Showing 12001 words to 15000 words out of 28291 words

Chapter 5 - BAKAR TAFIYA BY MEENART A YANDOMA.txt

Wayyo Ɗana wayyo mijina."
Haka taita sambatu tana kuka kamar ta 6a66a.


Kece wa da dariya Jamcy tayi tareda kallon Basma.


"To la'anan na mai kama da ƴa'ƴan yahudawa wakikema dariya?."


Ci gaba da dariyar Jamcy tayi ta nuna Basma da yatsa.
"Wa fa nike ma dariya in ba ke ba, tsabar gantali da aurenki amma kika baro mijinki kika taho bikin wata ƙawa."




Ashariya Basma ta tattaro ta ɗurama Jamcy tare da miƙewa tayo kanta gadan_gadan.


Da ƙyar Jafar yayi nasarar raba wannan faɗan daya yaso barkewa.


Ƙutawa kawai Basma keyi tana hararar Jamcy, ita kau Jamcy da sun haɗa ido saitayima Basma kwalo tana mata dariya.


Iya ƙuluwa ta ƙulu da Jamcy, jira kawai take Jafar ya ɗan kauce tasamu sa'ar tumurmusa Jamcy.


Jafar daya lura Tk ɗan zafin kai ne tunda suka haɗu sai wani shan ƙamshi yake yana hura hanci.


"Tk ka taso muɗan zagaya cikin jejin nan musamu abinda zamu sama cikunnan mu."




Kallon up and down Tk yayima Jafar.
"Ok muje."
Yafaɗa yana yamutsa fuska kamar yaga kashi.


"Ku su Basma ku tsaya nan kujiramu mu dawo."


Tsalle Mandiya tayi ta dire ita bazata tsaya nan ba wani abu yazo ya hallakata.


Suma sauran mara mata baya akan bazasu zauna ba.


Sunyi tafiya mai ɗan tsayi suka iso wani wuri mai yalwar ganyayen bishiyoyi.


"Laaah! Kuduba ku gani chocolate da sweet a chan."


Dubansu suka kai wurin suna masu mamaki ganin kayan daɗin da ko a cikin gari sai kanada manyan kuɗi zaka mallakesu.


Hannun Jamcy Tk ya kamo saboda yasan mayyar kayan zaƙice.


"Sweety ka sakeni in ɗauko, kasan fa yadda nike bala'in son chocolate."


"Aa ƙaunata kada ki ɗauka zai iyafa cutar mani dake, kinsan da wani abu ya sameki ƙara ni ya sameni."


Shamatarshi tayi ta fizge ta ruga tana dariya ta nufi wurin chocolate ɗin.


Kafin hannunta ya ida isaga chocolate ɗin tuni sun rikiɗe sun koma wani jibgegen baƙin kumurci ya fasa kai yayo kanta.


"Nashiga ukku nalalace, Sweety ka kawo mani ɗauki wayyo na bani ni Jamilatu."


Cikin firgici da hargagi yake faɗar" kada ki motsa ƙaunata gani nan zuwa gareki."
Cikin zafin nama ya jawo Jamcy suka ɗiba ana kare,su Jafar take masu baya sukayi, ganin haka macijin ya bi bayansu.


Abinda suka lura macijin yabar binsu sai yanayin wurin daya chanza duhun wurin ya ƙaru.


Ƙarar tsuntsaye sukaji saman kawunansu.


Ɗaga kan da zasuyi suka ga Wasu irin jibga_jibgan tsuntsaye masu suffar jemage sai dai su sunfi jemage girma da suffa mai ban tsoro.


Ganin haka suka ƙara ƙaimi wurin gudun, tsuntsayen na biye dasu.




Ƙarar da sukaji an kwala ce ta sanyasu tsagaitawa da gudun suka juyo, Basma suka gani tsuntsayen sun sureta sunyi sama da ita...........




____________________
........Gudu suke gadar na ƙara karairayewa, sunyi nasarar ida ƙara sawa ƙarshen gadar, suna ida tsallaketa tana Rubzawa ƙasa.




Duƙawa sukayi wurin wasu kuma suka baje suna maida numfashi.
Mtsw Salma taja dogon tsoki.
"Aikin banza mutum gashi nan mugun rago da anshiga bala'i sai ya hau ihu yana cika ma mutane kunnuwa yen_yen_yen, mtsw sauna kawai."


Fashewa Rabson ya ƙarayi da dariya.
"Bakomi masoyiyata mai bakin shantu, kin ga yadda bakinki ke ƙara tsayi da kina kwaikwayar maganata kuwa."


A fusace ta nufo inda yake tana zazzaga masifa.


Ganin da gaske take ya sanya Rabso fara magana.
"Masoyiya kina ƙarasowa wurin nan zani chakumeki muyi ƙasan ramin nan muyi mutuwar shahada irinta masoya."
Ya ƙarashe maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya.


Tsayawa tayi daga nesa tana aiko mashi da baƙaƙen maganganu.


"Heeey! Yau ni naga marasa hankali, yanzu ku a halinda muke ciki har kunada bakunan yimana faɗa, to duk ɗan....Ta ɗura wata ashariya Daya ƙara mana fada saina hankaɗashi ya faɗa cikin ramin nan."
Kulu ta fada tana nuna Salma da yatsa.


"To ɗiyar matsiyata waya sako dake?, gantalalliya uwar ƴan yawon ganin ƙwaf."
Salma ta ƙarashe maganar kamar zata kai ma Kulu bugu.




"Wa'iyazubillah! Ku kam ko gasar ƙunduma ashariya muka fito sai haka, abinda ya kamata mu dage da addu'a amma kun dage sai zagi da ashar kuke ɗurawa, kuyima kanku faɗa kufa ƴa'Ƴan musulmai ne."


Shiru suka yi kowa na hararar ɗan uwanshi.


"Haba babynah, ki rabu da ita Ke ba sa'ar yinta bace."
Nas ya karashe maganar da sigar rarrashi.


Nausawa suka kuma yi ciki dajin suna rarraba idanu.


A hankali wata iska ta fara kaɗawa tamkar irin in hadari ya fara tasowa.


Jin wannan baƙon lamari ya sanya suka ƙara matsewa wuri ɗaya.


Duhu wurin ya farayi tamkar ruwan sama zai balle.


Gudu suka farayi suna sassarfa,kafin su ankara an kece da wani irin mamakon ruwan sama mai haɗe da iska mai ƙarfin gaske.


Gudu suke idanunsu rufe basu ganin gabansu saboda Iskar da ake, wani wawakeken kogon dutse suka gani basu yi wata shawara ba suka afka cikinshi, suna ida shigewa ƙofar kogon Wani dutse ya tugo ya rufeta garam!......




*NIMA KAI NA JIN ƘARAR RUFEWAR ƘOFAR SAI DA WAYATA TA KUSA KUFCEWA* 😂😜
































*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅






















*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰






*NASADAUKAR DA WANNAN PAHE ƊIN GAREKI KHADIJA S SAMSHARE AR GATAN MAMA, ALLAH YA ƘARA ZAƘIN HANNU*


______________________
*PAGE 18_19*


.........Ihu Basma keyi tana naiman agajin su Jafar.


Lokaci guda ƙwalwarta ta fara tunano mata inda Ammar ya basu addu'a insun shiga bala'i.


"LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN."
Basma ta furta da ƙarfin gaske.


Tsunsun jiyayi kamar ya ta ɗauko garwashin wuta, bai bata lokaciba ya sakota ƙasa shida sauran ƴan uwanshi suka bace bat! Kamar basu ta6a wanzuwa a wurinba.


Duk da buguwar da Basma tayi sanadiyyar faɗowar da ta yi amma haka ta miƙe tana gudu tana ɗingishi.


Tun kafin dare yayi sosai suke gudu har saida duhun dare ya raba sannan suka zube suna maida numfashi.


"Wayyoh! Zani mutu, wayyo Umma na, na shiga ukku, shikenan mu haka zamu dawwama cikin bala'i muna mutuwa ɗaya bayan ɗaya, koda waɗan nan Aljanun basu kashemu ba yunwar cikin mu kaɗai ta isa tayi sanadin mutuwarmu, wayyo Ummana shikenan bazan ƙara ganinkiba."Jamcy ta ƙarashe maganar tana harba ƙafafu a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana kuka tana kuka.


Tk jiyayi kamar ya mangare Jamcy, amma soyayyar daya ke mata bazata bari ya iya yi mata komiba.


Dare ya raba sosai ga wani irin sanyi da ilahirin dajin ya ɗauka.


Matan su duka haɗe suke wuri ɗaya suna gyangyaɗi ga kyarmar sanyi sunayi.


Tk da Jafar wuri suka gyara da hannuwansu tareda kwantawa.


Wuri yayi tsit! Bakajin mitsin komi sai kuka tsuntsaye, bacci yayi nasarar sace su.




Cikin Bacci Basma taji kamar ana ja mata ƙafa, ƙara gyara kwanciyarta tayi.


Fizgar ƙafar akayi da ƙarfin gaske aka jawota daga inda take kwance.


Ƙara ta ƙala da tayi sanadiyyar farkawar su Jafar suka miƙe a firgice.


Wasu irin mulmula_mulmulan halittu masu kama da dodanni jikinsu duk gashi,ga wasu zara_zaran farata masu tsini, in ka kallesu sau ɗaya bakayi Marmatin sake kallonsu ba saboda tsananin muninsu.


Kafin suyi ko ƙarin guduwa tuni dodannin sunyi nasarar kamesu sun sa awani keji, suka ɗauki kejin da hannu ɗaya suka ci gaba da tafiya.


Ihu kawai suke in banda Jafar da tuni bakinahi ya fara ambaton Allah da naiman agaji a wurinshi.


Tsawa ya daka masu wadda tayi sanadiyyar yin shirunsu.
"Bashakka ina ga mun kusa raba tafiyar nan daku, kuna ganin halinda muke ciki amma kun wage baki kuna wani kukan banza da bazai amfanemu da komiba, Shawara ɗayace muyi ƙokarin tseratar da rayuwarmu domin bashakka in muka bari dodannin nan suka ida isa damu lofa lalla mun zama nama cinyemu zasuyi."


"Eh musan yadda zamuyi mu buɗe kejin nan mu kubutar da rayukanmu."
Tk ya ƙarashe maganar yana ƙara riƙe hannun Jafar kamar za'a kwace mashi shi


(😂😂 Niko nace Tk ina ɗagin kan? Ko ka sauko tun yanzu.)


"Amma abinda nike gani naga mun fara hango alamu kamar a kwai kogi nan gabanmu in muka buɗe saimu faɗa ruwan, abinda nasani dodanni basu san ruwa mu bari sai muna gaf da ida isa wurin sai muhaɗa ƙarfi mu buɗe ƙofar nan."


Sun yi na'am da wannan shawarar ta Jafar, suna gani sun doshi gefen ruwan suka fara koƙarin tserewa.


Da ƙyar da ji6in goshi suka samu ƙofar ta ɗan buɗe yadda mutum zai iya fitowa daga cikin kejin.


Da ɗai ɗaya suka riƙa dirowa suna ficewa a guje, Mandiyace ƙarshen fitowa tana dirowa Dodan daya ɗauko kejin yaji kamar kejin ya rage nauyi.


Kejin daya gani a buɗe duk sun fice ya sanyashi wata irin kuwwa da sai da dajin yayi amsa Amo!.


Jin wannan ƙarar ya sanya sauran Dodannin rugowa domin sun fahimci naman da suka kamo ya sun tsere,agujsuka bi bayansu Jafar suna gudu suna daka wani irin tsalle tamkar ƙwaɗanni.


Gani irin azababben gudun da Dodannin keyi suna ƙoƙarin iskosu yasa su Jafar ƙara ƙaimi suna ƙoƙarin isa ga wannan kogi.


Sunyi nasarar isowa
Tk ya fara isowa wani irin birki ya ja ya tsaya ganin irin zurfin da ke akwai kafin ka isa zuwa ciikin kogin, Jamcy na isowa batare da ta luraba ta banka Tk sukayi ƙasa, suma sauran baya suka mara masu.


Dodannin na isowa basu iske kowa ba, ganin haka ya sanya suka fasheda wani irin kuka daya sanya wurin amsa kuwwa.


Abinda ya basu mamaki kuma ya tsorata su shine ganin ƙasan ruwan haske fayau tamkar ba dareba.


Iyakar ƙarfinsu suke iyo amma abinda suka lura shine duk ƙokarin da suke suna nan tsaye a wurin da suka faɗo, wannan al'amari ya matuƙar ɗaga masu hankali.


Ga iskar da suka shaƙo ta kusa karewa.


Lokaci ɗaya ruwan ya fara wani irin motsi tamkar wani abu ya fao cikinshi.


Duk ƙoƙarin da suke amma a banza, sai da Jafar ya fara karanto addu'a cikin zuciyarshi sannan suka ga kamar an saki jijiyoyin jikinsu sun fara wuce wurin.


Tamkar an wulloshi haka suka tsinci Nura gabarsu kamanninshi su sauya yakoma Horror idanunshi babu ƙwayar baƙi sunyi fari tas!.


Kafin suyi wsni yunƙuri ya warci Mandiya yayi ƙasan ruwan da ita.........


__________________________
"Allahumma ajirnifiy musibati wa'aklifini khairan minha."
Biba ta ƙarashe Addu'ar yayin da taga ƙofar na rufewa.


Tsaye suke ido ya raina fata, kowa ka kalla zaka hango tsananin firgici atattare dashi.


Ko ƙwaƙwƙwaran motsi bakaji kogon yayi tsit!


Jin motsi bayansu yadawo dasu daga duniyar tunanin da suka lula.


Kulu da Nas su suka farayin gaba sai Biba Rabson da Salma suka take masu baya.


Tunda suka fara tafiya basu haɗu da komi ba sai yana da ta dabaibaye ilahirin kogon sai sun sanya hannu sun ɗebeta sannan suke samu su wuce.


Abinda suka lura kogon wata irin doguwar hanya gareshi tunda suka fara bi har yanzu basu zo ƙarshenta ba.


Wani irin daddaɗan ƙamshin abinci hanci nansu suka fara shaƙo masu.


"Wow! Nas kaji abinda hancina ya jiyo mani?."


"Nima shinike jiyowa masoyiya."


Sauri suka riƙayi tamkar zasu tashi sama, turus! Suka ja wani birki yawunsu na tsinkewa.


Abinci ne aƙasa cikin filattai jere reras!, shinkafa damiya hada naman kaji zuƙu_zuƙu.


Rabson wani yawu ya haɗiye ƙut! Tare da lasar la66anshi.


"Kada kuci abincin nan, wani tarko ne aka haɗa mana, kuyi tunani."
Biba ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Kulu dake ƙoƙarin bin Nas daya kusa isa ga abincin.


"Malama sakar mani hannu, ke in bakici muki ƙyalemu muje muci iya cin mu."
Ta fizge hannuta tayi gaba.


Salma gallama Rabson harara tayi.
"To jikan ƴan lasau, kaje kaci naga tun ɗazu sai lasar baki kake kamar sabon kamu."


"Hhh! Haba my Salmaty na hanaki yawan magana fa, kinga yadda kike komawa bakinki har hawa yake kamar tsohuwa zata kira tukur."
Ya ƙarashe maganar yana cigaba da dariyarshi.


"Bani da lokacinka marar aikinyi kawai mtsw!."


"Niko nike da aikinyi, in zauna inta kallon bakinki yadda yayi suntum ɗin nan in kina magana tamkar yadda kikasan bakin aku haka kike komawa."


Iya ƙuluwa Salma ta gama ƙulewa da rainin wayon Rabson, a fusace tayo kanshi tamkar zata kai mashi bugu.


Ihu Kulu ta fasa wanda ya jawo hankalinsu Biba.


Abincin da suka fara ɗiba ne ya koma tsutsotsi Nas da ya kai abincin cikinshi tuni ya baje ƙasa ko motsi bai yi.


Ihu take tana girgiza Nas Amma babu alamar zai tashi.


Biba ta matso tahau tofa mashi addu'o'i a hankali ya fara buɗe idanunshi, wata mahaukaciyar ƙasa da sukaji tasanya shi ida miƙewa tsaye.




Tsutsotsin ne suke haɗewa wuri ɗaya suna zama ƙatuwar tsutsa mai hannuwa bila adadin.


Salma da Rabson wuri ɗaya suka haɗe tana ihun kiran sunan dadyn ta shikuma yana kiran Wayyo Kaka wayyo bunsurunleee....








🤧🤧 Kuyi haƙuri da wannan, banijin dadi alƙawarin danayi makune yasa naƙoƙarta nayi wannan.🤧🤧












*COMMENT*✅
*SHARE*✅
























*MEEN@RT...✍🏻*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: 💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀


( *HORROR STORY* )


*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*


🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*




*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*




*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*


🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*




*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰




_______________________
*PAGE 20_21*


............ganin anjanye Mandiya yasan ya su Jafar tsananin ruɗuwa suka ƙara himma wurin yin iyo.




Da ƙyar suka samu suka ƙaraso ga6ar ruwan.


Kowa ka kalla fuskarshi cikin firgice take da tsananin tashin hankali.


Basma tunda suka fito take zazzaga uban aman ruwa, saboda ruwan da ta shaƙa.


Aman da takeyi kamar zata amayo ƴan hanjinta.


Jamcy kuka kawai take tana tashiga ukku lokacin mutuwarta yayi, da ta sani da bata fito ganin kwaf ba.
Tk bai hanata yin kukan ba dominshima a halinda suke ciki inda zaiyi kukan zai fijin sauƙin abinda Yakeji cikin zuciyarshi.


Sun ɗan jima awurin suna jimamin abinda ya faru da Mandiya.




Ɗunguma sukayi sukabar wurin suna tafiya da ƙyar jikinsu babu kuzari.


Jamcy faɗuwa tayi ta tare da fashewa da kuka.
"Wayyo masoyi, Mutuwa zaniyi bani iya tafiya, ga yunwa nikeji, dan Allah koɗan naman kifi kayo iyo cikin ruwan nan ka gasa mani inci , ni bazan iya cigaba da tafiyaba."
Taci gaba da kukanta.


Galala suka yi suna kallonta.


Basma kallon bakida hankali tayi mata cikin 6acin rai ta fara zazzaga bala'i.
"Ke yanzu in baccin kin maidamu marasa hankali da tunani irinki, gidan ubanwa zamu samu maki irin waɗan nan kayan?, ko kitashi mutafi ko muyi gaba mubarki nan wurin."


Zagita aikoma Basma dashi cikin masifa dake cinta ta miƙe tayo kan Basma.
"Ke harkin gaya mani wannan maganar?, kinsan ko wacece Jamcy bala'i, nayayimi kankazar_kazarki kaga tunkiya uwar tan6ele ke in banda gantali miya fiddoki kika baro mijinki kika fito yawon gantali."


Tatss! Kakeji Basma ta ɗauke Jamcy da kyakykyawan mari, chakumar juna sukayi sukai faɗi kowa tana naushin ƴar uwarta, an rasa mai raba faɗan sunyi tsaitsaye sunkasa koda furta kalmar kudaina faɗan.


Ƙyalesu sukayi suka samu wuri suka zauna suka zuba masu ido.


Sun bugu sunjigata.
Jamcy da taji bugu fuskarta ta chanza kamanni samu tayi ta kubce daga hannun Basma takoma gefe tana maida numfashi ta fara magana da ƙyar.
"Muguwa azzaluma, wannan ai zaluncine ace ana faɗa bazaki bari a huta ba sannan muci gaba dan zalunci ,muguwa mai suffar agwagwa Allah ya isana ban yafe maki ba."


"Nikike kira mai suffar agwagwa?, kiƙara maimaita abinda kika faɗa yanzu in take maki kai in maimaita maki bugun da yafi wannan 6allagaza mai zubin muciya."
Basma ta ƙarashe maganar tana huttai.


"Idan kun gama faɗan kutashi mucigaba da tafiya, nikam kunkusa daina ganina dan tsaf zani rabu daku in raba tafiya daku."
Jafar ya ƙarashe maganar ranshi a 6ace.


Harararshi Jamcy tayi tana gunguni.


"Kai kuma maloho kayi sakaka kana kallo wannan matar tayi mani wannan bugun, wallahi zaka gane in muka koma gida."




Tk banza yayi ya kyaleta kamar baijita ba, domin shi yanzu abinda ke damunshi taya zai tseratar da rayuwar da daga wannan Baƙar tafiyar.


Sunyi tafiya mai ɗan nisa suka samu bishiyar ruman suka tsiga suka sha suka zauna suna hutawa.


Motsin da sukaji alamun takun sawun mutum ya nufo inda suke yasanya su ɗago kawunansu.


A firgice suka miƙe tsaye suna kallo cikin matuƙar mamaki atare suka furta Rabson!.


Tsaye yake yana kallonsu yana murmushi.
"Nine zuwa nayi domin intafi daku wurin sauran abokan tafiyarmu, tunda kuka bace mana muke yawon naimanku sai yanzu Allah yasa na ganku."


Cikin zaƙuwa Basma tayo wurinshi, "yauwa Mutumina Rabson ina su Salma da su Biba."


Jin an ambaci sunan Biba yasa Jafar matsowa domin yaji inda aka baro mashi abar ƙaunarshi.


"Suna chan suna jiranku, kuyi sauri mu ƙarasa wurinsu."


Ɗunguma sukayi suka mara mashi baya.


Sunyi tafiya maitsananin nisa har suka fara gajiya da sunce Rabson har yanzu bamu iso ba sai yace masu ku ƙara haƙuri munkusa ƙarsawa.


Wani wuri suka iso mai matuƙar duhuwa ga yawan bishiyoyi ganyayen jikinsu duk sun zubo ƙasa, ta cikin duhuwar suk riƙa ratsawa har suka iso wani bangare daya matuƙar basu mamaki.
Gani sukayi Rabson ya tsaya yaƙi gaba yaƙi baya.
"Rabson mun iso ko?." Basma ta faɗa tana ƙoƙarin shan gabanshi, dariyar daya tuntsire da i ta ce tasanyasu ja da baya bashiri.
Suffarshi tariƙa rikiɗewa tana kasuwa kashi_kashi yana komawa wasu irin maridan Aljanu hannuwansu ɗauke da muggan makamai tamkar waɗanda zasuje yaƙi.
Ga wata iriyar guguwa da ta turniƙe wurin........


__________________________
.......Ida haɗewa tsutsar tayi wuri ɗaya tana wata irin dariya mai haddasama kunnuwan bil adam ɗaukewar jin su na wucin gadi.


Rabson da Salma haɗe suke suna kuka suna sambatu domin yau sun fidda rai da rayuwarsu, Salma wani zazzafan fitsarine ya wanke mata ƙafafu batareda tasani ba.


Tsutsar dariyar datake ta tsagaita tafara magana cikin amon sauti tafara magana.
"Yaku waɗannan halittu masu tsananin taurin kai yau kwananku yazo ƙarshe kushirya baƙuntar lahira."


Jin wannan jawabi ba ƙaramin tada hankalinsu Kulu da Nas tuni jikin Nas ya fara rawa tsabar tashin hankali.


Tamkar maciji haka tsutsar tasulalo tayo kan Kulu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login