Showing 36001 words to 39000 words out of 119289 words
Yar shila kyakyawa 18yrs,Umma tace ba matsala sai ku Fara bada cin hanci kafin alkalami tafawa sukayi,Sukace me kike so na cin haccin?Umma tace Ina lace din kike saidawa Yan 30k to a bani guda daya kyauta,ke Kuma Hajara cikin shaddojin nan,babu Bata lokaci Suka ce zasu Aiko Mata da su sun san Umma bata aikin banza.
Da dare kuwa Abba yasha masifa akan me bai taho da yaran ba ai ba sai ya jira wani Jawad ba,Abba yace Yarinyar ce akwai kirki shi yasa gwara mubi ta hannunsa,ki jira ya dawo ai dole a dawo Miki da yaran nan tunda kina so ki Kwantar da hankalinki ni banga ma abin so a Yara ba wlh ni bana son Yara dan Kawai kin nace ne mun rabu da Kaya yanzu Zaki kuma jajibo Mana masifar data fi karfinmu amma tunda kina so shike nan,Umma tace ni a dawo min da su,to cewar Abba shi ba a son ransa ba baya son Yara Sam,yace bahaushe ba wata gaskiya da yayi a nan Wai wani da na kowa ne,Ni nawa sune nawa ko ya muke da mutum ba abinda ya shafeni bazan iya kashe kudina akan wani ba,Ni nace ya tara yaran Sanda na masa fada ai bai saurare ni ba,Umma tace to ni ance maka son na wani nake,to Mene naki na Neman su dawo Mana ya juyawa Umma baya Yana uban tsaki
Washe gari Umma har Kaduna taje inda Babar Hafeez take,tayi mamakin ganin Umma tunda aka saketa bata sake ganinsu ba ko yaronta bata sake waiwayarsa ba gashi gidansu talakawa ne na karshe Kuma tayi aure har sau har sau Uku tana son zaman auren amma ya gagareta ko Ina ta Shiga sai wata silar tazo an sake ta,Ga gidansu talauci kamar ya kashe su,Umma ta shiga bayan sun gaisa an kawo Mata ruwa a kofi da shinkafa Fara da Mai da yaji,Umma tace sauri nake bazan iya cin abinci ba a gurguje nake
Maman Hafeez ke Kuwa Anya kina da rabo ace Kamar ki a gidan iyayenki kalli mamanku ta tsufa ga tarin Yan Uwa ga talauci ga danki can a gidan Jawad ya shahara ya girma ya Zama saurayi Yana ta shanawa da kudi ke ya barki a nan kina da arzikin da ai kin gama komai wlh da nice ke zuwa zanyi na dakko abina ko banza idan Yana kusa da ke duk abinda ya nemo ke zai kawowa yanzu danki ya Zama abin mora kije ki dakko abinki ko da tsiya,matar Jawad tana can tana sashi aiki har breziyya yake wanke mata sai abinda tace,yaushe Jawad yayi aure? ai munji a radio yau bai fi kwana hudu ba amma a haka matarsa har take abinda taga dama komai tsiyarta ai ta daga kafa tukun,Umma tace baki yarda ba kije ki ganewa idonki,yanzu ko na cewa Hafeez yazo ai bazai saurareni ba,kice Zaki tsine Masa kece Kika haife shi cewar Umma,to Ni dai bani da kudin mota Kuma a Ina zanyi masauki kafin ya yarda ya bini,shirya na Miki kudin jurgi ma ba mota ba sai ki zauna a gidana har ki kwaci yancinki,Maman Hafeez tace ah to muje ai baza ka bari danka ya manta da Kai ba ayi ta cinye maka moriyar yaro,Haka ta shirya tayiwa Yan gidansu sallama tabi Umma zata samo kudi.
Kafin su Isa Zamfara Umma ta gama zuga Maman Hafeez tas suna zuwa Zamfara wajen Maman Ahmad Suka je itama Wai tazo ta dauki danta,tace ni ba mahaukaciya bace tunda Muka watsar da Yara ba wani zuwa muke ba an rike Mana su basu rasa komai ba sai yanzu dan yaro ya girma Yana karatunsa naje nace ya taho sai yanzu nasan Ina da yaro to bazan dakko shi ba kokari ma nake Nan gaba naje na bada hakuri nayi aurena Ina zamana lfy baza kuzo ku zugani ba,naki wayon Nima bazan tsaya ku kaini ku baro ba ta yiwa su Umma fata fata Suka fice daga Nan Kawai Lagos Suka nufa gidan Umma a ranta tace dole fa idan wannan bai bulle ba sai wannan ya bulle dani cewar Umma,Haka Kawai yarinya a auro ki mijinki yafi mijina kudi Kuma bazan karu da ku ba Impossible
Bangarena Kuwa Muna zaman mu lfy da yara Ina kula da su yanda ya kamata suna zuwa school dinsu idan sun dawo na koya musu assignment ga islamiyya suna zuwa Ina koya musu Nima na addini sosai nake sasu a hanya har na kwashe kwana goma Sha uku a gidan Jawad mun Saba da Yara mun shaku har na Saba ma ba wata wahala nake Sha ba tunda Yan aiki suna tayani duk da cewa raino ba sauki, Maman Hafeez har yanzu tana gidan Umma bata Zo Nan ba suna jira Jawad ya dawo.
Tunda ya tafi bamu Yi waya ba,yau ana gobe zai dawo Ummiya ce ta kirani a waya Wai ga su Kadada nan da Tahantsi zasu zo da gara da akace za a kawo nace a barta sunce su abin kunya ne sai anyi tunda Babana ya dawo shi ya bada komai na garar Driver yasa ya kawo su idan sunyi sati sai su dawo a motar haya Ina ta murna zanga dangi Yan gida.
Tun safe Suka taho amma sai washe gari da asuba Suka sauka a Lagos,Hafeez na tura yaje ya taho dasu,Yana zuwa ya iske Kadada ta fito tana cewa a nuna min gidan wanka nayi fitsari ko nayi a jikina,Hafeez yace to tsaya a nemo na kusa,Ni bazan iya jira ba,Allah yasa daga wajen gari Suka tsaya tace zanje can nayi,Hafeez Yana tsaye ya jingina da mota tace cutar sanyi ce da ni tayi karfi a jikina sanyin mafitsara shi yasa bana iya rike fitsari,Uhm cewar Hafeez Kadada taje bayan ciyayi tayi fitsari ta dawo Suka wuce.
Kadada tana ta kallon arna da Kaya bingilallu Kamar zasu tafi tsirara tace ga Yar uwarku tazo hausawa ne Suka bata mu da sa Kaya irin nasu gamu a Kauye shegiyar Atamfa kullum kamfani sai yo su yake kala kala,Hafeez yace wannan suna da addini Christian ne ku wa kuke bautawa in ba dodon tsafi kuka sani ba,Kadada Nan take sai ta ji haushi ta bata rai dan Kaine Kawai kaci albarkacin Fara da take aure a gidanku yau da na cika maka aljihu,Tahantsi ta gaji shi yasa bata iya magana amma tace Hafeezu mun kulla da Kai Ina nan da kai sai na girgiza gidanku bari na huta,Drivern Babana yace Kai samari yau naji ashariya iri iri wata Kalar tunda uwata ta kawoni duniya ban taba Jin irinta sai yau,Ni kaga Ina sauke su wlh bazan kwana inda wannan suke ba Ina da aboki gidansa Zan kwana da asuba Zan juya kano,Hafeez Yana ta dariya yace haba driver can Kuwa ta gidanmu bata yi,ai a haka yayanka ya aureta? Hafeez yace gaskiya ita ta daban ce,Kadada tace Fara dince ta daban? to wallahi Sallah ce Kawai banbancinmu amma na tabbata tunda kace Fara Bata Yi ashariya ba da dalili ko tantama banayi dole da dalili tunda kace a gidan kake yanzu,har kanne na cewar Hafeez,Kuma babu Wanda ta narkawa ko Daya? Hafeez yace kwarai kuwa,Kadada tace akwai wani abu a kasa karya ne,Fara ko kauyenmu taje Watarana tana finmu zage zage dan Kai Ummiya ma mamanta sunanta Hakuri sabo da hakurinta amma tana ashariya, Tahantsi tace bari muje gidan Allah yasa mu ga Umman nan da Kadada kika bamu labari yau sai nayi sama da shegiya sai ta karewa gajimare kallo sannan na saketa tayo kasa.
Hafeez yace ai Kuwa baza ku ganta ba tun zuwan farko bata sake zuwa ba,har Suka je gidan Tahantsi tace lallai tun a duniya Fara ta Fara Jin kamshin Aljanna inji musulmai tace bari naje ta sa min Albarka irin tasu ta musulmai ko nima zan dace,da Zan samu irin haka a guje Zan Shige addinin su Fara,Kadada tace tab ni Kuwa tuba babu,kije kullum sai kin ta wanke Fuska sau biyar.
Suna fita a motar gashi ba Yara bare a sauke musu kayan abincin Ummiya ce tace ba sai manya sunje ba tunda garar ma ba so su Jawad suke ba, Su Haruna Hafeez ya Kira Suka shigar da kayan abincin har store su Kuma su Kadada Suka Shige da kayansu,Driver ko tsayawa mu gaisa baiyi ba ya fece, lokacin duk Yara suna school sai ni kadai na gama gyara part din Jawad,gyara na musamman nayi sabo da anjima zai dawo duk da a bakin su Hafeez naji,Su Kadada ne Suka shigo Muna ta murna Muka rungume juna, Tahantsi ashar ta kutuntumo tace wannan kyau haka kinyi kiba ji yanda Kika Kara haske,Babu shakar doyin kwatar unguwar ku cewar Kadada,nace Zan ci ubanki,Kadada ta rike baki tace Ashe da gaske Hafeezu yake Wai bakya zagi yanzu? Nace hmm bari kedai Ina Yi a zuciyata,na durata a zuciyata a kullum na kanyi sau goma a cikin Raina ko na buya a daki nayi da yawa na fito, Tahantsi tace rayuwa yau Fara namiji ke juyawa har ya hanaki ki hanu Kuma bakya Masa karya Dan nasan Ummiya ma ninke kike
Nace aure ya wuce tunaninku Kadada na Isa nayi zagi a gabansa tab rufa min asiri,ah lallai Zamu fadawa Ummiya yarta ta shiryu,nace dole ce ta sa amma Ina nan akan bakana,iceko bakya barin ko ta kwana? Nace ai Kuma Kun San ba wannan zance waye ya Isa sai me gidan,sama Muka haura Kadada tace su Fara an Kara yin duwawu nace wlh kuwa sunji Kaji,tunda Muka shiga bedroom Suka zauna Suka tasa Ni gaba Kamar sun samu tv suna ta kallo na,Tahantsi tace yanzu Fara kema fa a Bude kike a haka Kamar budurcinki nanan Kai Watarana Ina yarda da Addininku Kinga an sirrinta abin babu me gani sai ogan,Kadada tace bari muyi wanka ki bamu aron kayanki na Yan gayu mu saka,nace ai gwara na siya muku sababbi haka Kawai mijina ya dawo ya ganku da kayana a jikinku yaga wata tayi kyau ko ku fini kyau a ciki bada ni ba ku bari ya dawo a siyo muku Zan baku wasu dai kyauta Wanda bai Sanni da su ba.
Suka rike baki kawai,sai da sukayi wanka na basu sababbin Kaya Suka zaba tare da cin abinci sannan Suka kwanta suna hutawa
Hafeez ne yazo ya fada min yanzu Asif zai je dakko Yaya Jawad,nasan ba birge shi nake ba akan me Zan wahalar da kaina wajen yin girki tea Kawai irin Wanda yake Sha na dafa masa,wanka Kawai nayi bana so ya sake rainani Ina da kana nan Kaya na masifa amma bazan iya sawa ba sabo da su Hafeez haka na zabo wata Atamfa sea green me golden a jiki,dinkin ya hadu riga da skert ne,Kamar a jikina aka dinka nayi kyau sosai,na saka sarka da dankunne da agogo na duka golden color naci dauri na, gashi na me tsayi na tufke shi na saki jelar a baya yana gadon bayana sai dai ni gashina ba baki bane haka dai yake shi ba baki ba kuma ba ja ba irin na Yan Fulani,na turarukan dana siya a wajen Mmn Mujaheed na shafa masu azabar kamshi na fito kamar zanje biki,palon nawa dama na sa an sake gare shi Yana kamshi ta ko Ina Kamar ba Yara a gidan haka gidan yake sabo da Ina kula,Ina shafa maroon jambaki naji motoci nasan ma shine tunda naji mota ba daya ba.
ta sama window na leka na hango shi yaci uwar gayu cikin Jean arsh da farar Riga me gajeren hannu,akwatuna har biyu manya a hannunsa suna magana da Asif sai dariya Asif yake shi kuwa Fuska a hade kadaram kadaham,Hafeez yaje sun gaisa ya Masa Sannu da zuwa,banyi gigin sauka kasa ba zamana nayi gefen su Kadada da suke ta bacci,mintuna kadan Jawad ya wuce part dinsa Hafeez Yana binsa da akwatuna,baiyi tunanin zai iske shi kal kal haka ba sai yaji sanyi ga kamshi ko Ina Yana shining,Hafeez ya juya yace bari na fadawa Aunty,Jawad yace Kaine ma zaka fada Mata nufinka bata sani ba bana son gulma,Hafeez dai ya wuce sum sum ya Kama Kansa,banje nima ganin Yara ma sun kusa dawowa na shirya musu abinci a inda Suka Saba ci babu hawa dining sai iya manya sune kadai ke Zama a dining,Jawad Kuwa wanka ya Shiga ya fito ya shirya cikin Jallabiya dark milk,sannan yayi Sallar azahar ya zauna Yana Addua sabo da la'asar ta kusa su Kadada na tasa nace idan Zaku ci wani abu kuje ku duba kitchen nasan ba Sallah suke ba Suka tafi Kuwa kitchen.
Ihun Yara ne ya tsoratasu Suka shigo da gudu wasu suna wakar makaranta wasu suna karatu a bakinsu wasu suna surutu har da masu fada a ciki, Tahantsi Suka leko da iya kansu daga kitchen duk Suka rike baki,Suka ga na fito da masu aiki yaran suna ta rungumeni ni da Yan aiki Muka hau cire musu kaya,Su Bintu Suka zuba a washing machine Zakiyatu ta tattarasu wanka,Na dauko Abeed a dakin bintu naji Yana kuka Ina daukansa ya Fara dariya yana ja min sarka,Kadada tuni ta daura Hannaye a kai tace ke Tahantsi da ayar tambaya a nan wannan yaran fa? Kan uba,Ina kallon kofar kitchen na hango su Kadada Suka koma ciki da sauri tsoro ya shige su,Murmushi nayi na tashi tare da shiga kitchen din Abeed Yana saman kafada ta,Kadada tace wannan su waye Fara? Ina iyayensu? na sansu da surutu nace I will Explain,zanyi bayani amma dan Allah karku fadawa kowa,Kadada tace to koma mene ke dai Kika jiyo suka dauki Apple suka Yi waje tare da komawa sama suna ta mamaki
Suna cin abinci cikin Shirin Islamiyyarsu na tattara su har Abeed Yana hannuna Humaira tana hannun Waleed muka tafi part dinsu basu San ya dawo ba sai da naje bakin kofar Palo nace Yaya ya dawo....kafin na rufe baki sun fada ciki da ihu,Ina cewa su nutsu amma Ina tuni sunyi ciki sai fadawa sukeyi jikinsa,daga baya na shiga dauke da Abeed, kallo daya ya min muka hada Ido nace ga su Abeed sunzo maka Sannu da zuwa..ai nasan sune Suka zo ba ke ba,nace tabbas kuwa,Waleed yace Kai Aunty daga dawowarsa sai fada,nace kai baka san wasa ba Waleed na furta Ina dariyar yake, Abeed ne yake ta Mika Masa hannu,ya Miko hannaye zai dauke shi hannaye sai jikin nonuwa na, Kamar bai sani ba ya fuske yace ashe Meenat ta ganewa idonta gaskiya Abeed da Humaira sun girma sunyi bulbul haka,har gabana ya Fadi da ya ambaci Meenat ban gane ba Ashe shi dai Boobs yake nufi,Ni da bangane ba na goce da labarin su Abeed nace ai madarar nan tayi yanzu wa zai ce Madara suke Sha,bamu taba Hira ba sai yau yace ai naji alama gasu nan lukutaye ban gane wanne yafi wani ba,ai Yara irin Meenat basira ce da su har na rasa irin kwakwalwar Meenat akwai wayo tana ganin abu ta haddace duk ta fisu ganewa na furta Ina murmushi
Yace kanta Yana ja,nace hmm irin labari yayi dadi, har da cewa su Kadada sun Zo Wai Ummiya ce tace dole sai anyi gara yace uhm to an gode ki bani number na Mata godiya,naji Dadi ya daraja nawa dalilinsa ashe tunda ban wulakanta nasa dangin ba bai kamata ya wulakanta nawa ba,yace kowa ya tafi school ya raba musu biscuits da alawa suna murna Suka tafi,bayan sun maidawa Bintu Abeed da Humaira
Sai lokacin yace to me ya rage Miki? nace na wuce part dina,good girl ayi gaba ko? nace wacce Gaba ai Allah ya kera shi tuni ka taba ganin an haifi mutum yazo babu gaba,ka tambaya kaji da nazo duniya sai dana tsula fitsari a gadon Ummiya sabo da lafiyarsa Kuma kaima nasan haka ko a gidan umma ana yin wani ne special? Yace 1-1 kenan Nace me kayi ya Zama 1-1 haba ai 1-0,yace kwakwalwarki ce bata ja shi yasa tun farko baki gane ba.
Tunani na lula Nan take na gano, kukan shagwaba na Fara na manta da yara,Hafeez suna kusa ta jikin window na Jawad suna surutunsu,Muna fuki Hafeez yace to Aunty kambu ya motsa yau yara uku zamu samu ya furta a ransa,Yana cewa Kai Yaya Allah ya bamu I taka ko da irin Kadada na samu,Ahmad yace what? Wannan Yar kauyen in banda wari me wajen zaiyi Hafeez yace ai Kuwa da Allah sai ya tsine mata,Waleed yace Babanmu ya gada muku masifa, Hafeez yace Mata biyu zanyi aure sai inda Allah ya tsai dani, baka da hankali kana ganin yanda Muka Kare iyayenmu duk sun wulakantamu da Jawad bai da zuciya me kyau wlh da yanzu maybe sai munyi bara ka canja tunani wannan ba girmanka bane,Sai na fadawa Yaya ni kake fadawa haka,sorry amma gaskiya ce ai.
Farooq ne yazo Wanda aka dakko daga airport Rannan,waya ya Kira yace Kai maye daga dawowata kazo,tashi nayi tsam nayi waje muka hadu da Farooq a hanya sai kallona yake Ina komawa su Kadada Suka tafa Fara sau Nawa akayi? baku da aikin yi,Wai Addininsu ya hana fada to mudai fada muke yi Suka furta.
Farooq kasa zaune yayi ya kasa tsaye yace wai wannan zukekiyar fa,Jawad yace matata ce, baki ya rufe yace Allah na tuba na Mata kallon da ya keta shariya,Jawad yace kullum Addua muke maka Allah ya shiryeka Farooq kowacce kazama ka bude Mata tsaraicinka ta gani wannan wacce lalacewa ce?
Farooq ya sosa Kai yace ai ni wlh bana Bari suga nawa,Jawad ya furta to nasu fa ai kana gani ko? Farooq da saurin bakinsa yace ahhh wannan kuma settellite Dina ce ai ana budewa sai kallo,Dan ubansu Ni nace su bude,Kuma ka Kara dage min da Addua Jawad bana dadewa in da ka San