Showing 57001 words to 58506 words out of 58506 words
lokacin da yakoma gida bai sameta afalo ba iya hafsat kadai yatarar tana zaune tana kallon wani Indian film kites,
Jiki asabule yazauna akusa da ita ya mika mata maganin ta karba tana kallonsa bayan tahada ledar maganin da hannunsa ta ruke,
Jingina da jikinta yayi ya ajiye kansa bisa kafadarta......
_Gaisuwa mai tarin yawa ga besty na Phertymarh Xarah._
*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_DEDICATED TO MISS XOXO_
*55*
***Hular kanshi ta cire tasoma shafa sumarshi ahankali, dan lumlumshe ido yafara yana sake nanuka jikinta domin wani kamshine yake fusgarsa,
"Yaya yusleem lafiya kuwa?" Tace dashi tana rike hannunshi,
"Lafiya lau baby, kamshinki ne yake neman tada min da hankali..."
Saurin juyowa tayi ta kalleshi,
"Meyayi? Ko kamshinsa ne baiyi maka ba?"
Murmushi yayi yadafa kafadarta,
"Easy, ba abinda nake nufi kenanba, tsananin dadin kamshinshi ne ke neman juyar min da kwakwalwa..."
Murmushi tayi ta tureshi ta tashi tanufi dakin mami domin kai mata maganin da yasiyo mata,
Mintuna kadan tafito ta dauki ruwa roba daya tasake komawa, wannan karon ta dan jima sannan tafito, amike taganshi kwance kan doguwar kujera,
Durkusawa tayi akasa ta dora hannuwanta ajikin kujerar,
"Ba yanzu zaka shiga ka kwanta ba?"
Hannuwanta duka ya riko yajata kan ruwan cikinshi,
"Gani nayi kinje wurin mami kinyi zamanki shiyasa na kwanta anan..."
"To ba gashi nafito ba"
Yana kokarin kai hannunta guda daya bakinshi mami tafito,
Tashi hafsat tayi gaba daya kunya tagama lullubeta domin tasan mami tagansu, sum sum tawuce cikin bedroom batare da tayi magana ba,
Zaune yatashi yana kallon mami wacce tawuce dining area batare da ta kalli wurin da yakeba,
Handset dinta yaga ta dauko wanda da alama mantata tayi awurin,
"Sannu mami, yajikin naki"
"Yawwa sannu, dasauki"
Mami tace dashi tareda wucewa bedroom dinta, yajima zaune awurin kafin ya mike ya nufi bedroom wurin hafsat, tana gaban mirror daure da zani tana shafa wasu dadadan turaruka, khalta maryam,da musk altahara,
Ajiye mata ledar maganinta yayi yatsaya kawai yana kallonta,
Juyawa tayi ta kalleshi itama,
"Ya yusleem ya akayi?"
Hannunta yariko cikin nashi yazauna agefen gado ya zaunar da ita ajikinshi,
"Yau basai kinsa sleeping dress ba" yarada mata acikin kunnenta, kunyace ta rufeta, dan dukan kirjinshi tayi ahankali, ta cusa kanta agefen wuyanshi,
"Kaga dazu ma haka kasani naji kunya"
"Da nayi me?"
"Da ka sa mami tazo taganmu mana"
Mikewa yayi ya kwanta ya kwantar da ita ajikinshi yana murmushi,
"Ai ba laifina bane"
"Laifin waye?"
"Laifinki mana"
"Laifina fa kace"
Lumshe idanuwanshi yayi yana sake matseta ajikinshi,
Sun jima ahaka zuwa can bata san meya faruba sai ji tayi ya sassauta rungumar dayayi mata yafada kogin tunani,
Kin bari yayi ta fuskanci cewar akwai abinda yake damunsa nan ya lallabata bacci ya dauketa, kwantar da ita yayi yatashi zaune yayi shiru yana nazari,
Jin zaman ya gundureshi yasashi tashi tsaye yafara kai kawo acikin dakin, sam yau bayajin bacci sannan yarasa dalilinsa na damuwa da lamarin hafsat yar gidan alh musa, haka kuma yana jin wani irin abu mai kamada tausayi tausayi yana yimasa yawo akirjinsa gameda ita,
Kukan da yaga tatafi tanayi shine yafi komai tsaya masa arai,kusanma shine makasudin rashin baccinsa, yarasa ta inda zaibi ya bullowa wannan al'amari domin shi dai ara'ayinsa baida niyyar kara aure, yafi son ya zauna da Hafsat ita kadai ya nuna mata soyayyar da sauran mata basu samuba to amma kuma ita rayuwa kana nakane Allah yana nashi kuma komai mukaddarine daga gareshi,
Bude idanuwanta tayi nan taganshi tsaye yayi shiru abisa dukkan alamu baiyi bacci ba,
Sauka tayi ahankali daga kan gadon tanufi wurinshi, dafa kafadarshi tayi nan yayi saurin juyowa yana kallonta,
"Ya yusleem...., meke damunka? Menene ya hanaka bacci? Tunanin mekakeyi?"
Kago murmushin dole yayi yasa tausasan yan yatsunshi ya kamo nata,
"Babu abinda nake tunani baby nah, baccin ne naji yaki daukata shine kawai nataho nan nake dan zagayawa"
Murmushi tayi ta dan sake yin kasa da muryarta,
"Kafada min gaskiya dai, kodai?"
Murmushin shima yayi mata ya dauketa cak yanufi makwancinsu da ita,
"Kema kindai san idan nace miki bata damuna karya nake yimiki...."
Mayar da fuskarta gefe daya tayi tana murmushi aranta tana tunanin abinda zaije yazo duk ranar da aka tabbatar masa da yagama samun lafiya domin shima taga kamar fitinanne ne,
"Yanaji kinyi shiru?"
"Ehh bacci nake son komawa"
Mirginata yayi takoma kasa yayi pillow da kirjinta, tun tana dan shafa sumarshi har yaji shiru alamun tayi bacci, shikam dakyar yasamu ya iya bacci cikin wannan dare.
Tunda wannan maganar ta shiga tsakaninsu da Hafsat shikenan bai sake ganinta ba koda yaje gidan sai dai kusan kullum yana ganin massage dinta taturo mishi,
Bayan kamar sati biyu da faruwar al'amarin da wani yammaci yaje gidan bayan sun gaisa da alh musa yafito ya hangeta tsaye jikin motarshi tana wasa da key din motarta wanda da alama dawowarta kenan taga motarshi,
Dan hade rai yayi yanufi wurin,
Ganinshi haka yasata yin dan murmushi,
"Ya yusleem menene abin bata ran? Dama kawai tsayawa nayi mugaisa sannan in tambayi lafiyar takwarata da na yaranta"
Batare da yasaki fuskarshi ba yace,
"Tana lafiya"
Bashi wuri tayi ta tsaya tana kallonshi bata kara maganaba yashiga motarsa yafita daga gidan, yana cikin driving yaji karar shigowar text massage,
_Ya yusleem insha Allah sai na aureka kuma zakace nafada maka..._
Cilla wayar kan kujera yayi yaci gaba da driving dinshi bayan yagama karanta sakon.
Akasalance ya karasa gida,babu kowa afalon mami dan haka kai tsaye yawuce cikin bedroom dinta nan dinma bata nan sai lokacin yatuna da cewar baiga motarta ba lokacin da yashigo, dakin hafsat yawuce ita dinma bata ciki, fitowa yayi yana tunanin to kodai tareda mamin suka fita da wannan tunanin yakarasa cikin bedroom,
Zaune yaganta tana goge mishi kananan kayanshi data wanke ta kunna laptop dinshi tana sauraren wakar dayake muradin so wadda kusan koda yaushe sai yajita,
Tsaye yayi yana kallonta yana dan murmushi domin yasan bata san yashigo ba,
Ahankali ya sadada yarufe mata ido da hannuwanshi ai kuwa ta kurma wani uban ihu tana salati,
Dariya ce taci karfinshi ya fada jikinta yanayi bayan ya bude mata idanuwan,
Kashe iron din tayi tahau dukanshi, hada hannayenta duka guda biyun yayi ya rike yana yimata dariya,
"Allah ya yusleem sai nafawa mami abinda kayi..."
"Yi hakuri hafsat, ke dince kika bani dariya sosai"
"To bakaine ka tsorata ni ba"
"To kiyi hakuri, kinga anjima dama ina son ki rakani anguwa"
Fadada murmushinta tayi,
"Tom shikenan, yanzu bari inhada maka ruwan wanka idan ka shirya sai muje kaci abinci"
"To tashi ki hada min"
Tashi tayi tashiga bathroom kafin tafito yayi sauri ya cire kayan jikinshi yabita ciki dole sai tare sukayi suka fito tanata kumbura fuska,
"Shikenan bazan karaba tunda bakya son ladan, kiyi hakuri"
Kin kallonshi tayi yayinda shikuma ya kafeta da nashi manyan idanuwan, bai san daliliba bakar fatarta tana yimasa kyau,
"Gaskiya koda ace mata hudu zanyi to duk bakake zan aura"
Dan harararshi tayi taci gaba da shafa masa mai,
"Kullum kuma sai kaita ganin kala daya babu canji?"
"Ehh mana ai tafi kyau"
Shiru tayi masa takarasa shiryashi takoma shirya kanta, kananan kaya yasa dark blue din t shirt da blue din jeans iya gwiwa,
Tattarawa sukayi suka nufi part din mami lokacin tadawo tana zaune tana waya dasu Abdul wadanda zasu dawo wani satin,
Zama sukayi takawo masa abinci yaci sannan suka yiwa mami sallama suka fita,
Ac ya kunna musu acikin motar ya rufe gaba daya glasses din ya kunna wata waka ta turanci _you are my African queen..._,ahankali wakar take tashi yanabi yana makale da hannun hafsat guda daya acikin nashi yana driving da dayan,
Wata hamshakiyar unguwa tamasu fada aji taga yakaisu, wani tangamemen gida suka shiga mai manya manyan part har guda hudu sannan kowanne upstairs ne,kuma daga can gefe B/Q ne,
Nafarkon yabude suka shiga nan taga tangamemen falo da kitchen da store sai dining area, saman kuma bedrooms ne guda biyu masu dauke da bathroom acikin kowanne,
"Kinga gidan da na sai mana zamu dawo nan bada jimawa ba domin har nabada asiyo furniture's,nafi son ina dawowa daga Cairo insauka anan"
"Wai amma gidan ya hadu yaya, ga girma komai awadace.."
Murmushi yayi yariko hannunta suka fito, "kin dai k'i zancen ko?"
Murmushi tayi,
"To amma yanaga part din guda hudu?"
"Daya namu, daya na mami, daya nasu Abdul"
"To dayan fa?"
"Na amarenki"
Duka takai mishi,
"Allah kabari"
Dariya yayi yabude musu motar suka shiga batare da sun shiga sauran part dinba domin gaba daya parts din tsarin gininsu da komai iri dayane,
Saida suka gama yawonsu agari sannan suka koma gida.
Washe gari hafsat gidan umminta tatafi tawuni acan, misalin karfe 2 narana mami nazaune tana yin lunch taji sallama, har cikin falon mai sallamar tashiga sai faman budada kamshi take nan ta durkusa tagaida mami,
"A'a tashi ki zauna, sannu da zuwa"
Saida mami ta gabatar mata da abinci da abubuwan sha sannan ta dubeta da fara'a,
"Sai dai kuma ban ganeki ba" inji mami,
"Ehh ai momy baki sanni ba, sunana hafsat kuma ni yar gidan alh musa ce ubangidan ya yusleem"
Sake fadada fara'arta mami tayi ta dubeta....
_Fans kuyi min uzuri zakuji ni shiru kwana biyu saboda wani uzuri da ya taso min na gaggawa amma insha Allah nanda sati daya zaku cigaba da jina ina fata zaku yimin afuwa..._
*_Ummi Shatu_*👌🏻