Showing 6001 words to 7238 words out of 7238 words
FARA BAZAKI BARIBA DOMIN KOWANNE BAKI YASON DAƊI GA KUMA BIYAN BUƘATA CIKIN SAUƘI, GAME BUƘATAR GARIN BOBOTIC SABAYA ZE IYA NEMAN WANNAN CONTACT ƊIN 👉07073092176 KAYANMU BASUDA NABIYU💃💃💃
Misalin ƙarfe 8:00am kowa ya hallara akan dining ana breakfast, can nahangosu suna saukowa hannunsu maƙale dajuna cikin kyakkyawar shiga shi yasaka yadi fari ƙal ɗinki rocas yakafa hular yarbawa akanshi, red color hakan kuwa baƙaramin kyau yaƙarawa kyakkyawar fuskarshi ba, itama jannat farar atanface ajikinta ɗinki foguwar riga meratsin followers red color acikinta. Kana itama tasaka hula me kyau red, sosai sukayi kyau ba'amagana yadda suke tafiya takon takalmisu natashi shine yaja hankalin mutane kowa yakoma kansu. "Wow Masha allah gaskiya inaga duk a family nan namu acikin maza dai kan yah shead duk yafi kyau, cewar Zainab, dassuri Yusuf yace "acikin mata kuwa se aka fidda muku kyakkyawar acikin ƴaƴa tunda dukkanku jannat tafiku kyau. Harara tadoka Mishi kamar zata mare Mishi baki tace "wannan sarkin rigimarce kyakkyawa? Humm Zainab banason rigima fa harun yafaɗa cikin tsare gida domin yasan hakan ya ishesu jidali tunda mabiyan junane...ahakan suka maraso dining ɗin. Cikin girmamawa su Yusuf da harun Zainab hamida Marwan da naja ke gaidashi. Hannu kawai yaɗaga musu inda yabawa harun da Yusuf hannu suka gaisa kana yayiwa Marwan kiss yana rungume ghaisha cikinson mahaifiyar tashi yake faɗar "Barka da safiya my lovely mom.. Murmushi ghaisha tayi tace "yawwa barka babana katashi lafiya ya kwanan ƴar taka? Lpy Alhmdllh ghaisha, daga hakan yaɗuka yaɗauki naja yarinyar da Habibar harun ke goyo ayanzu. "Goog morning uncle, tafaɗa cikin sassayar Muryart... morning too jannat kintashi lpy? Lpy qalau, morning anty zee. Morning too amaryar Dady kintashi lpy. Share Zainab tayi bace mata komaiba setaje gun Yusuf yace morning uncle Yusuf. Morning too baby. Hamida kuwa hannu tabata suka taɓa domin sa'anin junane. Dasuri Marwan yazo wurinta tarida riƙo hannunta yace "good morning anty jannat. "Dan kallon yaron tayi sekuma tajanyoshi jikinta tana murmushi batace Mishi Komaiba. Sekuma tariƙa hannunshi sukaje tarungumi ghaisha tare da gaidata, "ƴar lelen babana kintashi lpy? "Murmushi taƙara faɗaɗawa tana ƙarajin son matar aranta tace "lpy qalau ghaisha na. "Anty jannat zakije gidan abey Dady ƙarami anjima? Cikin zumuɗi jannat tace "eh zanje mutsinko mango ko? Eh anty jannat.
Sakinshi tayi tadawo gunda shaheed ke zaune tsakiyar kujerar da table ɗin tadawo Dede gaban shaheed tashiga tsakaninshi da abincin dake kan dining ɗin seta ɗara hannayenta awuyanshi tazagayo wuyan suna fuskantar juna...ɗagowa yayi da dara daran idanuwanshi yana kallonta amma bece komaiba. Sukuwa duka mutanen wurin kowa ajiye spon yayi aka zuba musu ido. Ahankali itama tasaka idonshi cikin nata kafin tabuɗe baki cikin wata irin murya wadda shikaɗai take yiwa maga da ita tace "uncle shead na zaka kaimu gidan dadyn uncle ƙarami please? Taƙarasa zancen a shagwaɓa. Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi yanajin yadda zuciyarshi ke bugawa da dasauri. Ƙara matsoshi tayi takowa bakinta Dede kunnenshi tace "please my sweet uncle sheaddd, taƙarasa zancen tana jan sunan kamar tana huramai iska akunne, ita duk a zuwan rarrashine takeyi danya kaisu. Aibubu shiri shaheed yabuɗe idonshi tare da saurin yi ƙasa dasu murya can ƙasan maƙoshi yace "it's okay zankaiku. "Yeeee tafaɗa alokacinda tajaye daga jikinshi tarungumi hamida da Marwan suka shiga tsallen murna, sunjima sunayi kafin sufaracin nasu abincin....shiko shaheed yana ga taɗaga mishi yamiƙe dasuri yabar perlor.
Se kusan karfe 11:00am tukunnah yadawo gidan yadaukesu se gidan abey ya ajiyesu kana yakoma warshi office....da gudu suka shiga perlor gidan inda suka samu innayi zaune tana lazimi se uncle ƙarami wato Babil shine suke kira uncle ƙarami. "Innayin Abeyyy sukafaɗa atare sunayi kanta. "Ikon Allah yau tawagar ghaisha gidannan? Tonidai karku katayani irin wannan haƙilo haka. Dariya Babil yayi yana miƙewa tsaye yace tab ɗijam yau innayi kinada manyan baƙi harda ƴar lelen yah shead abuna musamman ne. "Uncle ƙarami Bara muzo katsinko mana mango cewar jannat tana miƙewa daga jikin innayi tabi bayanshi hakama hamida da Marwan....dariya kawai innayi tayi tana girgiza kanta tare da cewa jannat akwai ƙiriniya sam baki biyu halin mahaifiyarkiba.
A gadin suka je inda Babil yashiga tsinko musu ƴaƴan itatuwa kala kala sunasha suna zubarwa cikin farin ciki suna wasarsu, har Abey yadawo darana yasamesu nan aiko yakwashesu suka tafi yawo bayan sunyi lunch ɗin rana, gidajen wasa kala kala Abey yakaisu daga ƙarshe yakaisu shopping mool inda yayi musu ƴar banzar siyayya tukunnah suka dawo gidan innayi cikin jin daɗi da farin ciki...anan suka baje perlor aka ɗora daga inda aka tsaya se yamma liss kana lubnah tadawo gidan cikin shigarta ta likitoci ƙananun kaya da lab Cord akai. Tunda yayi sallama perlor tagansu ta haɗe girar sama da ƙasa domin sam batashan inuwa ɗaya da yaran gidan ghaisha sabida lubnah batada mutunci ko kaɗan, wani tsinanen kallo take binsu dashi. Hamida cikin sauri tace inawu anty lubnah kindawo lafiya? Inawuni anty lubnah cewar Marwan shima. "Lpy waya kawoku gidannan mikukazoyi? Dady, cikin sauri jannat tabigewa hamida baki dataje gaya mata Dady shead ne yakawosu, tana murguɗa baki. "Keee marar kunya nisa'arkice zantambayi abu baki gayaminba kuma kihana wani yafaɗa tukunnah ma baki iya gaisuwa bane? Dabazaki gaidaniba ina ƙanwar uwarki, shegiya me jajayen kununwa. "Baki jannat tatura gaba kana tace "sallah naje koya tukunnah idan nadawo seki koyamun gaisuwar, taƙarasa zancen tana wani jujjuya ido..itama lubnah idon tawaro kenan jannat magana tagaya mata tana nufin batayi sallamaba kome shine zata gaya mata ahagunce. "Ke dan ubanka nizaki gayawa magana wlh Sena ɓallaki agidannan, tafaɗa tanayi kan jannat dake tsaye ƙiƙam ko ɗarr babu. "Kaki kuskura kitaɓa mun ƴa wlh, tatsinkayo Muryar shaheed dake tsaye shida hafees tun shigowar lubnah ɗin suna bayanta.
Cak tatsaya tare da jiyowa tana kallonsu, wani mugun kallo hafees kejifanta dashi yayinda shaheed ko gefen datake be kallah ba... jannat kuwa dagudu tazo gun shaheed tarungumeshi tana faɗar "oyoyo uncle shead na yazo...shima rungumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya....galala lubnah tayi tana kallonsu domin tunda taji muryar shaheed tanemi nutsuwar ta tarasa Domin Allah yajarabeta da mahaukacin sonshi amma shi sam bata gabanshi, bata tashi dawowa hayyacintaba seda taji rufo kofar dasukayi dasauri tajuya zata bisu taji Muryar innayi tana faɗar ina kuma yaran sukayi ne? Ke lubnah kindawo ina zakije? "Suntafi innayi shead ne yadaukesu domin yaga wannan banzar zata dokar mishi ƴa bayan kuma duk abinda tayi mata itace taja domin duk muna tsaye akayi, hafees yafaɗa cikin jin haushin karwar tashi...faɗa sosai innayi tashiga yiwa lubnah domin taji ciwon tafiyarsu sosai batareda tasaniba.
Shaheed kam yana kaisu gida yawuce pert ɗinshi ahasale domin mugun haushin lubnah yakeji akan dukan da taso yiwa jannat ɗinshi, shiyasa ko jannat ɗin tun cikin mota data dameshi yadoka mata tsawa beƙara bi takantaba...itama akunbure tashigo gidan tawuce bedroom ɗinsu. Se mahida ce tabawa ghaisha labarin abinda ya faru. Ghaisha kan Allah ya kyauta kawai tace domin tasan halin lubnah sarai..awannan. Daren dai hakan suka kwana kowa rayuwarshi babu daɗi..
Washe gari jimu'a
Kowa awannan family masallacin baba mlm yake Sallah kasancewar shi babban masallaci acikin unguwar. Daga shaheed har hafees da iyayensu harsu harin dukkansu dai anan suke sallah. Bayan an idarda sallar jimu'a ne akashiga ɗaurin aure kamar daga sama sukaji ana haɗar anɗaura auren shaheed zayyan maƙarfi da lubnah basheer maƙarfi akan sadaki dubu hamsin.😱
SHUGER DADY paid book ne akan 1k kacal 👌 banyadda kowa yakaranta min book bebiyani hakkinaba idan kinshirya biya zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA Bank, kana kitura shaidar biyanki awannan nomber 👉 07037092176🙏
Autar alheri ✍️