lallai ba ne ace ka samu soyayyar Kowa ba a duniya.
Wasa-wasa kud'i sosai Abdullahi ya yi wanda duk Dangin sun huta don su na cikin daula sosai shamsiya ma tana hutawa sosai, ta haifi 'yarta mace suna kiran ta da Safnah.
Bayan shekara Biyar da auren Shamsiyya, Al-amin ma yayi aure ya auri matar shi khadija 'yar zaria ce ita acan ma yake zaune, don yanzu ya gama karatun shi yana neman aiki ne kuma yana sana'ar shi, a shekarar ne kuma Mallam suleiman Allah ya yi mai rasuwa inda ya bar matar shi ita kad'ai agidan Al-amin yayi da Innar ta su ta dawo gidan shi da zama amma tace tafi son gidan da take, hakan yasa shi ya siyar da gidan na su dayake yana da girma sosai, ya gina mata d'an madai-daici don waccan ya mata girma ya zuba mata kayan abincin da komai na bu'kata daya ke maman na su akwai son yara shiyasa yaran anguwan su ma suna son ta don idan kazo gidan cike zaka gani da 'yan mata suna ta hira su mata girki da komai ko yaranta se haka, shiyasa ma hankalin Al-amin ya kwanta.
Yanzu yarinyar Shamsiya ta girma sosai don tana da shekara Takwas ta na karatun ta don ta gama primary ma yanzu don ta shiga makaranta da wuri.
A shekarar ne kuma Su ka shirya zuwa Aikin Hajji na biyu don sun ta'ba zuwa da shamsiya da Abdullahi sun so su tafi da safnah amma ƴan uwa su ka ce abarta kawai, su ka shirya su biyu su ka tafi, sun yi aikin hajji lafiya sun gama a hanyar dawowa su ka yi hatsarin jirgin sama, yayin da jirgin ta 'kone 'kurmus ko gawan su ba'a fitar ba.
Sosai aka ji mutuwar su Al-amin ma ya ji mutuwar 'yar uwan shi, Inna ma ta ji mutuwar 'yar ta ta, sosai, haka su ka yi hakuri su ka yi musu addu'a.
Safnah ko da ta ji mutuwar iyayen nata sosai abun ya ta'ba ta don se da ta dinga ciwo kamar ma bazata rayu ba, daga nan ta dangana ta na yiwa iyayen ta addu'a, ta na zaune acikin familyn Baban ta, don Al-amin yayi su ba shi ita sun'ki hakan yasa ya hakura.
Bayan shekara biyu lokacin Safnah ta na da shekara goma kuma ta shiga jss 1 wata rana ta shirya zuwa ziyara gidan Kawun ta Al-amin, daga sati biyu se da ta yi wata biyu sosai ta ji dad'in zaman gidan don matar kawun nata akwai mutunci ga yaran ta su na da tarbiya sosai don su na girmama ta kamar antyn su wanda su ke ciki d'aya.
Da dangin mahaifin ta su kaji shiru ne su kayi tattaki don zuwa d'aukan ta amma fir!, Safnah ta'ki se ma kuka da ta dinga yi musu ta fi son nan hakan yasa aka ce ta 'kara wata d'aya.
Bayan wata d'ayan ma dai Safnah ta'ki komawa, ga gidan su gidan kud'i komai akwai gata take samu sosai amma kuma tace ita nan ya fi mata hakan yasa su 'kyaleta se dai ta kai musu ziyara shima se ta shekara bata je ba, ta dawo gidan kawun ta dai da zama yayin da take son su su ke son ta don tun da ta zo khadija ta huta don tun bata iya aikin ba kasancewar bata saba ba har ta kware don ko ta hana ta ma se tayi.
Makaranta me tsada kawun nata ya saka ta anan ne kuma su ka had'u da Safwan...
SAFWAN
Alhaji muhammad (Naira) ya kasance shahararren mai kud'i ne shi d'an asalin zaria ne a Samaru yana zaune da matar shi guda d'aya Maimuna, da yaron su guda d'aya da Allah ya ba su, wanda su ke so fiye da yanda su ke son ran su ma, MUHAMMAD wanda su ke kiran shi (SAFWAN) sunan baban shi yaci kasancewar baban nashi shima sunan Baban shi yaci, sosai Safwan ke samun gata awajen Mahaifan nashi.
Safwan yana da shekara goma sha takwas yanzu, yana Jss3 yanzu don be shiga makaranta da wuri ba, lesson akeyi mai a gida kafin ya shiga.
Alokacin ne kuma Dad shi iyayen shi su ka matsa mai sai ya 'kara aure don baze zauna da matar da bata haihuwa ba tun da tayi ɗaya kusan shekara goma sha takwas, dama can ba wani son maimuna su ke yi ba kasancewar ita 'yar kano ce ya auro ta ba a garin ta ke ba, nan su ka had'a shi da wata 'yar uwan Dad su Hajara.
Hajara irin matan nan ne makirai wanda su ka san kan makirci sosai ga shi tun da ta shigo gidan momim Safwan bata yi kishi da ita ba amma ita bata 'kaunar ganin su a gidan daga ita har d'anta Safwan.
Shekarar Hajara Biyu a gidan Ta haifi d'an ta namiji, wanda ya ci suna, mansur, awannan lokacin ne kuma Daddn Safwan ya saki maimuna, (momin Safwan) hakan ya matu'kar 'bata ma Safwan rai sosai momin shi ta koma kano garin su da zama yanzu shi d'aya ne a gidan Dad shi gashi baya zama daga shi sai Hajara da ya ke ce mata anty, tun da momin shi ta bar gidan Hajara kullum da salon zagin da zata yi mai da tsinuwa sosai abun ya ke damun Safwan ya na ta'ba mai zuciya, amma Safwan be cika yanka mata ba, domin yana da haƙuri sosai, amma ba kowa ne se gane hakan ba.
Da taimakon abokai da kuma aminin shi kamal Safwan ya fara shaye-shaye, ba irin abun da baya sha, don Kamal ba ƙaramin hatsabibi ba ne, har zuwa club duk Kamal ya koya mai abu d'aya ne dai Safwan ya kasa koya neman mata domin Kamal gwani ne ta nan ma, abun na Safwan wasa-wasa se gaba yake yi, don idan ya sha se dai ma akawo shi gida ko kuma ya shigo a bige, sosai abun ya ke bawa Daddyn shi mamaki wai Safwan ne da wannan d'abi'a, momin shi kuwa da ta samu labari har kuka ta yi, ta cigaba da yi mai addu'a.
Ranar da Safnah ta fara zuwa makaranta an saka ta a Jss2 kasancewar ta yi one a garin su, ta fara two d'in ma, sati biyu ta yi ta na zuwa, ta samu kawun ta tace don Allah ayi mata Jumping zuwa