Showing 93001 words to 94165 words out of 94165 words

Chapter 32 - TA FITA ZAKKA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

su ya Jafar har ta bar Duniya bata taba Daga baki akansu ba sai ita kadai da ta fita Zakka cikin ya"yanta..!
Karfe Daya na rana aka saka za"ayi Jana"izarta zuwa Lokacin harta kannen iyayenta da suka rage na nan Gumel din sun zo sai wata goggonta goggo Jumai Sun zo suna gidan Sai su ya Zulaihat da suna Jigawa Labarin Rasuwar ya isketa sai ya Ikram da ke kusa duk suna nan gidan suna ta kuka Goggo Husai Mallam da kansa ya Kirata ya Fadamata,Ita ta shaidama Jadwa wanda akace sai da ta suma Mijinta na chan na nema musu Visar tahowa sai Mutanen gusai da Aba ya Kirasu ya shaida musu..!
Jaleela kuma ya kira mijinta ya Fadamai shi ya Fadamata sai kuka Domin mutuwar farar Daya tafi shiga Jiki sosai ance sun samu Jirgi sun taho Ita da megidanta da ya"yanta da Ya Nazir da matarsa tafiyar su daya..!
Sai ya Jamila Dake gombe ita din ma Mijinta aka kira aka Fadawa yace suna Tafe suma,Jawahir kuma da yan Gusai zata taho Allahu akbar rai bakon Duniya..!
Zulfa ma an gayamata tana Hanyan Tahowa ita da Nazeem Uzairu na Exam,sai Zahra Dake parthercourt Itama Tafiyar Jirgi tace zatayi sauran Iyalan Baba Mallam na kusa duk sun ce suna Hanyar Tahowa..tunda Rasuwar ta Safe ce..!
Dan mallam Dake chan Madina abakin Ya Nasir yaji Rasuwar Yaya Mutuwar data sanyayamai jiki matuka yana cikin makaranta sanda yaji Rasuwar ko kafin ya koma gida Sakina taji Labari itama cikin Tashin hankali ya fita nema musu Visar tafiya shi da Sakina Sarood nan zai barta Saboda kada Zirga zirgan tayi yawa..!
Ko kafin karfe Dayan an gama Hada yaya,Hajiya Babba da Wata Tsohuwa daga Gusai da suka iso suka hadu suka mata wanka suka shirya har alokacin Amina bata bar dakin ba kuma ko Hawaye Daya batayi ba..!
Kofar gida kuma ya cika Damkam da Jama"a tunda har agidan Radio an Sanar da Rasuwar zuwa Lokacin yan gusai sun iso sannan Ya Fati dake Dutse ta iso ita da Ya akila da Jidda ko"ina ya cika ba matsaka tsinke domin Yaya ta jama"a ce uwa uba kuma Aba dasu ya Jafar da abokan aikinsu sun cika wajen Allah sarki Aliyu abokin Danmallan yazo Jana"iza Tunda Umar ya fadamai yace sai yazo ya samu Janaza..!
Gida bai kara Daukan Kuka ba sai da aka zo fita da gawa bayan an kira duka Ya"yan Aba domin su mata addu"a wadanda suka iso kenan Ya Jawahir da ya Jafar sune manya sai su Amina da su hamida addu"a suka mata da Fatan dacewa Har Hamida da Hanne sun duka gaban gawanta sun mata addu"a Amina kuma sai da Hajiya ta Dukar da ita gaban gawan tana Fadin"Mamah yi ma mahaifiyarki addu"a..!
Sai ta zama out of Control yan"uwanta nata basu damu da Rashin kukanta ba susan bata Damu da yayan ba sai dai abunda basu sani ba awannan gabar Amina ta fisu bukatar uwa a raye domin ita ke cikin Tsaka mai wuyar da Uwace kadai zata Tsaya akanta da addu"a ammh kuma addu"a uwa ga ya"yanta har gaban Abada bata yankewa..!
Tana gaban gawan Kanta sara mata yake yi gabadaya yan Dakin sun koma masu fararan kaya haka take ganinsu kuka take so tayi ammh ta kasa kawai sai ta Sulale ta Rumgume gawan Yaya tana Fadin"Ki yafemin Ki yafemin..MAMA..!


Haka take ta fada cikin ihu Saboda tana so tayi kuka ta kasa sai Tsausayinta ya kamasu Da jawaad suke Tsausayamawa ammh Halin da suka ga Amina sai Rauni ya Tarun musu mamanmu na wajen tana ta kuka Hajiya Babba ke fadan ba kyau wannan kukan da suke mata..!
Ya Jafar ne ya jawo Amina Jikinsa ya Rumgume su ya Nasir suka kama gawa zasu fice tana ganin haka ta fara Fizge fizge tana Fadin"Ku bar min gawanta..Don Allah ku bar min ita..!
MAAMA...!


MAAAAMMAA..!!!!


Hake take fada cikin karyen Sautin da duka kowa yasan ba Sautin Amina bane Ana fita da gawan ta fara Bige Bigen da sai da tafi karfin Jafar su Hajiya suka taso suka sakamata karfi. Da Karfi take fadin"Ku dawomin da ita..Mamatace..!
Haj Nasara na sharan Hawaye tace"Allah sarki..akace Uwa uwace Ko da akan Bola take kwana..!ba wanda yayi Tunanin Amina zata damu don Yaya ta bar gidan Duniya..!
Ana gama Fita da gawan sai ta Daina ihu da Fizga ta koma kuma ta Sume musu kamar yadda aka kwashi mamanmu da ya Jawahir suma sun Zube kai anga Tashin hankali gida ya Rude da koke ba wanda akayi mamakinsa sai Aba ya nuna Jarumta ko Daya ba wanda yaga kukansa Dashi aka sallaci gawan Yaya aka kuma kaita makabarta yana rike da Hannun Jawaad da yaci kuka ya koshi..Aba bai yi kuka ba sai da Mallam yace ya matso shi da Ya Jafar da Ya Nasir da yan"uwanta suka sakata Cikin Kabarinta su ka kuma Debo kasa suka Rufe dashi sai alokacin yaji kuka ya taho masa Baba Mallam na bashi baki kan kabarinta ya Duka har su ya jafar suka gama mata addu"a bai tashi ba Fadi kaawai yake,"Tun zamana da ita bata taba Sabanin da gangan ba..Allah ya jikanki Hadiza har abada bazan samu makwafinki ba..!
Dakyar Baba Mallam ya rikosa suka bar makabarta suka Dawo nan Haraban gidan Mallam aka Saka Dardumai da Tabarmu ana karban gaisuwan maza, mata kuma suna cikin gidan Aba ko"ina Kaje sai yabon yaya ake yi ba wamda zai Bude baki bai Fadi Alherinta ba an samu su Amina sun Farfado sai dai ita Tunda ta Farfado bata kara mgana ba kuma bata kuka tana kusa da Hajiya kogaisuwa akazo sai dai tabi mutane da kallo..!
Sai Dare gidan ya kara Rudewa isowar sauran baki su ya Zahra da ya Zulfa da su ya Jaleela da yaya Jameela sai ya Nazir da Matarsa su ya Aisha duk sunzo karon farko zuwansu gida ba cikin Dadin rai ba,ya Sadiya ce bata zo ba suna Ameriaca inda Mijinta ke aiki tadai kira tayi gaisuwa..!
Ita Mutuwa daman ai bata da Sabo..ko abinci ba wanda ya Nema duk da ana ta kawowa Sadaqa,haka wadanda Mutuwar ta shafa sukayi kwanan zaune suna kuka da addu"an Allah ya jikan Yaya su ya jafar kuma suna waje suna karban gaisuwa sai dai in Mazan sun nemi shigowa sai suyi musu Jagora..!
Ko su saka su shamsu su shiga dasu hatta yan makarantar Islamiyansu da Hadda sun zo gaisuwa su da Malamanau da Dalibansu Sai alokacin akaji Amina tayi mgana data amsa gaisuwan mariya yar ajinsu Sa"adatu duk suna nan gidan suna tare dasu Hanne duk wani mai imani in yaga Amina sai ya tsausaya mata ta Fyade ta rame bata ci bata sha sai an matsa mata..!
Ranar da akayi sadakar uku Goggo Husai ta iso da ita da Jadwa sai mutuwar ta Dawo sabo aka fara koke koken Zuwa yammah sai ga Yaya Danmallam da Sakina sun iso suma..!






*AKWAI SOFTY COPY DA HARDCOPY NA LITTAFIN GIDANMU MAI BUKATA SAI YAMIN MGANA SANNAN LITTAFIN ZAMAN GIDANMU MAI CIKE DA KUNCI SHIMA ZA"A SAMESA A SOFTY COPY DA HARDCOPY KAN FARASHI MAI SAUKI A TUNTUBE NI TA WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI 09069067488*












*Janafty*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login