Showing 6001 words to 6136 words out of 6136 words
Chapter 3 - KOWA YA DEBO DA ZAFI Book 1 Complete FREE PAGES BY MEENAT YANDOMA & ZAHRA ROYAL.txt
duniya anyi da su akan su shiga inda aka tanada domin kwanan masu jinya amma fur sunki tafiya sai ma suka kwanta saman kujeru dake daf da ɗakin da su Ammar suke. Dare ya tsala asibitin tayi tsit baka jin karar komi sai ta karnuka alamun kowa ya yi bacci. Su George tare da su Ammar dake kwance a gadajensu lokaci daya idanunsu suka bude. Dirowa suka fara yi daga saman gadajensu suna jan kafa kansu ya karkace kafa a murgude tare da nufar kofar fita. Cikin baccin Ibina ta ji kamar mutum tsaye a kanta, bude idanunta yayi daidai da sakin gigitacciyar karar da ta saka su Fu'ad farkawa, bude idon da zasu yi su Ammar suka gane sun zagaye da su sun saka su tsakiya idanunsu fari fat bakunansu na dalalar da jini....
Meenat yandoma