Showing 1 words to 3000 words out of 119289 words
🌏JIKAR MAGUZAWA🌏
1-5
Official
By
AsmaBaffa
SHIN KIN SAN SHAHARARRAN GROUP ƊIN NAN DAYA SHAHARA WAJEN KAWO SHAHARARRIN FINA-FINAN DA SUKA SHAHARA WAJEN SAKA MA’ABOCIN KALLONSA A CIKIN NISHAƊI DA FARIN CIKI?
IDAN HAR BAKI SANI BA LALLAI KUWA ANA YI BABU KE!
KODA YAKE HAR YANZU AKWAI BABBAR DAMAR ZUWANKI DON A CIGABA DA DAMAWA DA KE IDAN HAR KIKA JONE DA MU!
Kuna ina ma’abota kallon shirye-shiryen Arewa24 na ƙasashen waje da suka fara ba su ƙarasa ba? Yi Maza ka garzayo wannan maƙala don ƙarasq kallon shirye-shiryen.
Kuna ina ma’abota karatun lobayya wato ma’abota karatun littafan hausa? Shin na tambayeku akwai wani novel da kuka karanta har yau baka samu karashensa ba? Ko kuwa akwai novel ɗin da kake nema ruwa a jallo ka rasa? To kaima garzayo wannan maƙala domin dacewa da haziƙan fasahan littattafai.
‘Yan gayu sam! Bamu barku ba! Kina son koyon kwalliya ɗaurin dankwali kala-kala? Yi maza ki jone da mu kin ji? In sha Allahu sai dai ki koyawa wasu, domin an tanadar muku kyawawan vedios wanda zasu taimaka ki koyi kwalliya da kanki, ki koyi ɗauri da kanki.
Anzo wajen! Wato fannin girki! Ayyuriririiiii!
Duk kyan mace sai ta iya girki ta cika sunanta kyakkyawa! Maza-maza yar’uwa ki jone da mu don kuwa muna kawo manyan-manyan girki masu daɗi da ɗanɗano wanda ba su da wuya balle ma ace sai ankashe musu kuɗi. Ke dai shigo ki ganewa idonki!
Ƙarshen-ƙarshe kenan! Wato ba anan fa aka tsaya ba akwai wani babban albishir ga masu son group ɗin, shi ne babban tanadin da akai don kawai a faranta muku! Tanadin kuwa shi ne, akwai haɗaɗɗan novel da ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa da aka yi shi musamman dan ku, wato wanda ake sakinsa a iya group ɗin kacal, wanda wasu manyan marubuta ne ke rubuta su, duk dai sai kin antayo zaki ganewa idonki. Wannan ma na ɗaya daga cikin littafan.
Kalli katsa kaɗan!
*TSARE TSAREN WOMEN24 TV WHATSAPP DA WOMEN24 TV VIP👇🏾*
DAURE KI KARANTA DAKYAU
Akwai groups guda biyar(5) da muke tura littafi wanda marubuta keyi kyauta da kuma littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24
Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro
*KUDIN WOMEN24 TV VIP*
Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada
Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne
*KUDIN WOMEN24 TV*
*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in
Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv
*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*
1.WOMEN24 TV VIP NOVELS
2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS
3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS
4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS
A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa'in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu
5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE
Kinajin sunan groups innan kinsan meye za'a dungayi a groups in
DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.
Account number.
2065301650
Zubairu Hayat Iman
Uba bank.
Number waya.
09030159301
Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN
Kada kibari gara basannan ta wuceki.
Yan Niger ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39
Sadaukarwa ne ga
ZAINAB GARBA BUTALAWA
Page na farko na
AUTA ne
Bismillah
Mutane cike suke a bakin wani katafaren gida ana Zaman makoki kana ganin irin yawan mutanen kasan babban mutum ne ya mutu,ga yan samari duk suna Kama baza su wuce shekaru Sha shida Sha bakwai ba a kalla sunkai su hudu,wani Handsome matashi zai Kai 28yrs Yana zaune da samari matasa da alama abokansa ne harda dan guntun hawayensa,cikin matasan wani Asif cike da tausayawa yace Hakuri zaka Yi Jawad dukkan Mai rai mamaci ne kowa na haka ne,Jawad ya daga Kai sama Yana dan maze damuwarsa
Cikin taron masu gaisuwar wani Dattijo ne yake ta kururuwar kuka babu ji babu gani,wani yace haba Alhaji Nasir hakuri akeyi an San ka rasa dan uwanka kaninka amma Addua ce ta kamaceka,Alhaji Nasir ya nuna yaran nan Yan maza yace ba kukan mutuwar Alhaji Muhammad nake ba kalli bataliyar da ya mutu ya barmin ya sake fashewa da kuka yace babu fadan da ban Masa ba akan ya daina auri saki yaki ji gashi kowanne yaro uwarsa daban kadan ne suke a dakinsu su biyu kowa uwarsa daban ga Yara Mata Suma dukkansu Yara ne basu Isa aure ba a bala'in rayuwar nan da ake ciki yasan ni bana son haihuwa a duniya
Kuka ya sake fashewa da shi yace Yara na uku kacal a duniya sabo da gudun rayuwa na kayyade iya yaran da Zan Haifa a duniya sabo da rayuwar yanzu ni ko badan rayuwa ba bana kaunar Yara da yawa yau gashi tawa bata ja min ba ta wani ta ja min,Ina fada masa Muhammadu ka daina tara Yara ka daina auri saki ko wacce tazo sai ta haihu sannan ya saketa ashe ni ake tarawa yaran ban sani ba wayyoooooo Allah Muhammadu anyi dan banzan yaro Muhammadu ya jawo min dole Yara su zauna a wajena na basu tarbiyya idan banyi ba duniyace zata zageni Alhaji Nasir Yana ta sambatu
Wani dan uwansu yace kayiwa Allah kayi Shuru a gaban mutane duk an tsaya Kai kadai ake kallo Wai to ba Yana da Babban da ba ance tunda ya auri wata Yar labenon wannan yaron ai Mai kudi ne ance me zuciya ya gaji arzikin mahaifiyarsa,yace gashi can ai baiyi aure ba,Kuma ai yaro ne ko yayi aure Ina raye ai baza a Kai Masa Yara sunfi ashirin gidansa ba,gashi me Kama da bature sannan Ina zai iya wani tarbiyya bai dade da dawowa kasar ba,shi kanshi tarbiyyar yake bukata a bashi,Jawad dake jinsu yayi shuru kawai mutuwa ce a gabansa.
Cikin gidan Kuwa dangi ne da abokan arziki ana ta zaman makoki matar Alhaji Nasir tana zaune sanye cikin zundumemen hijab hannunta dauke da carbi mutane yan Uwa da makwafta Mata cike a palon ga Yara marayun da aka mutu aka bari Mata rututu duk Yan Yara Wanda suke 12yrs sune manyan ma ko kuka basa yi suna zaune harda matansa biyu da ya mutu ya bari duk shayarwa sukeyi suna zaune Suma suna kuka sosai,Hajiya A'i tana jijjiga yarinyarta da take shayarwa sai faman kuka takeyi ga zafin mutuwa ga kukan yarinya wacce tana rarrafe ma hakan yasa takaici ya isheta ta fara dimawa Yarinyar duka a baya ana bata hakuri,Wata dattijuwa tace haba ke Kuwa A'i ita yarinya me ta sani haka dai ta lallashi yarinyar, suna zaman makoki har akayi sadakar bakwai.
Mutane ne talakawa masu yawan gaske iya kallonka gasu Nan da miskinai da Wanda talauci ya musu muguwar Shaka manya da Yara wasu da yaransu sun cika inda aka tanadar musu sabo da wannan bawan Allah mai taimakon talakawa zaizo ya raba taimako sannan zai saurari matsalolin bayin Allah ya tallafa musu,mutanen Nan rana tana dukansu amma sun cika makil duk securities sun shirya su sunyi layi sahu sahu ana jiran wannan bawan Allah.
Wasu jibgan jibgan motoci ne na Alfarma guda Uku inda aka tanada Suka Yi parking, cikin kwalla kwallan motocin Wanda securities ne suka fito motar da tafi kowacce kyau Suka zagaye ga yaransa na jikinsa duk matasa Wanda baza su wuce 29 to 30 yrs ba duk sun dau wanka,kana ganinsu kasan suna cikin hutu da Jin dadi.
Motar data fi kowacce kyau aka bude wani sanyi da kamshi ya feso wajen farar kafarsa ya zuro waje yasha uban takalmi na nunawa sa'a,Fitowa yayi gaba daya kowa ya saki baki Yana kallonsa duk da cewa wasu sun taba ganinsa,ya gaji da haduwa cikin wata almurar shadda Fara kal,dinkin Kamar a jikinsa aka dinka shi ya zuba uban kyau,gashi Kyakyawa na gaban kwatance,tun daga kan tsayinsa dai dai,sannan ba siriri ba baza a kirashi da me kiba ba,gashi fari kal skin dinsa Banda sheki ba abinda take,gashin Kansa Baki wuluk kamar na larabawa ya tarashi an Masa aski na Yan gayu Kamar a film, hancinsa normal ba me tsayi da yawa ba Kuma ba gajere ba haka ba siriri ba sannan ba me Fadi ba,bakinsa karami me dauke da jerarrun hakoransa masu kyau farare tas,gashin girarsa me yawa baki wuluk,idonsa madaidaita farare tas suna wani lumshewa Kamar zaiyi bacci .
Kowa dake wajen kallonsa yake ana murnar ganinsa talakawa sai daga Masa hannu sukeyi suna sowa da ihu ana ta faman gaisar da shi,cikin tafiyarsa me Jan hankali ya fara taku Yana bin sahu sahu da kallo Yana daga musu Hannu,layin karshe na Mata ya tsaya layin da na taho da gudu Zan Shige Ina magana da karfi Ina furta a taimaki marainiya,Marainiya ta ajin karshe,duk wani maraya a ajin farko yake ni Ina ajin karshe na Shige cikin layi tare da cukulewa ba mutunci,Ina tsaye Ina fushi na fice a layin na tsaya a gefe sabo da sun dade suna jira yaki zuwa ya sallamesu gashi har nima na zo shi yasa naji haushinsa
Kallo daya ya min ya juya tare da yiwa yaronsa magana cewar a maida Ni cikin layin duk Maganar nan da yakeyi babu Wanda yaga murmushinsa wannan shine karon farko dana taba zuwa karbar kudinsa labarinsa Kawai nake ji a layinmu shi yasa nazo nima,yaronsa ne da sauri ya bude mota ya ebo kudi masu uban yawa ya Mika Masa ya karba Ina kallo Yana bi layi layi Yana rabawa dubu biyu biyu dubu uku uku,idan kana da babbar matsala ka fada Masa zaice ka koma gefe ka jira shi, wata cikin mutanen tace dan Allah ka taimaka min kudin gidan hayata ya Kare gani da Yara su biyar marayu babansu ya mutu ya barmu,Nan take yace wacce sana'a Zaki iya Yi? Tace Ina siyar da su maggi,wake da manja tare da sauran kayan kanti,ba tare da ya kalleta ba ya tambaya Nawa ne kudin gidan? Dubu dari, yace alright yanzu za a Baki dubu dari biyu dubu dari kudin jari dari Kuma kudin hayar,a kasa ta zube tana kuka tare da sa Masa albarka yaronsa Kuma abokinsa Asif yace bata kudin Nan take ya sallami matar.
Haka ya dinga rabon kudin Yana sauraren matsalolin mutane Yana Sallamarsu har yazo layin karshe wasu Yan Mata suka ce aure za musu babu katifa Nan take ya bada kudin suka tafi su ma har aka karaso inda nake na karaso da sauri tare da durkusawa har kasa Kamar yanda naga sauran sunyi Yana sauri ya fara irgo dubu uku zai bani nace Nifa waec da Neco Zan zana bamu da hali Kuma naga kana Shirin bani wasu dubu uku na karasa da shagwaba kamar Zan narke,ba shiri ya kalleni haka bai saurare ni ba yace nawa ne? dubu talatin da bakwai na furta nan take ya irgo ya bani nace Saura kudin Uniform Yaya nawa duk sun rube,kallo daya ya min wai yaji na ce masa Yaya yace Nawa ne? 7k ya irgo ya bani na karba nace na gode ya juya zai tafi nace na manta takalmi na Wanda nake zuwa school duk sun lalace Asif ya kalla tare da cewa karasa sallamarta mu wuce flight dina ya kusa time is going,Asif ne ya Kara min 10k yace gashi nan,nace rayuwa tayi tsada fa bawan Allah har school bag zan siya,Asif ya bude baki yana kallona yace ke Wai baki to tarbiyya ne daga taimako sai kace kudin ubanki sai matsaloli kike kawowa kina ta karbar kudi dama irinku ne bata gari da kuke hana bayin Allah taimako
Na kalle shi nace Kai kudinka ne to ai sai ku rage min hanya ku sauke ni a layin gidanmu dan Allah da nisa Sabo da Takaici Asif juyawa yayi Kawai ya shiga dalleliyar mota Suka Yi gaba,suna tafiya Jawad ya dafe kai yace Asif Ina magani na?wani wuri ya jawo ya bude a motar ya dakko Masa wani magani dake cikin Yar farar roba ya dauki daya tare da korawa da ruwa
Kallonsa Asif yayi ya furta ranka ya dade ko mu Shiga asibiti a duba ka? no need yace a hankali,sai da yaji kansa ya daina ciwo sannan yace mu biya naci abinci but nafi son fura kawai,Asif yace a Ina zamu samu fura to me kyau? Driver yace nasan wani gida amma mun bar layin a baya matar me tsafta ce sannan da Engine take komai na furar Kamar ta kamfani,Jawad Yana Jin haka yace muje please,motar ya juya sauran motocin ma na securities suka bi bayansa a nutse zuwa wata tsohuwar unguwa ta talakawa layin baida kyan gani ko kadan kamar ba a cikin birni ba.
Ina zuwa kofar gidanmu na iske motocin Jawad Wanda ya gama raba Mana kudi Ina murna nayi mamakin ganinsu a kofar gidanmu amma bai fito ba,duk suna cikin motocinsu,Wucewa nayi abina Zan Shiga gidanmu naji an kwala min Kira ke Marainiya,da sauri na juyo naga Asif,dawowa nayi Ina gyara wuyan hijab dina red, yace a nan ake siyar da fura? da sauri nace ae Mamata ke yi,a kawo mana,Murmushi na saki nace ai wannan salon a baku kyauta ne kawai taimakon da kuka bani a baku fura ta kudinku,Asif share ni yayi yace jeki da yawa za a kawo kiyi sauri to na furta na Shiga gida da gudu
Ina Shiga Ina haki nayi sallama na iske Ummiya a kitchen tana wanke abinda ta hada furar,nace na dawo Ummiya gashi na samo kudi da yawa sun Isa na biya kudin school mutumin me kirki gasu sunzo siyen fura da yawa sunce da yawa hope tayi sanyi? Na fito da kudin na bawa Ummiya baki ta bude tace Ashe taimakon da gaske ne? Ei baki gani ba nayi ta shagwaba ana Kara min kalla ki gani,Ummiya tace ai nasan sai kinyi Iskanci an gode Allah ya biya sa a lahira yanzu a Kai musu furar ai baza mu karba kudinsa ba,Nace sai mun karba so kike su karya Mana jari su tafi,furar na jera manyan ledoji roba roba irin ta Rufaida na fito da manyan ledoji har biyu Ina Fitowa numfashi na ya dauke ganin Jawad da nayi a jikin mota a tsaye Yana kallon layinmu,sai da na saki salati sabo da tsabar kyawunsa,a hankali na karasa gabansa da ledojin a hannuna.
Asif ne yazo ya karba yace tsaya musha muji irinta idan bata Yi ba baza mu siya ba,Ni dai ban ce komai ba haka ya dauki roba daya ya bude tun a Ido kasan tayi Spoon ya sawa Jawad yace taste,a hankali yasa hannu ya wani dan ebo a spoon ya Sha yaji shegen Dadi yace tayi let's go ko kallona baiyi ba tunda nake sintiri a wajen bai ko kalle ni ba,Asif yace ta Nawa ce duka nace ta dubu buyar, kacal? Ya tambaya na kalleshi nace dan Allah ka dinga rage Fadin rai kai ba me kudin ba harda wani kacal,sai lokacin Jawad ya kalleni a ransa yace bata da kunya Asif zata Kira da me Iyayi, Asif zaiyi magana Jawad ya furta don't, let's go please,Nace ya sunan Ogan naku? Asif ya kalleni sannan yace Jawad sunansa,Kai na girgiza tare da cewa nice name sunansa Zan sawa Dana na fari idan nayi aure,Asif yace babanki fa? nan take na bata Fuska nace idan yaci sa'a zan maida shi akan Dan Auta na,ai sai dai yazo a Dan Auta Maybe,Farko idan Namiji ne Jawad sabo da ya taimakeni,idan macece Ummiyata Baba Kuwa ai ya samu sa'ar gaske yazo a Dan Auta,Asif ya dinga dariya yace shi kuwa Baba me ya Miki haka baza a sashi a Kan arziki ba har sai Dan Auta,nace ai Dan Autan ma ba guarantee watakil nace,Jawad Yana jinsu Yana karanta Jarida ta bashi dariya sosai,Asif yace ke mun tafi tace ku gaida tsofaffin kace da Oganka godiya dubu dubu kace Yana da kyau ya dinga Sallar dare Yana godewa Allah shi kadai ne baida damuwa a duniya komai an bashi,jarabtarsa Kawai akan fura ne duk inda take sai ya nema,Asif mota ya shiga kenan Nace kudin fa ku Kuna da karfi ba sai an Muku mutunci ba ku biya kudinku,Asif Yana dariya ya zaro kudin ya Mika Min na karba ta window
Suka ja motocinsu sukayi gaba nima na shiga gidanmu Ina murna.
Ummiya sai fada take min me yasa na karbi kudinsu,Haka Muka gama tsara kudin ya zamuyi da su har na school dina an ware,sabo da mijin Ummiya yace dama shi bazai iya daukan nauyin agola Yar wani ba in zata iya wahalar to ko ubana mahaifi yayi dawainiyar yarsa shi yasa ko sana'ar da Ummiya ke Yi sabo da ni takeyi,shi yasa ko yaushe adduarta Allah ya fito min da Miji na gari da wuri ta aurar dani itama ta huta,Nima dake da kuruciya son auren nakeyi ni koma waye na aure shi,akwai Saurayina Salisu da ya nace min to bashi da kudin aure yaro ne Nima ba wani damuwa nayi da shi ba
Bayan kwana Uku na fito nace Ummiya zan tafi cewata a kalla bazan wuce 18yrs ba,Matashiyar dattijuwa Ummiyata a kalla bata wuce 37Yrs ba dauke da katuwar Leda ta fito a hannunta ta mika min gashi Najla ki gaishe su kafin na Zo ki samu Mahaifiyata a sirri ki fada mata ba kudi a hannuna shi yasa ban Zo ba,sannan na fada miki in kinje