Showing 18001 words to 21000 words out of 36457 words

Chapter 7 - Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel By Fatima Zahra Lawan.txt

Wani irin kallo ta wurga masa Wanda yasashi sakin hannun ta batare da ya shirya ba,a jiyan zuciya yayi sannan ya dubeta yace"Shakeerah yarana kusan goma sha Amma yau duk Allah yamusu rasuwa Banda sauran ko daya, sannan mata na biyun nan duk Basu haihuwa sai dai yanzu inason haihuwa sosai.
Cikin bariki da sanyin jiki Shakeerah tace "ayya Allah yayi musu gafara yasa suna kyakkyawan matsayi.Ameen! Daddy ya fada can dai yace"Shakeerah Aure nakeson na kara,Ina neman wacce zata kula dani sai yau Allah yanuna mun ita.
Duban shi tayi yanda yake magana like saurayi dan 30 da wani Abu.
Shakeerah tace"wacece ita? Kece Mana Shakeerah kece macen da nakeso
_I NEED UR COMMENT_






Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )








Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______








*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))


*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________




Marubuciyar⬇️


_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_




*DA*


_ _MIJIN ZAHRA_




*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*




Bismillahir-rahmanir-raheem.




*Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai....*






_FREE PAGE_




Page:2️⃣0️⃣--2️⃣1️⃣🖊️






_________Koda ta nufi part din fulani jitayi hayaniyar tasake yawa,cikin Sauri tashiga Falon, fulani tagani duke a kasa tana kuka,wata yarinyace tsaye akanta a kalla bazata wuce sa'an marigayiya Aunty saudah ba sai wasu mata manya akan sofa su uku duk tana Kama da fulani sai guda a cikinsu,fulani tace"Hjy baraka a gabanki jikanki na zagina ba zaki tanka ba? tabe baki wacce akakira da hjy baraka tayi tace" Ai anyimata ne,nikaina Yaya kinbani mmki Saboda Kuna da kudi shine duk wulakancin da kuka ga dama sai ku sauki kan laweezah Saboda ta auri Jalal?to Meye Jalal din yakedashi da ake wannan abun?


Su dai sauran matan babu wacce tatanka Banda zare Ido babu abinda suke,Laweezah ta juya tadubi fulani tace"Ku rabu da munafukar tsohuwa,tsohuwar banza wacce a haka zaki Kare.




Kutumar uba kayyasa, Shakeerah tafada tana shigowa falon, gabadaya suka tsaya kallon ta ko da takariso jikake tassss! Ta dauke Laweezah da Mari,ko kafin ta Kuma cewa wani Abu tasake dauketa da Mari ihu Laweezah tasaka tana sake dafe kuncinta.


Shakeerah tace"Bura ubaki wacece ke Dan Ubanki?da Zaki Zo kitsaya a gaban tsohuwa kamar wannan kina zaginta sa'anki ne?
Mikewa hjy baraka tayi tace"wacece ke kekuma daga Ina kike harda zakizo kishiga fadar da ba'a gayyace kiba?


Harara Shakeerah ta maka ma Hjy Baraka tace"Sanin ko Ni wacece Sam baida amfani,mgnr shshhigi kuwa yanzu nafara indai Akan fulani ne.
Tajuyo ta dubi fulani tace"kekam baki da tarbiyya wallahi tallahi Muddin Ina Falon nan Kika sake zagin fulani sai na hada Miki jini da majina,tsoro sosai Shakeerah tabawa Laweezah,su kansu matan dake falon Sunyi farin cikin faruwar wannan lamarin.


Karisawa wajen fulani Shakeerah tayi tare da sharemata tears ta dagata ta dorata Akan sofa,dubanta fulani tayi tanason tayi magana tasaka.
Kama hannun Laweezah hjy Baraka tayi tace muje diyar albarka,wallahi kuma Marin nan dakika mata kisan cewa kinci bashi ne zanga ubanda yatsaya maki,dage kafada Shakeerah tayi tare da tabe mouth tace"Ganinan daram dam dakam a turo ubanda za'a turo dai-dai nake da kugun kowa.
Fita sukayi daga cikin Falon suna zage-zage,Daya daga cikin matan tadubi Shakeerah tace"yarinyar nan Allah yayi Miki albarka wallahi duk cikin zuri'ah namu Mutane suna tsoron Hjy Baraka ake da iyalenta kamar ba 'yan uwa ba,kinganmu nan uwa daya uba daya muke da bala'i Hjy Baraka tasa Jalal babban jikan fulani ya auri Laweezah ba don Yana sonta ba,shine fa kullum Basu da aiki sai korafe-korafe.


Shakeerah tace"Allah ya kyauta Babu mnyan 'yaya ne?
Matar tace"Akwai mana Aida ana biye tatasu da tuni anyanke zumunci,Bata da kirki Saboda taga fulani nada hakuri sosai.
Dayan matan tace"Shiyasa Sam Auren zumunci yafita kaina domin gashi a dalilin halinta na yanke zumunci da ita.
Shakeerah tace"Allah dai ya kyauta kawai shine abin cewa itakuma Allah ya shiryeta.


Ameen gabadaya suka fada.


Duban fulani Shakeerah tayi tace"Fulani zan koma school gobe insha Allah.
Duk cikansu fatan alkhairi suka yima Shakeerah sannan tamusu sallama tafita.


A harabar gidan taga motoci sun shisshigo akalla zasuyi motoci uku a tunanin Shakeerah ko Hjy Baraka ce tadawo da iyalenta,sai Kuma taga maza ne manya sosai su uku domin zasu haifeta ma tare da mata biyu.


Wucewa part dinsu tayi cikin Sauri.




Sukuwa da sallama suka Isa part din fulani kyawawan yara masu tashe da jindadin rayuwa,ilimi,kyau,addini,uwa uba Nairaaaaaaaa.
Cikin Sauri duk cikansu sunkai su biyar suka Isa wajen fulani suna tambayarta meke faruwa?
Itadai fulani Bata tanka ba tace Babu komai,kuyanginta gidan suka shiga hidima dasu sosai.




_WACECE FULANI_




Sarki Abdallah Sarki ne na garin itophia Sarki ne Mai adalci Wanda iyayenshi shi kadai suka Haifa, yataso talakawa na alfahari dashi a rayuwa Yana kula da talakawa,duk zaluncin da sarakan Bayan sukayi shi Sam baiyyi ba.


Akwana atashi Allah ya azurta shi da 'Yaya hudu duka mata,da hjy Rahma (Fulani) da Hjy Baraka da Aisha sai autansu hjy Maryam.


Manyan garin azzalumai da Basu son mulkin adalci sukayi kokarin kashe Sarki Abdallah,suka bashi zabi ko ya zabi iyalensa ko ya zabi mulki.
Jin haka yasa Sarki Abdallah ya hakura da mulkin ya zabi iyalensa,shi yasanya ma fulani suna fulani,sannan suka bukaci ya bar kasar sa na haihuwa tare da dukiya Mai tarin yawa.


Nigeria yadawo da Zama ya sauka a garin maidugri,Bayan zuwansu da shekara guda mahaifiyar su fulani ta rasu Sarki Abdallah ya cigaba da kula da 'yayansa mata,jikin hukuncin Allah,Allah ya kawowa fulani miji hamshakin mai kudi da sarauta domin Dan Sarkin ne Alhj yunusa Hameed dan garin Senegal,kasuwanci yakawo shi Nigeria nan yayi arziki sosai Bayan iyayenshi sun rasu.


Sosai yake son fulani da Bata kulawa na musamman a haka aka daura Aure cikin hukuncin Allah tasamu cikin danta na fari Bayan tahaifeshi yaron ya rasu.
Still ta kuma Samun cikin Allah ya azurta ta da haihuwan 'ya mace hjy Kaltume kyakkyan jinjira me sirrin wani irin kyau,bayan ta haifi Alhj kabeer shima kyakkyawan namiji mai jida kyau,sai Alhj Khamees shima haka,sai Hjy shamsiyya sai Alhj Ahmad shine autan ta.


Itakuma Hjy Baraka tayi Aure a garin zamfara wani kauye ne duk da bawani kauye bane can-can Amma Basu da wani wayewan kai,sai dai suna takama da rashin mutumci 'yan garin basa saurarawa kowa,dama Hjy Baraka fitinanniya ce tafison kanta akan komai.
Sam 'yan uwanta da mahaifinta Basu Jin dadin hulda da ita don ya zame musu Dole ne,itama hjy Aisha tayi Aure sai dai bata taba haihuwa ba, Hjy Maryam ma tayi Aure don tanada yara biyu.




Hjy Kaltume dan ta daya ne a duniya Jalal Bayan ta haifeshi tayi aure ta auri wani babban costume yanzu suna garin Abuja,domin mahaifin Jalal dan Sudan ne,shine babban jikan fulani jalal daga baya Allah ya ma mahaifinsa rasuwa,itama babban jikan Hjy Baraka itace Laweezah tunda tataso takeson Jalal duk da cewa shi Sam baya sonta,hasalima dabi'unta da habbit nata sam basuyi masa ba,bata cikin tsarin kalan matan da yakeso,hakanan yayi ma fulani biyayya ya aureta domin yana kallonta kamar uwace a gareshi.


Dalilin zuwan fulani kaduna kuwa nan mijinta ya'ajeta tare da kuyangi,ko Bayan rasuwarsa batai Aure ba.


A hakadai aka daura Auren Jalal da Laweezah Yana karatun Dr ne a Saudiya bangaren zuciya,sai dai Sam bai tafi da Laweezah ba.Sun haifi yara biyu Bayan sun girma yatafi da su saudiyya yasasu a MAKARANTA to shine rikicin da akeyi suna cewa fulani ke zugashi.



_CIGABAN LABARI_




Nan su hjy Maryam suke sanar da su Alhj kabeer duk abinda yafaru,da labarin Shakeerah ajiyan zuciya hjy Kaltume tayi da yake macece mai sanyin hali,hjy shamsiyya ko Banda huci Babu abinda take tace"Jar uba! Aiko da inanan sai naga ubanda yatsaya mata Kuma wannan yarinyar Allah ya mata albarka.


Cikin sanyin murya hjy Kaltume tace"Fulani ina yarinyar take ne?Fulani tace"Suna can bangaren nan bana cemuku na siyar ba?duk cikansu suka ce suka amsa da hakane Akira musu Shakeerah,Kiran daya daga cikin kuyangin fulani akayi akace ta Kira Shakeerah,cikin biyayya ta amsa da to ta fita.


Shakeerah kuwa Bayan fitan ta direct part din su ta nufa ta cidda Ammi tana kitchen tana hada Mata dambun naman zabi Wanda zata tafi dashi gobe,Shiga kitchen din tayi tafara tayata aiki sunayi suna hira batare da tasanar ma Ammi abinda yafaru a part din fulani ba, knocking din kofar Falon su akafara,cikin Sauri Shakeerah ta nufi kofan tare da budewa.
Kuyanga ta dubi Shakeerah tace"ranki yadade fulani na san ganinki cikin gaggawa,da Sauri Shakeerah tace"toh kice mata ganinan.
Juyawa tayi ta Shiga bedroom dinta ta dauko long hijjab dinta pink colour ta zira,Shiga kitchen tayi ta sanar da Ammi xataje sashin fulani tana kiranta,da toh Ammi ta bata amsa,har ta juya zata fita, Ammi ta kirata.
Dawowa tayi sannan Ammi tace"bude cikin carbinet dinnan ki dauko min karamin bowl.
Budewa Shakeerah tayi ta Ciro taba Ammi,amsa tayi ta cika shi da dambun nama,sannan tace ta dauki jug ta zuba mata kunun ayar da tahada a cikin firij.


Duk haka Shakeerah tayi ta dauki Kayan niki-niki ta nufi part din fulani,da alamu bakinnan na falon,kamar ta juya sai dai ta daure da kyar ta nufi cikin farlon.


Da sallama tashiga,duk cikansu suka amsa tare da zubama mata idanuwa sosai,kura mata idanu tayi gabanta na faduwa duk da tasan face din sai dai ta rasa inda tasan face din.


Karisowa tayi tana murmushi ta nufi wajen fulani,dire Mata jug din da bowl din d ke rufe da murfinshi tayi tace"fulani gashi inji Ammi na,cikin Sauri Hjy kaltume ta Kuma kallon ta,tasan muryan sai dai ta mance wacce tasani da muryan.


Shakeerah ta juyo ta gaida duk bakin dake falon,da Murmushi ko wannen su ke amsa was,hjy shamsiyya tace"munji abin arzikin da kikayi 'yan Mata,yabaki miji nagari mai kula dake.
Shiru Shakeerah tayi tana me amsawa da ameen a zuciyar ta,hjy shamsiyya tace"kinsan me nakeso dake?girgiza Kai Shakeerah tayi.
"Ga amanar fulani nan a hannunki duk Wanda yayi mata ba dai-dai ba kici kaniyar sa kada ki saurarawa kowa ninasaki.
Murmushi Shakeerah tayi tace"Aunty aini ko ansa ni ko ba'asani ba,ba'a Isa ataka fulani Ina wajen na kyaleva Koda kuwa kashe ni za'ayi.
Dariya ma abun yabawa su Alhj Khamees dariya, Alhj Ahmad yace"hjy shamsiyya adaiyi hudubar arziki Koh? Duk cikan su dariya sukasa hjy shamsiyya tace"Wallahi abun ne daban haushi sai kace Laweezan 'yar gwal ita ba kyau ba ba komai ba,Wallahi bacin zumunci da tuni yadanna mata saki kowa ya huta.
Shakeerah tace"Fulani gani. Dafa kanta fulani tayi tace"tashi kitafi Shakeerah Allah ya Miki albarka,kicema Maryam din ina gaisheta da aiki Allah yajikan Muhammadu.
"Ameen Shakeerah tafada sannan tamike tatafi.


Bayan fitan ta su Alhj kabeer suka Mike Dan zuwa masallaci.
Hjy shamsiyya ta dubi su hjy Maryam tace"Inna Maryam gani da shawara.


Gaba Daya maida hankali sukayi wajenta don jin shawarar.
_I NEED UR COMMENT_












Xahratty ce✍🏽


Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
(Daukar Fansa)







Story&writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
_______✍🏽_______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tamvarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*T.W.A*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________




Marubuciya:-
_ *A DALILIN 'YAR TSUNTUWA*


_ *MIJIN ZAHRA*

*ND*
*NOW*
*DIAMOND LADIES*
(Daukar Fansa)




*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa)na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari 100 na waya ta wannan number 08060719719,sai nayi adding dinsa a group din*




Bismillahir-rahmanir-raheem.


*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....*






_FREE PAGE_




Page:2️⃣6️⃣--2️⃣7️⃣🖊️










___________To aini banid matsala sai dai Ammi na but abinda yafi sauki Ummi kizo kiyima Ammi magana muji ba.
Shiru Ummi tayi tace"To shikenan babu matsala zanzo insha Allah.




Washegari da safe su Shakeerah suka nufi gidan su harda khadee,direct part din fulani suka wuce,a guje taje ta rungume fulani.
Itama fulanin Cike da farin ciki tayo gareta tana murna, Shakeerah ta dubi su fauzy tace"Diamond ladies ga fulani na nan,Cike da girmamawa suka gaida fulani,fulani tace"Allah sarki ai inajin labarin ku a wajenta sosai,Suma sukace sunajin labarin ta wajen Shakeerah.
Nan suka nufi part din Ammi suka bar Shakeerah Anan da alamu tana son magana da fulani.


Duban ta fulani tayi tace"Shakeerah na hala kina da magana danine? Murmushi Shakeerah tayi tace"Eah fulani dama nan Shakeerah ta zauna ta bawa labarun duk abinda ke faruwa.
Shiruuuu fulani tayi da alamu ta zurfafa ne a wajen tunani can tadago ta dubi Shakeerah tace"kisani shi din bai tsari da irin mazan da Zaki Aura ba Koh?
"Eah nasani inaso in hada iyayen karya ne,Kuma ba son sa nake ba sai dai tahaka ne kawai zamu samu hujjar da zai gamsar a gaban alkali,kuma ni bazan yar da dashi ba,bazanyi rayuwar Aure dashi ba.


Fulani tace"Toh shikenan Shakeerah na goyi bayan ki hundred% sai dai yakamata yazama like Auren sirri Koh?
Shakeerah tace"Eah fulani kusan hakane,to Amma ba'anan gizo ke sakar ba Ammi kawai nakeji.
Shiru fulani tayi tace"kada kidamu zan shawo kanta, Shakeerah tace"yawwa fukani na tnx so much bari naje zamu dawo wajen ki yau za'a baza chapter tayi maganar tana fita Falon a guje, Murmushi fulani tayi tace"tabbas inason hada zuri'ah daku.


Sosai Ammi tayi farin cikin ganin su yanda suke zaune suna hira suna ihu lokaci daya tunanin Abba da Aunty saudah suka fado mata a hankali kwalla ya taro a eyes dinta,cikin Sauri ta maidasu a ranta tana me musu addu'ah akan Allah yagafarta musu,tana farin cikin ganin yau Shakeeran ta cikin rayuwar farin ciki ga wani irin kyau da take dashi kaman jinin larabawa.


Tasowa Shakeerah tayi tare da kwantar da kanta jikin Ammi tace"Ammi yau part din fulani zamu gudu don acan zamuyi hira, Ammi tace"Toh shikenan ku dawo dai da wuri,da toh suka amsa mata daga nan suka nufi part din fulani.




Kwadon zogale fulani tayi musu,gashi anzuba shuger Dan dai-dai yayi Dadi sosai,hadda yankakken dafaffen kwai .


Bayan sunga ma ci aka dasa hira,nan su khadee da fauzy suka Bata labarin rayuwar su,sosai fulani ta tausaya musu tasake bawa Shakeerah goyon bayan wannan abun.






Washe gari kuwa wajen azahar Ummi tazo ita da sajeeda,sosai Ammi ta karbeta hannu bibbiyu,nan itama fulani tashigo, Anan suka bawa Ammi labarin abinda ke faruwa,sannan suka ce ta'amin ce da bukatan Shakeerah domin hakan shine mafita.


Kada wuya Ammi tayi Cike da damuwa tace"Amma kukunsan hatsarin shi meyasa sai ta haka ne za'a hukunta shi? tayi maganar voice dinta na cracking.


Ammi tace"Saboda ita din jajir tacciya ce,Kuma Yana mata so mai tsanani,sannan tana da wayau sai dai duk wuya insha Allah zata dawo batare da wani Abu yashiga tsakanin su ba.




Still voice din Ammi cracking yake a hankali tace"Toh shikenan ina matukar son ta banason na rasata kaman yarda na rasa mahaifinta da 'yar uwar ta, Amma zan cigaba da yimata addu'ah har Allah yabata nasara.
Gaba daya suka amsa da Ameen.




Su Shakeerah sunyi farin ciki sosai da amincewar Ammi sai dai gabadaya Ammi ta canza mata face tarage yimata walwala,a dalilin hakan ba karamin tashi hankalin Shakeerah yayi ba,wata rana ana saura 3days su Kuma school ta Shiga dakin Ammi da sallama tashiga dakin, Ammi tana gyara kayan wadrope din ta,Babu yabo Babu fallasa ta amsa batare data kalli inda Shakeerah take,cikin sanyin jiki Shakeerah tajuya domin fita dakin tsayawa tayi tare da juyowa four eyes sukayi da Ammi,kwallah ne suka tsiyayo ma Shakeerah da gudu taje ta rungume Ammi tana mae fashewa da kuka tace"Kiya hakuri Ammi indai saboda Auren Daddyn khadee kike fushi dani to wallahi ni na hakura da maganar,dama ban sanar mai ba.


Tausayi Shakeerah taba Ammi a hankali tafara shafa bayanta tana bubbuga wa tace"ba fushi nake dake ba sai dai tausayi kike bani sosai Shakeerah saboda inda zaki dosa akwai tsananin risk sai dai zan cigaba da yimiki addu'ah kuma inaso kafin ki koma school ki Kira shi a waya ki ce iyayen ki sun amince sai dai idan kun koma school ki maida hankali wajen karatun ki kinji?cikin Sauri Shakeerah tace"Toh Ammi habu matsala,ya zanyi da karatu na?




Shiru Ammi tayi tace"yanda Kika gano abin da kka cema kawayen ki na Auren shi yanzu ma keda kanki Zaki natsu kiyi tunanin abinyi.


Cikin sanyin jiki Shakeerah tace"Toh shikenan Ammi,tabbas tafara karaya da lamarin.


Ammi tace"Shakeerah ta kisa ma zuciyar ki wannan lamarin anci nasara angama,ke mai taimako ne irin Abban ki,kada ki manta da wasiyyar da Abban ki ya bar Miki akan files din nan.
"Ina sane dashi Ammi sai dai ina neman jarumin namiji mai Amana shi zanyi aikin dashi.


Ammi tace"Toh shikenan ubangiji ya shige miki gaba a dukkan lamuran ki kinji?
Ameen Ammi na.




Gabadaya suke bedroom din Shakeerah suna kallon Shirin jamai raja da akeyi a Arewa24,wayar Shakeerah ne yayi kara,dauko wayar tayi tare da duban screen din number Daddy ne domin ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login