Showing 9001 words to 12000 words out of 25118 words

Chapter 4 - YADIN MAGE Book Complete writing by oum yasmeen .txt

Allah gidan ta sannan mahaifiyar samha kasheta akai ya kamata ma abinciken wanda suka haura musu gida suka kashe ta sannan,




Ai kafin ya ƙarasa lauyan Alhaji Kabiru ya tashi yace




"Ya me Shari'a duk wannan ba gaskiya yake faɗi ba yana ƙoƙarin fitar da wanda ake zargi ina neman alfarmar wannan kotu da ta bani ikon gabatar da shedata ta gaba wato malam idi dillali wanda shi ya siyar wa da Alhaji Kabiru gida kuma ya ce a nemo yan haya ya nemo wannan mutumin ya sa shi,




Ɗago wa yayi yace




"Kotu ta baka dama,




Baki abba ya saka ganin amininsa malam idi dillali duniya ina zaki damu yanzu ya yarda ya goyi bayin ƙarya shiga wannan gun yayi ya tsaya ya dauke ido daga kallon abba yace




"Ni ne malam idi dillali Ni na siyarwa da Alhaji kabiru gida sannan na dauko malam sulaiman ya zauna haya duk shekara sai nazo akan ya bani kuɗin haya sai yace bashi da shi har na gaji da zuwa ganin suna ƙoƙarin cin yemai gida na bashi shawarar ya kai su kotu a karɓar mai gidan sa ,




Alkhali ne yace ya koma sannan ya dubi jama'ar kotu yace zai tafi hutun rabin awaya ya buga gudumar sa




_____________________ *ABUJA*




Cikin sirri aka zo aka dauke shi sai unguwar osokoro abuja lumshe idanuwansa yayi tambas kowa yabar gida gida yabar sa gaban wani tafkeken gida motar ta tsaya tayi horn aikuwa kamar jira ake gate man ɗin ya buɗe mai gate iya haɗuwa gidan ya haɗu gidan shiru ba kaji inhun komai sai na tsuntsaye


ga wasu irin flowers masu kyau koraye shar da su A parking space aka sauke shi fitowa yayi yana tako cike da izza gaban wani ƙaton apartment ya tsaya gabaki ɗaya gun glass ne ƙofar tana jin hucin mutum take buɗewa


wani haɗadɗan floor ya shiga ga kyau ga tsaruwa ga wasu irin luxury sofa masu kyau assalama wata kyakkyawar matace tafito fara tas da ita fuskarta cike da fara'a tace




"Wa'alaikassalam mu'aruf,






Murmushi ya sakar mata yace




"Ammi na samike lafiya qalau,




Cikin so da kaunar ɗan nata tace




"Wallahi lafiya qalau ya hanya ?,




Zama yayi yace




"Alhmdllh,




Dinning room ta nufa ta ajiye stainless steel flask ɗan gidan vacuum sannan ta fito ta dawo floor ta zauna tace




"Wanka za kai ko kuma zaka tsaya kaci abinci,




Tashi yayi yace




"Ammi bara inyi wanka inna tashi daga bacci naci auta tana makaranta ko ,






Eh wallahi ai sun kusan hutu ta dawo gida




Ma'aruf yace






"Allah ya temaka,






Amin tace








Raƙiba ce ta shigo sanye da abaya shuɗiya yar gidan kahu saminu da nazifa sai hura hanci suke kai kace ya'yan wasu ne shigowa sukai shi kuma har yabi hanyar da zata sada shi da ɓangaransa zama nazifa tayi tace




"Ammi kamar ƙamahin turaren ya jj nashi ya dawo ne ,




Zuba mata ido ammi tayi yawa me karantar wani abun sannan tace




"Eh ya dawo,




Wata irin murna ce ta kamata raƙiba tace




"Amma ammi tun safe baki faɗan ba inmai abincin tarba,




Ammi tace




"Aikin san baya cin ko wanne abinci shi yasa tana kai wannan ta tashi bata fatan ko sau daya mu'aruf ya aure ɗaya daga cikin ya'yan baffaninsa saboda ita ta sani wataran zasu iya harar ransa ba son gaskiya suke mai ba abin hannun sa suke so,


tafi so ya aure wacce bata san waye shi ba




_______________ *kotu*






Alkhali ne ya dawo daga hutun da ya tafi yace






"Duba da irin hujjujin da Alhaji kabiru ya kawo nawa ba malam sulaiman kwana ɗaya tak ya tashi ya bashi gidan sa sannan zai biya shi tarar dubu talatin da hudu,




Jirine yake neman zuwar da abba nima da nake zaune kuka nasa tambas yanzu mutane basa tsoran cin haram wannan wacce kaddara ce haka ɗaga hannu tayi hawaye na bin kuncinta tace






"ya Allah mu bayin kane baka barin kuma zalinci kai me adalci ne Allah ka saka mana ya Allah kazamu gatan mu bamu da gata sai kai,




Wani ne ya juyo ya kalle ta tausayi ta bashi tashi yayi ya zura hannunsa a aljihu yace






"Ungo ku biya tarar da ake bin ku ,






Hannun samha na karkarwa ta amsa tace






"Nagode Allah ya saka da alkhairi ya jikan mahaifa ,






Amin yace ya yatashi ya fita daman ya kan je kotu me gidan sane yake aikensa ya biya tarar wanda yasan bashi da shi......✍️




*YA ƊIN MGE*






_story and writing_


_by_




*Oum Yasmeen*








*Part37-40*






Bayan sun biya suka fito akafa suka ɗinga tafiya har unguwar su shiga gida sukai zama samha tayi ta zuba tagumi tace




"Abba kar wannan ta tada maka da hankali kai haƙuri komai me huce wane ,






Kujera ya ja ya zauna yace






"Samha wallahi Ubangiji ya yaye min damuwata insha Allahu komai zai dai daita shi kuma yaje shi da Allah bana ko tantama cin hanci suka bawa alkhalin sai dai sun manta da cewa ita dukiyar maraya yaɗin mage ce wataran sai yayi amansa ta saniyar haka ma zata iya cinye arzikinsa ,




Ajiyar zuciya ta saki tace




"Abba yanzu sai mu haɗa kayan mu tafi kan karofi ko ,






Tashi yayi ya ɗebo ruwa sai ayanzu yaga kofar inna hajara a rufe girgiza kai yayi abin hajara ya ishe shi yawa yawa taci kafar kare yace




"Bara hajara ta dawo sai itama ta haɗa kayanta,






Tashi tayi ta shiga ɗaki hawaye ne ke bin fuskarta




Haiye yaraye iye nanaye takun bana yafi nabara saki ɗan yaƙe haƙura naji kina takun kasaita tafiyar bata chanza zani ba shigowa tayi bako sallama turuss tayi ganin malam ya zuba ta gumi tace






"Bar ta gumin nan daga gidan Alhaji kabiru nake yace zai siyar min da gidan nan kaga sana'a tayi zaman banza kuwa ai yanzu anga ribar sa ko ta sheƙe da dariya ta shiga ɗaki a guje ta fito tana gyara daurin zaninta tace




"kan uban can tab yasin in nayar da meta tsina ya dawo duniya wato Ni zubi zata yiwa haka yasin ko ita takawo son kuɗi duniya sai ta bani zanin ta na kuncewa tana ƙara soke shi ta fita tana babbami ,


Tashi yayi ya shiga ɗaki yace






"Samha haɗo kayan ki mu tafi ban ga alamon Hajara zata biyuni ba we siyan gidan xata yi ,






Tashi tayi tace






"To, har hada kayan suka shiga yi ya dau wasu samha ta dau wasu suka fara tafiya daman ba wani shirgene da suba






______________________




Ma'ruf na yarda Allah ya baka sa'a




Amin yace ya tashi ya fita a floor ya tarda raƙiba da nazeefa ko wacce harkar gaban ta take har ƙasa suka durƙusa suna gai da shi ciki ciki ya amsa ya fita yana fita ya samu wanda zai kai shi airport yana jiranshi shiga yayi ya zauna a kujerar me zaman banza aiki yake a system ɗin sa har suka isa be gama ba rufewa yayi ya fito




baya tafiya tare da mutane ba shi yasa kowane ya san sa ba sai de sunan sa da ya karaɗe duniya baya yarda yan jarida suyi hira da shi picture ɗinsa ma ba ya yarda ya shiga media ba we baya yi bane a'a yana hi yana kallo meke wakana


Akwai ma wani hira da ya gani ana hira da yan makaranta ana tambayarsu we in jj ya baka dama ka rubuta adadin kuɗin da ake son nawa zaka rubuta sosai yayi dariya har da ce wa gabaki daya kuɗin dake account ɗinsa zan rubuta kayan sa wani ya zo ya karɓa haka akai tayi


sosai son duniyar mutane ke bashi mamaki Basu san ya akai ya sami kuɗinsa ba basu san wahalar da yasha ba kawai dukiyar suke hange






tafiya yake yana bin bayansa kai tsaye reception ya nufa bayan ya ɗan wani rubuce rubuce ya ɗauko dalar America besan iya adadinsa ba ya basu su rabawa duk wanda ke airport ɗin ya shiga jirgi nan fa yan jaridu sukai dirar mikiya kash sai de daukar pictures ɗin jirginsa sukai nan fa wani dan jaridar c.r.l yace




"Ayau munyi rashin sa'a ba mu tarar da j.j ba amma zaku ga photo jirgin da ya hau munyi ƙoƙarin jin ta baki detractor manager na airport amma be fada mana inda yaje ba assali ma yace we besan da zuwansa ba shin me zaku ce da j.j ,






Nan fa labare suka karaɗe duniya kowa na fadin albarkacin bakin sa wasu ma cewa suke ba mutun bane wasu suce kawe bashi da kyakkyawar kamane wasu cewa suke wasa yake da hankali mutane akai kuma masu fatan alkhari






*Nikwa nace lol nagan sa Nima na karɓi nawa kuɗin😁😁💵💵💵*


*YA ƊIN MGE*






_story and writing_






_by_






*Oum Yasmeen*






*Part41-50*






*KANO TA DABO TUNBIN GIWA*




Karfe shidda na yammaci jirgin sa yayi durar mikiya a filin tashi da sauka na malam aminu kano international airport fitowa yayi ruƙe da briefcase ɗinsa tsaya wa yayi wani matashi ne ya matso kusa da shi ya karɓi kayan sa yace




"Barka da zuwa sir,




Amsa wa yayi yayi gaba buɗemai mota yayi yashiga tuƙi ya fara matashin yace






"Yanzu ina za'a kai ka ,






Glasses ɗinsa ya zare yace






"Kai ni tahir guest place Tahir ,




to yashi kai shi yayi yace






"Tsaya in fito sai muje gidan naku,




Okay sir yace




Kayan sa ya ajiye yasa wasu kayan fitowa yayi cikin sauri matashinnan yafito yana sakar baki yana kallonsa ganinsa yayi yawa be taɓa sanin dadin kuɗi ba ko shi yafi shi kyan gani kayan nan sun ƙoɗe duk sunbi sun ɓole ga sumar sa duk ta cukurkuɗe wandon ma ya ɗage mai ga wani matatcan takalmi yawa kofato yace






"Wallahi oga ban gane ka ba,




Murmushi yayi ya shiga ba tare da yayi mai magana ba shima be damuba sanin da yayi shi ba me magana bane wata matatciyar waya ya ɗauko ya sa wani lahi duk an ɗaureta da ƙyeuro ya ɓoye babbar wayar sa ajikin sa yace






"gobe sai ka kaine inda zan dauki hayar napep ,


To yace


gidan su dake jakara ya kai shi Assalam sukai har ƙasa ya ɗurƙusa ya gaishe da mahaifan sagir masawa sukai cikin mutunci ni'ima ce ta shigo sanye da doguwar riga da mayafi Zata kai shekara ashirin da daya gaidashi tayi tana ya mutsa fuska yawa taga kashi sagir yace






"Inno ga Ma'aruf zai zauna a shagona kafin yasa mi kuɗin kama shago daman tun sauran sati zuwansa na faɗa muku,






Yaya ne ya washe baki da yake haka suke kiran mahaifin nasu yace






"Ba matsala Allah ya kai mu lafiya yaro a kula aruƙe gaskiya da amana insha Allah zakaga ancin ma gaci komai zai zamo tahiri kaga abin da ke hana mutanen mu ci gaba rashin riƙe gaskiya da amana


suna da babbar illar dan Allah kuma a ruƙe imani kar ka ga ba kowa naka kace za kai abin da kaga dama Allah yana ko ina ko dan mutuncin kan mu ya kamata mu tsare imanin mu ,




Sosai yaji dadin nasiyar mahaifin sagir daman har yanzu akwai irin mutanen nan ya yar da cewa na Allah basa ƙarewa yace






"Insha Allah zan ruƙe zaka sameni ma fiye da harda bakai tsammani ba Nagode sosai,






Ita kuwa mama tana zaune tana taɓe baki shi wannan mutumin ma talaucin sa har yafi na ɗanta ga kayansa yawa wani mahaukaci


yaya ne ya tashi ya shiga ɗaki ganin daga shi sai wani buhun babko alamu ma kaya ɗayane a cikin amma yana mamakin kyan fatarsa duk da yayi mata fenti ta koma me dan duhu amma a kwai hasƙen ka ɗan da alama bafilatani ne haka ya raya a ransa fito wa yayi ɗauke da kaya ya miƙo mai yace






"Ɗana gashi ahi haƙuri komai na rayuwa me hucewa ne ,




Ɗagowa yayi ya faɗaɗa murmushinsa tabbas yana ganin yaya kamar mahaifinsa wata irin daraja yake ganinsa da ita ba ƙyama yace




"Nagode da karamcin ku ,




dariya yaya yayi yace






"Ɗana Allah ne abin godiya wallahi ina jinka kamar abokina da narasa shekara da shekaru Allah yayi masa rasuwa tare muke faɗi tashi wallahi ciwon yunwane ya kasheshi


wallahi a lokacin yana tsananin rayuwa nima haka daga haka da ya mutu ya'yansa suka bar unguwar nan wallahi kamar ku daya da shi nayi neman su har nagaji,




Ƙasa yayi da kansa kwalla ta tarar mai tabbas mahaifin sa yake nufi yace






"Allah ya jikansa,




Amin ya Allah yace inno ce ta tashi ta ja dogon tsaki ta shige ɗaki


Ni'ima ce ta fito ko kallon sa batayi ba inta kalle sa zuciyar ta tashi take Allah yayi mata ƙamatar talaka gashi bawani kuɗine na kuzo a gani da suba


amma bata kaunar haɗa hanya da talauci kullum bata da zance sai tace yaya sagir dan Allah ka haɗani da me gidan ka jj ko number ka bani sai dai yace mata ni ƙaramin ma aikaci ne bani da iƙon ganin sa ko samin number sa har inno ce kesa baki tace






"Kai baka da kishin kanka ka shigewa mana manyan ma aikatan nasa kasamo mana muma mu warke,




Saide ya ce musu inno kenan to baya zama a ƙasar nan fa kullum yana kasar waje har karsuwancin sa amma yana gab da zuwa kano




________________________






Kai kai kaiyasa butar uwarnan sule kai ka dawomin bayan na aurar da kai ina ma laifin ka dawo kai ka ɗe kata shi ka dawo har da ƙari to wallahi bazata saɓo ba




Ƙasa yayi da kansa yace






"Innna wallahi haka jarabawar rayuwa tayi dani nasame ki lafiya,






Zama tayi ta ɗaura hijabin sallarta a kai kai kace gwawgwaro ta ɗaura tace






"Uhmmm gaskiya ne ta ƙutsiri goro ta fara taunawa,




Tashi yayi ya gyara tsohon ɗakin sa ya zuba kayansa ya dubi samha yace






"Jiki ɗakin yaya isah ki zauna a can ,






Tashi tayi ta kwashi kayanta sosai nuratu tayi murna da ganinta inna zenaru ta jajanta musu hamziyyah ce ta shigo tana dadɗaga kai sama ta girmin samha da shekara biyu yanzu ita na sha tara ita sha bakwai ko kallon inda samha take batayi bace






"Nuratu aramin wayar ki in dau number anty salma,




Miƙo mata tayi zama tayi tana wani daddauke kai we ita ala dole bata harka da kananan yara sai manyan kai wayar hannunta me tsada ce iPhone 7 CE gamawa tayi ta tashi ta fita ta zo ƙofar fita ta takewa samha kafa da sauri ta janye ta rasa wacce irin tsana hamziyya take mata nuratu ce tace




"Hmmm samha sabeereen fa ta zo gidan nan nan fa ta kwashe komai ta fada mata ,




Mamaki ne ya isheta tace




"Tab ita kenan da ace baku rabu ba ba sai ta yi miki abin da yafi haka?,






Ehmn wallahi ai taban mamaki Allah muma ya azurta mu




Samha tace






"Amin ya Allah,




____________________ *Karfe 12:30 dare*


Bacci take cikin jindadi ko tsoro bata ji na ita kaɗai ce a gidan kamar an tashe ta taji ana bugun gidan zunbur ta tashi daman su da ba wata kofar arziki ba fitila ta kunna tana zare idanuwa tsoro ne ya kamata daman dan ta kunsawa sule haushi ne yasa tace daga gidan Alhaji kabiru take jitayi an buga lalgalangar gidan ya buɗe zaro ido tayi gabanta ya yanke ya waɗi jin maganar yan daba sauri tayi ta kashe futila


Jitayi suna cewa yasin yace duk wanda muka samu mu rotsai mai kai tunda shi ya jawa kansa tun da ai kotu tace su tashi


Ɗayan yace






"Kai ai kaga honourable cewa yayi mu cire wa mutun jijiya tunda shi ya jawa kansa ,




Bata san lokacin da ta saki fitsari ba ta dafa kirji tace




''na shiga ukku neman magana ta ya jamin wayyo Allah malam,




Kai shiga ka fara dubawa ko zamu ga dan yarinya sauran dakunan suka buɗe har suka zo kan ɗakin inna hajara suka hasketa da fitila duk wari dakin yake da alama gudawa ta saki ganin yarda ta jiƙe da gumi sharkaf sai zare ido take fuskarta yawa an lotsa tasa basu san lokacin da suka dinga dariya ba ganin ogansu ya tsaya suma suka tsaya yac.......✍️




*YA ƊIN MGE*



*Oum Yasmeen*






*Part 51-60*






"Keee futo wato kece me taurin kai ko to yasin yau zamu koya miki darasi ,




Jikin baba hajara narawa ta fito da rarrafe tace




"Dan girman Allah kuyi haƙuri ni marainiya ce ,


Hhhhhhhh to wane ba maraya ba yasin yau sai kinci ubanki ba ke ce uwar karuwai gobe ki basu labarin abin da ya faru




Blet ya ciro ya fara zabga mata ihu take tana kururuwa ba maƙotan da ya shigo inda sabo ai sun saba da tujarar ta dan haka yanzu ma ganin ake faɗa suke yi ita da kawayenta bayan sun gama yace






"Hado kayan ki ki bar gidan nan sannan kije gidan da mijinki yake kar ki sake muji ance bakije caba shegiya duk bleaching ya kodar miki da fuska,






Ihu ta dena ta shiga ga ɗakin ta wardrobe ɗinta ta buɗe tafara haɗa kan kuɗinta




zata daure a ƙugu dayan dan daban ne ya ganta yace




"Arniya kawosu nan,




Jiki na rawa ta bayar hada komai tayi tana haɗawa suka dinga kwasa suna zubawa a mota ko tsinki basu bar mata ba




tana kuka da danasani ta kama hanyar kan karofi tafiya take tana wayai waye har ta isa bugu ta shiga yi sosai inna zulai ta ke shara baccin ta ga wani irin mafarki da take me dadi we gata a makka tana ta ciye ciyen Kayan dadi irin su chocolate ga kuɗi masu yawa tasa hannu zata dauka ta farka tsaki ta shiga yi tana tsinewa wannan wanda ke buga musu gidan ganin abin yayi yawa yasa ta sa hannu ta dauko fitila ta kunna samha ta duba dake bacci cikin natsuwa buga mata tayi bakin ta dauke da salati ta tashi ta dube inna tayi shiru jikin ta na kyarma domin Allah ya dora mata tsoron inna zulai




A zafafe tace






"Ke tashi muje ki buɗa ƙofa daukomin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login