Showing 42001 words to 45000 words out of 129912 words
Chapter 15 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Real Ladingo.txt
cak ya dauketa zatayi ihu ya mutse bakin sama ya haura da ita Dan yaji dadin mata mugunta bedroom dinsa ya kaita yana shiga ya sabketa ya matseta abango kiciniyar matsawa take Dan tasan idan ya dosa mugunta zai mata murmushi yayi" haba yarinya ina zaki wlh sai na Rama mata Akan me zaki dokarmun 'yata cike, da tsoro tace" yo ba itabace ta shiga sabgata matseta yayi da bango ya rike kanta yana goga mata kirjinsa ya tallabo kanta yana sakar mata
murmushi yana daga mata gira yana tambayarta nayi kiss kai ta kauda ta cika tayi fam Dan tasan mugunta ya shirya mata juyo da ita yayi ya had'e bakinsu saida ya mata tsotsar dadi har ta sakankance tanajin dadin tsotsa taji ya kantsara mata cizo aharshe da kafi ya dawo ya kamo labbanta yana cicizawa cikin mugunta tun tana daurewa tana hawaye har ta fara kuka tana dukan kirjinshi sai ya taune mata baki sukayi jajur tana kuka harda shasheka ya saketa yana dariya" Allah gobema bintu ki sake dukan Rauda kigani kawai cin zali ke wa yaci zalinki biyosa tayi tana kuka" wlh bazan yardaba kalli bakina sun kumbura wlh kaine kaci zalina gwalo ya mata ya fice da gudu yabar mata dakin ya sabko k'asa Rauda na zaune da chocolate ba kadanba sai ci take gunta ya nufi ya leka zahara yaga bacci take dauketa yayi daga Dan gadonta ya rumgumeta yana mata kiss Rauda na dariya "Dady kana son baby karama dani ko "ai Dole kuma kuna sona kamarmu daya tafiyar bintu yaji da Sauri ya ajiye zahara ya bar gun ya nufi bedroom d'insa yanajin wayoyinsa cikin aljihu sunyi ringing yafi akirga ya kalli su muneerat "yaran kirki sannuku atare sukace "yauwa babamun kai ya girgiza ya fice Bintu ta bishi da harara Rauda na ganin bintu ta Mike tayi gun yan uwanta, bayan Aliyun tabi tana gunguni
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bangaran Teemah tana shiga cikin a parlor ta isko malika su shoriem sunzo sai wani turo baki take ta isa gun malika ta zauna" ah amare babu ko sallama kwanciya tayi jikin malika ta rufe idanunta tana turo baki" kai anty nafa yi sallama bakiji bane hajiya tace na gaisheku, wlh tanada kirki sosai kamar ta goyani"ah masha Allah naji dadi muna amsawa " anty kinsan me?" inafa sai kin fada " yo ba matar Haidar bace taje dan karya harda cewa yarsa ta rasu Ashe damunace shiko ya wani rumgumota ko kunya basaji ni wlh sunban haushi ai ko hajiyarmu sama kara ko ta fada tana kunkumbura idanu Malika ta zaro dan ta gano kanwarta tsagwaron kishine ke damunta rumgumota tayi" haba Autar iyayye yi hakuri mana kirika boye kishinki kefa kikace sunyi tunanin yarsu ta rasu kinga ko ai Dole zai rumgume matarsa ya lallasheta ko agaban waye Allah yasa baki nuna damuwarki ba? " yo ni ina ruwana dasu sucinye junansu ma mana" oh ni Malika mu'azzam ne ya shigo
"Malika gaya masa, tayi abinda ya faru aikuwa, ya bushe da dariya Teemah ko ta cika tayi fam" to Matar gwamna ashema kinaso yanzu babu maganar rabuwa ko? "yo ni cewa nayi ina sonsa ne kawai dan na tayar da, zance shikenan ni nama tafi mik'ewa tayi ta nufi bedroom Rasheed ya bita mu'azzam ya gayama Malika yada sukayi Da Aliyu "to my darling ai kuwa Dole mansurah ta dage da gyara ana jibi biki sai mutafi da sauran abubuwan gyaran zan karasa mata acan wayarsa ya ciro a aljihu ya kira hajiya mansura ya mata bayani tace" babu matsala daga gobe zata fara mata gyara na tsawon kwana biyar amma dukanta gidanta zata koma sai ranar tafiya zasu zo su dauketa dan abubuwa dayawa zata koya mata ba dare ba rana godiya mu'azzam ya mata ya kashe wayar sukaci gaba da hirasu Teemah tana shiga, ta cire kayan jikinta ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tayi shirin bacci ta Haye gado ta kashe, wutar d'akin wayarta ta dauka karfe, shadaya na dare taga bai kirataba baki ta turo " ai dama nasan ba kiraba zakayi an hanaka ko nima, bazaka sameni ba bari na kashe wayata dama ba sonaba kake Nice, nake haukana My Haidar ni nasan zamanmu bazai yuba ta fada hawaye na zubowa saman fuskarta wayar ta kashe baki daya tayi jifa da ita ta shige bargo tana kuka" wayyo my chocolatyna kuka take tin karfinta har tagaji bacci ya kwasheta hawaye, sun bushe mata afuska, asubah ta gari
Bangaran Aliyu kuwa Bintu ce ta sakashi a gaba da fitina sai daya ya dawo mata Aliyunsa sak yasamun kanta tayi lakwas yanzu haka tana bedroom d'insa rumgume take ajikinsa tana kallonsa yada ya birkice mata, ko kallo bata ishesa ba wayarsa yake yana dariya Dole ta sabko tana kallonsa takirasa"my man buris yayi da ita fuskarsa ta shafa"nace kayi hakuri kaji my man sanin idan yan buris din sunzo tofa bazai kulata ba Dole tayi shiru ta lafe jikinsa tana shafa gefen fuskarsa har bacci ya dauketa haka yayi ta amsa waya da mutane yana rumgume da ita sai shabiyu da rabi ya janyeta jikinsa yana murmushi ya dauketa ya kaita dakinta ya saka mata kayan bacci ya kwantar da ita ya mata kiss agoshinta" wlh duk nasan maganinku haka kawai kukeson haukatani sai kace akaina aka fara auren mace biyu duk kishin yabi ya adabeku fitinanun matana duk zanyi maganinku ya fada yana shafar fuskarta yaje ya dauko zahara ya rumguma mata ita ya tofesu da Addu'a ya lullubesu da blanket ya dauki Rauda ya tafi da ita d'akinsa ya kwantar da ita a makeken gadonsa waya ya dauka ya kira teemah wayar akashe murmushi yasaki" My Noor duk zaku sani ne wayoyinsa ya kashe baki daya ya shige bathroom yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito ya bude wardrobe ya ciro jallabiya fara tas ya saka ya fesa turare ya shimfida Dadduma ya tayar da sallah, raka'a hudu yayi yajima sosai yana Add'ua ta yama matansa Addu'ar Allah ya rabasu da zafin kishi Allah yabasu zama lfy yabashi ikon yin Adalci tsakaninsu Allah ya shirya masa, zuri'a da Al'ummar musulumi baki daya sai karfe biyu ya gama ya Mike ya nufi CC TV camera yana kallon cikin gidansa zuwa titin gidan shiru babu kowa tsakar gidan ma haka sai sai sojoji da bindigogi suke shawagi kai ya girgiza ya cire jallabiya ya saka kayan barci ya hauro gadon ya tofe Rauda da Addu'a ya kashe wutar dakin ya rumgume yarsa ya jamusu blanket yana karanto Addu'ar bacci bai wani jimaba bacci ya daukesa asuba ta gari,
***********************************
*bayan kwana hudu*
yau kwana biyu da aka kai kayan Teemah garin sarki Su halima ne suka kai yayar Aliyu dasu Safah da marwa da maradiya kanwar hajiyarsu Aliyu kayane na kece raini motocine guda biyu lumtsuma kumtsuma aka tafi dasu ranar fah kauyen garin sarki ba masayar haki akwatunane 24 shake da kaya na kece raini Aliyu yama teema sun samu tarbar karamci anyi dafe dafe Abba ya rasa inda zaisa kansa dan farin ciki iyayye ko harda su kuka tace bazasu amshi kayanba su ba siyar da yarsu zasu ba ya za'a kwaso kayan kanti guda ace kayan mace dayane abin yana su halima dariya suna mamakin irin wannan kauyanci amma kuma sunji dadi dan uwansu yayi aure gidan mutumci abin duniya baya gabansu kwanansu daya suka juyo Safah dama amatse take dan haushi takeji ita yar wajan bintu ce batayin teemah dan ahaukanta da taga kursu kawar teemah tana washe baki sai mutane take ja yowa tana shiga tana fita ana cemata kaga manyan amare ta zata itace sai yawu take zubarwa tana mamakin ya akayi yayanta ya kwashi kucaka yar kauye Allah Allah take sukoma Gombe ta fadawa bintu Amaryata kucakace k'azama dan sam bataji lokacin da akace amarya na Gombe sai jibi aure zatazo haka suka baro Gombe washe gari taje ta rarab'awa Bintu abinda ta gani harda pic d'in kursu ta dauko aikuwa Bintu dariya harda rike ciki tace" wlh indai akan wannan kucakar ne to nabar kishi aruwan sanyi zan kori shigiya ko kamshin my man bazata shakaba bare ya rumgumota jikinsa ahaka suka rika kullu yada zata azabtar da ita har tabar gidan shiyasa bintu ta saki jiki da mijinta dama kwana biyu miskilincinsa na kansa shan kamshi yake mata dan yasamu kanta yaga idan ya zuba mata idanu fitina zasu rika masa agida itama kaya ya hadama bintu na kece reni da, zunzuru tun kudi million guda ganin fuskarsa babu wasa, ta amsa tayi godiya tana zuwa dakinta ta rufe tayita rusar kuka tana tsinewa teemah albarka da ta auri mijinta duk tasan kaddara ce ba sonta zaiyiba amma ta
Kasa sama zuciyarta hakuri akan abun amma yanzu bata nunawa agabansa bangaran teemah kuwa cikin kwana hudunan wlh idan baka mata farin saniba bazaka ganetaba dan gidan mansurah aka maidata kuma da sanin mijinta mu'azzam ya fada masa sai jibi aure za'a tafi da ita shiyasa ma ya barta ta ajiye hankalinta akoya mata abinda yasan shine zai anfana ko kiranta bayayi dan yasan fitinace zata masa teemah tana shan gyara cikinta da wajanta tana shan murza jiki da wasu irin turaruka da l'alle wani irin tsumine ake mata nasha jikinta sai sheki yake ga wani uban kamshi da take abubuwan ake koya mata akullum basuda adadi sam bata boye mata komaiba tunba wajan kwanciyar aureba da kukan kisa yada, zata rika masa, ya, haukace mata kuma ko batajin dadi ta nuna tanaji tamkar zata zauce ta rika masa, kuka mai had'e da yar shasheka tana daga masa, kafafu dakyau da, irin abubuwan da zata rika, tabo masa tun teemah bata ganeba har ta gane tanajin kunya har tafasa jin kunya ta tsaya tana daukar darasi irin kalolun kwanciyar da hajiya mansura ta kowa teema Allah yayi yawa dasu da kissa da kisisina iya zama da kishiya ta duk inda ta bullo zata tareta ta nuna mata ba haka abun yake ba iya tafiya karairaya shagwaba magana iya daukan dress da girki tun safe idan sun fara sallah ke dakatar dasu ko cin abunci cikin ikon Allah teemah babu abinda bata daukaba komai ya zauna akanta har wata yar kiba tayi dan mansura tace ta cire tunanin mijinta ta maida gefe yanzu lokacin darasine ba soyayya ba dama bata kunna wayarta ba ta maida hankali kan abinda ake koya mata taciko tayi mugun kyau fatarta ta goge batada
ruwan sha sai hadin hatsi da aya da kanafari sune aka hada mata hadi mai kauri yazama ruwanta nasha shiyasa take yoyo wuni take tana sauya pant jagaf takeyi saboda abubuwan da hajiya mansura ba karamun tsumi takema teemah ba ga wani shegen turare da take mata shima duk ya burkitata batason komai ayanzu sai Haidar dinta
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
yau saura kwana biyu bikin teemah kuma yau zasu tafi Niger garin sarki da misalin karfe goma Nasafe na hango teemah gaban hajiya mansura wlh teemah ta tayi mugun canzawa babu abinda yakebani mamaki sai yar kibar da tayi duk ba wani abun kirki ta karuba amma tayi mugun kyau fatarta ta murje tayi haske sosai wani irin kitsone da kunshi aka mata tamkar shuwa arab ta koma muryata na tsunto tamkar. bata son magana sai wani lumshe idanu take tace"Aunty mansura wlh insha Allah
zan shanye ko munje bazan fasaba tafawa mansura tayi"gud matar gwamna wlh naji dadin yada komai ya zauna kanki kiyi kokari ki aikata daide banda kuskure ko tsoro kanta ta sada tana murmushi Malika ce ta shigo da sallama idanu ta zaro ganin kanwarta ta zama tauraruwa kunshinta kadai abun kallone bare kitson kanta ga wani uban kyau da tayi dan rabonta da ita tun ranar da suka kawota mansura tace kowa karyazo abarta ta gudanar da komai saboda babu isashan lokacin da gudu Malika ta nufi gun teemah ta rumgume "wayyo tauraruwa zahara dariya teemah tayi"kai anty karki karyani mana dariya mansura tayi ta mikar da teemah tana mai cike da mamakin kanwar tata harda kiba tayi gawani shegen kamshi da take jikinta luwai luwai mai sunan iyayye teemah ta amasa tana mata kiss Malika tace"hajiya mude wlh muna mutikar godiya da wannan gudun muwa da kika ba kanwata wlh ninasan zata samu daraja mai girma gun mijinta kome muka baki bamu fadiba mun gode kwarai dariya mansurah tayi"wlh babu komai Allah dai ya kaiku lfy Allah yasa ayi biki lfy akawo mana Amaryamu lfy jibin zaku dawo?"wlh ban saniba idan mijinta ya tura akawo masa matarsa ai Dole naji mu'azzam yace ajirgi za'a kawota fa idanu teemah ta zaro ta turo baki dariya suka mata malika tace"maza muje mu'azzam na jiranmu kofar gida kuma canma gyara ke jiranki tun jiya
haja Nanu ta adabemu da kira diyar na bata na nufi bedroom din da aka sabkeni na tataro kayana nasaka hijabi kan doguwar rigata duk wani iri nakejina ga tunanin my haidar DINA ina fitowa muka ma Aunty mansura sallama kuka naji yazo mun saboda kwanakin da nayi mun saba sosai lallashina tayi tayi tarakamu har gun mota mu'azzam ne yakemun dariya fashewa nayi da kuka har motar mansurah ta shiga ta lallasheni har nayi shiru"mu'azzam banda tsokana zan hadaka da mai girma gwamna fah "tuba nakeyi hajiya na bari Watsime kiyi hakuri kinji kallon mansurah nayi na b'are baki ta rufemun"kibarsa zan hadashi da Aliyu ta danne dariyarta ta fito ta rufe motar mu'azzam yaja Malika tace"auta kibarsa zan rama maki ai yau kashi zan basa irin Wanda kikaji yana ihu nayi ta zuba masa bulala dukanta mu'azzam yayi "wlh my love ki iya bakinki ko kin manta daga daukar darasi take dariya teemah tayi"wlh Aunty da kin burgeni kinga yanzu har so biyu yana sani kuka Allah kuwa bazan rababa yanzu haka ranar ma wayancewa yayi kin jibagesa bushewa sukayi da dariya mu'azzam yace"yanzu mubar maganar muje ki kwashi kayanki mu kama hanya su watsime sai kwanan garin Sarki Malika tace"dan Allah karki kulashi kawai dan yasaki kukane dariya tayi "yo Aunty ni banida lokacinsa yaje yayi tayi malika mamaki watsime take bata yada take wani lankwashe murya tana yanga teemah ko kwanciya tayi tana matsar kafafonta dan jaraba ke cinta abubuwan sun mata yawa ta tsumu sosai batada aiki sai zuba su shoriem ne suka Haye samanta suna dariya turesu tayi ta zauna tana matsar kwalla "dallah can kurabu dani ku bakusan masifar da mutum yake cikiba kun wani dameni Malika zatayi magana mu'azzam yace "ishiru kawai neman Wanda zaimatane tayi kuka take shiru malika tayi tana murmushi aikuwa sukaji shashekar kukan nata tanacewa "yo idan ba'amun ba abun kukan ai bazan yiba ko danme zasuzo suna dukana kunaji bazaku musu maganaba idanu mu'azza ya zaro har suka iso kofar gidansu babu Wanda ya kulata har tagaji tayi shiru honr mu'azzam yayi mai gadi ya bude masa get ya shige da motar dan so yake yanzu su kama hanyanr Niger............✍🏻
Rahma ummu fareesa ce😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page2⃣0⃣*
......Mu'azzam na parking suka fito suna shiga teemah ta tatara duk abinda ta keso malika ta tayata suka kawo mota dan tasan ko tace ta bari idan sun dawo zata kaimata can gidanta kukane busu wani jimaba suka fito sukama baba warsu mai gadi sallama suka nufi gidan inna hajiyarsu mu'azzam domin mata sallama, koda sukaje basu wani jimaba suka fito innah ta rakosu har mota"Fatima sai naje ganin daki ko shiru tayi ta tashige mota tana turo baki mu'azzam yayi dariya sukama hajiyar mu'azzam yaja motar ya Teemah tace"Aunty ni wlh bacci ma nakeji mu'azzam yace"watsime yo kiyi abunki mana ko dai so kike muga gwamna banza ta masa dan ta gane tsokanace amma aranta tana son hakan fiye da komai Malika ta kallesa" wlh kafiye tsokana amma bankwanane kuke teemah kwanciyarta tayi ta lumshe idanu tana tunani gwamna sai tsinkayo kyakywar fuskarsa take yana sakar mata murmushi baki ta turo" Allah my Haidar idan na kamaka zaka sani sai nacinye wannan bakin nan naka mai shegen dadin tsotsa tana gunguninta har bacci ya dauketa Mu'azzam gudu yake sosai tunda sukama Gombe fintinkau sai sharara gudu yakeyi Allah yatsare hanya ya kaiku lafiya, muje masha biki
Da misalin karfe hudu da rabi na yamma Aliyu ne zauna a tafkeken parlonsa na tarbar baki ya hade cikin wani yadi baki mai masifar tsada da kyau yayi masa masifar kyau shida wasu baki da yayi fuskarsa dauke da murmushi yana shafa sumar kansa yace da sanata Nuradeen" wlh ni bana tashin hankali asiyasa please Nuradeen kubi komai ahankali mulki ba hauka bane Alhaji tasi'u Sani babu abinda ya isa yamun sai Wanda Allah bai kaddara ba zai sameni dan haka karku sake saka damuwa akanku sanata kaifa ba yaro bane wlh shiyasa nace karkaje Office kazo gida mu hadu ajiyar zuciya sanata Nuradeen ya sabke"Yallabai kai wlh hakurinka yayi yawa haba Dan Allah mutun kirikiri yake nunama kiyayya amma baka damuba Alhaji Nasidi yace" wlh shi ai kalli fah dazu gun meeting yada yake wani jefama magana kuma ai mai girma shugaba ya shiga tsakaninku shi bayama jin tsoron labari yaje kunnesa" oh my God don Allah kubar maganar wayarsa ce ta dauki ringing yaga boos ne dagawa yayi" hello ya akayi" Oga masu gyaran part din Amarya sun gama koma komai yayi ba karya murmushi Aliyu ya Saki ya lumshe idanunsa" gud boos bayan kudin hakkinsu ina so ka basu dubu Hamsin wannan kyauta tace ta musamman " OK Oga an gama kitt Aliyu ya kashe wayar sokaci gaba da
tataunawa ya hana sume maganar abokan gaba sukaci gaba da tataunawa Akan harakokinsu na siyasa wayoyi daga ko ina kiran Aliyu akeyi wasu ya amsa wasu bai amsaba sai karfe biyar da rabi suka fito suna tafiya Aliyu yanufi Part din Noor dinsa tundaga kofar parlon nake kallon haduwa da tsaruwar gidan teemah wani Dan madanin ya danna kofar ta bude wacce dukanta glass ne parlon sai kamshi yake