Showing 3001 words to 3533 words out of 3533 words
Chapter 2 - KARFE A WUTA Original Book Complete PDF Writing by Ayshercoll.txt
iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ƙarshe yayi breaking heart ɗina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ɗi na ba kin dai gane"
Sumayya ta ce "Au ke yanzu har wane zaɓe-zaɓe ki ke yi?"
Nabila ta ce "To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma ƴan wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba"
Sumayya ta ce "Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka kuɗin"
Nabila ta ce "Ke uban waye ya ce miki ina da kuɗi?" Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila.
Nabila ta yi ƙwafa ta ce "Zamu haɗu ne, zaki ga wulaƙanci".
***
A hankali yake buɗe jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matuƙa.
Tamkar an jefo shi, haka ya faɗo ɗakin, yana rarraba ido.
A hankali ya ɗaga kai ya kalli wanda ya shigo ɗin, ya mayar da kansa ƙasa ya sunkuyar.
"Allah ya taimaki oga..." Bai amsa ba kawai ya buɗe tafin hannunsa ya miƙa masa.
Wata baƙar leda ya ciro, ya ɗora masa a hannun, sannan ya ce "Sai dai Oga ba a samu da yawa ba, ƴar kaɗan ce, cinnaku sun yi wa kasuwar ƙawanya, shiga da fitar kaya na bayar da wahala, da ƙyar na samu wannan wurin wani ɗan inyamura, ina ga wuri zan canza, saboda kamar ana son yi mini cune".
Bai ce masa uffan ba, ya kwance ledar, ya fito da kwalin wata allura pack guda, mai ɗauke da ampoule na allura guda goma.
Sirinji lamba biyar ya ɗauka, ya din ga fasa alluran yana zuƙa, sai da ya cika sirinjin, sannan ya miƙe hannunsa.
Ya ɗaga kansa ya kalli matashin da ya kawo masa allurar, bai ce masa komai ba, matashin ya bar ɗakin.
Ya mayar da idonsa kan hannunsa, ya yana kallon jijiyoyin da suka kwanta ɗoɗar a ƙarƙashin fatarsa, suka yi ruɗu-ruɗu, manya da ƙanana.
Ya dubi guda ɗaya, ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara bawa kansa allurar sannu a hankali. Sai da ya zuba ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, ya sunkuyar da kansa ya na jiran Sakamakon hukuncin da ya ɗauka.
Sai dai kusan mintuna goma sha biyar, bai ji abun da yake so ba, sai wani irin nauyi da kansa ya ƙara, idonsa ya din ga yi masa yaji, ya rintse idanunsa amma bai ji alamar abun da yake so ba.
Abu kamar wasa kansa ya din ga wani irin sarawa, ƙirjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da hannunsa bibbiyu yana jujjuyawa tare da rufe idanunsa.
Ihu ya fara yi iya ƙarfin sa yana taƙarƙrewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga.
Da gudu suka shiga ɗakin, suka fara ƙoƙarin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da su baki ɗaya ya cigaba da kururuwa.
Ayshercool.
08081012143