Showing 96001 words to 99000 words out of 132515 words
Chapter 33 - BAKAR WASIKA- Book 1 By Khadeeja Candy .txt
da shadda da kuma lace ta daukar mata kusan kala 25, ban da talkami da hijab da veil. Suna zuwa gurin biya kamin su yi wani yunkuri ta mika atm dinta. Talba ya kalleta.
“i can pay”
“Dan Allah ka bari na yi wannan aikin ladar”
Be saki cewa komai ba, ya kalli Aminatu.
“Muje mu jirata a mota”
Ba musu Aminatu ta mika masa hannu ya rikata tana takawa a hankali suka fice, kamar dazun a yanzun ma front seat ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya zauna a side dinsa.
“You got lucky ba yayanki kadai yake son hidima dake ba, har da Kawar Matata”
Kallonsa kawai tai ta sauke kai kasa, shiru ne ya biyo baya har Madina ta fito tare da masu rika mata ledodin kayan Talba ya bude musu bayan motar suka saka, sannan ta rufe ta bude back seat din ta zauna, yana kokarin yin reverse ta mika masa box din agogon hannu that worth 150k.
“Zan yi farinciki idan ka karbi wannan kyautar daga gareni”
Kallonta yai sai kuma ya kalli Amintu.
“Shalele karba min”
Aminatu ta karba ta rike ba tare data buda ba, har suka isa gidansu Madina be karbi agogon ya duba ba, balle yai mata godiya, hakan da yai sai yasa ta ji wani iri, yanzu kam ta tabbatar akwai babban aiki a gabanta, domin samun abun da zai burge Talba a take ko kuma ya dauki hankalinsa ba abu ne mai sauki ba.
A harabar gidan ya faka motarsa, ya mika hannu ya budewa Aminatu.
“Ki taka da kafarki ki fita, kuma ki rika tafiya ke kadai ba sai an rika ki ba”
Ta lake kafada tana dan turo baki, sai dai bata ce masa komai ba kuma bata yarda ta kalli inda yake ba. Shi kam sai kallonta yake yana ayyana irin shagwabar da take a gaban iyayenta domin kana ganinta ka san shagwababbiya ce, dan farin ma wani yai shagwaba balle auta autar ma ta maza.
“Yaya Madina zaki rika ni ko?”
Ta fada tana jiya fuska ta kalli inda Madina take tsaye tana mikawa hadiman gidan ledidin hannunta.
“Eh”
Ta fada sannan ta nufo inda Aminatu take zaune ta rikata, sai da Aminatu ta aje masa agogon sannan ta fita Madina ta rufo masa motar.
A tunaninta zai mata godiyar siyayyar da tai ma Aminatu amman bata ji hakan daga bakinsa ba, ta san kuma hakan ya masa dadi ko da ba a fada ba, sai a yanzu ta tabbatar da miskilacinsa ya wuce inda take zato.
Sai da suka shige cikin main house din sannan ya ja motarsa ya bar gidan, at first restaurant ya so ya tafi ya ci abinci even though baya son cin abinci a waje sai dole, but yana son ya kaurace ma cin abincin Momy saboda ta fahimci be jidadin abun da tai masa ba, sai dai hakan ba zai saka shi gaba da ita ba, kamar yadda dazun ma be kasa kiranta a waya yai mata barka da safiya ba, bayan kuma ya saba da shiga part din ko wace safiya ya gaishe ta. Kamin ya karasa restaurant din kiran Amal ya shigo wayarsa, sai yai picking call din ya saka wayar a hands-free ya aje ta kusa da shi.
“Lil Sis”
“Yaya”
Ta amsa masa cikin kuka, ya san halinta da shagwaba sometime kan sily abu sai tai ta kuka, hakan yasa be tashi hankalinsa ba.
“Waya taba ki me kike yi ma kuka?”
“Momy ce ta yi fada da Daddy, kuma har ya sake a ta debi wani tufafinta ta bar gidan, ta bar mu ni da Leila tun dazun sai kuka muke”
Wani irin faduwar gaba ne ya same shi, sai yai sauri sauka daga titi ya faka motar gefe, ya dauki wayar ya kai kunnensa.
“Ba a wasa da irin wannan maganar Amal”
“Wallahi da gaske nake”
“Miya faru?”
“Ni na yi komai, Ya Kabir ya fada min abun da ya faru ni kuma na fadawa Daddy, shi ya zo bangaren Momy yana ta masifa and Momy ta kiraka da tsintacciyar mage, shi kuma yace ba zai dauka ba, shi ne ya saketa...”
Be ce mata komai ba ya yanke wayar, ya shiga kiran Daddy, amman har wayar tai ringing ta gaji ta tsinke Daddy be daga ba, Talba ya sake kiransa nan ma the same thing, tun yana kira yana sa ran zai dauka har ya cire rai, hakan ya tabbatar masa da cewar ran Daddy ya bace sosai, domin abu ne mai wahala yai masa two miss calls be daga ba, amman a yau ya jera masa 11 miss calls be yi picking ba. Sai ya sake kiran Amal.
“Yana gida?”
“Aa ya fita”
Ya yanke kiran sannan ya duba agogon hannunsa biyu saura kwata ya gani, take hau titi ya fisgi motar kamar zai bar gari, cikin yan mintuna sai gashi Harabar ma'aikatar su Daddy, ko fakin din kirki be yi ba ya fito da sauri ya shiga cikin ma'aikatan, kusan ya san mutane da yawa a ciki kamar yadda mutanen gurin ma suka san shi saboda yawan fadarsa da Daddy yake da kuma zuwa gurin, sai dai be tsaya gaisawa da kowa ba daman ba gaisuwar yake so ba, saboda ta zame masa kamar ta dole ce kasancewar su abokan mahaifinsa. Kai tsaye ya nufi bangaren da office din Daddy yake yana ta zuba sauri. Sai dai yana shiga sakariyar ta hana Talba ganin Daddy.
“Yace baya son a dame shi kowaye ya zo kar a bari ya shiga ciki”
“Kin san waye ni kuwa?”
Talba ya nuna kansa.
“Na sani dan Allah kai hakuri, aikina nake yi”
Ta fada cikin damuwa, sai ya wuce ta ya karasa gurin office din ya bude ya shiga ita kuma ta biyo bayansa da sauri tana kokarin dakatar da shi.
“Duk kika yi kuskuren taba ni sai na mareki Wallahi”
Ya furta yana nuna ta da yatsansa, babu alamar wasa a fuskarsa. Daddy dake tsaye yana kallonsu ya ce.
“Amman na tabbatar da kai ne, korarta zaka yi, yanzu kuma kana kokarin hanata aikinta, you can go Hannatu”
Sai ta juya da sauri ta fice. Daddy ya kalleshi.
“Ya akai?”
“Haba Daddy miya saka zaka yi haka?”
“Hey my friend, control your tongue, I'm your father and you're my son, so ni zan tambayi dalilin da zai saka kai wani abu ba wai kai tambaye ni ba”
Talba ya karaso kusa da teburin Daddy cikin yanayin damuwa.
“Daddy please, be kamata ba Wallahi, da girmanku ace kun rabu? Mu ya kake son ku yi? Baka duba Amal da Leila ba? Baka duba ni yadda zan ji ba? Da wane ido zaka kallemu? And baka yi tunanin yadda Momy zata ji ba?”
“So a idonku nine mai laifi? Ni baku ayyana yadda zan ji ba?”
“Ni kullum a gurina kai ne mai laifi daddy, kai namiji ne ya kamata ka rika kawarda ido, amman sai ka rika biyewa Momy da take mace? Hankalinta da tunaninta ba daya ba ne da naka”
Daddy yayi murmushi ya nuna masa kujera.
“Have a seat my friend”
“No ni ban zo nan domin zama ba, kawai na zo na dauke ka ne mu tafi da kai ka bawa Momy hakuri ka dawo da ita”
“Have a seat”
Daddy ya maimaita wannan karon ya fada tare da zaunawa. Sai da Talba ya sauke ajiyar zuciya sannan ya zauna.
“Fada min gaskiya, ban san ka da karya ba Son, abun da Amina tai be bata maka rai ba?”
“I feel bad, amman be kamata ya saka ka yanke wannan hukuncin ba”
“Ban yanke hukunci saboda ta kori yarinyar daka kawo ba, na yanke wannan hukuncin ne saboda ta kira ka da tsintacciyar mage”
“Fushin zuciya... ”
Daddy yayi saurin dakatar da shi with serious face ta hanyar daga masa hannu.
“No, bari na baka wani labari da ban taba fada maka ba. A cikin wani babban gida mai rufin asiri mata har hudu, kowa a wannan gidan yana da manyan y’ay’a da kanana, ko wace mace a cikin matansa ta haihu shida wata tara wata goma sha daya, sai karamar matarsa ce kawai ta haifi yaya biyu maza wanda ta kasance karama ce kuma ita ce ta hudu, tana tsaka da rainon yayanta sai mutuwa ta sallamo mata, yaya da kanensa suna daji gurin noma, ka zo kiransu aka fada musu cewar mahaifiyarsu bata da lafiya, sai dai kamin su kawo rai yai halinsa, ita ce karama kuma ita ta riga tafiya ta bar kananan yayanta guda biyu, haka yaran biyu suka tashi cikin yan'ubanci da kuma kyara ta matan uba, idan uban ya dawo sai a nuna ana son su kamar za a hade su, idan kuma ya saka kafa ya fita abinci ma sai sun yi bara su ci, wata rana kwatsan wannan mutuwar ta sake kwankwaso kofar mahaifinsu, kuma ta dage sai da ta tafi da shi, daga lokacin sai rayuwa ta kara zame musu abun tausayi, domin a gidan da suka taso gida ne da babu hadin kai a ciki, kowa kansa ya sani kuma ga kishi da nunawa uba aka hada ba uwa ba, idan aka dafa abinci masu ake bawa, ba marasa uwa ba, idan sallah ta tashi sai dai yan'uwa mahaifiyarsu su yi musu dinki, wani lokacin abinci ma a can suke zuwa su ci, suna cikin wannan rayuwarsa sai yayan ya fara bin shanu yana rakiyarsu zuwa inda ake saidawa sai masu shanun su biyashi, sai kuma ya shiga daji yai itace sai ya shiga gidaje ya bada itacen a bashi abinci sai kawo wa kanensa, kudin da yake tarawa kuma idan kanensa yana jin yunwa ko rashin lafiya ta kama shi, zai siya masa magani ne, da haka ya fara faskare, da duk wani aikin karfi da yan'uwan mahaifiyarsa suka samu labari sai suka zo suka dauke su suka tafi da su gurinsu, sai dai hakan be kashe guiwar yayan ba, da yan kudin da ya samu ya saka kenansa a makaranta, kullum kokarinsa na yadda dan'uwansa zai gina kansa ne, da wannan tunanin ya tsallaka zuwa birni yana achaba, daga nan ya fara zuwa kudu, idan ya samu kudi sai yace a bawa Mu'azu, a siyawa Mu'azu abu kasa, a biya masa kudin makaranta, sannu sannu dan'uwansa yana ta karatu shi kuma yayansa yana ta neman kudi saboda rayuwar kanensa ta inganta, achaba da yake a can sai ya karbe shi har ya zamana yana zuwa siyen wasu abubuwa daga nan arewa ya kai can, wani abun kuma sai ya siyo ya zo da shi nan, kamin a ankaro kudi suka taso masa kofafin arziki suka bude masa, sai ya dawo a nan yai aure, ana zaune kalau kanensa yana zuwa makarantar kwana a birni idan hutu ya samu sai ya dawo gida, sai matar yayan ta fara nuna bata son kanensa tana hana shi yi masa wasu abubuwan daya kamata, ganin haka yace ba zai iya sake dan'uwa ba, amman zai iya canja mata, sai ya sake ta ya auro wata, ita ma da ta zo sai ta fara nuna wannan halin, a take ya sallame ta ya auro wata, bayan ya jaddada nata cewar shi kam a duniyar nan be da kamar dan'uwansa, sai matar nan ta rike kenan da mutuncin da amana, shi kuma ya maida hankali gurin kasuwancinsa, har ya zamana yayyunsa da suka wofintar da shi a wacan lokacin suka dawo suna neman ci a karkashin inuwarsa, wasa wasa ya fara siye gonaki da gidaje irin na kauye yana saidawa yana samun riba, kamin kace kwabo ya zama daya daga cikin masu kudin kauye na wacan lokacin duk da kasancewar yana da samarta ba tsoho ba ne, da haka ya fada siyasa sai kuma abun ya karbe shi kofofi suka bude masa, yai taraka kuma ya cinye, sai dai har kanensa ya gama karatu ya tafi jami'a Allah be bawa yayansa haihuwa ba, yana cikin karatun ya hadu da wata a jami'ar suka yi aure, yayan ya siya masa gida a birni suka zauna, ana wata na uku da saurensa ya samu aiki a babban gurin saboda yayansa babban dan siyasa ne na taraiya, a kuma wannan lokacin matar yayan ta samu ciki, a kullum wakensa idan ta haifa masa namiji za a saka sunan kanensa, idan kuma mace ta haifa za a saka sunan mahaifiyarsa, ashe Allah be yi ba zai ga abun da zai haifa, wata rana aka samu wani gurbi na babban matsayi a Lagos, sai ya dage akan sai kanensa za a bawa saboda yana da takardu da duk wani abu da ake bukata, sai dai abu na yan siyasa su ma wadancan suna so, bayan ya bada sunan kanensa da takardunsa, sai abokin hamayyarsa yace ya saurari abun da zai same shi matukar be janye kudirinsa ba, be fada masa baki da baki ba, amman ya fada ta inda zai iya ji kuma ya ji, amman be janye kudirin ba, abun ka da mutanen kauye ana zaune kalau kafarsa ta fara kumbura har ya zamana baya iya zuwa majalisa, har ta kai ko gidansa baya iya fita, cikin sati jikinsa ya kumbura kamin wani makon ya dawo ya ce ga garinku, haka muka ta jimamin rashinsa musamman ne kuma mutuwarsa bata hana Allah hukuncinsa ba na dora ni a wannan matsayin, ashe kuma wani kukan yana tafe a gaba, a lokacin da muke ta murna matarsa ta shiga watan haihuwarta zata haifa mana da ko ya, ashe ban kwana take ta mana ba mu sani ba, ranar da ta haihu aa fiti ana da lafiya kalau mahaifiyarsa kuma ta koma ga Ubangijinta... ”
Tun da Daddy ya fara bawa Talba labarin be mumfasa ba sai da ya kai aya.
“Ka san waye wannan yaya da kanen Mu'az...?”
Talba ya kalli Daddy hawaye na sauko masa, kamar yadda suke saukowa Daddy.
“Kai ne kanen Daddy shi ne Yayanka... ”
Daddy ya girgiza kai yana cige bakinsa da karfin sosai yake yakar zuciyarsa yana hanata kukan dake son gabato masa da shi, daya wuce na zuciya har yake neman muhalli a bakinsa.
“A haka kaka tunanin wata macen zata kalli kwayar idona ta kira dan 'uwana na jini da jini da tsintacciyar mage kuma na kasa fusata na kasa yin komai? Macen da take karkashin ikona da kulawata? Ina raye wata mace tana nuna min tafi son yayanta da dan'uwana na jini? Ina jin sonka a cikin jinina Mu'az, ina jin wani irin son a jini da zuciyata, bana jin akwai wani uba da yake son dansa kamar yadda nake sonka, ko kadan bana son na ji wani abu da zai bata maka rai, zan iya daukar komai ban da a taba ka”
Talba ya mike tsaye hawaye na sauko masa ya nufi windows din office din Daddy ya tsaya. Sai Daddy ya dauko tissue ya goge hawayensa yana kallon Talba.
“Ban taba baka labarin nan ba, saboda bana son ka ji a ranki cewar kai maraya ne, alhalin ina raye”
Talba kamar jiran kalaman Daddy yake, sai ya fashe da kuka marar sauti irin na maza ya jimke hannunsa zuciyarsa na sosuwa da labarin da Daddy ya bashi. Da hannunsa na dama ya share hawayensa sannan ya juyo ya kalli Daddy yana jin wani irin shaukin kaunarsa.
“Ka yi duk abun da ya kamata Daddy, shiyasa ban taba jin maraici ba, kuma ban taba tambayar labarin iyayena ba, ka bani gata ka nuna min kauna wanda ba ko wane mai uba ke samu ba”
“Abun nan akwai ciwo Mu'az, saboda ni ma na taso a maraici, kana ji kana gani abu ya gagareka, kana gani a nun maka abu nan ba naka ba ne, idan aka bata maka rai, babu uwa ko uba da zai rarrasheka ya baka hakuri, musaman ma uwa, shiyasa ba zan taba bari kai maraici ba, idan har kaga ka rasa sai idan bana raye, ko da ma ace na mutu na ginaka kuma na bar maka abun da zai taimaki rayuwarka ba zaka taba rasa komai ba, ba zaka taba kukan rashin uwa ko uba ba, musamman uwa”
Talba ya gyada kai wasu hawayen na sauko masa.
“Kamar yadda na ji a yanzu nan Daddy, amman duk da haka Ina rokon Alfarma a yafewa Momy, ita ma ta rike ni kamar danta, na taso ban ta wata uba ba bayan ita, dan Allah Daddy ka dawo da ita”
“Of course zan dawo da ita, do you think I can live without Amina? Zan dawo da ita amman sai ta karbi hukuncinta, ni ma ina fatar za a daga min kafa”
Talba yayi murmushi idonsa na cika da wasu hawayen.
“Ina kaunarka Daddy, Allah kara maka lafiya”
“Amin Allah ya maka albarka”
“Amin”
Ya amsa sannan ya dauki tissue ya gyara idonsa, sannan ya nufi kofar fita.
“Mu'az ina ka kai yarinyar nan?”
“Gidansu Madina”
“Ka dawo da ita gida”
“A can din ma ta fi sakewa, Madina tana sonta”
“Baka da inda yafi gida, kuma be kamata akaita ko'ina ba, bayan ga inda kake da iko”
“Na ji, amman sai ka fara dawowa da Momy”
Daddy yayi murmushi yana daga masa hannu alamar ya tafi, shi ma murmushin yai kadan ya fice yana jin zuciyarsa wani iri, samun kansa yai a motarsa yana ta sauke ajiyar zuciya, be taba jin irin yadda yake ji a yau ba. Sai dai babu wanda ta fado masa a rai sai Aminatu, shi da be taba ganin iyayensa ba, be san su ba amman a yau yaji yana marmarin ganinsu yana kewarsu balle ita data rayu da iyayenta ta girma tare da su ta san dadinsu ace an raba ta da su lokaci daya, kuma a gaban idonta, ya tabbatar abu ne da ba zata taba iya mantawa da shi ba, ba kuma zai gogu a zuciyarta da idanuwanta ba. A masallacin gurin yai sallah azahar sannan ya fito yana ta tukin ba dan ya san inda zai je ba, baya tunanin zuwa gida a yanzu, dan baya jin zaman gidan zai masa dadi, but ina zai je? Office? No baya bukatar komawa can, gurin Ali? Nope zai fara damunsa da maganar Leila, haka yai ta yawo idan ya gaji da tukin sai ya saka motarsa ya zauna a motar, uku da rabi ya nufi gidan marayunsa be fito ba sai hudu da rabi. Kai tsaye ya nufo gidansu Madina domin zuciyarsa ta bukaci