Showing 33001 words to 36000 words out of 126095 words
Chapter 12 - DAUDAR GORA BOOK 1 (CiKI KA SHATA) COMPLETE .txt
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_14_*
.........Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai bayan mutuwarta suzo jana'izarta batare da ko kan gawarta an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo kashetane.
Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa, dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi....
Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai, sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai babban muƙami da matsayi....
“Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.
Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin, “Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama (baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a gareki”.
Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu mata guda biyu.
“Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a yanzu”.
Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta cigaba da yin addu'a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan ƙasar ta Ruman keda ya bayyana.
“ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine na wanka”.
Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga ƙoƙarin binta da suke.
Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su kuma gyara miki kai kawai su fito”.
“Karki damu zanyi da kaina”.
Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu, sai dai bakinta ɗauke yake da addu'a. Wani irin harbawa zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi, yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu takai saman kanta tana karanto addu'a bayan ta shiga toilet da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau'inkan ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan halin da suke ba a yanzun suma....
Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa, sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi. Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.
Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama kanta a ƙasa, tun'a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar da nuna bayanta.
Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi. “Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.
Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai. “Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.
Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta kasancewar bana ɗazun bane.
“Dan ALLAH ku miƙe”.
Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk da ƙanƙantar ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.
Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba. Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko da takejin tsantsenin gani a jikinta.
Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka....
“Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin kumallonki”.
Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”.
Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Ki gafarceni ranki ya daɗe. Wannan suna bai dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”.
(Ya rabba).
Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar. Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da ita.
“Bani zan sha ba ai mama naki ne”.
A wani irin matuƙar hargitse Diwa ta ɗago tana duban ta, jikinta har wani karkarwa yake. “R....ran...ki ya daɗe w...w..wan nan ai ba hurumina bane”.
Iffah data kafeta da idanu ko ƙyaftawa batayi ta janyesu a hankali tana mai miƙewa abinta batare da tace komai ba. Da sauri Diwa ta ƙara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki ya daɗe dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai anan umarnine”.
Bata zauna ɗin ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma ɗakin da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba suka iso da wata hamshaƙiyar riga mai kamar alƙyabba daga Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa. Addu'a ta shiga ambato a zuciyarta har suka kammala saka mata ƙawatacciyar rigar alƙyabar mai tsananin ado da ɗaukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su.
Kallon juna sukai, kafin ɗaya tai saurin faɗin cikin ƙanƙan da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”.
Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na wannan bata san wacece autar Babiy ba ta ɗauke kai. A karon farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen ƙarfin zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina ne bana buƙata. Sai kumuje umarni na gaba”.
Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama ɗarsuwa a zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar wadda aka jefa da narkakken ƙarfe taji yafff! A ƙirjinta. Da sauri ta dafe ƙirjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta ya farayi ya sata zubewa ƙasa tana mai ƙoƙarin ambaton sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naɗe zuciyartane da harshenta a lokaci guda......
Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na matuƙar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta miƙe da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin da Iffah take. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yay damm. Innalillahi..... ta shiga ambata dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci ta jiƙe sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta na hadima hanunta ya taɓa Zawjata-almilki. A daburce tai waje da nufin isar da saƙo ga Malikat Bushirat duk da bata da tabbacin samun iso cikin sauƙi........✍
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*Mg's skincare
Kunji takennan kunsake jinshi shin yar'uwa nace wai haryanzu baki jaraba products dinsu ba😵💫yar'uwa mace fa yar ado da kwalliyace koda kina dakyau akace kikara da wanka😍sufa kayan mg's basa bleaching duka kayansu 💯 natural ne sannan organic zasu gyara sukuma goge Miki jikine kawai yakara bayya ar da ainihin zallar Madarar kyawun halittar da Allah yayimiki🥰
Wai kinafama da pimples da spot afuska amma haryau baki nemi mg's ba🤔duk Mai tantama akan kayan gyaranjiki yacire mg's domin babu shakka sudin na dabanne indai problem dinki matsalan fatane yar'uwa kijaraba koda soap dinsu bi'iznillah zaki godemin👯♀️kayansu ga kamshi inkinjaraba kinga yanda suke na tabbatar bazakiso su Yanke Miki ba🤩08062991549 anatayi Baku sisters kusamu kugwada koda b duka kit din na gyaranjiki ba zakuga sauyin da fatarku zata samu cikin lokaci kalilan🥳jikin yazama so fresh ko Ina kikashiga kita glowing fatarki na walwali kamar madubi😘keda kanki zakina burge kanki balle wasu🤗08062991549
Adade anayi sai gaskiya sannan siyan nagari Maida kudi gida ❤️
Duk Mai bukatar products din mg's kutuntubi wadannan numbers din domin tasune kawai zaku samesu🙏
Chat 08062991549
07046881166,07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Team glow🧖♀️
Yauwa nace ba masu bukatar zuma original munadashi mekyau ba hadi Mai bukata yayimin mgn 08062991549
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_15_*
...........Ilai kuwa, duk yanda Diwa taso isa ga Malikat Bushirat akan lokaci hakan ya gagara, dama tasan ba abune mai sauƙiba. Amma kuma ƙin isar da saƙon a lokacin daya dace tamkar sakacintane. Zata kuma iya fuskantar kowane irin hukuncin da babu mai mata uziri a cikinsa...
A dai-dai lokacin da Diwa ke ƙoƙarin son isa gaban Malikat Bushirat ƴan uwa ga Malikat ɗin na can sun doshi sashen Iffah domin kai kayan al'ada da akema kowace Zawjata-almilki da zata saka kafin a wuce da ita wajen taron buɗar amarya da duk wani babba mai faɗa aji a daular ruman zai halarta, wanda kuma akaf matan Tajwar Eshaan ɗin da suka shuɗe huɗun farko ne kawai akaima wannan bikin sai Iffah a yanzun. Anan zata san kowa, kowa kuma ya santa. Tafe suke tare da rakkiyar hadimai masu ɗauke da wata lafiyayyar rigar alƙyabba mai tsananin ɗaukar hankali da aka ɗinkata ta musamman domin Zawjata-almilki da kuma wannan rana. Sai sauran kayan ado irin na hamshaƙan mata da akayisu da zallar zinare da diamond.
Sun ɗanyi mamakin rashin samun kowa a sashen, saboda sanin tunda safe an turo hadimai da zasu mata hidima. Yanayin tsaftar sashen kuma ta tabbatar musu hadiman sunzo. Tunanin ko itace ta sallamesu ya sakasu ture zancen a zukatansu suka bama cikin hadiman umarnin wata ta nema musu iso. Har hadimar ta nufi ɗakin da aka kai Iffah jiya ta tsaya cakk sakamakon wani irin kakari da sukeji tare da ɓarin fashewar abubuwa. Su dukansu dubansu suka maida ga ƙofar, da alamun mamaki ɗaya daga ciki ta sake bama wata hadimar umarnin zuwa ta duba. Minti ɗaya baima cika da shigar hadimar ba ta dawo a guje numfashinta na fita da ƙyar tana nuna ɗakin da faɗin, “Z...Z....Zawjata-almilki!......”
A kusan tare suka afka ciki. Su dukansu babu wanda bai firgita da ganin Iffah dake layi hanunta na dama dafe da ƙirjinta tana laluben hanya dana haggu ba. A dalilin laluben ne taketa faman zubda abubuwan da aka ƙawata adon ɗakin da su. Sakamakon hakan kuma duk ta jima hanunta ciwo sai jini yake yi. Da zafin nama ɗaya daga cikin matan nan ta riƙota cikin jikinta suna mai ambaton sunan ALLAH a tare. Ganin yanda ta jiƙe sharaf ga jikinta yayi jajur abinka da fara sai hankalinsu ya ƙara tashi. A fisge Iffah ta damƙo hanun matar ta haɗa da nata takai kirjinta tana fadin,