Showing 3001 words to 6000 words out of 65264 words
Chapter 2 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
*MY MOMY*
*BISMILLAHIR* *RAHMAIR RAHIM*
📝 *Page*9⃣⏩1⃣0⃣
*____________* 📖yace, "yanzu Al'mustapha sai da ka daurawa khaujut aure da wannan k'ask'anttacen to Wallahi ban yarda ba dole ya sake ta yanzun nan".
Cikin kidima sarki Fahad Abdullah ya kalle shi murya na rawa ya fara magana, "Dan Allah karka rabani da khaujut Wallahi Zan iya rasa Raina Ina sonta har cikin Raina" Yana magana hawaye na fita daga idon shi.
Al'mustapha da kan shi na k'asa ya kasa ko motsi ya d'ago ya kalle mahaifin shi yace, "BABA Dan Allah kayi hakuri Karka rabashi da matar shi tunda an riga an daura".
Ai be san lokacin da yayi Kan Al'mustapha ba ya shag'e shi ya fara marin shi ko ta Ina dukan shi yake sosai, da sauri uncle ya tashi ya gwace shi a Shak'ar da yayi ma Al'mustapha sannan yace,
"Wato ka nuna min bani na haifi khaujut ba ai bashi ya daura auran ba Ni na daura Amma shikenan ba komai za'a zakan ma Yar ka Amma Ni Zan bashi tawa Yar tunda Ni na haifa tawa".
Ai sarki Fahad Abdullah naji haka ya rushe da kuka yana fad'i, "ku taimake rayuwa ta Dan Allah karku rabani da khaujut".
Mahaifin Al'mustapha kon ko a jikin shi haka ma mahaifiyar shi duk Basu damu ba, khaujut ce ta shigo D'akin idon ta duk ya sauya sabida kuka tace, "BABA kayi hakuri Ni na yarda da auran shi zan bishi ko Dan cetun rayuwar shi Allah zai bamu lada".
Hararan ta maman ta tayi sannan tace, "Kar in k'ara jin bakin ki a maganar Nan kuma dole yanzu ya sake ki".
Durkusa tayi gaban mahaifin nata ta rik'e k'afar shi tace, "BABA ka taimaka nima yanzu Ina son shi zan iya zama da shi".
Kallon ta yayi sannan yace, "yanzu khaujut Zaki iya tafiya wata k'asar ki barmu to shikenan Amma da sharad'in in har kika fita daga cikin gidan nan na cire ki a cikin 'ya'yana".
Da sauri ta d'ago Kai ta kalle mahaifin nata sannan ta saki kuka Mai tsuma zuciya ta k'ara rik'e kafarshi tace, "Dan Allah BABA ka janye wannan maganar bazan iya tafiya bada izinin ka ba".
Ture ta yayi daga jikin shi yace, "yanda Kika zab'a Amma dai Ni na gama magana".
Uncle ne ya tashi ya d'ago ta ya sanya ta a jikin shi yace, "ba komai khaujut Allah yayi Miki albarka kibi mijin ki Dan shine yanzu yake da iko da ke kiyi hakuri kinji karki damu komai zai dawo dai-dai".
Kuka ta fashe da shi sannan tace, "uncle bazan iya binshi ba sabida iyaye na basa son shi yayi hakuri kawai".
Girgiza kai uncle yayi sannan yace, "ba komai Ni nace ki bishi Allah ya sanya muku albarka" kallan mahaifin Al'mustapha Uncle yayi sannan yace,
"Sai kasa musu albarka cikin auran ko shima baza kayi ba? ". Girgiza kai yayi sannan yace, "Zan sa musu albarka tunda Kaine kace hakan Allah ya basu zaman lafiya" sannan ya fita a D'akin.
Maman ta kuwa fashewa tayi da kuka tana zagin Al'mustapha Wai shi ya jefa mata yariya cikin wahala baza ta yafe Mai ba.
Al'mustapha ya kalle sarki Fahad Abdullah da ke zaune kaman ruwa yaci shi yace, "tom kaga duk yanda Abu ya zama to Wallahi Wallahi Dede da su daya ka batawa khaujut Wallahi sai na kashe ka".
Girgiza Kai sarki Fahad Abdullah yayi sannan yace, "insha Allah Ni da khaujut mutu ka raba baza ku taba jin kukan ta ba".
Tashi uncle yayi yace, "khaujut taje ta shirya yanzu zasu tafi".
Kuka sosai khaujut ta k'ara sake tana tunanin yanda rayuwa zata zamo Mata, addu'a shine Allah ya sansautu Mata da zuciyar iyayan ta.
Al'mustapha da kan shi ya dauko Mata abaya ta saka sannan ya rik'e hannun ta ya Kai ta gun mahaifiyar su ta durgusa tana kuka sannan tace, "Dan Allah ta yafe mata".
Ita ma mahaifiyar tasu kuka ta saki sannan ta rungume khaujut d'in kuka suke sosai sannan ta sake ta ta tashi ta bar gurin, hannun ta Al'mustapha ya rik'e ya fitar da ita d'aga D'akin.
Direct mota ya Kai ta sai da ya shigar da ita sannan ya dawo ya Sami Uncle yana k'ara wa sarki Fahad Abdullah fad'a akan ya rik'e musu 'ya Amana.
Magana yayi musu akan su zo su tafi sannan duk suka tashi har Uncle suka fita a gidan Suma mota suka shiga fadawan sarki Fahad Abdullah suka tuka su sai masaukin su.
Suna Isa suka fifito a motucin sannan Al'mustapha ya rik'e hannun khaujut har suka Isa d'akin da suke, shaga sukai suka zauna sannan Al'mustapha ya had'a hannun khaujut dana sarki Fahad Abdullah yace,
"Abokina ga Amana Amana Amana na baka amanar auran khaujut karka cutar da ita sannan karka Bari a cutar min da Yar uwa Ina son ta fiye da komai a rayuwata Dan haka nagode da nuna kaunar ta gare Ni".
Jinjina Kai yayi sannan yace, "insha Allah Zan rik'e ta kaman yanda Zan rik'e Kaina Allah ya bani ikon rik'e amanar da ka bani kuma bazan tab'a manta wa dakai a rayuwa ta nagode nagode sosai Allah ya saka ma da alkhairi".
Ameen yace sannan ya saki hannun su ya sunbaci goshin ta sannan yace, "ma'asallam my ukutee".
Kuka ta k'ara fashewa da shi lokacin uncle shima yazo ya sunbaci goshin ta sannan suka fita a D'akin nan ta k'ara fashewa da wani kukan Wanda sarki Fahad Abdullah yake ji kaman zuciyar shi zata fashe Dan Jin kukan yake har ran shi.
Rungumo ta yayi a jikin shi Yana lallashin ta Amma Ina kuka take kaman ranta zai fita Dan in ta tuna yanda ta baro iyayan ta hankalin ta na tashi.
Kiran yan Nigeria yayi yace musu yau insha Allah zasu tawo dashi da gimbiya khaujut. (tunda yanzu ai ta riga ta zama gimbiya😂)
Haba ai masarautar mure sai ta rud'e da murna aka fara shirye-shiryan taran amarya kuma gimbiya khaujut, gimbiya Haleematun-sa'adiya tunda taji zancen ta k'ara saka kanta cikin damuwa da bak'in ciki.
Ba'a Dade ba Nan ma suka fara Shirin barin k'asa Mai tsarki zuwa Nigeria kasar mu ta gado sarki Fahad Abdullah sai lallashi amaryar shi yake dan kukan Nan da take ji yake kaman ana yanka zuciyar shi.
Sai da suka je Haram suka k'ara d'awafi sannan suka wuce airport, tana manne a jikin shi Daman gashi khaujut bade na san jiki ba, Nan da nan kuwa suka shiga jirgi ya Lula dasu Nigeria.
Babban tarba ake shiryawa mai-martaba sarki Fahad Abdullah Wanda an Dade ba'a Yi irin bikin ba a masarautar mure, komai yayi dai-dai jiran isowar sarki Fahad Abdullah kawai ake.
Gimbiya Haleematun-sa'adiya kon tana D'akin ta kwance bakin ciki ya ishe ta kaman ta kashe masu wannan busa da kid'e-kiden take ji.
Tun kafin jirgin su ya sauka fadawa sun zagaye airport d'in jiran su kawai suke, akwai ba'a Dade ba jirgi ya fara k'asa-k'asa har ya sauko k'asa.
Nan da Nan mutane suka fara fitowa a Haka har su mai-martaba sarki Fahad Abdullah suka sauko shima fadawa ne suka zo da sauri suka rufe shi har sai da suka shiga mota shi da gimbiya khaujut.
Nan suma fadawan suka shiga suka fara tafiya ba'a Dade ba suka iso babban shiga Gate d'in masarautar tun daga Nan aka fara musu marhaba da zuwa, Busan da ake yi ya karu suna shiga kon cikin gidan nan aka fara fitowa ana musu albarka da dawowa.
Iyayan shi Mata suka zo Dan fito da amarya khaujut daga mota....
Vote
Comment
&
Share
*Aunty baby ce* 😉✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
*DEDICATED TO..*
*MISS XERKS*
*BISMILLAHIR* *RAHMAIR RAHIM*
📝 *Page* 7⃣⏩8⃣
*____________* 📖 *Nigeria* kuwa, komai na tafiya dai-dai duk abunda sarki ya Bari ai ma talakawa ana musu sannan kuma.
K'annin shi Aliyu na kula da komai gimbiya Haleematun-sa'adiya tana ta rainon cikin ta da yanzu yake wata hudu.
Kuma tana samun kula daga mahaifiyar sarki Fahad Abdullah da kuma yan uwa shiyasa hankalin ta kwance bata da matsalan komai.
*Saudiyya* Al'mustapha ya samu iyayan shi akan maganar Amma ina duk yanda yake tunanin abun ya huce nan sosai mahaifiyar shi.
Ta fara fad'a Wai baya son yar uwar shi tunda gashi har yana tunanin auran da Ita a Nigerian.
Sosai ya shiga tashin hankali dan gaba daya sarki Fahad Abdullah ya koma abin tausayi kullum zancen shi ya taimaka mai in be samu khaujut ba mutuwa zaiyi.
Daga karshe ma har cewa yayi bazai koma Nigeria ba zaice wani ya amsa sarautar, hakan da ya fad'a shi ya k'ara bawa Al'mustapha tausayi.
Ya dau aniyar insha Allah sai ya aura mishi khaujut, gurin wani babban uncle d'in su yaje Wanda duk family din su suke ji da shi kuma zasu ke jin maganar shi.
Duk ya gaggaya mai abunda ke faruwa sannan yace, shi tausayin abokin nashi yake kuma yana da hankali sun zauna har na tsawon shekara biyar Babu wani abun na banza da yake yi.
Jinjina Kai uncle d'in yayi sannan yace, "ita khaujut d'in tana son shi in dai tana son shi ba matsala".
Rasa abun da zaice Al'mustapha yayi kawai sai ya d'aga Kai alaman tana son shi tunda yasan halin khaujut tana da hakuri kuma yasan zata amince.
Uncle d'in yace. "to yanzu su tashi suje gidan iyayan nasu ya musu magana" hakan nan Al'mustapha ya tashi jikin shi duk a sanyaye, tunda ita khaujut ma bata san abunda ake ba shi kad'e yake kidan shi yake rawan shi.
Ko da suka je gidan uncle d'in yama iyayan nasu magana amma ina gaba daya sunce basu yarda ba sabida basu san ya Nigeria take ba, yayi ta basu hakuri da lallashi amma abun yaci tura har yayi fushi ma ya bar gidan.
Sarki Fahad Abdullah yana can masaukin su kuma ba lafiya sabida shi fa Allah ne ya daura mai san wannan yariya be iya zatun zai iya cire ta a ranshin mutanan shi hankalin su ya tashi sosai ganin yanda lokaci daya ya rame ya daina wal-wal kaman ba sarki Fahad Abdullah ba.
A haka har aka kwashi tsawon sati biyar suna cikin wannan halin gashi Al'mustapha yayi yayi abun ina kowa a family sun basu amince ayi wannan abu ba.
Wata ranar Friday Al'mustapha ya shirya yace Ita ma khaujut ta shirya zasu fita nan da nan ta shirya direct masaukin su sarki Fahad Abdullah suka je.
Yana kwance duk ya rame na lafiya gashi yanzu sauran sati daya su bar saudiyya shiyasa ya k'ara shiga tashin hankali, Al'mustapha da khaujut suka ganshi a cikin wannan halin duk da khaujut yariya ce amma be hana ta tausaya mai halin da ta ganshi a ciki ba.
Kallon ta Al'mustapha yayi yaga yanda tayi shuru tana kallon shi yayi murmushi sannan yace, "ya ukutee ki taimaki wannan bawan Allah nasan yar uwata tana da tausayi da sanin ya kama Dan Allah kinji my ukutee".
Hawaye ne suka fara zubowa sarki Fahad Abdullah ya taso daga in da yake zaune ya durkusa gaban ta yace, "dan Allah kiyi hakuri ki ceceni Wallahi zan iya mutuwa akan ki yanzu haka ciwan da nake ji a zuciya ta kaman za'a dauka raina ki taimaka min khaujut".
Kuka sosai khaujut ta fashe da shi sannan ta kalle Al'mustapha tace, "bani bace matsalan iyayan mu ne Ni na yarda in dai sun yarda".
Jinjina kai Al'mustapha yayi sannan yace, "ba komai daman buk'atata ki yarda Allah ya miki albarka khaujut Allah yasa yanda kikai farantawa wani ke ma Allah ya faranta miki".
Tashi tayi ta fita a D'akin mota ta shiga ta k'ara fashewa da kuka tana ganin Bata cuci kanta ba kuwa Anya zata iya bin shi Nigeria ta bar iyayan ta anan.
Haka dai take ta tunani iri-iri, Al'mustapha ya kalle sarki Fahad Abdullah yace, "abokina zanyi duk yanda zanyi in aura maka khaujut amma da alk'awarin zaka rik'e min ita Amana".
Da sauri ya d'aga Kai yace, "na yarda Wallahi na yarda duk abunda na Mata Kai min ko kashe ni ne kayi".
Dafa kafad'ar shi yayi sannan yace, "ba zancen kisa amma Wallahi ka batawa khaujut ba maganar abota, sabida a tsarin k'asar mu... " Ai be Bari ya k'arasa ba yace,
"Wallahi nayi maka alk'awari khaujut baza ta tab'a shiga wani hali ba kuma zan rik'e ta kaman yanda zan rik'e Kai na insha Allah".
Tashi Al'mustapha yayi yace, "ka shirya da Wanda zasu tsaya ma insha Allah yau za'a daura maka aure da khaujut".
Ai ya rasa wani irin farin ciki ma zaiyi kawai sai ya duk'a yayi sujjada ya gaida Allah yana nuna farin ciki mara musaltuwa.
Murmushi kawai Al'mustapha yayi yana jin dadin yanda yake nuna ma yar uwar shi soyayya, sannan yace, "su hadu a Haram bayan sallah JUMA'AT".
Sannan ya fita, sarki Fahad Abdullah ji yayi kaman an saka shi a aljanna Kiran yan Nigeria yayi ya sheda musu duk abunda ya faru, ba k'aramin murna masarautar mure ta shiga ba.
Barin ma iyayan shi Dan Daman burin du kenan dan ba'a tab'a sarki da Mata daya, haka mutan fada ma kowa ka gani yana cikin farin ciki.
Gimbiya Haleematun-sa'adiya kuwa tana Jin wannan maganar sai da ta suma nan fa ta fara kuka ita ba ai Mata adalci ba ko haihuwa batai ba za'a ce zaiyi aure.
Maman ta da kanta tazo tana lallashin ta kuma tana gaya Mata cewa ai Daman sarki baya Mata daya tayi hakuri ta kwantar da hankalin ta amma ina nunawa tayi bata san zancen ba.
Haka dai kowa ya hakura yasa Mata Ido sabida haukar da take tayi yawa.
Saudiyya kuwa bayan fitowa daga sallah JUMA'AT Al'mustapha da uncle d'in su suka daura auran khaujut da sarki Fahad Abdullah.
A iyayan su Al'mustapha ba Wanda ya sani duk da Al'mustapha yana cikin tashin hankali Amma hakan be sa ya sare ba.
Sarki Fahad Abdullah kuwa ai ya kasa rufe baki sabida tsabagin murna hamdallah kawai yake ma Allah da khaujut ta zama matar shi.
Bayan daurin aure uncle da Al'mustapha da sarki Fahad Abdullah suka huce gidan su Al'mustapha, lokacin kon duk kuwa na gidan na Nan Banda khaujut da take bedroom tana kuka.
Shiga sukayi babban parlour gidan sannan uncle d'in yace duk kowa na gidan yazo yana da magana da su, duk kon suka hadu sannan yayi gyaran murya ya fara magana da harshin su na larabci.
"Haka Allah ya tsara khaujut matar wannan bawan Allah ne ba yanda zamu iya sai dai hakuri tunda yau na daura musu aure".
Tashi tsaye mahaifin Al'mustapha yayi cikin kid'ima da tashin hankali yace,
*Vote*
*Comment*
*&*
*Share*
*Aunty babyn ku ce* ✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
*DEDICATED TO..*
*IZZAR SARAUTA* *fan's*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 **Page**1⃣3⃣to1⃣4⃣
Tace, "Allah ya baka yawan rai gimbiya khaujut Allah ya sauke ta lafiya" da sauri mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya daga hannun shi sama yana kabbara, sannan yace,
"Da fatan dai tana cikin koshin lafiya? ".
Murmushi jakadiya tayi sannan tace, "Allah ya kara ma nisan kwana baka tambaya mai aka samu ba".
Murmushi yayi sannan yace, "to Mai aka samu? " Cikin zumud'i jakadiya tace, "magajin ka insha Allah namiji ta samu mai kama da Kai".
Nan da nan farin ciki ya mamaye shi ya rasa ma ina zai sa kan shi dan murna bakin ciki ya kasa rufuwa, sabida be taba kawo wa zai samu namiji ba cikin farin ciki yace, "jakadiya kin zo min da albishir mai girma dole ki amsa kyauta mai girma".
Zubewa kasa tayi tana mai kirari da mika godiya sannan ta fita cikin farin ciki.
Nan da Nan masarautar mure ta san da wannan haihuwa kowa ka gani murna yake mai-martaba ya samu magaji,
Gimbiya khaujut tana can an kaita part d'in ta an gyara ta da jaririn ta da ka gan shi kaga jinin larabawa Amma fuskan shi sak na sarki Fahad Abdullah ne.
Ita ma tana cike da farin ciki sosai ganin Allah ya bata abun da bata taba tunani ba, sarki Fahad Abdullah ne ya shigo cikin farin ciki, ya zauna kusa da Ita yana jin sonta na k'ara shiga jikin shi.
Murmushi yayi sannan yace, "ban san da wani baki zan mik'a godiya ta ga Allah ba da ya bani ke sannan ya bani d'a namiji Wanda na dade ina so Allah nagode ma Allah na kara gode ma".
Shuru kawai gimbiya khaujut tayi tana jin kaunar mijin nata na Kara shiga zuciyar ta, tashi yayi ya dauko jaririn da yake kwance gadon shi irin na sarauta.
Kallon yaron yayi wani irin son shi da kaunar shi yaji ji yake kaman ya maida shi ciki Dan so, addu'a yayi mai sannan ya rungume shi a jikin shi yana kara gode ma Allah.
Gimbiya Haleematun-sa'adiya kuwa...
🥴 *Wallahi yau bani jin typing sai anjima ko gobe*
*Vote*
*Comment*
*&*
*Share*
*Aunty baby ce* 😁✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
*DEDICATED TO..*
*MAMAN MUHAMMAD*
*MAI-GWAZA*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *Page* 1⃣1⃣⏩1⃣2⃣
*____________* 📖 Gimbiya Mabaruka matar mai-martaba ita ta fito da amarya khaujut daga mota sannan ta shigar da ita babban parlour gidan, nan kuyangu suka fara gud'a masu busa nayi.
Wata kujeran sarauta aka zaunar da ita sarki Fahad Abdullah ya zo ya zauna kusa da ita, gimbiya Ameena ce ta matso kusa da ita tana Mata barka da zuwa masarautar mure.
Khaujut duk da Bata San abunda ake cewa ba Amma abun ya Burge ta ganin yanda ake murnar ganin ta sai ta tsinci Kan