Showing 30001 words to 33000 words out of 117763 words
Chapter 11 - ME ZANYI DA ITA COMPLETE By Nazeefa Sabo Nashe.txt
ma kallonsu yake....
*đ€ME ZAN YI DA ITA?*đ€
NAZEEFAH SABO NASHE
FREEđ
08033748387
-19
ELEGANT ONLINE WRITERS....
Ina miâka dâumbin godiyata ga masu karatun littafinnan nagode âkwarai da gaske da soyayyar da kuka nuna min da littafin me zan yi da ita?burina dama saka nishadâi a zuciyarku. Ina alfahari daku I Really appreciated wallahi, da zan iya da na mayar dashi 2pages kamar yarda kuka buâkata, to hakan ba zai yiwuba ina da scheduled da yawa so am sorry kuyi haâkuri dani a hakan har muje inda zamu. Nagode sosai.
**********************************
Aliyu ne ya dafa Imran yana dariya âAmma lallai guy dâin nan ka raina mana hankali yanzu dama mutum biyu zaka aura baka gaya mana baâ Abdul ya girgiza kai yana murmushi yace âwonderful ni bama wannan ba how comes kai da baka son hayaniya ka auri mata biyu ina cika bakin da kake mana na cewa mace dâaya ta isheka?â Yana jinsu duk suna surutunsu ya kasa furta komai zallar tunani da zuciyarsa ta tafi,sai zufa yake tunani yake wacece ita wacece ma wata Aysha da aka dâaura masa aure bai sani ba, tabbas ashe kuwa tayi shirin zama bazawara don sam bai ga dalilin da zai sa ya amince da mace har biyu ba. Koma waye ya bawa dahda wannan gurguwar shawarar. Tsawon lokaci zuciyarsa ta kasa hasasho masa shatu ce yarinyar gaba dâaya zuciyarsa ma bata hasasho masa shatu ba tunani yake a cikin âyaâyan abokan dahda da suka mayance masa cewa suna sonsa aka dâauki dâaya aka bashi. Bai cewa abokansa komai ba duk da surutan da suke masa, burinsa yaga dahda ko Ammar amma ba dâaya da ya gani,hakan yasa dole suka shiga motocinsu suka tafi masauki.Imran dai ya zama tamkar mutum mutumi.
Amarya shaheedah kuwa a bakin yayyenta maza da suka dawo dga dâaurin aure ta samu labari.shaheed da ya shigo a rudâe ne ya dafa ta murya can âkasa yace âHow comes shaheedah duk cika bakin da kike yi ba zaki zauna da kishiya ba sai gashi ko tarewa ba kiyi ba angonki ya auri wata zai hadâa ta dake.â Shaheedah da bata dâau zancen serious ba ta zabga masa harara âGod forbid don Allah shaheed ka daina wannan wasan bana son sa as per as am alive ko kallon âyan mata ba zan bar habibi yayi ba balle kishiya over my death bodyâ shaheed murmushi yayi kafin khalil âkaninta yace âai kuwa kin makaro don kuwa mata biyu aka dâaurawa aure da habibinnaki ke da wata Aysha.â Da sauri shaheedah ta miâke tana kallonsu âplease don Allah kuce min wasa kuke?what a nonsense?â Khalil da shaheed suka sake tabbatar mata haka nan sauran mutane da suka je dâaurin aurenma suka tabbatar mata,dalilin da yasa ta yanke jiki ta fadâi, tuni nmufashinta ya dâauke,hakan yasa da sauri aka rufu akanta ana âkoâkarin ceto ranta.
âYan kano kuwa tuni labari ya riski zainab ta hanyar mutane masu sanar da ita fadâuwar shaheedan da dalilin fadâuwarta ta.cikin tsananin mamaki take cewa âmata biyu a haba dai ba kuji da kyau ba idan kuwa hakan ya tabbata tabbas duk wacce tayi âkoâkarin zama kishiyar shaheedah tayi shirin riskar baâkin cikin da zai zama ajalinta wallahi.â Da sauri ta miâke ta nufi General parlour inda Hajja take.tun kafin ta furta komai hajja ta tabbatar da ba lafiya ba don yanayinta ya nuna âkarara. Da sauri Hajja ta miâke da niyyar ta jata su samu sirri don ganin dada a zaune da itama ta kasa ta tsare, amma ina zainab tuni ta furta abin da ya riâke mata maâkogaro âHajja da gaske ne? Da gaske ne Imran mata biyu aka aura masa da wata wai Aysha wacece ita?â Gaba dâaya gurin zaro ido su kayi, musamman Hajja da maganar tayi mata dirar mikiya, da sauri ta girgiza kai âwannan ba gaskiya bane ba yarda zaâayi manga ya zartar da wannan hukuncin bai gaya min ba sharri ne da surutu irin na dâan Adamâ zainab ta girgiza kai âHajja babu fa batun sharri a wannan zancen itâs true naji a bakunan da ba zasu min âkarya ba kuma sun halarci dâaurin auren ga shaheedah canma ance ta sume daga kin zancen.â Hajja ta ja ta zauna jaâbar a kujera âTo wacece yarinyar aka ce miki idan kuwa zancennan ya tabbata tabbas manga zai ga âbacin raina kuma Imran dole ya saketa koma wacece zancen banza zancen wofi kenan, ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa.â Mommah dake zaune murmushi kawai take zubawa ta tabbata yau gidannan akwai show idan har suka san wacece amaryar.tana kallonsu suka shige dâaki bayan hameedah ta tunatar dasu zancen a sirri ya kamata ayi shi.Mommah ta taâbe baki a zuciyarta tace âoho dai burina ya gama cika.â
Kowa burinsa Dahda ya dawo yaji ya gaskiyar lamarin yake.ko su Hajiya Mama mommah bata gayawaba ta ja bakinta tayi shiru tana jiran kowa yaji labarin kamar dirar mikiya tunda ta lura har yanzu basu san da shatunta aka dâaura aure ba.
Shi kuwa Imran yana can asibiti ya tasa shaheedah gaba da kallo da take ta kuka bayan farkowarta,ta kuma tabbatar da lamarin gaskiya ne.sai ga Imran ya âbige da jinya madadin hotunan dâaurin aure da suka ci burin aiwatarwa,irin dai wanda ake yayi a social media dâinnan.
Kukan take sosai da har ya âkarawa Imran zazzafan ciwon kai,ya kama kannasa ya riâke tun yana rarrashin ta da yi mata rantsuwar ta kwantar da hankalinta koma wacece idan ya tabbatar da auren sakinta zai yi kuma da gaske yake.amma ina shaheeda bata ji shi ba,hakan yasa kawai ya kama hannunta yana murzawa alamar rarrashi idanunsa a lumshe. Haushi ma lamarin ya bawa abokansa yanda take kuka kamar a kanta aka fara kishiya.Tsawon lokaci sannan aka sallamesu bayan ta gama shan drip.ana komawa gida Abbanta yace ta bari ta warware a kaita. Suna keâbewa da Imran tace yace kawai a kaita please Imran anty na nake son gani kawai ko zuciyata tayi sanyi.â Tausayinta yasa Imran gayawa wata âkanwar babanta cewar a kaita kawai ta âkarasa warwarewa a gidanta.
Haka kuwa aka yi babu âbata lokaci aka tafi airport dama sun yi booking jirgi.amarya dai ta tafi fuska âkozai-âkozai fuska ko kwalliya babu duk da burin da aka ci na budiri a wannan ranar.
Ana kaita ko ta kan mommah da danginta ba abi ba duk da tunasarwar da dangin ubanta suke musu amma Hajja âkememe taâki yarda tace âku shige da ita dâakinta mai aka yi aka yi wata dijah balle danginta wa ya san surkullen da suka yiwa manga ya dâaura masa aure da wata yarinyar.ku kaita gurin uwarta ni ina nan ina jiran shigowar manga tunda yaâki dâaga waya ta.âhakan yasa ba wanda ya sake bi ta kan uwar miji duk da alâada ta sharâanta a bata damarta a kai mata matar dâanta. Hakan sam bai damu mommah ba tunda burinta ya cika.
Shi kuwa ango Imran yana cikin dâakinsa zuciyarsa sai suya ta keyi shi mamakinsa dâaya dama ana yiwa namiji auren dole? Yana jiyo abokansa suna ta dariyar shegantkarsu.
SHIGOWAR DAHDA**************
Yana dawowa ya tarar Hajja da jamaâarta baje a parlourn,gefe dâaya ga Dada da tata jamaâar,zancen dai ya san ake hakan yasa bai san lokacin da murmushi ya kuâbuce masa ba ya san sarai zaâa rina,Dijah ta jawo masa rigima yau,da bai san yarda zaiyi solving dâinta ba. ya durâkusa ya gaida su Dada sannan ya âkarasa gefen hajja ya zauna, Da kyar take amsa gaisuwar da yake mata tana gama amsa gaisuwar ta dâora da âmeye gaskiyar labarin da naji game da aure biyu da akace an dâaurawa Imrana,wacece yarinyar da har ni ban isa kayi shawara dani ba?â Manga waigawa Yayi yaga Dijah bata wajen don haka ya ciro wayarsa ya kira ta yana kallon hararar da Hajja take masa ya cigaba da kiran Imran shima a waya,so yake su hallara duk ayi komai a gabansu. Tsawon mintuna mommah ta shigo da su Hajiya mama, sai ga Imran shima ya shigo jikinsa a sanyaye, ya zauna a gefen mommah, haka nan zainab da su shaheedah su hameedah suma duk suka bayyana.
Sannan manga ya gyara zama ya fara da âkamar yarda kuka saka Imran da shaheedah soyayya har suka amince da junansu suka âkaunar junansu haka ita ma Dijah mahaifiyarsa ta buâkaci son a hadâa Auren Imran da shatu yarinyar wajenta.........
Idanu waje kowa yake kallonsa cikin tsananin mamaki.Imran kuwa zama yayi kamar statue yayi masa âkuri da ido kawai yana tunani shatu shi aka aura ma Shatu,shatun dai da ya sani âkazama shi kuwa mai zai yi da ita a yanzu ba sai anjima ba zai saketa wallahi yaushe zai iya wannan abin kunyar mai zai cewa mutanen da yake cikawa baki yana fadâin mai zai yi da ita? Ita kuwa shaheeda tuni ta zube a jikin hameedah ta ma kasa kuka sai sakin ajiyar zuciya take.
Imran murya na rawa ya fara roâkon Dahda âplease dahda wallahi bana sonta ko kadâan kada kuyi min haka zaku sa min attack wallahi don Allah ka amince Na sake ta.â âWallahi Imran ka sake Na saki shatu sai dai ka sake uwa don wallahi sai na zare ka daga cikin âyaâyana Na gaya maka kada ma ka fara attempting zancen saki idan kuwa haka ta faru zan nuna wa kowa bad side dâina wallahi an kaini âkarsheâ sosai kuwa yake kallonta saboda yarda take maganar da gaske take daga âkasan zuciyarta take fitowa, ranta a âbace idanunta kuwa yayi jajir.
Sai ji su kayi Hajja ta saki dariya muryarta a sama tace âAi kuwa ba ki isa ba dijah ni kuma zan nuna miki nice uwar manga ko ki amince ya sake ta ko kuma ni na saka manga ya sake ki.......
*đ€ME ZAN YI DA ITA?*đ€
NAZEEFAH SABO NASHE
FREEđ
08033748387
-20
ELEGANT ONLINE WRITERS.....
âBabu wanda aurensa zai mutu saboda son zuciyarki,ashe abinda kike aikatawa kenan a gidan dâanki Hindatu duk abinda kike ciki labari yana zuwar min,kamar na san hakan zata faru nace a kawo ni nan dâin kafin na wuce gida na, gaskiya Hindatu kin bani mamaki kuma sam ba jinin yâar uwata ce a jikinkiba ita dâin macece mai kara mai mutunci mai yakana da alkunya idan Banda ma zamani mai ya kawoki gidan dâanki saboda abin kunya kuma kizo ki saka matarsa a gaba da rashin mutunci saboda siyawa kai raini,to bakin ki ya mutu anan wajen,aure dai ya dâauru kuma ba mai warwareshi manga ya sanar dani komai,don mai ita ba zata yi iko da dâanta ba alhali kema da naki dâan kike iko babu wacce zaka saki a cikinsu duka matanka ne kuma ban amince da saki ba zancen banza zancen wofi wa yace maka ana sakin mace haka kawai,to kada in sake jin makamancin wannan zancen, duk abinda kuke ina zaune ina jinku dama don inga kamun ludayin kowa shi yasa nayi bakam a waje na zauna, to hindatu naji duk tijararki.âsai a sannan dattijon arzikin yaja ajiyar numfashi ransa a matuâkar âbace yana kallon hindatu (Hajja yau dai munji sunan hajja na gaskiya a bakin kawunta kawu saâidu)Hajja tana shakkarsa sosai don duk dangi yanzu shine babba shine kuma mai fadâa aji, gashi dama mafadâaci ne baâa kuma isa yace ga abinda zaâayi ba a canja ba, kaifi dâaya ne kuma wargi yake dai-dai âkugun ko wani jaâiri. Parlourn shiru yayi kowa yana jin kawu yana ta fadâa Hajja zuciyarta sai tafasa take, tabbas kawu ya kawo mata cikas kuma sai taci uban manga da yaje ya sanar dashi. Kawu yayi fadâansa son ransa sannan ya kalli Imran âNa jiyo gareka ko gaba naji magana makamancin ta rabuwa da zaâbin uwarka sai naci mutuncinka,wa ya gaya maka ana jayayya da maganar uwa? Kada in sake jin haka ba and mamaki abinda ta hango kai baka hangoshi ba.â Haka ya gama fadâansa ya kuma ce gobe ana gama biki Hajja ta hadâa karonta ta tafi kada kuma ya sake ganin âkafarta a gidan dâanta ba da wani muhimmin daliliba.
Shatu kuwa tana can dâaki bata san budirin da ake ba, tana kwance saman bed dâin mommah da wayar mommah a hannunta tana buga game. Har sai da anty nahna ta shigo murmushi fal fuskarta ta dafa shatun âAmaryar Imran.â Shatu ta miâke zaune hankalinta na kan game tace âmai tayi amaryar tasa? Nahna tsaki tayi tace âakwai wata amaryar bayan ke.â Sam bata dâau zancen serious ba don ko a mafarki bata taâba sawa zuciyarta Imran ba balle har tayi tunanin zama amaryarsa tsokana ce dai irin ta Anty Nahna ina ita ina Imran da ko inuwa guda basa hadâawa. Shigowar mommah da fadâa da mitar Hajiya mama ne yasa su kayi shiru da zancen fadâa take tana âkarawa âHaba addarsu ai wallahi kin yi wauta ta ina aka taâba wasa da aure anyi magana kince wai nuna musu iko za kiyi to ikon me ki jefa yara cikin matsala, yaushe shatu ta isa aure fisabilillahi nawa shatun take? Ai shirme dai kinyi shi wallahi kuma ina jiye miki fadâan Babanku kin saka yrinya a matsala ke baki fita daga ciki ba kin jefa yâarki a ciki wannan dangin mijinnaki da ba kirki bane dasu.â Shatu dai miâkewa tayi daga kwancen da take tana kallonsu dâaya bayan dâaya wai mai take ji ne? Ita dai shatu aka dâaurawa aure da Imran da take ji duk duniya ba wanda ya kaishi tsanar ta ina ita ina Imran dâan gayu mai ji da kansa? Muryar Dada ce ta dawo da shatu duniyar su mommah tana jin Dada ta fara masifa âAh to ni ban ga laifin dijah ba ai maganin shege dâan banza yanzu Na san ashe Dijah jini na ta dâauko, ba naki ba soloâbiyo da abinda kika sani sai haâkuri,yo akan me? Wani shegen yayi mata naâkudar dâan sun dâauki wata âkanjamammiyar mata sun bashi, bayan a haka an zauna ana yi mata isa da iko da fankamar banza sai kace a kansu aka fara arziki ko da yake baâko a arziki shi yake nuna shi wani ne. Yanzu kuwa da tayi musu haka ai sa san annabi ya faku, to ina dalili idan ban da tsiya ma ace âyar kishiyarka dâanka zai aura ban taâba ganin wannan iskancin ba sai a dangin mijin dijah.ai gasu can dai wancan jarababben kawunnasu ya kashe bakin tsanya yayi min dai-dai wallahi.â Hajiya mama shiru kawai tayi tana jin fadâan Dada.ita kuwa shatu tayi zugum ba tare da ta san mai âkwaâkwalwarta zata tuna ba.wai ita shatu âyar âkaramar nan aka yiwa aure? Lura da haka da mommah tayi yasa ta isa bakin gadon ta kamata,rungumeta tayi a jikinta tana shafa bayanta âkwantar da hankalinki daughter na ba yanzu zaki tare ba sai kin girma kin gama karatu sannan zaki tare kin ga ko ai da dadâewa.â Sai sannan shatu ta saki ajiyar zuciya tana dariya ta rungume mommah. Gaba dâaya dâakin murmushi su kayi banda Dada da ta âbata fuska cikin masifa tace âzancen wofi kenan kaji shashancin banza shikkenan ita kuma sai ta âkare a gantale a titi to ba zai yiwuba yanzun zata tare mu da akayi mana aure yaushe muka kaita yarinya ta fara âkirgar dangi sannan ace wani sai ta girma yo girma na me? Kin san da hakan kika dâaura mata aure, to ban amince ba a sada ta da dâakin mijin ta cikin mutunci da kima wallahi kafin ayi abin kunya yayi mata ciki a gadonki.â Gaba dâaya dâakin kunya ce ta kama su wannan sakin baki na Dada, murya can âkasa mommah tace âTo shikkenan zata tare amma ai sai an gama shirya mata abinda zaâa kaita dâaki dashi ko?â Dada ta miâke tana fadâin âTo shine zance amma kya ajiye budurwa zangangan a gaba kice wani sai ta girma,girmo nace ba girma ba.â ficewa tayi tana âkananun mita. Hajiya mama fuska ba walwala tace âBa dai maganar Dada zaki bi ba na tariya ban amince da wannan shashancin ba ki bari ta girma ta san ciwon kanta tukunna.â Mommah dâaga mata kai tayi kafin tace âko dâaya Na dai amsa mata ne don mu huta da mita kafin ta tara mana gayyar jamaâa ba wani tarewa da zata yi sai ta gama makaranta tsaf tukun.â Hafsa tace âwannan shine dai-dai wallahi Addarmu gwara ma da kika yi maganin mutanen can haba ikon yayi yawa.âhaka dai aka yi ta tattauna zancen har Ammar da Hisham suka shigo hundred percent sun goyi bayan mommah.
Shi kuwa ango yana can zuciyarsa tamkar ta fashe bakâin ciki ya gama cika shi.yana ji abokansa suna ta tambayarsa wacece Amaryarsa ta biyu amma ya kasa basu amsa,sun lura ransa a matuâkar âbace yake don haka suka kyaleshi suna cigaba da shirin dinner shi kuwa ko kallonsu bai yi ba balle ya nuna alamar shirin.
A can âbangaren Amarya an sha baâkin gumurzu kafin ta haâkura ta saduda bayan mahaifiyarta ta tabbatar mata ko za tayi yawo tsirara sai ta raba auren Imran da wannan mai kama da bararojin.hakan yasa ta share hawayenta ta fara shirin dinner don mai kwalliya Nashe glam wato khadija Nashe tazo za tayi mata, kafin a fara kuwa tace bari ta je ta ga angon.
Cikin part dâinsu ta shiga duk da abokansa da suke zaune damâkar a parlourn bai hana ta kutsa kai ba, ba tare da wani shakka ba tace musu âsannunkuâ Gaba dâaya suka amsa ta dubi Ali da shi suka fi dâan sabawa tace Imran fa?nuna mata cikin bedroom yayi yana sakin murmushi a zuciyarsa yake tunanin ko mai Imran zai yi da wannan ai shi cetonsa aka yi da aka bashi wata duk da waccen dâin ma basu san wacece ba. Suna kallo ta shige uwar dâaka ba tare da shakka ko kunya ba Amarya ta kawo kanta kenan sabon salo abdul ya fadâa yana dariyar shaâkiyanci.
Tana shiga ta tarar dashi kwance a rigingine saman carpet idonsa a lumshe da alama dai ba barci yake ba,zama tayi a gefensa tana jan yatsun hannunsa, a hankali ya budâe idonsa yana ganinta ya dâan saki murmushi tare da miâkewa zaune ya jawo ta yayi mata kyakykyawar runguma ita ma âkanâkameshi tayi kawai ta