Showing 12001 words to 15000 words out of 35734 words
Chapter 5 - TUN KAFIN AURE BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Batul Mamman--.txt
ga....da dai sauran aikin sabo. A bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai daga Allah. Ban farga da munin share lamuran yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma nasan haramcin nema akan nema. To idan haka ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron. Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba don bata sonshi ba sai don ta koya masa hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke da ku ma...ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi watarana ya dawo ma lokacin da baka tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐17
Sakin baki Baffa yayi yana kallon Alh Bashir, Senator Rufai da Saif. Wane irin rainin hankali ne suka zo masa dashi. Gyara zama yayi ya kalli Alh Bashir...yanzu kana nufin ranar asabar da wani zaa daurawa Hafsa aure ba da Saifullahi ba? Wai ni Alhaji me kuke nufi da ni da iyalina ne? Akan hoton da yaron nan ya sa Hafsa taje suka yi babu abinda banyi mata ba karshe kuma sai kawai kace min daban yana son aurenta kuma ka amince. To kai ma ka amince ne? Ya tambayi Saif. Sunkuyar da kansa yayi kasa. Shi kam kunya tasa har zuci baya son auren nan don bazai juri haduwa da mahaifinta yana tuna ranar da ya kama su a mota ba.
Zuciyarsa har neman tafasa take don a yadda yake ji a ransa ko gyada aka dora masa a kan kirji tsaf zata soyu. Ina amfanin dan cikinka ya dauko maka abin kunya. Ba don hoton nan ba sam bazai damu ba idan Saif ya fasa auren Hafsi. Senator Rufai da yake gefe yana kallon abinda ke faruwa a falon yayi dan gyaran murya don ya fuskanci kwata kwata kudinsa da mukaminsa baiyi wa Mal Aminu kwarjini ba. Kallon da ya yiwa Baffan hafsi yasa yayi shiru...malam tun a gidansu munyi magana dasu yaron yace indai ka amince to zai iya hakura da ita. To a wane dalili ne wai zaku mayar dani karamin mutum irin haka? Ko don ba 'yarka bace shine zaku rinka juya min ita kamar waina. Bakin Baffa har kumfa yake yana magana ba karamin bacin rai ya shiga ba kila kudi senator ya basu shine suke neman yi masa wannan cin kashin. Senator Rufai yayi masa bayanin halin da dansa yake ciki da tsoron karin lalacewarsa sai baffa ya kada baki yace wato lalataccen danka kake so ya shiryu sanadiyarta ko? Idan kuma abin ya faskara ya dora min ita akan turbar lalacewa fa? Haka yayi ta fada karshe yace ni dai gaba daya na fasa bawa kowa Allah Ya hada kowa da rabonsa.
Abin da senator yake ta kokarin boyewa game da jikinsa ne ya faru don kuwa yana tashi kirjinsa ne ya fara ciwo sai jiri ya debeshi ya fadi. Baffa ko kallonsa baiyi ba don a tunaninsa na karya ne tunda yaga kudi bai dauke masa hankali ba. Saif da Alh Bashir kuwa da sauri suka yi kansa Alh Bashir a tsorace yace haba Aminu taimaka mana. Idan mutumin nan ya mutu a gidan nan wallahi duk sai an daure mu ko a yanke mana hukuncin kisa.
*******************
Alh Bashir da Mal Aminu ne tsaye gaban gadon da aka kwantar da Senator Rufai bayan yasa iyalinsa sun dan basu wuri. Da kyar yake maģana yace nasan a dalilina kun sami sabani amma bisa amana zan fada muku sirrina. Hakika duk wata kujerar iko a kasar nan is addictive maana idan aka hau ba'a son sauka indai ba ta sama za a hau ba. Magudin siyasa da hadamar kudin talakawa duk munayi. Ina tsammanin ma shiyasa Allah Yake jarrabarmu da lalurori da kala kala da 'ya'ya marasa da'a. Yasa hannu ya share hawaye. Ina matukar son Junaid ganinsa nake tamkar mahaifina saboda kamaninsu. Duk abinda ya zama a yau laifina ne saboda yadda na sakar masa yake facaka da kudin talakawan kasar nan. Tun farkon abin mahaifiyarsa ta fara hanawa ni kuma ina ta ganin kamar lokacinsa ne. Maganar tasa sarkewa tayi saboda tari Mal Aminu ya rirrike shi. Sai da abin ya lafa ya cigaba da magana. Muna cikin wani lokaci da yaran da ka tsaya da kyau wurin tarbiyarsu ma baci suke balle wanda aka sakewa. Masifu sunyi mana yawa duk a dalilin nesanta kanmu da mukayi daga Allah da koyarwar Annabi SAW.
Mal Aminu ya dan tabe baki don shima sheda ne akan rashin adalcin kasarnan da yadda yake ganin tarbiyar yara yanzu a matsayinsa na malamin sakandire. Ji yayi senator ya rike masa hannu wanda hakan ya dan tsorata shi. Sati biyar kenan da likita ya tabbatar min da cewar inada ciwon zuciya kitse ya lullube ta. Babu wanda na fadawa sai ku biyun nan da na hadu daku a yau. Likitan ya tabbatar min ko dai na cigaba da rayuwar shan magani ko na mutu. Subhanallahi Alh Bashir ya fada.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 18
Hakika mutuwa abin tsoro ce musamman ga irinmu masu aikata sabo muna sane. Kamar yadda na fada a gidanka Alhaji waazi naji yayi matukar razana ni. Ina tsoron mulki yanzu, ina tsoron kudi, ina tsoron haduwa da Allah akan laifukana sannan ina tsoron samun kamasho daga laifukan Junaid tunda laifina ne abinda yake yi. Akan yarinyar nan ya dawo gida da guduwa yayi. Akan ta yayi min alkawarin shiryuwa shiyasa kaga na dage. Idan har na mutu yana wanan rayuwar kabari zai min kunci. Kuka ne yaci karfin senator sai dai su uku mazan akwai hawaye a idanunsu. A wannan zamani hanyoyin dulmiyar da bayin Allah akwai yawa ga bayyana sabo saboda rashin tsoro. Mal Aminu yace zan amince amma sai anyi masa gwaje gwajen cutuka saboda lafiyar Hafsa. Ko sau daya kada yazo gidana sai na tabbatar da lafiyarsa sannan zaa fara maganar aure. Abu na karshe zamu rubuta yarjejeniya kai Alhaji ka zama shaida duk ranar da ya koma ga miyagun halayensa bayan aurensu kun amince kotu ta raba auren idan yaki shiryuwa. Na yarda na amince kawai senator yake fada. Ba zai iya fada musu mugun mafarkin da yayi yaga kansa cikin wuta yana ta shan azaba ba a dalilin dukiyar da suke wadaka da ita. Abin tamkar gaske ya gani. Mutuwar abokinsa washegarin mafarkin wani wanda yayi gwamna karo biyu sun shiga sun fita ya zama minista shi ya kara tada masa hankali. Gawar abokin nasa bakikkirin kamar an shafa gawayi gashi yaransa suna ta murna harda party ranar da yayi bakwai wai giwa ta fadi. Sosai ya tsorata har baya iya baccin kirki. Uwa uba kuma yaga yadda hukumar kama masu watanda da arzikin kasa su cinye a cikinsu tasa mutane a gaba. Wannan tonon asirin ma na duniya ya ishi bawa mai tsoron Allah.
*******************
Kuka take sosai a daki tunda Baffa ya sanar da ita abinda ke faruwa. Duk gidan al'amarin bai musu dadi ba Mama tana ta mita. Hafsi tayi fushi sosai da Saif da ace wani abu ma ya faru tsakaninsu haka zai fasa auren karshe duk wanda ta aura yaci mata zarafi. Yanzu duk farincikin da take baffa ya yafe mata ashe hoton nan bazai fasa jawo mata sabbin masifu ba kullum.
Ummati ce ta shigo da sallamarta Hafsi ni fa ban gane zancenki ba a waya. Rungume aminiyarta tayi tana kuka tana sake mata bayani. Ummati ta kalleta yanzu shi dan sanatan kin ganshi? Ke wa yake ta tashi ko sunansa ma ban sani ba. Ai kinji dadi Lawal baizo kun yi naku hotunan ba. Wannan hoto bai zo min da komai ba sai sharri. Ummati rarrashinta kawai take tana tuna yadda Allah Yasa ta auna arziki bata riga tayi hoton ba. A da suna wa abin kallon wayewa sai dai yanzu sunyi karatun ta nutsu. Duk wani hani ko umarni a musulunci akwai alkhairi mai kyau a tare da shi.
*******************
Da sassafe Junaid ya tafi asibiti. Sam daren jiya baiyi bacci ba tunda Hajiyan Dangi ta sanar dashi yadda mahaifinsa yayi dasu Baffa. Ya tabbatar ba wani abu Baffan ke tsoro ba sai HIV da sauran dangin cututtukan da ake kamuwa dasu ta wannan hanyoyin.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐19
Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama gano gidan da yayi masauki abinda ya rage mata yadda zata sami damar yi masa abinda bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari motar nan ta bace mana bazan biyaka ba yau...dreban taxi din ya kara gyara mirror din gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har mace sai dai babu alamun mutumci a tare da ita. Kallonta yake yana hadiyar yawu saboda irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A bakin gate din wani asibiti yayi parking inda yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar da gayya don ta tada hankalin maza...a zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba aure ba kullum yana yawo da ita a gari.
Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi masa wanda suka hada da HIV da hepatitis. Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba kowacce mace yake muamala da ita ba kuma yana amfani da hanyoyin kariya amma dai gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane baka da wayo a hannuna.
******************
Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya nema take shiyasa suka yi shawara da ummati kan cewa bazata musa musu zancen auren dan senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa yi mata zancensa.
A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie. To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi ko hello. Harara ta galla mata Ke ni bani abinci kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.
Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta ture plate din abincin can gefe. Tana sakace hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi ba these days amma naga baya zuwa wuraren shakatawa. Da na yanke shawarar na biya doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi tunanin kada yaje wani ya sake aga negative. Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two months kawai sai muje gidansu. Two months kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin shawara don har yau Mal Aminu bai gama sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka asirce.
Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano. Baffa kam sai da yaga result din tests har daga asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid damar yazo ganin Hafsi.
******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa yace su zauna yadda mutane zasu rinka wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa mata. Ido kawai ya bita dashi.....you are so beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana Hafsi ko....ya fada yana daga gira daya. Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can't wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin wanda black americans na ghetto suke sawa. Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko? Firgigit ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai sai tace masa a'a. Ya zaro ido me kika ce? Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa. Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐20
Ke kada ki raina min hankali mana. Ya daga zuwana zaki ce wani zaki shiga gida. Ya kara kankance ido irin na 'yan duniya ko kina son nayi miki irin abinda wanan matsiyacin yayi miki ne a wadannan pictures din? Gyara zama tayi tana kallonshi. Kaddai ace a hotunansu da Saif ya ganta. Tasan ance a hoto ya ganta amma bata da details din abinda ya faru. Da kyar tace wane hoton kake nufi ne. Wata babbar waya da bata taba gani ba ya dauko ya nuna mata hotunan. Gabanta ne ya fadi a tsorace ta mike wallahi ni ba yar iska bace idan ma abinda ya kawo ka kenan. It was my first and it will be my last in sha Allah. Tafi ya rinka yi tana magana eyye! eyye yarinyar ta iya turanci ashe. Kunya taji ta kamata shi kuwa ya cigaba da magana. Kar ki damu fa Juni has done worst amma tunda naga babanki yana pretending kamar ke saint ce ba komai shiyasa ma zan aure ki. Daga nan har muyi aure zanyi kokarin dena kula wasu matan sai ki dage ki koyi jan hankalina. Da wuya ake impressing din Juni. Yana gama magana ya tashi ya good night Hafsi Hafsi. Daga bakin kofa yayi blowing mata kiss. Sai da ya fita taja wani numfashi. Lallai akwai matsala ina ita ina wannan mai zubin 'yan iskan.
*********************
Fuska ba annuri ya shigar mata daki ba ko sallama. Junaidu abin ya motsa ne ka shigo min daki kai tsaye. Dafe kai yayi oh sorry Hajiyata raina ne a bace. Dan murmushi tayi tana nuna masa wurin zama. Zo nan dan Hajiya bani labarin yadda kuka yi da Hafsa. Kara zumburu baki yayi wai don rainin hankali baki ga yadda take min wani irin kallo ba. Hajiyan dangi dariya tayi ya bita da ido me kuma ya faru kike min dariya? Yo dannan banda abinka ji irin shigar da kayi kamar wani tsohon dan tasha. Duk kayan jikinka sunyi maka yawa. Lah Hajiya gayun kenan fa. Black americans hadaddu ai irin shigar nan suke irinsu ice cube, snoop dog, kanye west da....kafin ya kara magana ta daga masa hannu dakata haka. Yanzu don Allah zaka iya kawo min sunayen Annabawa ko Sahabbai goma? Ka rasa wanda zakayi koyi dashi sai makiyan musulunci? Kaji tsoron Allah Junaidu ka gyara rayuwarka. Yanzu dubi wani gashi a kanka kamar juji kuma nasan kana sane ka tara shi. Kana girma kana kara cin kasa. Bakin nan na Junaid kam yayi tsine saboda yadda yake zumburo shi..dan me zaayi masa fada. Sai dai kuma maganar ta dan shige shi. Ya mike zai fita daga dakin Hajiya kiyi hakuri da yardar Allah zaki ga na zama salihin mutum ko, yanzu ma ai kinsan Juni yayi sanyi. Filo ta jefe shi dashi ya gudu don yasan ta tsani Junin nan da ake kiransa.
*******************
To baiwar ciki ina nan ina ta nema miki mafita