Showing 3001 words to 6000 words out of 56271 words
Chapter 2 - KURKUKUN KADDARA 3 Original Document Takun karshe by boss Bature .txt
ɗagowa ta ɗanyi ta kalli chief dake a gefenta, face mask din fuskarshi Ya hana ta ganshi da kyau, sai dai kyawawan idanuwanshi.
Tana faman zazzare idanuwanta haɗi da ƙyafƙyaftasu ta nufi sheikh iman, ta ɗaura hannunta asaman nashi daya miƙa mata.
"Unaisah ko"? Ɗaga mashi kai tayi alamar Eh.
"Meyasa kina ji muna magana ki ka yi shiru baki tanka mana ba kamar wata mai laifi, ai ba wani abu bane don kinzo duba ɗan uwanki"
Shiru tayi bata ce komai ba, duk ta kama kanta kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.
"Zonan surukata" prime minister ne ya kirata, da sauri ta wurga eye balls dinta kan fuskarshi rass taji gabanta Yai mugun faɗuwa, har saida ta zaro ido waje ta saki baki tana kallon ikon Allah, duk sun fahimci dalilin ruɗawarta.
da sauri ta kalli Boss man ta kuma kalli Salsabeel dake atsaye fuskarshi ɗauke da murmushi
"Baki ji Yana magana ba? Kije ku gaisah" acewar Salsabeel
Zuwa tayi gaban prime minister ta tsaya muryarta adabarbarce ta furta"Ina kwana,"
Murmushi yasakar mata Ya ɗaura tafin hannunshi saman sumar kanta
"Ba ki yi breakfast bane? Ko baki duba time ba, Naji kina fadin Ina kwana bayan rana tayi" cikin kulawa yayi mata maganar.
Muryarta kamar ta salihar baiwa ta furta"mantawa nayi,'
"Okey, surukata Ina fata kina lafiya"?
"Lafiyalou"
"Naji dadin haɗuwa dake, ke fa"?
Ɗaga mashi kai tayi"nima"
"Unaisah" Boss ne ya kira sunanta, ta juya tana kallonshi.
"Sunan shi prime minister, uncle na chief namu, kuma shine ya kira sheikh Imam don Ya duba lafiyar ɗan uwanki"
Da sauri ta maida kallonta ga prime minister, farin cikin yasa taji hawaye sun cika mata idanuwanta, miryarta na rawa ta furta.
"Mun.... gode, Ubangiji Allah yasaka maka da gidan Aljanna, kamar yadda ka sanya mu farin ciki kaima Allah Ya faranta maka, In sha Allah duk idan nayi sallah zanyi maka addu'a'.
Murmushi kowan nan su yasaki, musamman prime minister har cikin ranshi yaji daɗin kalamanta.
"Nagode surukata,"
Juyawa tayi da sauri ta dubi sheikh imam.
"Baba mungode, Allah ya saka maka da mafificin Alkhairinsa" addu'o'i ta dinga yiwa sheikh imam, Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya shafa sumarta da hannun shi tare da cewa"Nagode da addu'arki agare ni, kina da kaifin basira, kuma kina da hankali, Iyayenki sun baki Tarbiya, Allah yayi maki albarka tare da sauran ƴan uwanki" amsa mashi tayi da ameen, haƙiƙa taji daɗin kalaman sheikh imam, ƴan hawayen da take 6oyewa cikin idanuwanta tuni sun fara gangarowa kan kuncinta.
"Unaisah, saura chief namu, yakamata kiyi mashi godiya" Boss Man ne ya faɗa yana nuna mata shi, tamkar mai jin shakkar shi ta juya tare da ɗaura idanuwanta kanshi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi on his broad chest, harta ɗaga ƙafa zata nufe shi Big guy yai hanzarin dakatar da ita ta hanyar yi mata Magana.
Nufota yayi adai dai bayan ta ya dakata tare da duƙo da kanshi saitin kafaɗarta Yayi mata raɗa.
"You don't need to thank him, saboda baya so, but be kind to him. If you give me the chance, I'll guide you.
Cikin sanyin murya ta amsa amshi da toh.
"Good Girl," Ya ambaci hakan tare da ɗago da kanshi, babu wanda yaji me suke tattaunawa.
Boss Man Yace"Unaisah zoki wuce ki tafi ɗaki ki yi sallah, Yanzu za'a kawo maku lunch ɗinku" amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi ƙofar room ɗin ta fuce da sauri.
Kafin wani ya kuma yin magana acikinsu, Danish dake akwance Yaja dogon Numfashi, Yatsun ƙafarshi suka soma yin kerma da na hannayensa nan take suka fahimci ya farka daga bacci, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar prime minister.
Salsabeel Yace"Ya farka, Yakamata akawo mashi abincin Yanzun"
"Wani kalar abinci zai Iya ci"? big guy ne ya tambaya.
"Abinci mai ruwa zaifi yi mashi sauƙin wuce wa ta maƙoshi, don bazai Iya tauna abu mai tauri ba"
"Okey, bari naje na kawo mashi" big guy ya faɗa tare da juyawa a hanzarce ya fuce daga ɗakin.
Fitarshi keda wuya, Wayar Chief ta fara Ringing, gaba ɗaya suka ɗago suna kallon shi
Prime minister yace"Wanene ke kiranka"
Curo wayar yayi daga aljihu Ya duba screen din kafin Ya bashi amsa da cewa"Dad Lateef ne"
"Okey, idan kana buƙatar ka shirya kafin mu tafi can gidan ka tafi ɗaki, in sha Allah kafin ka dawo na kammala bashi abincin mu sai mu fara zuwa gida"
Chief ya furta"okey," kafin ya juya ya nufi room door din, bayan fitarsa
Sheikh Imam Yace"atare zamu tafi gidan baban naku, Inason in gaishe da aminina da sauran mutanan gidan"
Prime minister Yace"Toh,"
Shigowa ɗakin Big guy yai hannayen shi a ruƙe da tray madaidaici, kan carpet din gefen gadon Ya daurashi, kafin Ya haye saman gadon Yayi ma salsabeel alamar yazo Ya taimaka mashi, atare suka ɗaɗɗago da Danish suka jinginar da bayanshi jikin headboard din gadon bayan sun sanya mashi pillow, Yalwatacciyar sumar kanshi ta sauko kan shoulders dinshi.
"Baba, ko zaku je gidana ka huta, kafin in kammala bashi abinci, in yaso daga baya zamu zo tare da Chief owais, sai mu wuce gidan baban"
Jinjina kai Sheikh Imam Yayi, Hakan yayi nima inaso in canza kayan jikina, Wa zai kai ni gidan"?
Big guy yace"Aikina ne wannan" ya faɗa tare da saukowa daga kan gadon, Yace da sheikh su tafi Ya sauke shi a mota, Sallama sheikh Yayi ma Prime minister kafin fitarshi saida Ya faɗa cewa idan sunga wani abu badai dai ba dangane da Danish su kira shi awaya su sanar da shi.
Prime minister Ya amsa mashi da toh haɗi da yi mashi godiya, bayan fitarsu, wayar boss tayi ringing, da sauri ya zaro daga aljihu, sunan chief ne ya bayyana akan screen din da sauri yai Ya kara wayar a kunnanshi.
Bayan sun kammala yin wayar Ya dubi Salsabeel.
"Chief Yace ka koma gida wurinsu khadeeja" Amsa mashi yayi da toh,
"Yalla6ai zan wuce, In sha zuwa gobe zan shigo in ƙara duba jikinshi" cikin girmamawa yayi maganar Yana duban Prime minister
Fuskarshi asake yace"Allah yakaimu Lafiya, Amma nayi tunanin kaima agidan nan kake zaune"
Salsabeel Yace"a'a, gidanmu daban, Ina kula da sauran Ƴan uwanmu ne"
"Akwai sauran Yaran kenan bayan wanda ke acikin gidan nan"?
"Eh yalla6ai"
"Allah ya tayaku ruƙo, Sai Allah Yakaimu"
"Ameen" ya fada tare da kallon boss yayi mashi sallama.
"chief yayi magana da Jami'in da zai yi driving dinka, Yana awaje Yana jiranka"
Amsa yayi da toh, kafin Yasakai Ya fuce daga ɗakin.
Ya rage saura prime minister da Boss man sai Danish da ke asaman gadon.
"Yalla6ai zan taimaka maka mu bashi abincin"
Prime minister yace"Okey,"
Boss man ne ya ɗauki tray din abincin Ya ɗaura shi daga gefen gadon, Ya ɗauki robar madara Ya cire murfin a cup ya tsiyaya madarar, kafin Ya miƙa ma prime minister yasa hannu ya kar6a haɗi da furta mashi thanks.
Abaki ya kanga ma Danish sai dai yaƙi buɗe bakin ya rufe shi gam.
Ajiye robar milk din boss yayi, tare dakai hannu ya ruƙo la66ansa ya buɗe mashi baki daƙyar, a hankali milk din take shiga bakinshi hankalin prime minister ya kwanta ganin yana swallowing dinta, duka ya shanye, murmushi yasaki yana kallon boss man yace"naji dadi daya sha, ka ƙara mashi da yogurt"
Martanin murmushin Boss yayi mashi kafin ya kar6i cup din ya zuba mashi yogurt ya miƙa ma hateem, cikin ikon Allah danish ya shanye, sai da ya tabbatar daya cika mashi cikin shi tukunna yace.
"Bari nabarshi haka, kada naci ka mashi ciki," Hateem ne ya faɗi hakan idanunsa akan fuskar Danish wani irin kallon so da ƙauna yake jefa mashi.
Sauke tray din boss yayi kan carpet, kafin ya ɗago yana kallon hateem daya ƙurawa danish ido kamar mai karanto wani abu akan fuskarshi, tun ɗazu yake ta son ya tambayeshi wani abu sai dai ya kasa, gani yake kamar raini ne yayi magana da mutun mai babban muƙami irin Hateem.
Daurewa yayi muryarshi da alamun jin shakkar furta maganar yace"yalla6ai..." kallon da prime minister yayi mashi ne yasa shi saurin haɗiyar maganar.
Murmushi ya sakar mashi tare da cewa "I'm listening to you, and I heard you mention my name. Why did you go silent? Is there something you want to tell me?"
Sunnar dakai ƙasa Tajo yayi"bakomai subul da baka nayi wurin furta sunan"
"Ban yarda ba, please tell me what you want to talk to me about. Kada kaji nauyin yi min magana, I'm a human being like everyone else."
Da sauri boss ya ɗago da ido ya kalleshi, haƙiƙa yana matuƙar mamakin sauƙin kan prime minister Hateem, tun da yake arayuwarshi bai ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zato zo har ya sami damar ganawa da shugaban ƙasar Nigeria sai gashi cikin ikon Allah ya haɗu da mutun bai ruƙe da babban muƙami na shugaban ƙasar canada ƙasar da tana ɗaya cikin Manyan ƙasashen duniya da suke da tarin jama'a da wadatar arziƙi...
Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar prime minister ta katse shi"kayi shiru baka ce komai ba,"
Sosa ƙeya ya ɗanyi da hannunshi kafin ya furta"am....dama yalla6ai tambayace nakeso nayi maka idan ka bani dama, amma dan Allah kada ka ɗauka da wata manufa"
Da fara'a akan fuskar Hateem Yace"kada hakan ya dame ka, Nifa ɗan siyasane, tambayoyi har marasa kan gado ƴan jarida sunayi min kuma in basu amsa dai dai dasu, ballanta kuma kai dana yaba da hankalin ka, duk mutumin da Owais ya yarda dashi toh nima na yarda dashi, don haka kada kaji komai na baka damar yi min kowace irin tambaya ce"
Ajiyar zuciya boss man ya sauke, har cikin ranshi yaji dadin kalaman prime minister, kuma ya ƙara jin ƙaunar mutumin aranshi.
Sai dai duk da haka nauyin shi yake yi, daƙyar ya iya buɗe baki yace"yalla6ai, naji kamar ance baka ta6a haihuwar ɗa namiji ba, ƴa'ƴan biyu duka mata ne shin dagaske ne"? Boss Na ƙare maganar yayi saurin kau da idonshi gefe ɗaya saboda kunyar tambayar da yayi mashi
Shiru prime minister ya ɗanyi, na ƴan mintuna yana maimaita maganar taj acikin zuciyarshi, yayin da yake kallon fuskar danish
"Am sorry Sir, idan tambayata ta 6ata maka rai" acewar Tajj.
Calmly Hateem Ya soma magana ba tare da ya kau idon shi daga kan fuskar Danish ba.
"Ka fama min raunin da yake kwance acikin zuciyata, tsawon shekaru da suka gabata, bana son tuna haukan da nayi, da hawayen dana zubar, da kuma ƙunci da raɗaɗin dana fuskanta saboda rashin da nayi na abun da na ƙwallafawa rai........" tuni yanayin fuskarshi ya canza zuwa matsananciyar damuwa, yayin da yake yin maganar farin ruwane kwance acikin fararen idanuwanshi.
Hatta tajj dake sauraronshi, Jikinshi yayi mugun yin sanyi tunkafin Ya ƙarasa jin zancen nashi
Numfasawa prime minister yayi before saying"I've lost so much that I still haven't forgotten him. I loved him more than I love my children now, and I've never stopped missing him. I know if I tell you that, you'll think it's crazy." He said it with a smile on his face.
("nayi babban rashi da har yau bana manta shi, inason shi fiye da ƴa'ƴan da nake dasu a yanzu, kuma har yau ban ta6a cire shi araina ba, nasan idan na faɗa maka zaka ji abun wani iri" ya faɗa fuskarshi da murmushi.)
"Bayan gimbiya mujeedat ta yi haihuwa ta biyu ta haifi Yazrin, a ƙalla ta ɗauki shekaru bata sake haihuwa ba, tunda Allah ya bani ƴan mata har biyu, sai na ƙwallafa rai ga son samun ɗa Namiji har tsakar dare inayin nafilfili akan Allah ya bani ɗa namiji, cikin ikon Allah a lokacin da banyi tsammani ba, Allah ya kar6i addu'ata, Matata ta samu ciki a daren ranar ko runtsawa banyi ba.. though I wasn't sure if it was a girl or a boy, nidai kawai nasanyawa raina namiji ne.." dakatawa yaɗan yi da yin maganar, tajj ya natsu yana sauraronshi, tun yana daga tsaye har dai yakai ga janyo kujerar gaban mirror ya ajiyeta daga gefen gadon ya zauna yana kallon prime minister.
Cigaba da magana yayi"tun kafin a haife shi na fidda mashi suna, na tsara mashi kalar rayuwar jin daɗin da zaiyi, hatta makarantar da zan sanya shi da komai ma na rayuwarshi sai da na rubuta a diary din dana ajiye domin shi kawai, ita kanta gimbiyata mamaki ta dinga yi ganin yadda na haukace akan son abunda ke acikinta, har fadi take yi na fahimci kafi sonshi akan sauran yaran dana haifa maka, idan ta fadi hakan sai dai nayi murmushi, ba ita kadai ba hatta family dina na Canada dana Nigeria sai da suka shaida ƙaunar dana ke yi mashi, duk rana ta Allah saina kirasu awaya nace su tayani da addu'a Allah ya sauki matana lafiya, saida na addabi kowa da zancen cikinta, mahaifina har tsakar dare nake tada shi daga bacci ince mashi ya tashi yayi nafila ya taya matana da addu'a......" shiru ya ɗanyi idanuwanshi akan agogon hannunshi.
Tajj duk ya ƙagara da sonjin ƙarashen zancen.
"Ban ta6a kawowa raina cewa yaron zaizo duniya amace ko zai mutu bayan an haife shi, kana Naka Allah Yana nashi, sai gashi an haife shi babu rai, wallahi bazan iya misalta haukan da nayi ba a asibitin da ta haihu, likitan daya fara furta mun zancen an haifi yarona babu rai da hannu biyu na cakumi wuyan rigarshi na shaƙe shi tamkar zan kashe shi daƙyar dangina suka raba ni dashi, na dinga yi masu sambatu ina fadin karya sukeyi min ni yarona bai mutu ba da ranshi, daga ni har mahaifiyarshi ba'a bari munganshi ba, ita bata acikin hayyacinta bacci takeyi, ni kuma an hana in ganshi gudun kada in haukace masu saboda sun fahimci na mutu akan ƙaunarsa, tun bayan 2 weeks da faruwar lamarin, Ina kwance gadon asibiti Ina jinyar zuciyata, duk na fita hayyacina sai sambatu nake yi ina fadin ina yarona baba kana gani za'a raba ni dashi, ni nasan ɗana bai mutu ba, baba ina jin bugun zuciyarshi acikin zuciyata, ire iren kalaman da nake fadi masu ba ƙaramin raunata masu zuciya nayi ba, babu wanda bai zubar min da kwalla ba, haka suka dinga lallashina sunayi min nasiha, daƙyar suka shawo kaina har suka samu na haƙura nabarma Allah komai sai gashi yanzu tamkar ba'ayi ba" Prime minister Hateem ya ƙare maganar yayin da hawaye ke ƙoƙarin gangarowa saman kuncinshi, da sauri boss man yayi saurin share mashi hawayen don bazai juri ganin babban mutun kamar prime minister yana zubar da hawayensa akan idonsa.
"Nayi kuskure dana yi maka tambayar nan, ka gafarceni yalla6ai, ni kaina jikina yayi sanyi kuma banji daɗin yanayin da na jefa ka ba, da ace nasan maganata zata fama maka raunin dake acikin zuciyarka wallahi daban furtata ba" cikin sanyin murya murya Boss man Yayi maganar.
Cikin karyayyar murya yace"kada ka damu, ay yanzu komai ya riga daya wuce,"
Ƙarfin hali taj yayi wurin furta"yalla6ai ko zan Iya sanin sunan baby boy din da ka rasa"
He smiled a little before saying, "Sunanshi *OMAIR BIN HATEEM OBINNA* wannan shine sunan da nayi niyar sanya mashi, Allah bai nufa ba"
Maimaita sunan taj yayi"suna mai daɗi, ubangiji Allah ya baka mafiyin abunda ka rasa, In sha Allah zan tayaka da addu'a"
"Nagode sosai"
"Yalla6ai, zan fada maka wani abu, ni tunda nake arayuwata ban ta6a ganin mutun mai babban muƙami mara girman kai irin ka, A yanzu haka da muke yin magana sai nake jin tamkar a mafarki ne
Murmushin gefen fuska prime minister ya saki jin abunda taj yace.
"Ba kai kaɗai ba, mutane dayawa suna mamakin halina, ni ta inda na banbanta da sauran, bani da girman kai, kuma bana ɗaukar kaina wani, duk idan na tuna cewa mu dukkanmu bayin Allah ne, kuma babu wanda yafi wani awurinshi sai wanda yafi jin tsoronshi sai in ƙara jin ni ba wani bane, idan na shiga cikin takalawa sai in manta wanene ni, zan saki jiki dasu muyi mu'amala tamkar bani da ko sisi, haka zalika idan na shiga cikin masu kuɗi sai inji dai dai nake da su, yanzu haka da nake atare dakai, kallon aboki nake yi maka" zaro ido taj yayi fuskar shi da alamun mamaki.
"Ni kuma yalla6ai"
Ɗaga mashi kai hateem yayi alamar eh, wani irin farin cikine ya lullu6e Taj sai faman sakin murmushi yake yi jin prime minister ya kira shi da sunan aboki.
A hankali Hateem Ya mayar da idanuwanshi kan fuskar Danish, ya miƙa hannu ya shafi gefen fuskarshi.
"Allah ya jarabceni da ƙaunarka, Ina fata ka zama alkhairi arayuwata, zan cigaba da yi maka addu'a Allah Ya baka lafiya, bana so in koma ƙasar canada batare da ka buɗe idanuwanka kayi tozali dani ba" cikin sanyin mirya ya ƙare maganar, ba zato ba tsammani yaji saukar yatsun hannun danish acikin nashi wata irin cakuma yayi ma hannun prime minister ya ƙanƙame shi, hankalin Taj ba ƙaramin tashi yayi ba, har ya yunƙura zai raba hannun Danish daga ruƙon da yayi ma Hateem, da sauri ya girgiza mashi kai alamar a'a, komawa yayi ya zauna still hankalin shi bai kwanta ba, idanun shi akan hannayensu dake harɗe cikin na juna, lamarin yayi mugun ɗaure mashi kai ganin mutumin da ko yatsan shi bai iya ɗagawa amma yayi ƙarfin halin ruƙe hannun mai girma Hateem.
Tun da ya kafe hannun Danish dake a ruƙe da nashi da ido, bai ko ƙyafta ba, wani irin yanayi yake ji atattare dashi mara misaltuwa, ga wani bugu da zuciyarshi take yi mashi, gaba ɗaya ya shagala da kallon hannayensu na tsawon awa batare daya ankara da gudun da lokaci ke yi ba
Motsin buɗe ƙofar ɗakinne Yaja hankalin boss ga kallon mai shigowa,