Showing 1 words to 3000 words out of 6136 words
Chapter 1 - KOWA YA DEBO DA ZAFI Book 1 Complete FREE PAGES BY MEENAT YANDOMA & ZAHRA ROYAL.txt
KOWA YA ƊEBO DA ZAFI...
NA
MEENAT A 'YANDOMA
DA
ZARAH ROYAL STAR
WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI
FREE PAGE 1&2
Ƙarar saukar ruwan sama me haɗe da iska yayi sanadin farkarwarta, a firgice tana me maƙurewa can ƙarshen gado tare da sakin a jiyar zuciya. Mummunan mafarkin da tayi ne ya dawo mata sabo fil, tamkar yadda mirror ke maido ma mutum ainahin suffar shi. Tuntsurewa tayi da dariya sakamakon tunawa da tayi da ƙudirinsu, sai dai saurin haɗiye dariyarta tayi sakamakon turo ƙofar ɗakinta da ta ji anyi. "Ninaah! Dariyar me kike yi haka? Ke tsaya ma! Me ya hanaki rufe ƙofa duk da ruwan nan da ake tsalawa?" "Umma bacci ne ya sace ni ina gama sallah, amma yanzu zan rufe" kallon tuhuma Mahaifiyar ta ke mata sakamakon hango rashin gaskiya ƙarara a fuskarta. Ganin Mahaifiyarta zata karbo jirgin ta ya sakata saurin kawar da zancen "Umma Abba ya dawo?" "A'a bai dawo ba ke ya ke jira" Umma ta ƙarasa maganar tare da ficewa daga ɗakin. Murmushi ta sake saki a karo na barkatai tare da ɗaukar wayarta tana tafiya cikin sanɗa. Jin mahaifiyarta ta shige ɗaki hakan ya bata damar shiga ɗakin da mahaifinta ke ajiye kudi ta kwashi adadin da zai isheta. Ƙarar shigowar sako a wayarta yasa ta firgita tare da saurin kallon screen "Lokaci ya na tafiya, ki tabbatar kin kasance cikin shiri" dariya ta saki tare da daka tsalle ta rungume wayarta, cikin sanda ta koma daki tare da fara haɗa kayanta bakin ta ɗauke da wakar Umar m Sharif mai taken gamu nan dai...
Cikin nutsuwa ta sauke wayar daga kunnenta ta na kallon tagar dakin ta da iska ya bude da ƙarfi. Walkiyar da aka yi ce ta saka ta saurin duƙewa tare da ambaton Sunan mahaifiyar ta. Ta share daƙiƙu kafin ta ɗago cikin tashin hankali don in akwai abinda take tsoro to bayan ruwan sama yake. Kiran Ninaah ne ya shigo wayar ta cikin hanzarin ta dauka. "Yanzu haka cikin shiri nake, ruwan nan ne ya tsayar dani, kin san dai ba zamu fita ba sai su Hajiya sunyi bacci" "Ban gane sai munyi bacci ba" Mahaifiyar ta da shigowar ta kenan ɗakin ta karasa maganar tare da kafe Zainabu kamar yadda take kiranta da ido. Dabur-burcewa Zuzuuh tayi kamar yadda kawayena ke kiranta. "Hajiya dama yanzu nake shirin zuwa in duba in ga shin kinyi bacci?" " Ke kada ki mayar da ni shasha mana, ina za ki je kike fadar sai munyi bacci?" Hajiya ta ƙarasa maganar cikin haɗe fuska. "Dama... Dama, gobe ne zamu je wani bikin kawarmu shine na ce a bari da safe zan fada miki yanzu ina zanje tunda kinyi bacci"ƙure ta da ido Hajiya tayi tare da jefa mata kallon tuhuma don ko alama bata gamsu da wannan zancen ba, girgiza kai tayi tare da ficewa daga ɗakin. "Haba Hajiya! Sai ma gari ya waye kin nemeni kin rasa lokacin zaki gane karya na miki" Zuzuuh ta ƙarasa maganar tare da bude akwatin da ta zuba kayanta. Kudi ne barbaje da tayi nasarar kwasowa a dakin mahaifiyarta. Alamar shigowar sakon da taji ne ya saka ta daukar wayar "Ki fito yanzu, muna jira" kallon ƙofa tayi taga ruwan ya fara lafawa don haka daukar akwati ta tayi cikin sanda ta bar gidan ba tare da kowa ya sani ba...
Shurun da taji ita ta tabbatar mata da yan gidansu sunyi barci, don haka cikin natsuwa ta janyo katon akwatinta tana niyyar barin gidan. "Laaa! IBINA ina za ki je cikin daren nan ga ruwa anayi." Gabanta ne ya yi mummunar faduwa ganin asirinta na shirin tonuwa. A fusa ce ta kalli ƙaramin ƙaninta "zan kai kayana dakin Momy ne uban yan sa ido, me ya fiddoka cikin daren nan?" "Motsinki na ji na fito" cikin dabara ta mayar da akwatinta daki tare da jan hannun ƙaninta taje ta kwantar da shi sai da ta tabbatar yayi bacci sannan ta fito tare da ja masu dakin kasancewar ita ce babba duk dare sai kannena sunyi barci take yi. "Shukurah bakiyi bacci ba har yanzu ?" "E Momy yanzu dai zan kwanta" ta karasa maganar da sauri ta shige dakinta. Jin tsit! Da tayi hakan ya tabbatar mata kowa yayi barci don haka cikin sauri ta bar gidan. "Ke kadai muke jira" shine sakon da ta gani kwance a screen din wayar ta. Murmushi tayi tare da bin wata hanya, don tana da tabbacin suna can suna jiranta...
Meenat A 'Yandoma
0813356279
KOWA YA ƊEBO DA ZAFI...
NA
MEENAT A 'YANDOMA
DA
ZARAH ROYAL STAR
ƘIRƘIRARREN LABARI NE
Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji.
WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSA
PAGE 3&4
Sauri take gudun kada wani ya ganta, duk da duhun daren da ake amma haka ta rika zabga sauri tamkar zata tashi sama. Tsak! Ta tsaya cike da tashin hankali ganin kamar mutum ya gifta ta gabanta cikin babaken kaya. Ja da baya ta fara yi gabanta na tsananta faduwa. Hasken motar da ta fara hangowa ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da kara saurin barin wurin, domin bata yadda da inda take ba. Bude gidan baya tashi ta shige inda Ninaah da Zuzuuh suke sai ita cikon ta uku. A gaba kuma Fu'ad ne ke tuki sai Ammar da Haris a kujerar mai zaman banza. "Beb kin so fa ki bata mana lokaci, domin mun jima a wurin nan." Ta tsinkayo Muryar Fu'ad na fada. "Ba zaka gane bane, baro cikin gida a irin wannan lokacin ba ƙaramin tashin hankali bane." Fadar Ibina "Bari ke dai Ibina! Da kyar na baro gida, kadan ta hana asirina ya tonu." Cewar Zuzuuh. "Haba Guy’s! Mu je mana ni fa na kagara mubar garin nan kafin asirin mu ya tonu, don kunsan ko wane lokaci ana iya kama mu, ga jirginmu karfe bakwai na safe zai tashi." Ihu suka ɗauka a tare ganin suna daf da cimma burinsu. Gudu suke tsalawa cikin duhun daren ga ruwan sama da bai karasa daukewa ba. Karfe dayan dare suka sauka garin Abuja, kai tsaye Hotel suka nufa domin anyi masu booking din komai, gajiyar da suka kwaso ita ta saka suka kwantawa da wuri zuciyoyinsu fal da farin cikin ƙudurinsu. Karfe bakwai suka farka a gigice domin a tunaninsu sun maka sai Haris ke fada masu sai fa takwas jirginsu zai tashi. Shirye suke cikin kaya na alfarma, wanda kallo daya zakai masu ka fahimci gayu da kuma wayewa ta bi jikinsu. Abinda Ninaah bata taɓa ji ba shi ne ta fara jinsa, wato tuhumar kanta anya ta yima iyayenta adalci? Sai kuma wata zuciyar ta fara fada mata kada kuyi wasa da cikar burin ki, domin kuwa ranar huce takaici kai ya cire. Sanarwa aka fara don haka a tare suka shiga jirgin da yake niyyar tafiya kasar Umbull
Ammar ne ya fara magana "Ni fa a matse nake mu isa kasar nan kodan mu bazama ganin abubuwan mamaki" Haris ne ya karbe zancen "Ni dai damuwata daya ce, kada muje mutanen nan basu zo tarbar mu ba" "haba dai! Ai in kaga ana rashin daukar Costomers da muhimmanci to a naija ne, amma can mu gama magana da Company nin sune da zasu bamu wurin zama da komai hatta duk wuraren da zamu ziyartan su zasu kai mu" Fu'ad ya karasa maganar. " Yau fa ba zanyi bacci ba, haba dai gani a kasar da nafi kauna" cewar Ninaah. Tuntsurewa suka yi da dariya a tare. Nan suka cigaba da labari har jirgi ya sauko. Babu bata lokaci aka zo aka dauke su. Kamar yadda aka nuna masu wurin a online kafin zuwan su, a haka suka samu masaukin nasu. Katon daki mai dauke da gadaje shidda sai kujeru da sauran abubuwan bukata babu abinda babu. Tsalle Ibina tayi ta faɗa saman gadon tare da furta. "Rayuwar 'yanci Assalamu alaikum!" Tuntsurewa da dariya suka yi suna mata shegantaka cike da kaunar juna. "Kunga! Kada ku takurama masoyiya ta" cewar Fu'ad. "Fadama wanda bai da masoyi a kusa, Ammar ka fa ji abinda yake fada ko" Zuzuuh ta karasa maganar tare da kashe mai ido. "Beb zo ki kwanta ki huta, kada su dawo kan mu." Haris ya fada tare da kallon Ninaah.
"Jama'a a fidda batun wasa ni fa yunwa nake ji." Cewar Ninaah "Kura ci da gashi, daga saukar mu ko wanka ba muyi ba sai ki hau ciye-ciye." Cewar Ammar, Haris ne ya cabe zance. "Kada fa ku sako min masoyiya a gaba, kinga rabin rai je ki ci abinci kiyi nat! " Shigowar ma'aikatan wurin dauke da abinci mabanbanta ne ya saka su yin shuru tare da hadiye yawu. "Wow! Wannan rashana duk mu kadai" Fu'ad ya karasa maganar yana kokarin daukar abincin. Saukin rike ma shi hannu Ammar yayi "kaga Malam mu je kowa yayi wanka, muyi sallar azahar sannan a Ci. "Ci ya na gaba da sallah fa" "mu je kawai" Ninaah ta faɗa. Ɗaya bayan ɗaya suka yo wankan tare da gabatar da sallah domin lokacin azahar ya shiga. Nan fa suka fara shirin cin abinci "Drink din nan ban yadda da shi ba, kamar giya." Ibina ta faɗa tana jujjuya lemun. Amsar shi Haris yayi yana kare ma shi kallo "Da gaskiyar ki fa, to amma sun rubuta non alcohol." "Ku miko shi nan ku gani, tunda har suka rubuta ba giya a ciki tabbas sai na sha" Ammar ya karasa maganar tare da bude kwalbar ya kafa mata kai. "Zuzuuh nake don haka masoyi gama sha nima sai nasha, in mutuwa ce mu mutu tare, bare ma nasan bamu mutuwa sai munyi aure" Dariya suka kwashe da ita a tare ganin da gaske Zuzuuh take don har ta karasa shanye lemun. Ma'aikacin wurin dake laɓe yana kallon duk abinda ke faruwa murmushin mugunta ya saki ganin sun sha lemun. Tafiya ya yi domin ya sanar ma Shugabansu ce wa an samu waɗan da suka sha. Kamar yadda aka tsara karfe hudu na yamma cikin shigar kananun kaya suka fito motar Hotel din ta dauke su. Ba ƙaramin yawo suka yi ba domin basu dawo gida ba sai dare. A gajiye suka yi wanka suna labarin abubuwan da suka gani a fitar su. Zuzuuh ce tari ya sarke, sannu suke jero mata cike da tausaya wa. Duk Ammar ya rude, bayan ya lafa ta sha ruwa tana mayar da numfashi. Daki yayi tsit domin sun tsorata matuka, babu fa abinda ta ci amma ta hau tari ga idanunta lokaci daya sunyi jajur. Miƙewa tayi da nufin ta shiga Toilet, jirin da taji yana dibarta ne ya sakata dafe bango. Tamkar wadda aka fizgo haka suka ga ta baro bangon tare da yanke jiki ta zube ƙasa tana shure-shure. ƙasusuwanta suna wata irin lankwashewa. Cikin hanzari Ammar ya nufi inda take, sai dai kafin ya ƙarasa sai gani suka yi shi ma ya yanke jiki ya fadi. Cike da tashin hankali suka rasa wa zasu taba domin su biyun sai shure-shure suke. Cikin karfin hali Fu'ad ya kira daya daga cikin ma'aikatan wurin suka nufi su Ammar. Shure-shuren ya tsaya sai dai jini ne ke fita ta hanci da kuma bakinsu. Wata mace ce ta shigo dakin dauke da ɗan karamin akwati, na bada taimakon gaggawa. Nurse din saitin fuskar Zuzuuh ta kanga kanta don taji shin tana raye, sai dai kafin ta dago kanta ji tayi Zuzuuh ta cafke wuyanta tare da kafa mata hakoranta da suka yi tsini tamkar wuka. Ihu Nurse din keyi tana neman taimako, su Haris ja da baya suka fara yi cikin zallar rudewa. Ba zato ba tsammani sai gani suka yi Ammar ya daka tsalle tamkar an harbo shi a kibiya. Nan fa suka fara gudun ceton rai, kafar Ibina Ammar ya fizgo da karfin tsinya tare da jefa ta da daki bango. Ƙarar data saki ita tayi sanadin dakatawar guje-gujensu. Ibina ce a gefe kwance cikin jini kanta ya fashe jini na tsartuwa....
Meenat A 'Yandoma
08133562798
KOWA YA ƊEBO DA ZAFI...
NA
MEENAT A 'YANDOMA
DA
ZARAH ROYAL STAR
WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE AKAN 500 KACAL! ZAKU TURO DA KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2294023532 UBA AMINA ABUBAKAR KU TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08133562798 KO KUMA KU DAUKI HOTON KATIN MTN NA 500 KU TURO HOTONSHI
ƘIRƘIRARREN LABARI NE
Tun daga sunayen garuruwa har ma da wasu abubuwan da zaku ji.
PAGE 5-6
Ibina dake kwance a sume da mugun sauri Fu'ad ya nufi inda take kwance, wani sauran ruwa ya rarumo ya fesa mata a fuska. Wata irin zabura sukai su duka ganin Nurse d'in da Zuzuuh ta cafke ma wuya itama ta fara wata irin mik'a k'asosuwan jikinta na bada wani sauti, k'as-k'as.
Ninaah ce ta matsa kusa dasu Fu'ad dake bakin k'ofa, tana k'ank'ame Fu'ad dake tsaye rik'e da Ibina, zazzare ido sukai ganin Ammar da Zuzuuh da Nurse sun mik'e suna wata irin jijjiga bakinsu da hak'uransu sunyi wani mugun tsini, kwayar idonsu ta zama fari fat ta koma irin na horror, jikinsu da fatar jikin nasu tayi wata irin kala kamar yalo, kamar an shafa masu tuka. Banko k'ofar d'akin da akai ne yasa suka zabura sukayi waje a da mugun gudu. Shugaban hotel d'in ne ya zo, kai tsaye d'akin ya kutsakansa a ciki, wadda yaje ya sanar dashi jikinsa na kyarma da harshan turanci ya ce "ranka ya dad'e karfa ka shiga d'akin nan, wallahi gwajin nan an samu matsala,kamar wata annoba ce ke shirin tunkaro mu in..... "Ka rufe ma mutane baki na ce ko" da sauri ma'aikacin hotel d'in ya tushe bakinsa da tafin hannunsa yana zare ido. Kai tsaye shugaban hotel d'in ya Banga k'ofar d'akin dasu Ammar ke ciki. Ai da mugun sauri ya fara ja baya, ganin yadda suka nufo k'ofar gadan-gadan suna faman mik'a hannunsu gaba, suna son kamoshi. Da gudu ya juyo zaiyo waje, sai dai akwatin maganin da Nurse d'in nan ta shigo dashi ya tade shi ya zube a k'asa. Ammar ne yayi kukun kura ya fad'a kansa yana neman kaima wuyan sa cizo. Kokowa suka shiga yi yana ihun taimako, gasu Zuzuuh dake gaf rufe sa suna wani gurnani da shinshine-shinshine. Motar asibiti ce ta k'araso tare da doctors wadda ma'aikacin hotel d'in ya kira su cikin sauri. Wani mugun k'arfi ne ya zo mai ya jawo akwatin maganin yana kwad'ama Ammar shi a saman kai, ai ko danda nan ya zube a sume. Sai dai yana k'ok'arin tashi su Zuzuuh suka turmushe shi, wata irin kokowa suka kamayi dashi, Zuzuuh ce ta samu sa'ar sa y'an yatsunta masu d'auke da farce mai mugun tsini ta karci wuyansa, danda nan jini ya kama zuba ta wuyan nasa. Ma'aikacin hotel d'in ne yayi hanzarin d'aukar wani k'arfe ya daddage iya k'arfin sa ya kwad'ama Zuzuuh a kai, ai ko Nurse d'in nan data rage ganin ta nufo shi yasa baiyi wata-wata ba itama ya kwad'ama shi itama ta zube a sume. Wata irin zabura shugaban hotel d'in yayi yana rungume ma'aikacin hotel d'in, rik'e wuyansa yayi yana sauke ajiyar zuciya, da sauri ya kalli doctors d'in dake tsaye ya ce "ku kwashe su mu tafi asibiti, ayi bincike mike damunsu, tunda nake ban tab'a ganin masifa irin wannan ba" Da sauri Doctors suka sasu akan gadon aka daure su tare da yin asibiti dasu. Fu'ad dasu Ibina suka rungume ya janye su daga jikinsa yaja hannunsu da nufin subi su asibitin, sai dai Haris dake tsaye ya dakatar dashi yana cewa "mun shiga uku, wannan wacce irin masifa ce?, ina kuma zaku je naga kana niyar binsu?" "Zamu bisu asibitin ne ai, domin hankalin mu bazai tab'a kwanciya ba, har sai an duba mike dumunsu" Da sauri Haris yaja baya yana cewa "kutumelesi inbisu su cinye ni, kana ganin yadda suke cafke mutane suna neman cizon mutum, gaskiya ni tsoro nake ji" Da sauri Ibina ta dafa shi tana cewa "haba! Haris tare fa mukazo dasu bai kamata dan wani abu ya sami y'an uwanmu mu kuma mu juya masu baya ba, sorry muje kawai" Jikinsa ne yayi sanyi, ganin Fu'ad yayi gaba, yasa suka rufa masa baya
Motor hospital su duka suka shiga harda shugaban hotel, dake rik'e da wuyansa yana yamitse baki, saboda wani irin zafi da yake jin wajan na mai, gani yayi wajan jini ya daina zuba, sai wani irin jini kalar ruwan ganye dake zuba, wani iri ya fara ji cikin jikinsa, ya fara wani irin gurnani da tari yana tushe bakinsa, ji yayi ba abunda yake bala'in so irin yaci nama, ko wanne iri ne, bai dai idasa kamuwa da cutar ba, sai yayi saurin gyara wuyan rigar tasa dankar wani ma yaga wajan yadda ya koma. Har suka isa asibiti ba wadda yayi magana kowa d abunda yake sak'awa a ransa. Babban asibiti ne mai girman gaske, mai cike da marassa lafiya, kota ina da y'an uwan marassa lafiyar cike da hospital d'in. Kai tsaye da motar asibitin ta tsaya, wasu doctos ne da Nurses suka nufo wajan da gadon d'aukar marar lafiya guda hud'u, saboda shugaban hotel d'in, su duka sakkowa