Showing 15001 words to 18000 words out of 27791 words

Chapter 6 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi

yake.
Abu kamar wasa sai ga shi Rusayyat ta shafe tsawon daƙiƙa hamsin ta na bincike a turakar amma ba ta gano inda garin maganin yake ba kuma a dai-dai a wannan lokaci ne ta jiyo alamun takun sawaye yana kusanto turakar, al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan ta ta ji kamar ta saki fitsari a wando.






BABI NA SHA BIYU


A can Birnin Zainul-Ansar kuwa lokacin da aka cigaba da fafata azababban yaƙi tsakanin dakarun haɗin gwiwa da dakarun musulunci sai yazamana an rincaɓe MUTUWAR MAZAJE ihun dakaru gami da ƙarar karafniyar ƙarafa suka cika dodon kunne, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sama suna zuba a ƙasa JINI DA ƘASA suka cakuɗe babu kyawun gani.
A cikin gidan sarauta kuwa, sarki Nu'umanu da waziri Yazid sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin baƙin zafin nama JURIYA DAa BAJINTA, duk sa'adda takubbansu suka haɗu da juna sai ka ga tartsatsin wuta ya tashi haɗe da ƙara mara daɗin saurare,
Sai da suka shafe tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali suna ɗauki-ba-daɗi amma ɗayansu bai samu nasarar lakutar jikin ɗan uwansa da takobinshi ba har makamansu suka fara dakushewa, yayin da sarki Nu'umanu ya ga abin da ke faruwa sai ya shiga neman taimakon Ubangiji a cikin zuciyarshi yana mai cewa "Ya Ubangijin halitta ka taimaki bawanka mai rauni a bisa maƙiyin addininka".
Tabbas! Ubangiji mai amsa roƙon bayinsa ne a duk lokacin da suka miƙa komai nasu izuwa gare shi,
Ana cikin wannan yaƙi ne sarki Nu'umanu ya samu nasarar yiwa waziri Yazid wani lafcecen sara a kafaɗarshi jini ya yi tsartuwa, kafin ya sake mayar da wani martanin waziri ya kaiwa masa wani bahagon sara a kafaɗarshi, duk da irin zafin naman da waziri ya yi wajen kaucewa saran sai da takobin ta yi masa rauni jini ya yi tsartuwa,
Kafin shudewar daƙiƙa talatin kowannensu ya yiwa abokin faɗanshi rauni fiye da guda goma layi na ɗibarsu tamkar waɗanda suka sha barasa suka bugu,
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Nu'umanu kai kenan kuma ba shi mamki bisa ganin cewa duk da yana neman taimakon Ubangiji amma ya gaza samun nasara akan abokin gabarshi,
Abin da sarki Nu'umanu bai sani ba shi ne, kamar yadda yake neman taimakon Ubangijin Musulmi haka shi ma waziri ya ke yi.
Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "makashin ka yana nan tare da kai" kuma da zama da munafiki gwara zama da ɓarawo, domin shi dai munafiki yana tare da kai ne kuma yana cutar da kai ba tare da ka sani ba, shi kuwa ɓarawo sai ya ga kayanka zai ɗauka, yanzu dai ga shi Sarki Nu'umanu yana artabu da wazirinshi amma bai sani cewa shi ne abokin gabar shi ba,
Ana cikin wannan yaƙi ne sarki Nu'umanu da waziri Yazid suka cakawa junansu tsinin takubbansu a cinyoyinsu na hagu take wajen ya dare jini ya yi tsartuwa, a lokaci guda suka zube ƙasa magashiyan suna masu nishin wahala, a cikin wannan hali ne waziri ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi na dama ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
A lokacinne waɗansu likitoci suka rugo izuwa wajen ɗauke da gado na ɗaukar mara sa lafiya aka shigar da shi izuwa cikin gidan sarauta domin ba shi taimakon gaggawa.




***
Al'amarin aljani Lattul-kifas kuwa, wato hadimin boka kaddadul-Gurub da ya tura domin farauto mashi yaro mai hatimin takobi domin ya yanka shi ya sha jinin shi,
Tun sa'adda ya kammala fafata yaƙi da dakarun dake gadin gidan shugaban 'yan fashin duniya ya kwanta barci, bai kwanta ba har sai da gari ya waye rana da ƙwalle sannan ya farka ya yi miƙa gami da hamma,
Sannan ya miƙe tsaye yana nazarin Ƙofar da zai shiga gidan ko da kammala nazarin sai ya kaɗa fuka-fukanshi ya tunkari wani sashi, lokacin da ya rage saura taku goma ya isa ba sai kawai ya ji an ɗamƙe shi an shaƙama shi wani sinadari a hanci barci mai nauyi ya ɗauke shi,
Bai tsinci kanshi a ko ina ba sai a cikin ƙasaitaccen kurkuku mai matuƙar kwarjini, duk inda ya kai dubanshi a kurkukun babu abin da zai gani face bayi, da barori na jinsin mutum da aljan suna ta kai komo suna aiyukan wahala waɗansu kuwa ana gana masu ukuba nau'i daban-daban.
Sa'adda aljani Lattul-kifas ya tsinci kanshi a cikin wannan kurkuku sai ya firgita ainun jikinshi ya kama tsuma bai sa'adda ya saki fitsari a wando ba, kawai sai ya yunƙura da nufin ya tashi sama, amma sai ya ji shi ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa,
Yana cikin wannan hali ne waɗansu irin samudawan dakarun aljanu biyu suka tusa ƙeyarshi izuwa wani ɗaki na musamman a kurkukun wanda aka gina shi da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske,
A tsawon rayuwar Lattul-kifas bai taɓa gani ko jin labarin kurkuku mai ɗauke da musibu da annoba tamkar wannan kurkuku ba,
Shi dai wannan kurkuku ana yi masa laƙabi da Sarirul-Maut, ma'ana matattarar dukkan musibun duniya, bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa tun bayan rushewar kurkukun Sarkin bokayen duniya na farko wato boka shuyuɗan mai mallakin ANNOBA ƊARI ba a samu kurkuku mai ɗauke da musibu da nau'ikan azaba tamkar kurkukun Sarirul-Maut ba.
Ba wani ba ne ke ɗauke da mallakin kurkukun ba face sadauki fitinatul-Amir shugaban'yan fashin duniya, fiye da kaso hamsin na musibun dake kurkukun ya sana'anta su da ƙarfin shirin tsafi, kuma babu wata nau'in dabbar daji mai cutarwa da babu ita a cikin kurkukun, kuma a tarihin kurkukun ba a taɓa samun wani mahaluki da ya shiga kuma ya fito a raye ba.


***
Al'amarin sadauki ukaiza kuwa wato shugaban dakarun sarki Lamsarul-Azlam da ya tura domin farauto ma shi yaro mai hatimin takobi, sai da dare ya tsala sannan ya durfafi hanyar da zata sada shi da birnin Baitul-Ashmar, lokacin da ya zamana saura bai huce taku talatin tsakanin shi da birnin sai kawai ya yage wani yanki a tufafinshi ya rufe fuskarshi da shi ta yadda babu wanda zai iya gane shi, sannan ya durfafi ƙofar birnin,
Lokacin da dakarun dake tsaron ƙofa suka hango shi sai suka dafe kuben takubbansu domin jiran ko ta kwana,
Yayin da ya iso sai wani basamuden ƙato daga cikin dakarun wanda da alamu shi ne shugabansu ya dube shi da 'yan mini-minin idanuwanshi masu kama da garwashi saboda ja da suka yi ya dakama shi tsawa mai firgitarwa sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIKAR MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce "Shin wane ne kai? Kuma mene ne ke tafe da kai izuwa wannan birni namu mai albarka?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai ukaiza yayi shiru yana zurfafa cikin kogin tunani,
Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne shin yanzu zai miƙa wuya ne ga sarki Lamsarul-Azlam bayan cewa bai san halin da iyalanshi ke ciki ba?
Baka da wata mafita da huce ka yaƙi waɗannan dakaru domin ka isa inda iyalanka suke, ina amfanin ma miƙa wuya bayan baka da tabbacin ya lafiyarsu take.
Lokacin da Ukaiza ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya kame bakinshi ya yi tsit! Ba tare da ya amsa tambayoyi da shugaban ƙafa ya yi masa ba,
Al'amarin da ya fusata sarkin ƙofar kenan ya dakawa yaransa tsawa dake nuna ba su umarnin su afkawa mashi,
Cikin hanzari suka zare makamansu suna ihu da kururuwa mai firgitarwa su ka yi ɗauki kanshi kafin da isa gare shi sai suka cika da matuƙar mamaki, abin da basu mamaki shi ne yadda tsananin yawan su bai firgita baƙon ba tabbas wani sirri game da shi domin Ruwa baya tsami banza! Kuma idan ka ji makaho ya ce ayi wasan jifa to yaji ya taka dutse!
Lokacin da ya rage saura taku uku tsakaninsu sai Ukaiza ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a damtsenshi ya yi wata irin katan-tanwa a ƙasan dakarun take ya sare mutum goma ƙafafu suka zube ƙasa guragu suna masu kurma wawan ihu,
Sannan ya afkawa sauran aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro daban al'ajabi.








Mu haɗu a TAFARKIN TSIRA littafi na 7 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
08137237071




TAFARKIN TSIRA 7
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan yaƙi
Wthapp Number
08137237071






ELEGANT ONLINE WRITER'S




Littafan Marubucin


Kogon Annoba
Sarautar Mutuwa
Kangin Bauta
Jaruman Duniya
Takobin Ɗaukaka
Ƙarshen Zalunci
Fataucin Bayi
Sarkin Sadaukai
Goga Sha Fama
Tafarkin Tsira
Gasar Sarauta
Kundin Al'ajabi








BABI NA SHA UKU


Sa'adda muridi Zabratul-ukub ya samu nasarar ɗaukar wannan kyakkyawar dudurwar da ta fafata yaƙi da dakarun sarki Lamsarul-Azlam, kuma ya ɓace ɓat! Cikin alƙalumman sihiri, yana cikin wannan hali ne sai ya ji jikin shi ya ɗauki zafi, ba shiri ya bayyana ba a tsakiyar wani makeken fili mai ɗauke da rairayi, yana sauka sai ya duba tafin hannunshi aikuwa sai ya gan shi wayam babu wannan kyakkyawar dudurwa, cikin hanzari ya ɗaga kanshi izuwa sararin samaniya nan take ya yi arba da wani kyakkyawan aljani ɗauke wannan kyakkyawar dudurwa wato gimbiya NUWAIRAT yana tsala gudu a sararin samaniya, kafin ƙiftawar idanu ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Cikin matuƙar takaici Zabratul-ukub ya ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, a lokaci guda kuma ya turɓune fuska, sannan ya sake ɓacewa a karo na biyu bai bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar fadar sarki Lamsarul-Azlam ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuye,
Lamsarul-Azlam ya daka ma shi tsawa wacce ta sanya hantar cikin kowa dake fadar ta kaɗa saboda matuƙar tsoro, a lokaci guda ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da WASIƘAR MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce "Ya kai Zabratul-ukub shin wane irin rashin hankali ya sanya har ka yi sake gimbiya Nuwairat ta suɓuce daga hannunka ? Tabbas ka aikata babban kuskure a gare ni, na rantse da girman halarar tsafina sai na gana maka nau'ikan ANNOBA ƊARI wacce ba a taɓa yiwa wani mahaluki ita ba.
Ko da gama faɗin hakan sai ya nuna Zabratul-ukub da ɗan yatsanshi na hagu take nan take waɗansu irin sarƙoƙin wuta suka ɗaure shi hannu da ƙafa, nan fa ya shiga yin kururuwa da neman agaji saboda yadda sarƙoƙin ƙe ƙona sassan jikinshi,
Al'amarin da ya firgita Al'ummar fadar kenan kuma cikin ya ɗuru ruwa, waɗansu har suna sakin fitsari a wando,
Sa'adda Zabratul-ukub ya ga cewa a koda yaushe zai iya rasa rayuwarshi sai ya shiga yin magiya yana roƙon sarki akan ya cewa idan har ya ƙyale shi zai kirawo dukkan jinsinsu na muridai su je su yaƙi gaba ɗaya jama'ar birnin MADINATUL-AFNAN ko da kiyashi ba za su bar shi a raye ba,
Ko da jin wannan magajiya sai sai sarki ya yi nuni gare shi a karo na biyu take sarƙoƙin suka ɓace ɓat! Daga jikinshi tamkar ba su taɓa wanzuwa ba,
Sannan ya dube shi ya ce "Ka sani cewa kwanaki uku kacal na ɗaukar maka idan har aka samu matsala kafi kowa sanin abin da zai biyo baya,"
Cikin ladabi da ƙasƙantar da kai Zabratul-ukub ya ce muryarshi na rawa "Godi-ya na-ke ya ma-i du-ni-ya",
Yana gama faɗin hakan ya shafi shimfiɗar fadar ya sake ɓacewa a karo uku tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
A sannanne jama'a suka dawo cikin hayyacin su, shiru ne ya wanzu a fadar tamkar an yi ruwa an ɗauke, daga can sai sarki ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki ya dubi sarkin yaƙi ya ce "Ya kai dirkar birnina ka yi sani cewa ina so ka fara shirye-shiryen fita yaƙi ina so alfijir ɗin kwana biyu masu zuwa ya keto a lokacin da muke tsaye a Ƙofar birnin MADINATUL-AFNAN, domin wannan yaƙi da zamu fita ya bambanta da sauran yaƙoƙi, domin dole ka haɗa mana rundunar ƘARE DANGI,
Ko da sarkin yaƙi Huzmal ya ji wannan batu sai ya risina ya ce "An gama ya shugabana yaba gama faɗin hakan ya miƙe tsaye tsam! Daga kan kujerarshi ya durfafi ƙofar fita daga fadar,
Kallo ɗaya zaka yiwa Sarkin yaƙi ka fahimci cewa ya cika gwarzon Jiya, domin ya tara ƙwanji, kwarji da Haruna, komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da shi sai hantar cikinshi ta kaɗai,
Ko da ficewar shi sai sarki Lamsarul-Azlam ya tafi ya shiga izuwa gidan sarauta dakaru na take masa baya, nan take fadar ta watse kowa ya kama gabanshi tamkar wata halitta bata taɓa wanzuwa ba.


***
Lokacin da Rusayyat ta ci gaba da gudanar da bincike a turakar maigidanta sadauki fitinatul-Amir domin ta gano wannan garin magani na sihiri don tseratar da rayuwar yaro Usaiba mai hatimin takobi, lokacin da ta ji alamun takun sawaye na tunkaro turakar, sai kawai ta miƙe tsaye zumbur! Ta ruga izuwa bakin ƙofar shigowa ta sanya idanuwanta a tsakiyar wata 'yar siririyar ƙofa dake jikin ƙofar, nan take ta hango cewa ashe wata kuyanga ce ɗauke da wani ruwa a cikin kasko, nan take ta cika da matuƙar farin ciki, jim kaɗan ƙofar ta buɗe, Rusayyat ta dakawa kuyangar tsawa cikin matuƙar fushi ta dube ta ta ce "Ya ke Hulaifa shin mene ne ya kawo ki nan ? Bayan cewa an kawo dukkan abin da na buƙata ?
Ko da jin wannan tambaya sai jikin Hulaifa ya kama kyarma ta buɗi baki cikin ladabi ta ce "Ki gafarce ni ya shugabata na manta ne ba a kawo ruwan ɗauraye hannu ba ne, shi ne yanzu na kawo",
"Bama buƙatar komai yanzu".
Rusayyat ta bata amsa.
Hulaifa ta risina sannan ta juya ta fice daga turakar, dakarun dake tsaron ƙofar suka sake kulleta,
Kawai sai Rusayyat ta koma izuwa cikin turakar ta cigaba da binciken cikin hanzari, cikin sa'a ta samu nasarar gano garin maganin, cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta sanya shi a cikin aljihun rigarta na hagu, sannan ta sanya hannunta a aljihun na dama ta ɗauko hodar banju ta taka da ƙafafuwanta izuwa wajen da teburin abinci yake ta buɗe kofin dake ɗauke da taceccen ruwan inibi ta zuba a banjun a ciki, sannan ta mayar ta rufe ta zauna a ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun dake wajen.
Jim kaɗan da aiwatar da hakan sai ƙofar da ke ɓangaren yamma a turakar ta buɗe sai Fitinatul-Amir ya bayyana sanye cikin tufafin alfarma irin na hamshaƙan sarakai, wani irin daddaɗan ƙamshi na tashi a jikinshi,
Haƙiƙa shigar ta yi matuƙar fito da tsantsar kyawunshi, domin babu wata mace da za tayi arba da shi a cikin wannan yanayi face ta kamu da matuƙar ƙaunarshi,
Yayin da Rusayyat tayi arba da shi sai miƙe tsaye tsam! Ta tare shi suka rungume juna na tsawon daƙiƙa goma, sannan Fitinatul-Amir ya janye jikinshi daga nata, sannan ya ja hannunta har izuwa inda teburin abincin yake suna zaune a bisa kujerun,
Ba tare da wani jinkiri ba suka shiga kimtsa cikinsu suna fira cikin nishaɗi da tsantsar soyayyar juna, cikin matuƙar farin ciki Rusayyat ta ɗauki kofin da ta zuba wannan banju a cikin shi ta sanya wa mai gidanta a bakinshi ya shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ya sha ya ƙoshi,
Bayan sun kammala kalacen ne Rusayyat ta lura idanuwan mai gidanta sun fara lunshewa, sai ta dube shi cikin tattausan murmushi mai ɗimauta zuciyar masoya ta ce "Ya uban 'ya'yana lafiya kuwa na ga alamun ɓarci a fuskarka?
Koda jin wannan tambaya sai Fitinatul-Amir ya yi murmushi a gare ta sannan yace " kwarai kuwa zancenki duste ya abar kaunata, haƙiƙa ina jin barci mai nauyi sosai, koda gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye tsam! Ya kama hannun Rusayyat suka nufi wani ƙasaitaccen gado a turakar ya kishingiɗa akai, kafin Rusayyat ta yi wani yunƙuri har ya fara aikin rago idanuwanshi sun rufe,
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa Rusayyat ta miƙe tsaye zumbur! Ta fice daga turakar,
Kai tsaye turakar su yaro Usaiba ta nufa, duk inda ta gifta a gidan sarautar sai dai kaga dakaru, kuyangi, da bayi ba zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa,
Lokacin da ta shiga turakar ta su sai ta iske har yanzu barci suke yi ba su farka ba, cikin matuƙar farin ciki ta ɗauki garin magani na farko ta buɗe gadon bayan yaro Usaiba ta shafa masa, nan take zanen hatimin takobin Saiful-zayyad ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Sannan ta buɗe bakinta ta karanta dalasiman tsafi ta tofa akan garin magani na biyu wanda shine kaɗai zai iya ƙarya shirin zanen hatimin takobin ya bayyana, tana gama rufe bakinta garin maganin ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
A sannanne ta ja wata doguwar ajiyar zuciya, kuma ta ƙurawa Yaro Usaiba da 'yar uwarshi Hairat idanu hawayen farin ciki suna kwaranyo mata,
Domin a halin yanzu ta samu nutsuwa a zuciyarta tun da ta tseratar da rayuwar yaro Usaiba mai hatimin takobi daga sharrin mai gidanta shugaban'yan fashin duniya dake farautar shi dare da rana domin ya hallaka shi,
Wannan shi ne abin da ya faru da Jaruma Rusayyat da mai gidanta Sadauki Fitinatul-Amir.




Lokacin da lokacin birnin Zainul-Ansar suka ɗauki sarki Nu'umanu bisa ƙasaitaccen gadon marasa lafiya suka shiga da shi izuwa cikin gidan sarauta, sai suka huce kai tsaye da shi izuwa turakarshi suka shimfiɗe shi suka shiga duba lafiyar shi, suka ɗinke duk wani rauni dake jikinshi aka sanya masa magani, wani abu da ya bawa likitocin mamaki shine, duk da sarki Nu'umanu yana cikin halin jinya amma bakinshi bai gushe ba wajen ambaton Allah da yiwa annabin shi Salati.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa hamsin likitocin suka kammala aikin su, kawai sai wani dattijo ma'abocin haiba daga cikin likitocin ya ɗauki wani ruwan magani dake cikin kofin azurfa ya sanya hannunshi ɗaya ya tashi kafaɗun sarki domin ya ba shi maganin, amma sai sarki ya dakatar da shi ta hanyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login