Showing 60001 words to 63000 words out of 228147 words

Chapter 21 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Na Sajida Nijar.txt

28 Dec 2024

36585

ko? To na fada dan Allah ki dakeni ki huta mana tunda na ta a abokin tagwaitakarki!


Dawowar Anmy da waya a hannunta ya saka su yin shiru


Wayar ta mikawa Najeeba tana mai tsareta da mugun kallon idan bata amsa ba komai na iya faruwa


Wayar ta amsa da hannunta na hagu tana kallon saman screen din


Wauh na ce a lokacin da na ga wace ke zaune itama tana kallonta
Kallon kallo suke yiwa junnansu, har sai da matar ta dan saki murmushi ta lumshe idannuwanta ta bude cike da isa ta ce" ke yar Mutalab sai uwarki ta gaisheki ne?


Ta kasan idannuwanta ta kalli matar aman bata furta ko A ba


Murmushi ta yi tana yi mata kallo mai hade da madaukakiyar soyaya irin ta d'a da mahaifi
Ita kam ta ina zata bi y'ar tata ta dawo mata yanda take so?
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" yaya jikin ki?


Najeeba dai bata ce komai ba, Anky kuwa bata takurata ba ko amsar da ta yi ai ta yi kokari, hakama yan uwanta


Zahrau ce ta leko tana daria ta daga hannunta ta ce" Mama i miss u


Warcewa Ummulkhair ta yi tana ihun cewa" Mama, ni ke missing din ki


Ummukulsum ta amshe ta ce" mama ba ji ce tagwayenki ba?


Daria itama take a hankali ta dan juya idannuwanta wa'inda sukai wani farr da su gasu da girma masha Allah ga gyaran da suke dauke da shi ta ce" an matana, baku san irin yanda nake missing dinku ba, ina kewarku fiye da tunaninku, ina so na zo na ganku, na rungumeku, na ji me kuke ciki, ina son halartar auren Zahra, ina nan ina yi maku tanadin abubuwan da idan kuka saka baki daya damagaram sai ta girgiza


Bakinta ta tabe ta mike kwonciyarta tana lumshe ido, a kasan zuciyarta kuwa tana fadin" abinda kika fi kauri a kai kennan, abinda ya fi maki ni kennan wato abin duniya!


Anmy ta karasa kusa da ita ta ja bargo ta rufa mata, dan zaunawa ta yi gefenta a sanyaye ta ce" NAJEEBA


Kallonta ta yi da kallo irin na wanda take iya yiwa mahaifiyarta


Dukawa Anmy ta yi wajen goshinta ta yi mata kiss a goshin nata a sanyaye ta ce" ki huta kin ji? Dan ina so mu fita da ku duka gobe in sha Allah


Kanta ta dan gyadawa Anmy kafin ta maida idannuwanta ta lumshe


Su kuwa hira suka sha da mahaifiyar Najeeba wace du wasu abubuwa irin su wani lumshe ido, su shan iska, su shagwabe yannayi baki daya nata ne Najeeba ta kwasa, ba wai tana yi dan ta birge namiji bane, abinda dai ta kara a kai shine ta fahimci yana tsuma mazan sai take kara sakar masu shi




Kayan nasa ya tsurawa ido kafin ya watsar da su cikin kwondon kayan wanki


Kasan shower ya tsaya ya dora hannayensa jikin garun wajen yana jin saukar ruwa a jikinsa


Sai da ya gama ya darje jikin nasa da sabulu da soson wankansa kafij ya fito daure da tawul mai tsayi


A hankali ya karasa wajen miror ya tsaya


Turarensa ya dauko ya yiwa jikinsa bari da shi kafin ya jefar da kwalbar dan ya kare sai wani


Idannuwansa ya dan kurawa ido, yar yatsarsa ya kai wajen da bakin abin ya yi yar kwana tamkar wanda yake saka kwali
An haife shi ne da kwali a idannuwansa, shi kansa baya yiwa kansa kallon tsaf domin kwalin nan na tayar masa da tsigar jikinsa shi yasa baya matsewa mutun duba ko yace zai buda girman idannuwansa a kanka domin bai san yaya zaka ga idannuwan nasa ba


Juyawa ya yi ya ciro wata farar jalabiya marar nauyi sosai ya saka a jikinsa sannan ya saka dan gajeran wando


Wajen bed dinsa ya karasa ya kwonta yana mai adu'ar tsari dukan motsinsa


Rmt din Ac ya laluba ya dauka daga kwoncen ya kara masa karfi ya sada shi daidai kansa sannan ya lumshe idannuwansa


Tunanika ne birjik a cikin kwakwaluwarsa shi har ya yi watsi da abinda ya faru tsakaninsa da Najeeba domin ya ajiye hakan a fagen bata da kunya ne zai koya mata hankali a nitse


Baci ne ya sandeshi ya dauke shi , irin bacin nan wanda ke dan fizgarka sama sama
Irin abin nan dake zaburar da mutun a yayin da irin bacin nan ya zo masa ne ya zowa SARKI


Abin sai ya hade da a lokacin da ta kai masa damkar nan ta saka gwuiwar kafarta ta daki wajen da bai dace kafar tata ta kai ba, hakan ya saka shi kara jin wannan balakin da ya ji wanda da ba dan ya rintse idannuwansa ba a lokacin zai iya kurma ihu ne
A zabure ya farka yana mai kai hannunsa wajen ya damka yana mai rints ido domin sak mafarkin kamar a da gaske ne abin zai sake faruwa da shi


Da sauri ya kai dubansa wajen, idannuwansa ya mayar ya lumshe a cikin zuciyarsa ya furta" azaluma, na jikata da ruwa shine ta dakar min wajen da idan ta kasarani na gama wata takama a duniya ko? Ta Allah ba taki ba macuciya da lamarin maza ya gama bude maki ido!


Kuma lumshe idannuwansa ya yi yana tausar kansa
Bai taba nunawa Zinariya ta zo gareshi ba, ta yi kadan ba zinariya ba bai ga macen da zai je ya lalaba ko ya tura mata yar muryar cewa ta dube shi ba! Idan ta kawo kanta ne sannunta idan bata zo ba ko me zai ji yakan taushi kansa ya tirsasa kansa ne ya dane kamar yanda ya iya danne abubuwa da yawa a rayuwa
..........................................


Wajen karfe goma tuni sunna makeken fallonsa,
Fallon da ya saka yan matan daga kawunnansu sunna bi da kallo, falon da ya gama haduwa ya hade ya harhade


Sunna zaune ne saman maka makan kujerun falon na alfarma, kujerun kansu nishi suke sunna murmusmus a ido domin ba kananun kujeru bane baki dayansu irin na gidan sarakai manyan sarakai


Maka makan Ac din ne ke kara huro sanyi a falon wanda sakamakon zaman minti goman da suka yi har jikinsu ya gama daukan sanyin


Fitar da Anmy ne hakan ya sa dole kowace ta bi tsari na saka Alkyaba


NAJEEBA ta saka wata watsetsiyar atampa ja, an yi mata dinkin sket da riga ne , sket din daga baya an yi masa tsaga mai dan tsayi domin ta haye sama kadan sannan sket din ya kamata daga wajen duwawunta tsam sai ya tafi zuwat bai bude din nan ba
Rigar kuwa an yi mata dinkin zamani, an mata baban wuyan nan ne wanda ke saukowa kafada sannan daga gaban an dan yi yar tsaga an fitar da V
Hannayen kuwa an saka masu roba daga sama sun bude sosai daga cen kasa kuwa sun tsuke sakamakon robar da aka saka


Kanta kuwa dauri ne ta kashe na Zahra buhari


Ta rigaya ta saba da rashin zama fuskarta ba a gyare ba hakama ko fita zata yi sai ta tsuke ta gyara fuskarta tas
Hakama yanzun fuskarta a gyare take da simple mak up, idannuwanta kuwa ta yi masu sabo da dora natural gashin ido masu tsayi sukan karawa idon wani sirrin kyau da fuzga ne


A hankali ta sada kanta ta ce"Anmy, me zai hana mu bari gobe mu yi fitar nan? Duba da bai fito da wuri yau ba


Anmy ta buda baki zata yi magana jakadiya ta yi salama


Dukawa ta yi a hankali ta ce" Allah ya kara lafia, Elhaj Mutalab ya karaso


Kanta ta gyada mata dan haka ta mike da sauri ta fita


Tana fita bata jima sosai ba Abih ya shigo da salama


Murmushi ne kwonce saman fuskar Anmy tana amsawa kafin ta mike tsaye ta ce" yaya shigo zauna mana muma jiran fitowarsa ne muke


Karasowa ya yi ya zauna, yaren baki daya suka hadu sunna gaishe shi da yannayin murnar ganninsa


Hannunsa ya dora a gefen fuskar NAJEEBA ya ce" yaya jiki?


Murmushi ta yi ta dan dora gefen fuskar nata a hannun nasa


Ci gaba ya yi da shafa jelar gashinta dake yawo, dayan hannunsa kuwa Ummulkhair na rike da shi tana dan masaging daga kasa kuwa Zahra ta rike kafa daya tana masaging Ummukulsum kuwa tana daidaita masa ruwa daifai misalin shansa


Zamansa ya gyara ya ce" kin san me nake gani kuwa Anmynsu?


Anmy ta girgiza kai bayan ta ajiye masa abinci a plat domin komai a jere yake


Abih ya ce" sarka DAYABU ya saka aka yiwa yaren nan har shi aman banda NUSAIBA


Anmy ta dan yi turus tana kallonsa ta ce" kamar yaya banda Nusaiba? Me ta yi uta Nusaibar da ya wareta?


Abih ya dan yi murmushi ya ce" na tambayi kannen du sun ki fada min abinda aka yi, koma meye na san mai girma ne, aman kuma sun ki fada min abinda ya faru


Dubansu Anmy ta yi daya bayan daya a hankali ta ce" eyah, eyah, ashe zan ga haka da raina tun kasa bata rufe idannuwana ba?


Shigiwarsa da kamshin turarensa da ya shigo du kuwa da irin yanda dakin ke dauke da kamshin turaren wuta ya saka Anmy waigawa wajensa


Fuskarta ta sada, hankalinta ya tashi jin haka,


Yan matan ne du suka mimike aman Najeeba sai ta langwabe a jikin Abih ta lumshe idannuwanta tamkar bata san da fitowarsa ba


Da sauri Zahrau ta saka hannayenta ta mikar da ita inda ta sakar mata harare ita kuwa ta jinginar da ita a jikinta


Ya saka wata shigar ce mai birkita lisafin alhazai
Ya gama kashe shigarsa ne cikin shiga mai daraja
Ya fito a sarkinsa ga rawaninsa mai girma mai kayata sarautarsa


Ja ya yi ya tsaya gaban makeken abin turaran wutar da ake yi ana karawa kafin ya kone ake cirewa a zuba wani yana tashi a hankali domin ba garwashi bane a ciki toka ce mai zafin gaske


Hannunsa ya dora saman dokar wace ke dauke da zafin gaske domin ita ke saka turaren hayaki a hankali a hankali


Da yan yatsunsa ya marmatsa turaren dan ya isa haka sannan ya maida dubansa wajen mahaifiyarsa wace ta fi daukan hankalinsa gannin yannayinta


A hankali ya karaso har kusa da ita kafin ya rage tsayinsa sosai kansa sade ya furta" barka da safiya Anmy


Anmy ta dago ta sauke idannuwanta a saman kansa


Hannunsa ta kamo ta rike tana yi masa duba irin na ido cikin ido, a hankali ta ce" na kawo karar yan uwanka, ina so a mana shara'ar cikin gida , ina so ka zaunar da DAYABU MUTALAB tare da kannensa baki daya ka yi masu tambayar a kan me zasu ware daya daga cikinsu?


Najeeba ta lumshe idannuwanta, tabas itama tana son a hana wannan gaba tsakaninsu da yar kanwarsu, yarinyar zata baka tausayi ne idan ta ga daya daga cikinsu tana rarume rarumen ya dauketa tana kukan ya dauketa sai dai ba hali domin maganar dayabu maganar uba ce a wajensu, sai dai a yanzun fa ta ji azalumin nan ne zai yi maganar sai take jin a kan me?


Idannuwansa ya lumshe wanda hakan ke nufin amsarsa ne na ya karbi bukatar mahaifiyarsa


Agogon hannunsa ya duba a hankali ya furta" karfe tara na dare a falon karatu


Abih ya sauke ajiyar zuciya yana mai jin kanwar tasa a ransa, yana godewa Allah a kulun da ya bara masa ita, ita daya ta rage masa sai y'ayansu


Anmy ta dubi yan matan a hankali ta ce" na san ba zaku fadi laifin yayanku ba, kuma ba zaku fadi abinda kuka yi tsakaninku ba, aman ku sani idan kun ga kun samu wariyar kai to kasa ta birni idannuwana ne


Shi dai yana tsaye ne sai da ta gama ya kama hannayenta ya nufi wajen zama da ita


Yana zaunar da ita ya dawo suka gaisa da Abih kafin ya samu waje ya zauna


Du yan matan uku kasa suka kara zubewa
Aman Najeeba sai ta karasa saman kujerar da Anmy ke zaune ta dane gefen kujerar sannan ta dora kanta a kafadarta


Wannan karron kam komai a kan idannuwansa, mamakin yanda aka yi ta mike kan kafafuwanta da sauri haka da mamakin yanda aka yi ta manta gargadinsa da sauri haka suka saka shi tsaida dubansa a kanta


Lebensa na kasa ya dantse da hakoransa kafin a sanyaye ya buda bakinsa bayan ya gama harhada kalaman da zai yi anfani da su ya ce"
[31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻




*Na*




*SAJIDA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_





22




Cike da iza ya buda bakinsa ya kai dubansa wajen Abih, a hankali ya ce" Abih, in sha Allah auren Zahrau karshen watan nan na tsayar da shi


Abih ya ringa gyada kansa, tabas ya yarda da abinda ya yanke domin shi din uba ne a wajen yaren baki daya sannan shi da kansa ya isa da shi bale yaren


Sai da ya kara mintunna yana jin sai sanya albarka Abih da Amih suke, yaren kuwa du sun sada kawunansu
Anmy kuwa tana shafa bayan Najeeba, lalabata take domin bata da lafia konda safe da ta farka sai da ta sha maganinta na athsma domin numfashinta ba wai wani daidaituwa ya yi ba


Bakinsa ya buda a karo na biyu ya kaisasa muryarsa ya ce" sai dai ina so hakan ya zamo sirri
Ko da wasa bana so maganar ta fita tsakar gida bale waje domin BINTU kasheta aka yi


Gaba dayansu a zabure suka kale shi
Najeeba kuwa kamar wace aka jefo daga kan Anmy zuwa kasa sai gata ta wuntsilo tana kallonsa a tsorace


Abih ya yi gagawar furta" innalilahi wa ina ilaihi raj'une, wani irin kasheta aka yi? Wa ya kasheta?


Anmih ta kafeshi da ido, subahannalah kasheta? Wani irin kasheta? Gaba daya sai ta ji hankalinta ya tashi da maganar sannan ya sako cewar kar a fitar da maganar Zahrau kennan yana cikin tsantsamin wani ne ya yi hakan a tatare da shi?


Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Abih sannan ya kalli Anmih
A hankali ya ce" Allah masani, sai dai kowa ya yi taka tsantsan sawayen kowa a kirge yake


Gaba daya ta sha jinnin jikinta daga zaunen da take kafin ta maida dubanta wajen yan uwanta


Suma yanzun sarkin suke kallo a tsorace su duka


Yana gama magana ya mike tsaye


Baki dayansu suka sada kawunansu, a hankali suke furta" a huta lafia


Anmih cike da kaunar d'an nata kwaya daya da kuma tsantsar tausayin halin da yake ciki itama ta furta" a huta lafia


Sai da ya shige du suka dago da kawunansu


Rarafawa Zahrau ta yi da sauri ta dora kanta saman cinyar Anmih
Muryarta na dan rawa rawa ta ce" anmy, tsoro nake ji, kamar wanda ya kasheta yana iya kashe ni?


Anmy ta yi sauri girgiza kanta a hankali ta ce" ba zai kashe min ke ba, ba zai kashe min ke ba in sha Allahu
Allah zai hana, itama ki kadara lokacinta ne ya yi


A hankali Najeeba ta kama hannunta ta rike a nata itama cike da tunanin da ya gama hadasa mata zufa daga cikin jikinta


Fitar da suka fasa kennan, domin dama ta yi niyar fita da su ne su je wajen likita a kara duba Najeeba sannan su je wajen batuba wace ta yi niyar damka mata shirin Zahrau dan duka duka auren bai fi sati biyu ba


A dole suka koma bangarenta suka hadu ta saka a kawo mata kayayakin shirya amare a boye


Tun a ranar ta shiga baiwa Zahrau shiri irin na gyaran jiki da hade haden tsumi kala daban daban
Sai take jin dadin yannayin, dan ta tuna da, dan haka ta titino abubuwa irin na da wa'inda ta rike wuta sosai a zamanin mahaifin mai martaba ta ringa kawo dukan abin bukata
Kara kayan gyaran jikin ta yi sosai domin tana darzar fatar Zahrau sauran na darzar nasu da kansu
Tsumin nan ne kawai basa sha, sun rufe a falon Anmy na biyu sun shinfida katuwar tabarma sun dora mata leda du sun saka kannanun kaya sai raha suke, itama Anmy din sai daria takewa shirmensu har tsalen itama sai ta shafa suke hadin madara da kurkum fir ta ce ba zata shafa ba


Turaren wuta mai dadin kamshin ne ta zuba a dan kasko ya ringa ratsa jikin Zahrau,
Tana gamawa Ummulkhair ta dauko masu suma suka hadu a cikin abin rufa su uku suka zuba


Anmy ta bisu da da kallo ta yi murmushi tana girgiza kanta, fatanta Allah ya nuna mata nasu suma haka ta kimtsa su


Da sauri Najeeba ta cire abin rufar tana ta numfarfashi sama sama


Ummukulsum ta warce ta kara rufa su tana fadin" ke ja cen zaki wani bude mana dama mai numfashin kadangaru kawai


Najeeba ta matsa tana sauke numfashi, Anmy ta miko mata sansanyar madarar da ta kadawa Zahrau tana mata dariar itama ta ce" idan ba neman magana ba mai ya kaiki saka kanki ke mai cutar huka?


Amsa ta yi ta kafa kanta ta shanye tas sannan ta kalli anmy ta ce"Anmy ina son na turara jikina nima


Anmy ta ce" to zo nan


Mikewa ta yi ta karasa wajen da aka yiwa Zahrau


Zama ta yi saman kujerar Anmy ta rufa mata bargon aman kanta a waje ta zuba mata turaran mai sanyin kanshi ya shiga bin jikinta


Kafafuwanta ta wara cikin dabara ta kara matsa turaren wajen sosai harda rintse ido dan zafi ta ji na dukan wajen domin da pant a jikinta, tana ji su Nadia na fadin aba turara wajen da turaren wuta ko a yi matsi, to ita me hadinta da matsin? Aman wannan kam sai ta yi ((😲))


Sun jima a wajen kafin suke fitowa shima yama ta yi suka fito dan amsar baki


Bayan salar isha'i yaya Dayabu ya shigo tare da NAJEEB,
Sunna sanye da shada ne a jikinsu wando da riga iri daya sun yi tsaf da su


Ya gaishe da Anmy yana dan murmushi irin yana neman gyaran nan, sai Anmy ta hade fuskarta ta kawar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login