Showing 234001 words to 237000 words out of 237228 words
Chapter 79 - KURMAN ALLO COMPLATE JEEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU.txt
cikin kidimewa kana kuma ya saka wayar a speaker "Abbu na ce ɗanka sanyin idaniyarka Muhammad Azhar yana raye duk tsawon lokaci nan ina tare dashi bayan doguwar sumar da shiga sai yau Allah ya yi ikonsa ya farfaɗo, babban abin farin ciki yana cikin ƙoshin lafiya, Abbu nasan kana garin Kano zan turo ma da address ɗin gidan da muke ka zo ka gansa. Abbu kamar ka ɗaya dashi sai dai yafi ka kyau.
Anaal ta ƙarashe magana tana kuka tana dariya.
Gabaki ɗaya ɗakin rudewa ya yi da ihun farin ciki, Aydah kasa motsawa ta yi daga idan take zaune hatta da Maysun mai fama da kanta, ta ɗaga hannu sama tana godewa Allah. Siyama ta zo da sauri ta girgiza Aydah ita kaɗai ta fahimci suma Aydah ta yi, Mami ta ɗauki robar ruwa ta shafawa Aydah ta ja doguwar ajiyar zuciya tana bin kowa da idanu can ta furta "Gaske ne abun da kunnena ya ji da gaske ne Yayanmu yana raye bai mutu ba?"
Siyama da Sadiya ne suka tabbatar mata da hakan. Aliyu na Uku yana gani Anaal ta turo masa da address ya ce Daddy ya zo su je, nan da nan kowa ya ce zai je hatta da Maysun basu baro ta, tashi ta yi Mami ta kamata suka fito sauƙin su ɗaya Sadiya da Siyama da motocin su suka ga ta Daddy. Tafiya suke yi kowanne su gabansa na faɗuwa koda suka isa gidan Aydah ji take kamar ta buɗe ido ta ganta gaban AB.
Anaal tana ji dirar motocin su ta kalli AB tana murmushi "Ka gani ko yayana dama na gayama Abbuna yana matukar ƙaunarka kai ɗin ɗan gata ne gaba da baya.
Daddy ne a gaba sai faman saɓa babbar rigarsa yake yi tana zamewa, ya riga kowa isa dakin da AB yake yana arba dashi da sassarfa ya isa kan gado da yake ya rungume shi ya fashe da kuka shi ma Ab ƙanƙame Daddy ya yi, ya saki nasa kuka, sun ɗauki lokaci rungume da juna kamin Daddy ya sake shi ya kalli yadda su Aliyu suka yi cirko-cirko Anaal ta ruga ta rungume Aliyu tana "Faɗin Abbu na samo shi na samo maka farin cikinka, nasan daga yau ka yi bankwana da damuwa.
"Nagode Anaal Allah ya yi miki albarka yadda kika faranta min ke ma Allah ya faranta miki ya ba ki 'ya'ya nagari masu saki farin ciki.
"Amin Abbuna!
Anaal ta faɗa very excited, kamin ta je ta rungume Safiya.
Daddy ya kalli Aliyu na Uku dake tsaye yana kallonsu da murmushi akan fuskarsa "Zo mana Aliyu ku matso kusa ku ga ɗan nawa.
Kamin Aliyu na Uku ya cira sanyayyu ƙafafuwansa har Maysun ta ruga ta rungume AB, gan-gan kamar za ta mayar dashi ciki sai sumbatar sa take yi. Aliyu na Uku ya karasa ya zauna kusa da AB yana kallonsu yana murmushi hawaye na sauka a kamatunsa ga baki ɗaya ɗakin rikicewa ya yi da koke-koke musamman da AB ya tambaye Rumaisa da Aydah cikin raunin zuciya Daddy ya gayamasa Rumaisa ta rasu wurin haihuwa sai dai ta bar 'ya koda ya duba bai ga Aydah ba Daddy ya tambaye Siyama ina Aydah ta fice da sauri ta je ta dubata koda ta fito tana rakuɓe jikin bangon parlor tana kuka haiƙan "haba Aydah ke da ya dace ki yi farin ciki ki godewa ubangiji ya dawo miki da farin ciki da kika rasa.
"Yaya Siyam na kasa yarda shin mafarki nake yi ko kuma da gaske ne Yayanmu yana raye bai mutu ba?"
"Aydah a zahiri ba mafarki kike yi ba ta so mu je sai tambayarki yake yi.
Girgiza kai Aydah ta yi "Ba zan iya shiga ba idan su Daddy na ciki zan iya aikata abun kunya a gabansu zuciyata ba za ta iya jurewa ba dole sai na rungumesa na ji ɗumin jikinsa da na ɗauki tsawon lokaci ban ji ba.
Duk yadda Siyama taso Aydah ta, zo su shiga ciki taƙi.
Bayan sun gama koke-kokensu suka yi shirin barin gidan kuma har zuwa lokaci Aydah bata shigo ba tana parlor farin ciki da suke yi yasa ba wanda ya damu da sai ta shigo saɓanin Ab dake rungume da Baby Noor, ga baki ɗaya hankalinsa yana ga ƙofar shigowa yana kallon shigowar Babynsa, ita kadai zuciyarsa take mararin gani ya kosa ya ganta yaga ta canza ko tana nan yarda yasan ta. Anaal ta kira Dr Maheer fitowarsa daga ɗakin tiyata ta kira sa, agaggauce ya canza kaya jikinsa ya zo shi kansa ya yi farin ciki da ganin iyayen Anaal ya ƙara duba Ab ya basu tabbacin za su iya tafiya dashi, Siyama ce ta fara fitowa daga ɗakin ta kalli Aydah wacce har zuwa lokaci ta kasa tsayar da hawayen idonta.
Sai gashi su Daddy su dukka Dr Maheer da Anaal kaɗai aka bari a ciki suma dan za su taimaka masa ne saboda ba zai iya taka ƙafafuwansa ba duba da yarda ya daɗe a kwace ga ƙafarsa guda mai ciwo bata ƙarasa warkewa ba.
Aliyu na Uku ya kalli Aydah dake sharar hawaye yana murmushi ya ce "Shi ga ki gansa kamin a fito dashi tun da kunyar mu ta hana miki zuwa inda mijinki, sai rabon idanuwa yake yi yana kallon ta inda za ki fito. Da sauri Aydah ta sadda kanta ƙasa, cikin yanayi na jin kunya ta nufi ɗakin Siyama da Sadiya suka bi ta dariya. Cikin wani irin yanayi mai matukar wahalar fassarawa ta shiga ɗakin AB da ke kokarin sakkowa daga gado ga Dr Maheer da Anaal sun kama gefe kafaɗarsa Anaal tana riƙe da bangare hagu Dr Maheer dama, AB yana ganinta zuciyarsa ta yi wani irin bugawa da mugun ƙarfi ya koma ya zauna har ta ƙaraso kusa dashi bai ɗauke idanunsa daga kanta ba. Sosai yake mamakin girmanta kamar wacce aka zubawa fertilizer, ga wasu butt da ajiye ƙirjinta kuma ya ciko mayataccen kallo da yake mata yasa Anaal da Dr Maheer suka fice suna murumshi, yadda yake kallonta ita ma haka take kallonsa duk ya yi muguwar rama fuskarsa ta cika da gashi ga wani uban gemi da ya yi hakan bai dusashe kyawunsa ba sai ma Aydah taga gemun ya yi bala'in yi masa ya kyau kamar wani Sheikh, cike da zallan kewarta ya ware mata hannayensa a hankali ta shige jikinsa ya yi mata kyakkyawan masauki a faffadan ƙirjinsa, a lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya cikin muryar kuka ta kira sunansa "Yayanmu an gayamaka aunty Rumaisa ta rasu ko? Ka ga kyakkyawar 'yarmu da ta bar mana?"
Gyaɗa kansa kurum yake yi yayin da hawaye ke bin kumatunsa yana jin kewar Rumaisah a can kasan zuciyarsa addu'a yake mata. Sun ɗauki lokaci rungume da juna ya ɗago fuskarta yana lashe hawayen dake bin kumatunta kana ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta passionately, lallai kuwa sun yi kewar juna dan su Daddy tafiyarsu suka yi suka ce dasu Sadiya idan sun fito su yi gaba su same su a gida, da kyar Ab ya iya rarrashin zuciyarsa ya bar Aydah suka fito zuwa gidan Daddy.
*ALH SALISU GARKUWA MANSION*
Yau tun safe mai babban ɗaki ta tsira kuka taƙi cin komai kamar wata yarinyar goye sai kiran sunan Aliyu na uku take yi tana faɗin yaya Gimbiya ta kira mata shi ya zo ta ganshi kafin ta mutu wannan furuncin da take ta nanatawa, yasa jikin yaya Gimbiya ya yi sanyi ta kalli Marwan wanda jiya ya zo hutu daga Kano da yake a kano yake karatu "Marwan je ki ɗakina ka dauko min wayata na kira mata fitinannen yaro nan dama irin su Aliyu sun fi shiga ran iyaye, kana gani dai duk kulawar da muke nuna mata zuciyarta bata daina mararin sa ba.
Murmushi Marwan ya yi ya je ya dauko mata wayar ta kira layin Aliyu wanda isowarsu kenan gidan Daddy yana ganin kiranta sai da gabansa ya faɗi, cikin mutuwar jiki ya yi picking "Assalamu alaikum yaya Gimbiya!
"Kai fitinannen ka zo mahaifiyarka tana so ganinka tun da kai ka manta da ita. Ita kam ta kasa mantawa da kaine silar kwanciyarta gadon asibiti.
"Ki yi haƙuri yaya Gimbiya ta ya kike tunani zan iya mantawa da wacce ta kawo ni duniya, ki tambaye Magaji ƙarami babu ranar da bana kiransa na ji lafiyarta. Kuma koda ba ki kirani ba in shaa Allahu gobe zan zo tare da iyalina dukka.
#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.
[2/11, 2:29 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye
106- 🔚
Su Aydah suna isowa Daddy ya ce a wuce da AB part ɗinsa dake gidan ya yi wanka, a bedroom aka zaunar dashi Aydah ta wuce bathroom dinsa ta haɗa masa ruwa wanka. A hankali AB yake bin ɗakin da kallo yana tuna irin rayuwar da ya yi acikinsa. Sai kuma ya dawo da ganinsa kan baby Noor dake cinyarsa dan har Anaal za ta wuce da ita bangaren Mami ya karɓe ta, wata irin ƙaunarta yake ji hannunta ya kama ya kai bakinsa ya sumbata. Aydah ta fito ta zo kusa dashi tana faɗin "kawo ta ka je ka yi wankan na hada ruwa.
A maimakon ya miƙa mata ita sai rikon hannun Aydah ta zauna daf da ƙugunsa yana kallonta yana lumshe idanuwansa tamkar dai mai jin bacci "Baby kin canza ga baki ɗaya.
"Uhm!
Aydah ta faɗa tana murmushi.
"Me kike ci ne haka da kika kiɓa abubuwa nan sun fito.
Yana magana yana shafa duwawunta "wadannan kamar za su tsone min ido Allah baby kamar ba ke ba.
Ya ƙarashe maganar tare da ɗora hannunsa a boobs ɗinta, ture hannunsa ta yi tare da daukar Baby Noor "Da can ba raina su ka yi ba.
"Kai, kai! Baby me kuma ya kawo wannan zance?"
"Ka je ka yi wanka Yayanmu su Daddy na jiran mu kada mu barsu su ta jira.
"Ki ajiye Baby Noor ki zo mu je ki tayani wankan.
Batareda da tace komai ba ta shimfiɗe baby Noor akan gado ta kama shi ya miƙe ya sakala hannunsa a wuyanta ɗayan hannun yana can akan duwawunta yana matsawa, a zuciyar Aydah sai mamaki jarabarsa take yi kai da ka farfaɗo yau ban da jaraba me zai yi da mace. A wurin wanka sai da suka kwashe daro dan kuwa matseta ya yi ya dinga luguiguta ta, da kyar aka yi wanka koda suka fito baby Noor ta gaji da wasanta ta yi bacci, kasancewa dama akwai raguwar kayansa a ɗakin Aydah ta dauko masa wani filtex material brown colour ya saka, sosai kayan suka yi masa kyau, suka yo bangaren Mami Ab baya iya taka ƙafarsa sosai sai da taimakon sanda, hadaddun girke-girken da Huwaila ta yi musu suka haɗu a dining suka ci Daddy da Aliyu na uku aka kai musu nasu a bangaren Daddy, lokacin da AB ya sami labarin Daddy ya aure Huwaila addu'ar fatan alkhairi ya yi musu. Washegari ga baki ɗayansu suka dunguma suka yo garin Zaria gidan yaya Gimbiya, mai babban ɗaki tana gani Aliyu ga kuma Ab sai kurum ta fashe da kuka tare da godewa ubangiji, da ya kasance ɗanta yana da magaji saboda 'ya mace 'yar gidan wani ce ta kuma san rashin mai tallafa masa ne yasa ya zubawa Anaal ido batareda ta yi aure ba. Duk masifar yaya Gimbiya tana ji cutar da ke damun Maysun jikinta sanyi yayi ta jinginar da masifarta a gefe.
Marwan Garkuwa yana arba da Aydah zuciyarsa saura kaɗan ta buga bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da aka gabatar masa da ita a matsayin matar cousin ɗinsa, ɗakinsa ya shige duk hidimar da ake yi yana can kudundune cikin duvet zazzaɓi mai zafi ya rufe shi. Aydah kuma yi tayi kamar bata taɓa saninsa ba, a zuciyarta sai ƙara godewa ubangiji take yi da yasa bata karɓi soyayyarsa ba da yanzu shi da ita ne za su shiga wani hali.
Kwanan su ɗaya a Zaria Aliyu na Uku ya sami kira daga waziri, masarauta tana nemansu da kyar suka yi convince mai babban daki ta amince da zuwa kudu a cewarta ta bar masauratar Kudu bari na har abada. Wayar da Jakadiya ta jefar wani daga cikin bayi ya tsinta lokacin da yaga video dake cikin wayar ya girgiza matuƙa, sai kawai ya je ya kai ma shugaban bayi dake gidan shi kuma ya ba sarkin fada har dai wayar ta zo hannun waziri kasancewar ga baki ɗaya fada basa ƙaunar Ciroma, sai dai basu da yarda za su yi yanzu kuma da Allah ya kawo musu hanyar da za su tsige shi sai farin ciki suke yi. Yayin da Ciroma bai san wainar da ake toyawa ba sai shirye shiryen-shiryen naɗin Galadima yake yi wanda a tsarinsa gobe ne naɗin sarautar. Sosai Aliyu na Uku ya girgiza da jin Ciroma ne ya kashe sarki Mahmood na Uku don kawai ya hau karagar mulki wannan yana ɗaya daga cikin dalilai da yasa ya tsani sarauta. Ciroma yana gidansa jami'an farin kaya suka yi awon gaba dashi zuwa ofishin su, gani video yasa bai da wata mafita da ya wuce ya faɗi gaskiya wata kila zai sami sassauci daga hukunci da za a yi masa, nan da nan ya warware musu duk wani tuggu da muguye abubuwa da ya aikata nan take aka kamo Galadima da Fulani ƙarama duk wanda ya ji abun da suka aikata sai ya tsine musu albarka musamman da suka ji cewa Ciroma ne ya kashe Kilishi saboda ya gano ba ita bace ta haife shi. Kotu aka wuce dasu aka yanke wa Ciroma hukuncin kisa ta hanyar rataya, Fulani ƙarama da Galadima life imprisonment.
Ab ya yi farin ciki da ya haɗu da ahalinsa, shi ma dai kamar mahaifinsa ko kaɗan gidan sarauta baya burgesa tuni aka dawowa da Aliyu na Uku da sarautarsa ta sarkin sabon birnin kudu yayin da aka naɗa Ahmadu a matsayin sabon sarkin kudu saboda cancantarsa da sanin ya kamata sa yau ga Ahmadu a matsayin sarkin kudu Kilishi kuma tana lahira tana girbar abun da ta shukka da ta yi haƙuri da wata kila ta ga zuwan wannan rana sai ta bi son zuciya gashi nan inda ya kaita.
Aliyu na Uku ya zaunar da AB ya faɗa masa irin cutar da Maysun take damunta, sosai AB ya shiga damuwa ranar ko bacci kirki bai yi ba, tun daga lokaci yake ba wa mahaifiyarsa kulawa ta musamman anan Kudu su Daddy suka baro su shi da Aydah suka dawo Kano, ɗan zaman da Ab ya yi da Maysun wata irin shaƙuwa mai ban sha'awa ta shiga tsakaninsu, sai suka yi sati biyu a kudu sannan
Aliyu na Uku ya tattara dukka iyalinsa suka koma Lagos har da AB da Aydah sai satin su ɗaya a Lagos suna cin amarci sannan suka dawo Kano inda sukafi wayau domin har gobe Ab Daddy da Mami yake kallo a matsayin iyayensa ga baki ɗaya hankalin ahalin ya kwanta yanzu basu da wata matsala kowa yana gudanar da rayuwarsa cikin farin ciki. AB da Aydah sun koma gidansu sai zuba soyayya ta fitar hankali suke yi rayuwarsu gwanin ban sha'awa.
*BAYAN WATA BIYU*
A yau iyalin Aliyu na Uku suka waye gari cikin tashin hankali ciwon Maysun ne ya tashi, sun je asibiti likita ya tabbatar musu ciwonta ya zo matakin karshe su yi mata addu'a kawai domin babu sauran wani abu da za su iya mata. Wannan dalili yasa Aliyu na uku ya kira Ab ya faɗa masa, cikin tashin hankali ya siye tacket ya nufi lagos kamin ya iso Allah ya karbi rayuwar Maysun sun yi kuka rashinta sai dai kawai su bi ta da addu'a. Bayan sati biyu da rasuwar Maysun Ab ya yi musu visa shi da Aydah da baby Noor suka tafi Qatar wurin dangin Maysun sosai suka yi farin ciki da gani AB anan ya sami labarin tun bayan tafiyar Maysun Nigeria mahaifiyarta, ta mutu ya dai hadu da yayunta da ƙannanta tare da iyalansu watan su ɗaya a Qatar suka dawo Nigeria a lokaci Aydah tana ɗauki da ciki sai dai bata laulayi Ab sai kara shagwaɓa ta da rirrita ta yake yi.
Siyama ce ta fara haihuwa ta haifi ɗa namiji ana gobe suna Sadiya ta haifi 'ya mace tun sanda suka haihu Aydah bata zauna ba sai hidima take gashi sauran sati guda a fara bikin Anaal da Dr Maheer Ab sai korafi yake mata wai tana wahalar masa da Babynsa. An yi bikin Dr Maheer da Anaal lafiya amarya da ango sun tare a katafaren gidansu anan Kano. Rayuwa tana ta tafiya yau daɗi gobe akasin haka wasu suna farin ciki wasu suna baƙin ciki kamar dai yadda ta faru akan Alh Sanusi da Zeenah akan hanyar su na zuwa Katsina sun sami labarin wani mashahurin boka a wani ƙauye dake cikin Katsina so take ta kowanne hali sai sun ga bayan Daddy da iyalinsa dukka, Musamman da suka ga Ab ya dawo nan da nan hankalinsu ya yi mummunan tashi suka bazama yawon gidan bokaye da Malaman tsibu sai dai babu nasara, jiya suka sami labarin wannan bokan da za su kaima ziyara, anan suka haɗu da masu garkuwa da mutane sun tare hanya a kokarin Alh Sanusi da ya gudu suka harbe shi ko shurawa bai yi ba ya mutu, Zeenah tana gani haka ta ruga wurin gawar mijinta ita ma suka sakar mata harsashi a ciki ta fadi matatcciya. Duk da Zeenah ta gano Ab ɗan mijin ƙanwarta ce Safiya da iyayensu mata suke ɗa wa da ɗa ƙani amma bai sa Ab yaci wannan darajar zumunci dake tsakaninta da Safiya ba, kullum burinta ita da mijinta su kawo ƙarshen sa, sai gashi basu kawo karshen nasa ba kidnappers sun kawo karshen su. Allah yasa mu cika da imani yasa mu fi karfin zukatan mu ya tsare mu da mummunan ƙaddara.
Cikin hukunci Ubangiji Aydah ta haifi ɗa namiji kyakkyawan gaske mai kama da Ab, ranar suna yaro yaci sunan Daddy lokacin da Aydah ta ji sunan yaro kallon tuhuma ta riqa bin Ab dashi "Baby wannan kallon fa?"
AB ya faɗa